*SOYAYYAR MU๐ซ*
By Ganarious.
Page4⃣5⃣
√°•_<>gaisuwa ta mussamman ga mutan *KENYA,NAIROBI*...i heart u all.๐๐๐
√°•_<> *NAZHEE YAREEMA*✌๐ผ
√°•_<> baby love *UMAIMAH BASHIR GWANDU*๐๐คฑ๐ป, Allah ubangiji shi raya min ke.
√°•_<> domin ku mutan kontagora, *GIDAN SARKIN GOBIR* in particular.
√°•_<>inai mana fatan alkhairi yan'uwa marubata har makarantan ma๐ค๐ผ... *assalam*
** ** **
Ilham ta nemi da Cynthia ta zauna su fuskanci juna.
Bayan da ta zauna suna fuskantar juna kamar yanda ta bukata, ilham ta dube ta cikin ido, murmushi tayi sa'anan tace "hannayenki,kafafunki, duk ilahirin jikin ki rawa sukeyi,sabida a tsoroce kike...tayi furucin ne, a yayinda ta dukar da kanta karkashin table tana leken kafar cynthia.
Tayi shiru na dan lokaci, sannan ta cigaba da fadin "kina mamakin yanda akayi na san cewan ke ce ko??
Ta cigaba da kallon ta cikin ido "na san wannan aikin umurnin wa ko wani kika bi.....du ba ki gan halin tashin hankali da suka sanyanki,ina da tabbacin zuciyarki ma tana iya bugawa sabida tsoro,don haka inai maki gargadi da kuma baki shawara,ba sai kin bari wannan maganar tayi nisa ba kawai ki fadi gaskiya,ki fidda kanki.
Idan kuma kina tunanin baza'a iya kama ki ba, toh ki sani ina da hanyoyi da dama da zani bada ke tare da kyakyawan shaida.
Ilham ta sakeyi murmushi me dauke da ababe dayawa, ganin yanayi cynthia.
..."shin wai ko bikiyi tunanin yanda akayi nasan cewan ke ce kika sanya min kwayoyin nan a jaka ba?
Sai a lokacin cynthia ta fara in'in-niyah tana sonyi magana, sai dai maganar ma bata fita.....sai bebanci.
Ogan yan sanda dake tsaye yana kallon ikon Alla ya duko tareda da'fa ta.."calm down....calm down,u can do it ya fada.
Sai bayan da ta dan natsu sannan ta fara magana.
"Gaskiyarki...kamar yanda kika fada,ba sai an tafi da nisa ba,nice na saka kwayoyi a jakarki kuma umurni na bi.
Tsale Hisham ya da'ka tare da dan ihunsa yayisu ne lokaci daya, sa'anan yayi sujjada anan guri yana meyiwa Allah godiya.
Nan da nan gurin ya dauki sautin Alhamdulillah.
Ogan yan sanda ya zauna tare jan kujeransa yana fuskantan cynthia cikin mamaki...."ke ce fa?
Ta da'ga kai,a yayinda take share hawaye.
...eh,nice kuma kamar yanda ta fada, umurnin na bi.
Umurnin wa kika bi?
Wata ce me suna HAJIYA ZUBAIDA.
ilham ta kai kallonta ga mahaifinta, shima din, ita yake kallo wanda a zahiri,tashin hankali ya bayyana a fuskarsa.
Mutan gun kuwa,banda salati ba abinda sukeyi.
Nayi tunanin hakan,shiyasa banyi mamakin jin sunarta ba.
Ogan yan sanda ya nemi sanin,alakar hajiya zubaidada ilham...alhaji buba ne yayi masa bayani, mamaki ya bayyana a fuskarsa,yana mitan me zai sanya hajiya zubaida Tayiwa ilham haka.
Duban mr. Ahmad yayi "zamu bukaci wasu da'ga ma'aikatan ku,domin bin yan sanda mu zuwa nigeria tare da me laifi....idan sun isa,sai su damkawa polisawan ku da'ga nan suyi harraman chebke zubaidan..
"Tabbas ke mayyace....ya juya ga ilham.
Nan jama'an gurin suka fashe da dariya.
No...no....no......ni ba mayya ba ce,ta maida masa.
Toh idan ba hakan ba ya ya akayi kika san cynthia ce ta sanya maki kwayoyi a jakka?
"Hikima ds basirah..! Ta fada tana duban ogan yan sanda a ido.
Enhennn....karin bayani.
Ka ga......da farko dai tunda kuka taho dani nan nake addu'a,kuma na dogara ga Allah.....a lokacin da ka sanar da cewan ba wata kwakwaran shaida na shigadamuwa,haka kuma na karfafa addu'ata da Allah ya toni asirin mai wannan aikin.
ko da na nema alfarma a gun ka,ba ni da wata dabara ko hanya, tunani na shine wata sa'ain marar gaskiya baya ba'ta,don haka nayita rokon Allah da ya nunamin alama,idan har me laifin tana cikin su.
