Pages

Sunday 24 September 2017

SOYAYYARMU👫


             By Ganarious.
17
Ji nayi an zare littafin dake hannuna,haka yasa na da'go.mamatace tsaye a kaina muna ha'da ido na sauko kasa inayimata sannu da dawo wa.ta sami daya daga cikin kujeru ts zauna tana kallona.
  Ta dauki tsawon lokaci sa'anan ta tambaye ni tunanin me nake haka da take sallama ban amsa ba ko bansa da shigowarta ba ko!
    Shiru nayi ban amsa don bani da abin fadi... tayi ajiyar zuciya sa'anan ta cigaba fadin"ni da Babanki mun zauna don neman mafita akan matsalarki"
Nan na kalleta,watau kallon rashin fahimtar me take nufi da hakan.

 Nasan kina cikin rudani Aisha!. Ni da Babanki mun fahimci cewan kina matukar son dan filanin nan wanda son da kike masa ne ya sa ki a wannan halin..ni dai mahaifiyarki ce duk wani abu maikyau zan so maki shi.bana goyon bayan soyayyarki da wannan yaron sai dai hujojin mahaifinki ya gamsar dani....tun kina karama daya daga cikin abikan babanki ke cewa yayi wa yaron sa ka'me,haka wani dan uwansa ma,nima da'ga gefena akwai nazeer sai dai Babanki baiyi wa kowa alkawarin basu ke ba,sai ce masu yayi duk wanda diyata take so shi zan aurama ita...sai gashi ya fahimci cewan Dan fillon da ya fito daji kuma wanda baiyi karatun islamiya balle bokon shi kike so.
Ba damuwata bace ki aureshi,burina bai wuce nagan kinyi karatu kin zama abin koyi,abin kwatace da sauransu.ina son kiyi karatun da al-umma zasu amfana dake.
Bana ra'ayin ki auri me kudi ko dan wani-da-wata.
Mahaifinki ya zaunar da dan filanin yayi mishi tambayoyi Masu yawa ya kuma fahimci cewan shima yana sonki kamar yanda kikeson sa.Asalima yace dalilin zuwa sa birni shine  don ya aureki.ba zamu hanaki aurenshi ba amma kuma zakiyi karatu kamar yanda kikayi niyah tun kina karama,sa'anan daga yau bana son kina zuwa inda yake,ba mutuncin mace bane ta bi namiji sai dai shi ya biyo ta.don haka idan yanason ganinki yazo falo ku zauna anan kunyi hiranku.
  Jikina yayi sanyi sosai jin maganganunta,na tsinci kaina da jin tausayinta na kuma yi alkawarin faranta mata rai.
Bayan kwana biyu Babana ya sake kiran mu ni da fillo yayi mana nasihohi sa'anan yace  yasamo mana lesson teacher zai koyar da fillo kafin yasa shi makaranta,ni kuma zai yi min darasi akan jarabawar da zamuyi na barin makaranta.
           **          **         **
Akwana atashi,har zamu fara jarabawa.shi kuma fillo ya da'ge sosai,gashi da kaifin basira...nima kuma na natsu da kuma da'gewa ba don komai ba sai don na farantawa mahaifiyata rai.
Ranar farko da muka fara jarabawa na dawo gida na iske baba Lamido ya zo.bayan mun gaisa yake shaida min Binta batada lafiya don tayi bari,duk da ban ganta ba na tausaya mata...kwanarsa hudu ya koma.
Gama jarabawa ta yayi daidai da sanya fillo a makaranta..yayi murna sosai nima kuma na ji mashi dadi..a lokacin ne kuma yan'ne  na dasuke kasashe ketare suka dawo gaba dayan su domin kuwa biyu daga cikinsu sun shirya yin aure.
Sannu a hankali suka fara lura da soyayyarmu da fillo,wasun su basu so haka ba wai aji na ya wuce nan sai dai ba yanda zasuyi sabida babana ya goyamin baya.
