Pages

Thursday 24 May 2018

Page 44 of SOYAYYARMU 👫

SOYAYYARMU 👫
      By Ganarious.
Page4⃣4⃣

👉🏼 *ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA AL'AFIYAH.*🙏🏼

>mutan KENYA, 1 love💖..ina godiya sosai.

> *NAZEEHA YUSUF YAREEMA*, Allah ubangiji shi bar kauna, ur comments alone keep on moving the story...

>makarantan soyayyarmu,ina mika gaisuwa ta gareku.🤝🏼

>zaku iya samun latest page release a ganarious.blogspot.com/


       **         **         **
 Bayan da Amarah ta isa makaranta a ru'de,ta rasa sukuni,cikin tashin hankali ta dauki wayar ta,iyayenta ta nema.
Mamarta ce ta dauki waya,bata jira sun gaisa ba ta shiga fada masu abinda ya faru.
Nan mamarta ta bata shawara da ta kira iyayen ilham ta sanar da su.
Ba ta bata lokaci ba,ta nemo lambar mamee..
Mamee ta shiga tashin hankali,a haka ta kama hanyar gidan su,tana isa ta fadawa mahaifinta abinda ke faruwa,ba da bata lokaci ba sanya a binciko masa jirgin yan kasuwa,cikin sa'a kuwa suka samu.

Bayan da Amarah ta gama waya da mamee , lambar hisham ta nemo ta yi kiransa shi ma.
   Kayan jikinsa ne kawai be cire ko ya yaga su ba.
Sumbatu ya shiga yi,yana me bugun kansa sanin hukuncin duk wanda aka kama da miyagun kwayoyi a kasar ladon,sabida haka tunaninsa kawai ya ga'ma rasa ilham...

Sai da ya dan sami natsuwa, sannan ya mike ya nufi gidan kakaninsa ya sanar masu.
Jungum sukayiii....sun rasa mafita.
A halin da suke a yanzun,ba su da isasun kudi,da zai kai koda mutum daya ne kasar ladon.
Shi daman Hisham, bashi da aikin yi. Gwamnati ce ta bashi kyautuka a lokacin da ya kammala karatunsa domin kuwa babu kamarsa...Hisham dalibi ne da makarantar da kasar gaba daya ke alfahari da.
Bayan ya dawo gida nijeriya,ya sayi gida da mota,sauran kudin kuma ya' yita shagalguwa da su yana holewarsa.

Shiru shiru ba mafita, sai tambayoyi da suke masa kamar a gabansa abin ya faru..
Cikin jin takaici ya tashi ya tafi gidansu kareem....ganin yanayinsa ya tabbatarwa kareem cewan ba lafiya.

Zaunar dashi yayi ya na me tanbayar lafiya dai?
Ilham ce..ilham tana prison

What?...Kamar ya'ya tana prison,she just left.
Bani da lokacin ba'tawa, so nake duk wani kudi dake gare ka, ka bani aronsu pls, kuma zan sanya motata a kasuwa.
Ok...ok calm down,yanxun dai na tambayeka mana.

Ina sauraronka...
Ka dubo mameen nata ne?
No...ya fada a takaice.
Mikewa kareem yayi tare da mika masa hannu "tashi mu tafi gidan, lets get the information and what they inn first.

Bleesing tare da mujaheed suke zaune a falo, da'ga alama basu san wainar da ake toyawa ba.
Bayan da sun gaisa suke tanbayar ina mamee?.

Ta fita...fadin mujaheed.
Ok....suka fada tare da juyawa suka fice.

      Zaune take ta hade kai da gwiwa,a yayinda ta zurfafa a tunani..
Jin an da'fa kafadar ta yasa ta da'go..
Dan sanda ne a kanta,ya umurce ta da ta biyo shi zuwa amsa wasu tambayoyi da za'ayi mata,don gudanar da bincike kafin a zarta hukunci.

Da farko su nemi da ta ba su lanbar wani nata da'ga nigeria, ita kuwa a ranta bata son iyayenta su san da wannan maganar, don haka ta bayar da lambar wani mr.Ahmad dake aiki a embassy of nigeria dake a can.
Sunyi kiransa suka sanar masa daliba ce daga kasar najeriya aka kama da miyagun kwayoyi,don haka bayan bincike za'a zarta hukunci a kanta.

Bayan sun gama waya da mr. ahmad suka soma yi mata tambayoyi.
na take shaida masu bata da alaka da wadannan kwayoyin,an kuma sanya mata shi ne a jakarta sabida makirci da shairi irin ta muta ne.

