By Ganarious.
16
Da yatsa nayi mata nunin dakin fillo,sai saukan mari naji a kunci na.na dago kai muka hada ido da ita sai kuma ta hau duka tana shuri na..
Ranar ce ta farko da mamata ta kai hannunta jikina da sunar duka!.
Kaina na tsakanin gwiwowina ina kukan zuci,jin an daina bugun ne yasa na da'go.
fillo na gani duke a gaba na Babana kuwa yana rike da mamata ya janta zuwa cikin gida.na juyo muka hada ido da fillo,murmushi nayi masa sai dai shi bai mayar min ba.sai ya tsiramin ido.muna cikin haka babana ya dawo cikin rudani da'gani yana fadin ina ke maki ciwo...sai a lokacin na sami damar yin kuka duk da daurewan dana so yi.
Kuka nake yi sosai kamar a lokacin ta dake ni,hannuna babana ya rike muka nufi sashensa.ya umurce ni da na shiga toilet dinsa nayi wanka shikuma ya shiga cikin gida daukomin kayan sawana.
Bayanda babana baiyi ba akan nayi shiru na daina kuka abin ya gagara..
A falon sa hajiya ta isko mu itama ta shigano lallashi tana fadin baki kyauta wa mahaifiyarki ba kin daina jin maganarta....bata kai gama managarta ba mamata ta shigo tana huci.
Tana zama tacewa baba na duk hukuncin da ta so shi zata yake kuma bata son ya shiga ciki.ta kara da fadin na farko inason wannan yaron ya bar gidan nan gobe..sa'anan ita daga yau ba ita ba tsalake bakin kofar sashena sai da izini na...tunda kai tana jin shawararka kafada mata kar ta kuskura ta tsallake doka ta tunda na bita da lallashi bata ji ba,yanzun zata bi don dole.
Tana gama fadin haka ta mike zata fita nan baba ya dakatar da ita,shima rai abace yace bana son ki kara kai hannunki jikinta sai da izinina,daga yau na haramta maki bugunta.
Cikin fushi take amsa shi tana fadin ai shi ai shi ya batani...abu kamar wasa iyayena suka fara hayaniya a tsakaninsu wanda tun tasowata haka bai taba faruwa ba sai yau akaina.
Cikin kuka na tsaya a tsakaninsu ina me basu hankuri,ita ma hajiya hankuri take bayarwa...da dai hajiya ta gan basu da niyar bari ta rike hannun mamata zuwa sashenta.
Suna fita babana ya rikemin hannu ya zaunar dani,ya zauna...cikin shasshakar kuka na dago nace wa babana don Allah Baba kayi hankuri.
Ya murmusa yace ba komai mamana!.
Don Allah ku daina fada.ya daga kai kawai....Bayan dan wani lokaci na sake cewa Baba don Allah kar a koreshi,wallahi ba laifinsa bane ni nake zuwa gun sa.
Cikin yanayin tausayi yace zaman lafiyarki da mamanki nake so, bazan koreshi ba amma zan canza mashi gida...
Ah'ah Baba don Allah kar ka chanza mashi gida wallahi ida ban ganshi ba bana samun natsuwa cikin mamaki Babana ke kallona har sai da naji kunyar abinda na fada na dauke kai daga kallonsa.
Yayi ajiyar zuciya tare da fadin kina son sa ne! Kai na daga batare da na kalleshi ba,shima din shiru yayi na dan lokaci sa'anan yace tun yaushe kika fara sonsa.
Tun lokacin da muka hadu.
Ya sake ajiyar zuciya yace shikenan zan sake tunani.
Toh Baba nagode...
Nan ya mike zai shiga cikin gida nayi kiransa!
baba don Allah kar kayi fada da mama na..
*** *** * **
Bayan sallah magrib Babana ya dawo daga masallaci ya iske na idar da sallah nima,yace min na shiga cikin gida na baiwa mamata hankuri.
nace mashi baba tsoro nake ji
Ba abinda zatayi maki
Ah'ah baba...toh ka rakani.
Ba musu ya tashi.
A daki muka iske ta,babana ya zauna a gefen gadonta,ni kuma na tsuguna can nesa da ita amman ina fuskantarta.
Shiru shiru ba wanda yayi magana ita dinma bata dago ta kallemu ba....da ido babana yayimin alamar nayi mata magana.
cikin sanyi murya na shiga bata hakuri..babana ma ya bata hakuri sa'anan daga baya ta dago tace idan har inason ta hakura nayi mata alkawarin daina shige wa yaron nan,kuma zan sa ido a karatu.
Nayi mata alkawari sa ido a karatun sai dai ban fadi komai game da fillo ba..
Babana ya mike ya kuma kirata wai ta biyo shi daman ita ke da girki a ranar..
Hutu ya kare don haka mun koma makaranta kuma sakamakon jarabawar gwaji ya fito,an bawa kowa nashi sai ni ce ba'a bawa ba.nayi mamaki sosai safiya ce ta matsamin wai muje ta rakani gun malam sani ya bani nawa.
Mallam sani bai so bani ba wai sai an zauna da iyayena tukun,da kyar muka shawo kansa ya mika mana takardan...
Abin mamaki nice ta karshe a ajinmu,Nan ta'ke na fashe da kuka.
Ba mallamai kadai ba ,hatta dalibai sunyi mamakin ganin nice ta karshen ajinmu. Malam sani yasani gaba yana min tambayoyi wai ko da abinda ke damuna ne ko wani abu na faruwa a gidanmu ne dake hanani karatu...nace mashi a a.
yace chanzawata abu ne dake bashi mamaki.
Yinin ranar duk a sukurkuce nake,nima na tambayi kaina meke faruwa dani ne.
......Babana na kaiwa sakamakon,yana dubawa yayi murmushi yace shi yasa kikayi kuka har idanunki suka kumbure? Kuka yasake kubcemin..nace Baba na kasa gane kaina,ka duba fa na fi kowa kokari duk makarantar nan amma wai nice ta karshe a jarabawan
Cikin lallashi yace kiyi hakuri mamana kar ki sawa kanki damuwa komai zaiyi daidai.
Na tashi zan shiga ciki,Nace mashi ya bani takardan na kaiwa mamata yace ah'ah nakira mashi ita dai.
*** ***
A kwance nake ina karatu domin kuwa sauran wata daya mu fara jarabawan gama makaaranta.ina karatun ne ba tareda na fahimci me nake karantawa ba sabida kwana hudu ban sa fillo a ido ba,nayi kokarin samawa kaina natsuwa ne don gudun bacin ran mamata.
No comments:
Post a Comment