     **        **        **
A satin da za'ayi bikin su ya'Abdul ne sakamakon jarabawarmu ta fito.duk sunyi farin cikin ganin sakamako ba kamar mamata da har takai ga yi min godiya.
Su ya'ya Nazeer sun zo biki suma,yayi murnan ganin sakamako na da kuma shawaran na gaggauta wuce wa makarantar jami'a ta tukin jirgi.
Ranar daurin su,mamata ta bani wasu sets din zinari wai gift dinta kenan gareni.
Bayan kammala biki da kwana uku,mamata ta dawo da form din wata makaranta da ke kasar germany.Babana ta bawa  form din sa'anan suka kirani wai na cika.ina ganin abinda ke rubuce,naji gaba na gaba na na faduwa..shiru-shiru basuji nace wani Abu ba ko nuna farinciki ko gadiya..na dago na kallesu ashe ni suke kallo,muna hada ido mamata tace yaya dai,tayi maganar ne tare da da'ga hannunta.
Shiru nayi domin kuwa bazan iya misalta maku yanayin da na tsinci kaina ba alokacin.Babana ne ya dawo kusa dani ya zauna yace "yaya dai mamana"...nan ma shiru nayi,sai da ya sake magana sa'anan na dago ina kallonsa
Ya sake cewa"ki fadamana idan makarantace batayi maki ba sai a abinciko wata ko ki zabi wanda kike so.daman mamarki ce ta binciko wannan din.
Kai na girgiza....a'a makarantar tayi min.
Toh miye same ki..
BA komai baba nace dashi.
Shikenan,ki cika form din akai masu.
Bayan na koma dakina nayi kokarin gano abinda ke damuwata na kasa..tun bayan cika form nake tunanin fillo,nayi tunanin zan tafi na barshi kenan! A duk lokacin da na tuna haka sai naji tausayinsa ko nace tausayinmu.
Allah yayi na sami addmission a makarantan,ba da bata lokaci ba kuwa muka shirya tafiya zuwa germany.
  Da kyar na na lallashi fillo ya fahimce ni,amman yace shi zai koma ruggansu idan na tafi...ba yanda banyi ba akan ya jira ni.
A ranar da zan tafi fillo fito ba,bayan mun fito za'a shiga mota babana ya fahimci cewan bana cikin natsuwa,da kansa ya nufi dakin fillo.sai da ya kwankwasa kofar kamar so uku zuwa hudau sannan ya bude.ya leko suka hada ido ya risina ya gaida Babana.
ko kasan Aisha zatayi tafiya kuwa?.
Eh....
yaya ne toh!baka fito sallama ba ko rakiya.
A tare suka karaso inda muke.bai cemin komai ba don mamata dake tsaye gun..bayan nayi mashi sallama muka nufi airport.
              A GERMANY.
Gaba daya naji duniyar tayimin zafi....na kasa samun kwanciyar hankali ko natsuwa.
A wannan makarantar ka'idansu kafin ka shiga aji daya  sai kayi wata takwas ana koyon yaren kasar da kuma jaraba ka ko zaku bada himma.gun koyon abubuwa da ya shafi fannin tukin jirgi.
   Nidai kawai ina makarantar ne amma ba zani iyacewa ga abinda ke faruwa ba sabida hankalina da ruhina basu tare dani....bani da kawaye don kuwa bana hira da kowa,bana shiga harkan kowa.
  Duk karshen wata  Babana yana zuwa duba ni.ya kuma lura bana abin kirki,ya kan tambayeni ko da wata matsala.!
Nace mashi babu.
Idan muna hira dashi sai ya matsamin da tambaya ko akwai abinda nake bukata,nan ma nace mashi ah'ah....sai hira yayi ni'sa sa'anan zai dauko zancen fillo....bana danin lokacin da nake murmusawa hakan ko na farantawa babana rai.