A fusace wani dan sanda ....yace maganar banza,ta yaya zaki ce wani ne ya sanya maki su a jakarki?
.."baka tunanin idan da nice na saka su a jakkata za'a tsayar ko kamani tun a najeriya?...
idan da nice ke da su,kana ganin zani  yi sakacin sanya su inda za a gani...ka tuna fa ana bude jakat,akayi karo da kwayoyin...wannan kadai zai tabbatar maku da cewan a saka kwayoyine a jakata, don haka ina rokon ku da kuyi kwakwaran bincike.....ba ni ce zan fada maku abinyi ba,amman ina ganin mafi saukin kama me wannan laifin shine ku duba cctv cameras da kuma daukan thumb print da'ga jakan.

Shiru suka yi,suna jinjina maganarta me dauke da kamshin gaskiya.
...." kinyi gaskiya yarinya,yanda kika fada kuwa haka zamuyi,don haka yanzun zamu maida ki ciki.
Dai-dai nan mr.Ahmad ya iso,nan suka sanar masa komai,
Shi din ma rokan alfarma yayi, da su yi bincike sosai.

Ganin me kiran ya sanyata murmushi...."hello" ta fada cike da isa da gadara.
"Yes ma"...ina wuni
Lafiya lau cynthia,ya aiki?
Da godiyana kira ne na fada maki,na cike aikin.....tana can yan sanda sun tafi da ita.Don haka jibi jirginmu zai juyo,da fatan kema zaki cika alkawari.
Great job....na gode,kuma  ladan aikin ki na nan sai kin iso.
Ok ma.

Tana kashe wayar,ta fashe da dariya har tana hawaye..."yarinya kin ta'bo mutuwar ki.....mutum daya bazan bari ba cikin yan'uwanki,tunda kikayi sanadiyar rabuwata da mutumin da na ke so fiye  da rayuwata.

Jirgin su mamee na dirw ta nemi Amarah a waya.
Amarah da nazeeha sunje filin jirgi don tarbansu,da'ga nan kai tsaye polis station suka nufa.

Ba a basu damar gah'nawa da ilham ba,a dalilil wata dalilinsu na cewan sai sun kammala bincike.
Mamee da mahaifin ta sun tafi neman masauki ba don son ransu ba, kafin su kammala binciken su.

Washegari mamee da babanta tare da nazeeha da amarah suka yiwa polis station sammako...nan suka zauna, zaman jiran a fito masu da ilham.
Suna a haka, Hisham tareda alhaji Buba suka iso.

Alhaji buba cikin girmamawa ya risina ya gaida mahaifin mamee.
Bai gama gaisuwar ba, wani dan sanda ya fito ganin ya doso su, ya sanya gaba dayasu suka mike suka nufe shi da tambayar "me ake ciki?
"A bisa ga binciken mu,mun gano mutane da dama sun ta'ba wannan jakkat...don haka mun dauki thumb print na su.
Yazun zamu tafi airport,don samun wasu information sabida jirgin da ya kawo su zai koma gobe.

hukumar wannan filin jirgin ta baiwa yan sanda izinin gudanar da binciken su.
yan sanda sun bukaci da abasu vedio record wanda cctv camera ta gun ajiyan kaya tayi recording...bayan nan suka dauki thumb print din dukkanin ma'aikatan wannan jirgin wanda uku da'ga ciki sunyi matching da wanda aka dauka a jakkar....don haka suka tafi da wadannan ukun zuwa station dinsu.
Sunyi bincike da kuma yi masu tambayoyi akan wannan jakkan,sai dai sun nuna basu san da komai ba,iyaka aikinsu kawai sukayi...
Polisawa sun tsare su anan,don kara tsundumawa akan bincike.
Cctv camera kuwa cikin rashin sa'a batayi capturing gun jakkar ilham ba....don haka basu sami wata kwakwaran hujja  zai basu damar cewan ba ilham bace.
Ganin basu sami wata shaida ba ya sa sn sake fitowa da ilham don yi wata bincike,sun kuma shaida mata ba wata shaida,don haka dole a hukuntata.

Ilham ta roki alfarman da su bari ta gah'nah da iyayenta,da shike tun zuwanta gurin ta shigan masu rai,gaba dayan su suna kaunar ta.
sun fito da ita,a dai dai lokacin mr. AHMAD ya iso.
Mamee da Hisham har alhaji Buba rige'rigen rungumanta sukai,ilham kam gun mahaifinta ta nufa,ya rungume yar'sa ya na me shafan bayanta.
GANIn haka ya sanya mamee ta ja da baya tana kallonsu.
Sun jima a haka sa'anan ya sake ta,ta dubi mameenta tayi taku zuwa gare ta,. "Bani ba ce..bani bace...ta sake fadi a yayinda take shirin fashewa da kuka.
hannu mamee ta sa nisa le'ben ta'i know...i know,nasan irin tarbiyan da na baki,na kuma yarda da ke.
Ilham cikin kuka ta rungume mameen nata.