A lokacin da nake fitowa,idona kar a kansu ko zani gane wata alama daga garesu.
Allah cikin ikonsa ya nunamin, duk da bani da tabbaci a lokacin.
Bayan da na karaso kusa da su, sai nagan cynthia tana hura iska daga bakinta a takaice dai da ka ganta zaka fahimci cewan bata da sukuni.....don haka rai na yabani kawai itace.
Gashi yanayinta da ta sauran da bambacin,shiyasa kawai nayi amfani da hikimata na tsorartar da ita ba don ina da wata shaida ko hujjan da zani kama ta dashi ba
TAfawa polisawa suka shiga yi,suna yabon hikimarta....daga karshe ,suka sallame ta suna zolayyarta da zama polis.
Bayan an sallami ilham, ta bi su mamee zuwa masaukin su.
a daren ranar Alhaji Buba ya sa hisham gaba ya raka shi masaukin su mamee don gah'nawa da yar' sa ya kuma yi mata sallama,sabida gobe zasu tafi.
Mahaifin mamee ne yayi masu izini da su shigo.
A falo suka tarar da su,ciki harda nazeeha da Amarah.
Ilham tayiwa mahaifinta marhaba da zuwa, tareda nuna masa gurin zama.
Ya risina ya kara gaida mahaifin mamee,sa'annan su nazeeha suka gaida shi bayan ya zauna.
Mamee ce ta fara barin falon, sannan su nazheeha suka bi bayanta.
Ilham da Hisham sai Alhaji Buba da mahaifin mamee ne a falon.
Alhaji Buba yayiwa Allah godiya da ya kubutar da yar' sa,sannan yayi rokon Allah da ya tsare ta daga masu shairi irin su hajiya zubaida.
BAyan nan yayiwa ilham nasiha,ya kuma yi mata kare ta, a matsayinsa na uba.
mikewa ilham tayi,cikin farin ciki ta yi taku zuwa inda mahaifinta ke zaune
Ta rusuna a gabansa...."Alhamdulillah,ina godiya ga Allah da yasa ka gane halin hajiya zubaida,ina kuma yi masa godiya da ya maida mana ni'ima,watau ya maida mana da kai....ina rokon ka da ka yafemin laifin da nayi maka, na kin bin umurnin ka.da fatan zaka fahimce ni.
A hankali ya da'ga kai, na fahimta Aisha.
Ka yafe mi?
Na yafe maki...
Na gode baba, inn'shaa'Allah bazan sake sa'ba maka ba.
Da haka suka shagala da hirarraki,sai da mamee ta fito, ta ke sanar masu dare yayi nisa.
Cikin zumudi ilham tace ba sai su kwana nan ba!.
Uwar harara mamee ta jefe ta dashi, ba tare da ta ce wani abu ba.
Alhaji Buba ya mike ya na me yi wa mahaifin mamee sallama,ya kuma fada masa gobe za su tafi.
Nan mahaifin mamee yayi masu fatan alkhairi,sa'ana ya ciro kudi masu yawan gaske ya mikawa Hisham.
Kin karba yayi, har sai da mamee ta sanya baki, tare da matsa masa ala dole sai ya karba.
GABA Dayansu suka yo rakiya,ilham kam ta li'kewa mahaifinta kamar baza su rabu ba.
Bayan sun fito haraban hotel din,Hisham ya tsai da me taxi, sai dai me!. Ilham ta ki sakin mahaifin ta, ta makale shi.
Idan zai shiga mota, sai ta riko shi,tayi hakan ya kai sau uku, na hudun ya juyi yace "kar ki damu,xan sake zuwa na duba ki"...duk da haka ilham bata sakar masa hannun ba.
Mamee ce ta karaso a fusace ta rike hannunta tare da jan ta da karfi.
Kamar kullum, yau ma a gidan mallam lamido yan'uwa da abokan arziki suka yi taro don yi wa Alhaji buba jaje da kuma barka.
A filin jirgin saman birnin tarayya, yan sandan kasar ladon suka damkawa yan sanda ta kasar nijeriya cynthia.
Nan tayi masu kwatancen gidan hajiya zubaida,basu ba'ta lokaci ba, suka tafi a yayinda wasun su suka tafi da cynthia.
A kofar gida suka tarar da ita,ta bude murfin mota tana shirin shiga.
Sunyi parking gefenta,suka fito zuwa inda take.
Assalamu alaikum...daya da'ga cikin su ya fada.
Wa'alaikumussalam ta fada tana yatsine yatsine.
Don Allah ko nan ne gidan zubaida?
Eh....
Toh ko dai ke ce?
Eh...nice ta fada, cikin isa da takama.
"You are under arrest......"
Arrest?..... na me?
Ki biyo mu, idan kin je can din zaki ji.
Ganin cynthia ya sa ta razana,asirina ya tonu ta raya a zuciyarta.
Alhaji Buba ne tsaye kofan gidan hajiya zubaida, a fusace yake kwankwasa kofar.
