Pages

Monday 14 May 2018

Page 42 of SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫
         By Ganarious.
Page4⃣2⃣

*Assalamu alaikum.!ya yan uwa..ina mai yi mana fata, da rokon Allah da ya gafarta mana dukkan zunubanmu.*AMEEN YA'RABBIL'ALAMEEN.

*visit ganarious.blogspot.com/ fo more and more.

*one love💞💞...
Mutanen *Kenya* kuna raina a kodayaushe.

         **        **      **
Bayan day an bude taron da addu'a, malam lamido ya ya nemi sanin dalilin wannan taron.
Goggoji tayi gyaran murya..."daman ya'yan bubane suke son magana da ku..
Ba tare da ta jira abinda jama'an gurin zasu fada ba,ta juya ga Hisham.
"Shiga ciki ka kira su"

Da sallamar su suka shiga falon.
Sai dai falon a cike yake babu ko gurin zama,wasu ma a tsatsaye suke....nan ilham ta shiga gaishe su,hakan da tayi yasa kannenta sun bi bayanta suna gaida jama'un.

Shiru tayi bayan gaisuwan,ta rasa ta inda zata fara bayani, ganin idon kowa na kanta ya sanya tayi karfin hali ta soma magana.

  Dafatan zaku bani aron natsuwa da hankalinku,domin kuyi wa maganata kyakyawan fahimta.
Ina me neman alfarma,da ku bani lokaci don yi magana ba tare da  an katsai ne,ko shigar min maganata ba.

Da farko dai ina sane da cewan kun san wacece ni,a dalilin Hisham.
Ta nuna mujaheed dake gefen ta da yatsa, wannan shine mujaheed kanina,yana karatunsa a kasar korean.
Sai kuma wannan muhammad.
Na sami labarin farkon haduwar mahaifiyata da mahaifina har izuwa rabuwansu.....shiru tayi na dan lokaci,sa'anan ta ci gaba, a yayinda ita ake kallo.
Ta da'go ta dube su"kuyi hakuri da duk abinda zan fada,don Allah kar kuyi wa maganata wata fasara"..."na zaunan nai tunanin cewan fa albarkacin so da kauna da mahaifiyata take yi wa mahaifina ya shafe ku gabaki daya,har ku ka kai wannan matsayin a yau..nasan komai Allah ke yi,kuma ko ba'a dalilinta ba, idan a rubuce yake da zaku shigo birnin ,ko neman ilimi,ko aiki, da sauran su ba makawa hakan zata faru.amman fa ku duba rawar ganin da mahaifinta yayi don ganin ya haskaka rayuwar ku,ko ba komai kun sami kari da wayewan kai akan addinin musulunci.....akasin da aka samu,shine butulci da kuka yi mata ga baki dayanku,har shi mahaifinmu.
Ba ku waiwaye ta da ya'yanta ba....mun rasa soyayyar da shakuwa irinta mahaifi da ya'yansa.
Bayan da na sami labari irin rayuwar kunci da mahaifiyata ta shiga bayan rabuwarsu,Nayi kuka na kuma yi bakin ciki.haka yasa na yi alkawarin daukan fansa,ma'ana duk wandanda sukayi sanadin sanya ta kunci,sai na sun dan-dani kunci kamar yanda suka sa ta.

Matakin farko akan mahaifina na fara....na kuma yi nasara sabida sace takardun kamfani da akayi gun sa, ni ce na shirya hakan.

"Nan da nan falon ya dau salatai,kowa sai salati yakeyi,suna tafa hannun irinta idan abin al'ajabi ya faru din nan.
Ita ko hajiya zubaida mikewa tayi tsunbul,kamar an tsakale ta....."ke.!kehhh ke ce? Ta fadi hakan a yayin da take nunin ilham da yatsa.

Kwarai kuwa.!...ni ce, koma ki zauna,domin kuwa yanzun zani faro maganata.

Nan ta koma ta zauna jiki a mace.
"Tabbas ni ce na shirya duk abinda ya faru....na kuma yi bakin ciki a lokacin da Hisham ya sanar wa mahaifiyata   abinda ke faruwa,ta dakatar dani,ta kuma haneni da aiwatar da shiri na na daukan fansa akan kowanenku......a yau ina son na sanar da ku wata siri da baku sani ba game da hajiya zubaida.