Mr. Ahmad ya nemi sanin matakin binciken,nan polisawan suka fada ba bu wata kwakwaran shaida da nuna an saka mata kwayoyin ne a jaka..don haka nan da wasu awanni idan har basu sami wata shaida ba zamu sallami ma'aikatan da muka tsare, ita kuma ilham zata fuskanci hukunci.

NAN da nan mamee da suran jama'an dake gun suka shiga tashin hankali.
Gyaran muryan da ilham tayi ya janyo hankulansu gareta,duk suka maida kallonsu gareta.
TA dubi dan sanda dake yiwa mr. Ahmad bayani..."Idan baza ka damu ba, inason idan zaku sakeyi yiwa ma'aikatan tambayoyi kuyi involving di na,da yardan Allah zan fitar maku da ko wace a cikin su ta sanya man kwayoyi a jakka.
Dariya sosai polisawan suka shiga yi..."ta yaya zaki gane,alhalin mu ba mu gano ba? Fadin dan sanda.
Kar ka damu,nayi maku alkawarin kama ko wace ce.
CIKIN amince wa suka ce "wannan kuma sai gobe,sabida akwai case din da za'ayi yanzun.
godiya ilham tayi,haka iyayenta ma.bayan nan suka basu mintuna su tattauna,sannan suka maida ta ciki.
Mamee ta kwana tsaye tana yi wa yar'ta addu'a,Allah shi kubutar da ita.
Haka sauran yan uwa.
Washegari, misalin karfe goman safe, kowana station.
Karfe goma da rabi,suka fito da ma'aikatan jirgi,bayan an fito da su sun zauna aka koma ciki, don fito da ilham.

    Daga ne'sa take kallon ma'aikatan,tare da tsira masu ido.
Tana zama tace wa ogan yan sanda..."wace ta sako kwayoyi cikin jikkata, tana cikin su"
Dariya yayi, tare da fadin da ban dariya kike fa.....wai shin ko ke mayya ce?
kai ta girgiza ba tare da tamka ba.

"Toh idan ba aikin mayta ba, daga zuwan ki,tun ba'a soma bincike ba, sai ki ce tana cikin su.
"Ganin bashi da niyar daukan maganarta da muhimmaci,yasa ta dube shi rai bace...."na rantse da wanda ya busa min rai wace ta saka kwayoyin a jakkata tana cikin su, yanzun haka a tsoroce.
Shiru yyi sabida sautin muryan me dauke da bacin rai.
Shi kenan miss cute..miss cute shine sunar da suke kiranta tun  s higowarta station  din.
"Yanzun dai zamu soma gudanar da binciken mu kamar yanda mukayi a baya,amma kafin nan, me ne ne hujarki na cewan kina son ayi komai a gaban ki?
Sabida na taimaka maku don ganin kun kama me laifin.
Ok ya fada sa'anan ya soma yi masu tambayoyi.
Wace ta fara amsa tambayoyin, tayi bayani cewan an sami thumb print din tane sabida ta taimakawa ilham a yayinda take daukan jakkarta zata kai gun ajiyan kaya..
Ta biyu da ta uku,kuwa bayanin su daya, cewan sunyi aikin su ne na gera kaya da gyaran zaman su.

Gyaran murya ilham tayi tareda fadin "excuse me".....
Gaba daya suka maida hankalinsu gare ta.
"A bani damar nayi magana"
Da sauri ogan yansanda yace na baki miss cute.


"Kamar yanda na fada a baya,na riga da na gane ko wacece a cikin su ta saka kwayoyin a jakkata....don haka bazani bata lokaci gun bincikan sauran ba , kai tsaye ita zanyiwa tambayoyi.....

Ilham ta da'ga hannunta ta nuna daya daga cikin ma'aikatan da yatsa....ke ce. Ta fada cikin da'ga murya.

Duk gaba dayan su suka maida kallonsu ga wace ilham ta nuna
Ita ko cikin kankani lokaci jikin ta ya soma bari...."ni???...ta fada
eh ke fa...
Nan ta shiga rantse rantse tana fadin ba ita bace.
Ogan yansanda ya nemi da ilham ta yi bayani ko ta kawo hujarta na cewan cynthia ta saka kwayoyi a jakkarta,idan ko batayi hakan ba, maganarta ba ta muhimmaci kuma baza su duba ba,ballantana suyi amfanin da shi.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.