A guje me gadi ya zo, yana gunguni...
Ganin me bugun kofan ya sanya shi murmushi.
Har kasa ya duka..."sannuvda zuwa alhaji
..."yauwwa, sannunka dai,ya aiki?
taauuh....da godiya,amman tunda ka bar gidan nan gaskiya bani jin dadin aiki a gidan nan.
ba yanda dan adam ya iya sai hakuri...fadin alhaji buba.
"Gaskiya ne".
Me gidan tana ciki?
A'a....polisawa sun tafi da ity a.
Ok...ya fada a takaice,tare da sanya hannu a aljuhu ya ciri dubu daya ya mika masa..."gashi, a aikawa iyali, ba yawa.
Haba dai alhaji......Allah shi sanya albarka.
Da haka sukayi sallama da me gadi ya tafi gida.
Hisham ya ne ma a waya..."hello baba..
Binciko man polis statio din da zubaida take.
tau baba...
Sai da mamee da mahaifinta suka cike sati ,sannan suka dawo.....har ixuwa wannan lokacin hajiya zubaida na tsare.
Mahaifinta da abokansa sai sake sake sukeyi, suna neman duk wata hanya da zasu bi don ganin an basu belin hajiya zubaida.
Alhaji buba zaune tare da mahaifin mamee....
...."ina tsoron mutanen nan baba,tun ranar da na sami labarin neman belinta da sukeyi, hankalina ya saka kwanciya.
Ina tunani da tsoron abinda zai biyo baya idan ta fito.!
Mahaifin mamee ya gyara zamq yana me duban alhaji buba....cikin murmusawa yace ..."ka cire damuwa,Allah na tare da me gaskiya a koda yaushe,kuma inn'shaa'Allah baza su sake nasara akan duk wani shairin su ba.
SUNA cikin tattaunawa mamee ta shigo tare da mujaheed da abba.
Abba na ganin alhaji Buba ya nufe shi tare da rungumansa.
mujaheed ma ya karasa ya gaida mahaifinsa.
A Hankali mamee ta karaso cikin falon tana me satan kallon alhaji buba, wanda ta fahimci akwai wani abu da ke damunsa....wata zuciya ta kwabeta da fadin "toh miye naki?
Tsna cikin kallonsa ya da'go,sukayi ido hudu...murmushi ya sakar mata a yayinda ta kauda kanta.
..."baba jibi inn'shaa'Allah zan koma makaranta, niyata idan na sallami kaka swi na zo na sallame ka.
Shiru alhaji buba yayi yana duban sa,sannan yace "allah shi kai mu,nan ya shiga yi masa nasiha da kuma shawarwari daga baya yai masa addu'o'i, ya juya ya dubi mamee wace har lokacin idon ta na kansa.
"Please idan baza ki damu ba,zan zo sallamansa kafin ya tafi,don haka ina neman izinin zuwa gidan ki.
Ba amsa ba sai zancen zuci da ta shiga yi..."kamar daman ka sa'ba neman izini na kake zuwa.
Alhaji buba ya mike yana yi masu sallam, fatan alkhairi mahaifin mamee yayi masa tare da gargadinsa da ya cire damuwa a ransa...
Tunda mamee ta koma gida take tunanin alhaji buba ta rasa dalilin damuwansa...
Wayarta ta ciro tayi kiran ilham.
Mamee na....
Yes dear kina lafiya?
Lafiya lau hamdanllah.
Toh maasha'Allah, ina nazheeha Da Amarah.
Dariya ilham tayi,..."kin manta kunyi waya just an hour ago?
and so?....sai kar na tambaya lafiyarsu?
Tauh mamee, sun tafi massallaci.
KE kina ina?
Ina daki,bani da tsarki ne
Ok...
Mamee da magana ne?
A'a....i just wanna check on u.
Kiss ilham tayi mata a waya,tare da fadin thats my mum.
yes my love...mamee ta maida mata.
Mujaheed fa?
Yana daki..
Ok..
Kinyi waya da mahaifinki kuwa?
Eh....munyi waya dazun nan.
Me ya fada maki.?ba komai...
OK...
Da wani abu ne?
a'a.
Ok....yadai fadamin yana tsoron abinda zai biyo baya idan hajiya zubaida ta fito daga hannun yan sanda.
Oh..Allah ya tsare.
Ameen.
Yau laraba, itace ranar da mujaheed zai koma makaranta.
tun da suka tashi sallan asubahi, ba su koma bacci ba.
Mamee da blessing ne a kitchen suna hada abin kari, a yayinda mujaheed da abba suka fito waje don wanke motar da zasuyi tafiya da ita.
06:42am, alhaji buba ya iso, dai dai su mujaheed sun gama wanke motan
Bayan gaisuwa mujaheed yayi masa izini da ya shiga daga ciki.
..."je ka ka sanar wa mamanku, duk abinda ta fa'da sai ka zo ka sanar da ni.
Read More »