Nan ilham ta kwashi komai game da wasikar da kuma rayuwar mahaifiyar ta bayan rabuwarsu da mahaifinta ta sanar masu.....falo ya dauki hayaniya,daga masu jimamin wannan maganar,da masu tausayawa mamee da dai sauran su.
Ilham ta share hawayen da ke makale a idonta,ta juya zuwa ga hajiua zubaida....."kin cuci mahaifiyarmu,kin cuce mu, a sanadiyar son zuciya da makirci irin naki mun rasa soyayya da kulawa irinta mahaifi da ya'yansa.
Kanina muhammad bai taba gani ko jin dumin mahaifinsa ba...kin raba mu da mahaifinmu,na muzguna,an saka shi gidan yari akan laifin da baiyi ba......wace hukunci kike tunanin ta dace da ke?....
Hajiya zubaida sai rawan sayi takai,ganin haka ya sanya alhaji buba yayi gyaran murya sa'anan ya soma magana "ko kadan baki laifi ba....na chanchanci abinda da ya fi hakan ma da'ga gare ku.
Gaskiyar maganarki...da'ga ni har yan uwana albarkacin mahaifiyar ki muke ci har izuwa yanzun,don haka ina me neman afuwanku da ke da kannenki da ku yafe min....
Nan ilham ta fashe da kuka ba tareda ta bari baban ta ya karasa maganarsa ba...."me yasa hajiya zubaida tayi mana haka?....me yasa tayi wa mahaifiyata haka?
Alhaji buba ya mike yayi taku zuwa inda take tsaye" kiyi hakuri, ba laifinta ba ne...na da'de  da dawowa hayyacina,sai dai a lokacin komai yayi nisa baya gyaruwa shi yasa na hakura da na zauna da ita,ba tareda tasan na dawo hayacina ba.

No..no...baba da ka komawa mahaifiyata a lokacin...kai kawai take bukata a lokacin.
Kai ya girgiza.....bazata saurare ni ba a lokacin.

"Toh baba mu fa?.....me yesa baka zo neman mu ba?
Ya share hawayen da ke shirin zubo masa..""da'ga ranar da na rabu da mahaifiyar ku,har izuwa yanzun,kuna rai na.
dai dai sekan dayan ban taba mantaku ba,da ku nake kwana da ku nake tashi,ganin ba abinda zani baku na rayuwa ya sanya a koda yaushe ina me yi maku add'ua.
kuka takeyi sosai...
Mutan falon kuwa jikin su yai sanyi,wasu ma har suna sharan kwala.

""Baba ka yi hakuri,ni bazani yafe wa wannan matar ba".
Cikin rudani ya dube ta"haba ilham,kiyi hakuri mana"...

Ta girgiza kai.."kayi hakuri baba,kar kace na ki bin maganar,zan mata hakuri amman fa da sharadi, shine ta rabu da kai,idan kuma ba haka ba wallahi sai nayi mata abinda bata ta'ba zato ba a rayuwa don sai ta gwammaci lahira da duniya.
Kai ya da'ga..."shikenan,i will look into that, ya fada ayayinda ya yi taku zuwa gun da abba da mujaheed suke tsaye ya rungume su.

Maganar goggoji ce ta janyo hankali mutan falon gareta.
Tayiwa Allah godiya da ya kawo wanan raar sa'anan ta nemi alfarman  da su janye maganar auren hindo da Hisham.
Baba lamido ya da'go tare da fadin "kai goggoji....ya ya kike son toh muyi da jama'a?....an riga da an gayyace su fa.
Wannan ya rage naku,ni dai fatan na ku bar wannan yaron ya auri wace yake so
  Da haka taro ya watse wasu na banbami,wa su na mamaki.
Ita kuwa hajiya zubaida,ba wanda ya gan wucewarta,sai nemanta akayi aka rasa.
Abba makale yake da alhaji buba,don haka ya nemi da ilham ta bar masa shi na dan wani lokaci.

DUbu dari ilham ta baiwa goggoji.."ki rabawa mutanen rugga su sami na komawa"
Cikin mama goggoji take kallon kudin."keh yar' nan .....ina kika samu kudi masu yawa haka?
Murmushi tayi......zan fada maki inda na samu idan na sake dawowa.