   A daddafe na kai karshen wata takwas din..munyi jarabawa ta shiga aji daya,bayan jarabawar aka bada hutun wata daya.
 Na iso gida da murna ta.ba wanda nake son gani kamar fillo,sai dai anyi rashin sa'a shima ya tafi hutu ruggansu...
Na kuma tarar da su anty Aisha kan'nen ya'Nazeer sun zo hutu amma kuma hutun ya kare suna shirin komawa kenan.
  A sanyaye nake komai tun da naji labarin fillo ya hutu.
Su Anty Aisha sai zolayyata suke wai sun lura bani son dawowa  gashi germany din bai karbeni don na rame.
Ban tanka masu ba sabida ni kadai nasan abinda ke damuna.
A lokacin da zasu koma sun nemi alfarma gun Baba na,wai na biyosu nayi hutu a can,ko da na  sati daya ne..ya amince tare da shaida masu satinan daya da sukace shi zanyi.
Nayi da nasanin  biyosu sabida ya'Nazeer ya matsamin da soyayyar sa...wai shi yana ji a jikinsa akwai wani dake son dauke min hankali a germany don haka muyi aure bayan auren sai na cigaba da karatu a gidansa.....ban ce mashi komai ba sabida jin haushi maganganun sa.
   A daddafe nayi satinan daya na dawo garin kaduna.har zuwa wannan lokacin fillo bai dawo ba.
Abin kamar wasa har ya ragemin kwana uku na koma ba fillo ba alamunsa.
  Tare da Babana muka tafi germany sabida opening/matriculation da za'ayi mana..na lura da kallon da Babana yake min,na tabbatar a zuciyarsa yana son gano damuwata ne.sai bayan mun shiga jirgi hawayen da nake kokarin rikewa tun daren jiya ya kubce min.da sauri na goge kafin babana ya gani,sai dai abinda ban sani ba shine banana yana kallona ta gefen idonsa.
Hannun da na share hawayen dashi ya kama yana shafawa a hankali sa'anan ya kwantar min da kaina a kafadarsa,sai lokacin kuka ta zo,nayi kukan da basan dalilin yinsa ba.
 Karfe dayan dare muka isa germany,gidan babana muka nufa.muna gama cin abinci yace na tafi na kwanta sabida zuwa makarantan mu da safe.
Kashegari da safe na fito gaida babana bayan na idar da sallar sub'i.bayan mun gaisa yace kin makara!..na kalli agogo karfe takwas na gani,na da'fe kirji tare da fadin "Laa baba" wallahi ban san lokaci ya wuce ba.
yace na shigo ta tada ke ai..
Baba banma san kashigo ba.
Gajiyace...kije kiyi wanka ki shirya,ni na gama shirin koo!
Cikin hanzari na mike na shiga wanka.
   ***       ****       *****
Gun da aka tanadawa iyaye daban da na dalibai..Babana yana zaune ne inda iyayen dalibai suke,ni kuwa ina can zaune inda aka tanadar mana.
Bayan gama jawabai da surutansu.suka sanar wa iyaye cewan akwai wayanda zasu sake maimaita watannin takwas din idan har basu ci gwajin da akayi masu ba..sa'anan duk wand ya sami danshi ko diyarshi cikin masu maimaitawa,toh yayi hankuri hakan shi ya fi...bayan wannan jawabin ne aka kiran sunayen wayanda za'ayi wa matric,ma'ana wa'anda suka ci gwajin kenan..
Na kahsa kunne ina sauraran sunana amma har aka kai karshe banji sunkirani ba..bayan kiran wadannan sunaye,suka shiga kira masu maimaitawan.a masu maimaitawan ma,sunana ne aka kira karshe.
   Kuka nakeyi sosai tun daga wannan lokacin da naji an ambaci sunana karshe,har muka isa gida ban daina kukan ba bayanda Babana baiyi ba wai na kwantar da hankalina  na daina kuka,amma ina! Kukan sai alokacin yake zuwa. Domin kuwa mamata kawai nake tunani dakuma matakin da zata dauka.
Har dare ban daina kuka ba,da kyar babana ya samu na daina kukan shima din sabida na fara jin ciwon kaine.
 Kashegari tashi ne da ciwon ido.idanuwana sun kumbure,kuma bana gani sosai.na fito falo don gaisawa da Babana,nan ya gan ido,sallahti yayi sa'anan yace  muje asibiti.
Magunguna suka bani kawai sai muka dawo gida.
Kai tsaye dakina na nufa nayi lamo kan gado,tamabayr kaina nake mike shirin faruwa dani ne.!rayuwata na shirin baci tun bayan haduwar mu da fillo,haka dai na dinga ire-iren tunani hawaye na gangarowa.
Babana ne ya shigo dakin,ya zauna gefe yasa hannu ya dagoni na zauna.yace inason yi magana ta mahaifi da diyarsa da fatan kuma zaki bani hankalin ki don fahimatar zance na.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.