A falo suka tarad-da mamee tana shan fruits,hankalikwance..
Ta juyo ta dubi ilham nan ta karanci duk abinda ke tattare da ita....
Mujaheed ya nufi dakinsa, ita kuma ilham ta zauna a daya daga cikin kujerun,ta jima zaune ba tare da tacewa mamee uffan ba,hakan ita ma mamee.
Mikewa tayi ta haye sama..mamee ko ta bi ta da kallo,daga baya tayi ajiyan zuci,tare fadin "sun bar mani da' na acan"

Washe gari har goman safe, ilham bata sauko ba,ganin haka yasa mamee ta bi ta har daki.

Inakwana mamee.!ta fadi haka a lokacin da take saukowa daga gadon ta rusuna gaban mamee.
Samun guri tayi ta zauna ba tare da ta amsa ba.

Inakwana mamee..!
Me ya hanaki bacci?...mamee ta fada
Nayi bacci.
Ban yarda ba.....ga idon ki.
Wallahi,nayi mamee..
Toh naji.....jiya kun dawo,ba wanda yace min wani abu cikin ku,! Ina da'na yake?

Danki yana gurin mahaifinsa...
Shiru mamee tayi,da farko bata so yin tambayar ba, sabida ta karanci komai, amman kewan abba yasa yin magana.

Ilham ta matso dab da ita..."mamee..
Yes dear.
don Allah ina rokon ki da ki yafe wa mahaifin mu,ko don albarkacin mu da kuma abinda ke rubuce a wasikar da kaka ta bari....wallahi ba laifinsa bane.
Mikewa mamee tayi ta ficce da'ga dakin

Bayan sallan la'asar Hisham ya iso gidan sai da be karoso cikin gidan ba.
A waya yayi kiran ilham ta fito,kar kashin bishiya suka zauna.
"Hope u r ok"
I'm fine alhamdulillah....
sure?
yes sure..!
toh whats new..nasan ababe dayawa suna gudana a kwakwalwarki yanzun.
Yes my half...ta fada tanai masa kallon so,.....ina da'da son ka sabida duk yanayi na kana fahimta.
Ya murmusa tare da tsakalan hancinta....Oh yes! Ya fada, toh yanxun me ke tafe a mind dinki.
Uhmmm.....kawai dai ina tunanin yanda zani hada kan iyayena ne kafin na koma makaranta,and i wnt that should be done as soo as possible.

Great idea.,ina bayan ki.
Thanks...ta fada.
Bayan nan suka shiga hiransu na masoya.

        **      **    **
Tun bayan da hajiya zubaida ta bar gidan su goggoji take kwance a gadon asibiti,saura kiris ta rasa rayuwarta sabida *shock* da ta kamata.
Bude ido tayi tagan ilham a kanta,cikin mamaki take kallonta.
Ita ko murmushi ta shiga yi mata...."don Allah kiji sauki,sabida samun saukin ki alkhairi ce a garemu, don haka "get well soon matar babana!....
Kwanar ta bakwai suka sallame ta.
Ita da mahaifiyarta ne a zaune,ba abinda takeyi sai kuka me ratsa xuciya...a duniya babu wanda take so kamar alhaji buba, gashi tana shirin rasa shi.
"Na rasa me ke faruwa, duk farin cikin mu na nema ya gushe....
Kiyi hakuri komai zai dawo normal.

   Ilham kwance take,tana  chatin da kawar ta nazeeha yusuf yareema...nan nazeeha ke sanar da ita sati me zuwa zata tafi makaranta.
ilham ta roke ta da ta dakatar da tafiyar ta sabida su tafi a tare.
Neman Hisham tayi a waya..yana dauka ta nemi da yazo tana son ganin sa.
Bai dauki tsawon lokaci ba ya iso gidan,a falo suka zauna.
Nan take sanar dashi chatin dinta da nazeeha.
Oopss...ya fada.
Next din kenan zaku tafi.
Nop....nace mata ta jira mu tafi tare...kasan me?
Kallonta yakeyi,ba tareda ya amsa ba.
So nake ni da iyayena da kannena gabaki daya mu tafi zuwa aikin umrah kafin na koma.
Thats not bad..ya maida mata.
mamee ce zata biya maku?
Nop...ni ce, domin kuwa harda mahaifina nake son zamu tafi tare.
Ido waje yace da wani kudi?
kudin mahaifin hajiya zubaida....matsalan yanda zan yi convincing makes,itace  kawai matsalata
"A gaskiya,ki de'6o da zafi,....ban tsammani zakiyi nasra wannan karon ba,sai ba sun nemi sanin inda kika sami wadannan kudaden.
sai na fadamasu...ba shikenan ba?
haka ne....toh yaya kike ganin zamu soma kenan?
So nake muje muyi komai na tafiyan,idan komai yayi set sai kawai na sanar masu da batun tafiyan.
the idea,is not bad,amman ina shakku fa..
SAI gab da magrib Hisham ya tafi.
bayan sallan i'shai kowa ya fito falo,ciki harda blessing....karar-rawar kofa ce ta ja hankalinsu,nan blessing ta mike ta nufi kofan..Abba ne tsaye tare da alhaji buba.
blessing tayi masu marhaba,abba rike da hannun mahaifinsa yana jansa da su karasa ciki,amman ya ki.
ganin an dauki lokaci ba'a shigo ba ya sanya ilham tambayar blessing wanene?
Abba ne...
"Toh ya shigo mana!...ta fada a fusace.
shiru shiru bai shigo ba,don haka ta mike a fusace ta nufi gurin.
a sanyaye ta rusina ta gaidashi taredA fadin bisimillah baba...
a'a..ba sai na shiga ciki ba,daman na dawo da muhammad ne.
please baba ka shigo daga ciki mana,ta marairace tana me rokonsa haka yasa ya shiga ciki.
kiris ya rage zuciyar mamee ta buga, tabbas  fillonta ne.
Ta dafe tana me karaton addu'oi,don samun natsuwa...
tare suka karo so cikin falo,ilham tayi masa nuni da kujera tare da fadin bisimillah.
mujahees ya mike ya dawo kusa da shi,ya gaishe shi..ita kuwa ilham ta hanzarta zuwa kitchen...jim kadan sai ga ta ta fito rike da tire me dauke da kayan fruits,a gabansa ta ajiye tare da fadin bisimillah.
Murmushi yayi yace na gode..
shiru-shiru ba wanda ya sake magana a cikin su,yaran duk sun lulube babansu.
ganin bashi da niyar shan fruits din yasanya ilham ta sake yi masa magana.
"Kar ki damu,ciki na cike yake....so nake ki bani dama na gaida mamarki,sai a sa'anan suka juya gun mamee, wace banda dane dane waya ba abinda takeyi...tayi kamar ba ta san da mutane a gun ba.
shiru ilham tayi ta rasa abin yi...
baba ku gaisa kawai...fadin mujaheed
"Hajiya A'isha inawuni..
ba ta da'go ta dube inda yake ba ballantana ta amsa
yayi gaisuwa kamar sau uku bata amsa ba don haka ya mike yayiwa yaransa sallama.
gaba dayan su suka bi sa don yi masa rakiyah.

A KOFar falo suka tarar da mamee tana huci, suna karasawa gab da ita ta kaiwa ilham mari.
"Uban wa yace ki shigo min da ka'to cikin gida na?....ko gidan ubanki ne?
ilham rike da kuncinta tana duban mamee, karo na farko kenan da ta kai hannunta ga jikinta.
cikin muryan kuka tace "babana ne nkuma ka'to?
Eh.....idan ba ka'to bane shi,toh meye shi....watau ni zakuyi wa butulci ko?
toh da'ga ranar me kamn ta yau ba bu ku babu wannan mutumin..
sa'anan daga yau kar ki taka kofan falon nan da sunan fita,sai da izinina.
Tana kaiwa nan ta juya ..
NAn ilham TA fashe da kuka me ratsa jiki,kannenta  kuwa sai lallashi da ban hakuri
washegari ,har karfe dayan rana ilham bata fito ba,mamee ta shiga damuwa domin kuwa tayi da ta sani bayan da ta koma dakinta..ta rasa dalilin aikata hakan alhalin tayi farinciki ganin ya'yanta tareda da mahaifinsu.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.