Pages

Saturday 12 May 2018

KAZAMA CE MATATA6

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
*KAZAMA CE MATATA*
           πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
Written by Ganarious.
Page6

å Mutan Kenya,one love.
                 **          **

  A zaton engr. Munir kwana uku kacal ya ishe sa Gama aikin da ya kai shi can jihar potakot, sai dai abin ya sha bambam da zaton sa.
Abu kamar wasa,har yana neman kwana shidda kenan.

Zaune yake yana tunanin yar' mutane da ya baro a gida wace tun zuwansa bai ji duriyarta ba ko da a  wayane...gashi bata da wayan.
Wayarsa ya fiddo ya nemo lambar inno,bugu daya ta dauka kamar jiraye take da kiran nasa.
"Assalamualaikum....
"Wa'alaikumussalam....
Inakwana... ya fada.
Kwan lahiya,ya ya aiki?
Da haka suka yita gaisuwa,ya na me tambayarta mutan gida.
Shiru yayi bayan gaisuwan,yana tunanin da'ga inda zai fara tambayarta lafiyar suwaiba.

Injin dai lahiya ko? Ta fada.
Fargawa yayi daga dan tunanin da yakai..."eh lafiya lau ,na kira ne naji yanda kuke, na kuma sanar maku cewan aikina a nan zai iya daukan tsawon lokaci,don haka bazani samu dawowa yanzun ba.

Toh..toh...wai sabida wani dalili? Ga yar mutane ka ajiye, wa kake tunanin zai dauki nauyin ciyar da ita? Kudin da ka bari guri na sai da ta gan bayansa, sa'anan hankalinta ya kwanta.
Duk a fadace take wannan magana.
A sanyaye yace "kiyi hankuri inno, ba ina nufin zani dauki tsawon lokaci bane,nan da kwana hudu zuwa biyar zani dawo da yardan Allah.
Allah shi kaimu,ta fada a takaice.
Ameen.
Nan yayi mata sallama jin yanayi ya tabbar masa da idan ya cigaba da tsawai ta maganar toh kunnensa ba zasu kwashi me dadi ba.
Dan siririn tsuki yayi,bayan da ya kashe wayar...."inno ba za ta ta'ba canja hali ba!....ya furta a yayinda yakevjin takaicin irin halinta.

Lambar kanwarsa khadija ya nema,bayan da suka gama waya da inno.
"Yaushe zaka dawo?" Ta tambaya bayan sun gama gaisuwa.
Uhmmm....sai ranar da duk kuka ganni.
"Toh amma kwana uku kace zakayi  a can.

Eh..haka ne! A tunani na aikin zai zo da sauki, amman da yardan Allah mun kusa samun settin na'urorin.

Toh Allah shi taimaka.
"Ameen kanwata,na gode da addu'ar ki.
Haba yaya.....godiyar me kuma,ai ni wajibi ne a dunga yi maka addu'a.

Cikin dariya yace "toh naji,Allah shi karbi addu'o'in ki.
Ameen yaya.

"Yauwa fareeda na gida?
"A'a .....ba ta nan,da abinda zata yi maka ne?

Eh....idan ta dawo,ta je gidana,zan bugo ta wayar ta,nayi magana da suwaiba.
Toh,zani fada mata.

 Bayan sallan magriba,fareeda ta nufi gidan engr. Munir.
Sai da kai kimamin mitin arba'in tana buga kofa, sa'anan suwaiba ta fito ta bude.

A fusace fareeda ta dube ta "haba anty suwaiba...zaki rantse da Allah,baki ji duk bugun kofan nan da nayi ba?
Tayi dariya,kyawawan hakoranta sun bayyana...."kiyi hakuri,walle na dauka nan makwabta...ko a yanzun din na fito ne don aikan me gadi,ashe ke ce  ke kwankwasa kofat.

Cikin yatsine fuska fareeda tace "toh gaskiya  ki dunga dubawa a duk lokacin da kika ji ana buga maki kofa,ba kawai kiyi tunanin makwabta ake bugawa kofa ba.
Tana kaiwa nan ta ratsa ta gefenta ta shiga cikin falon.
Tsaye tayi chakk!...tana duban falon...ta girgiza kai,tareda fadin tabdi jam,a lokacin suwaiba ta karaso inda take tsaye tana me tambayar ta "mi halan?"

A gaskiya bazan boye maki ba,idan da ya'Munir  ne ya shigo ya tarar falonsa haka,baza ki kwasa me dadi ba.

Mi na na kika nufi da haka halan?
Abinda nake nufi shine wannan falon yayi dau'da,tsarinsa ma a yanzun baiyi ba, duk da dare ne,bai hana dattin falon ya nuna ba.
"Keehhh...kiji tsoron Allah,yau fa na share falon.

A hakan? Farida ta fada cikin fidda idanuwa.
"Shin wane irin dau'da na kika nufi?.
Ba tareda da fareeda ta amsa ta ba ,ta nemi daya daga cikin kujerun ta zauna.

"Ya'munir ne ke son yayi magana da ke,don haka ya umurce ni da na kawo maki waya.
"Kai,don Allah?......amman na ji dadi walle...
Bayan nan shiru ya ziyarci falon,ba me ce da wani kala,asalima kowa da abinda yake rayawa a zuci,fareeda na kaico da halin kazantar suwaiba da kuma tausayawa yayan nata.
A yayinda gimbiya suwaiba na lullube da farin ciki a zuciyarta,duk a matse take da ta ji muryarsa.
Suna a haka engr. Munir ya kira, fareeda ta dauki wayan ta mikawa suwaiba.
"Hello" ta fada cikin matsuwa.
"Hello kina lafiya?
lahiya lau nake muniru,ya ya aiki?
Alhamdulillah...
Madallah...kwana uku kace zakayi,sai gashi kana neman ta shidda kenan , gashi kayan shayi da barmani sun kare,idan kuma na je gun inno don karban kudin da ka bari gurinta sai tayi ta masifa,idan ko ta gama masifarta abinda take bani bai wuci dari uku ko hudu ba..
Ba ta tsai da maganar ta ba har sai da ta gama kwararo masa matsalolinta,sannan tayi shiru.
"Kina nufin kayan shayin sun kare cikin kwanakin nan biyar?
eh..walle ko,sun kare.
Shikenan naji,shi kudi da na bar maki kuma fa?
su ma din sun kare wallah.
What??..sun kare fa kikace?
Eh wallahi, Allah sun kare.......
Hmmmm...lallai,yanzun me kike bukata?
Kayan shayin da kudin rikewa a hannu.
Shikenan,za a kawo maki gobe da yardan Allah, don haka kar ki sake zuwa amsan kudin gurin inno.
Toh ko ai da sauran kudi a hannunta.
A fusace yace "na dai gargade ki.
Da haka sukayi sallama da shi.
Tunda ta soma wayan fareeda ta sa mata ido,mamaki da takaicin suwaiba duk ya ishe ta,ba wata magana me dada zuciya sai korafi da bani?tabdijam ashe ya'munir na dauke da katon aiki.

Washe gari engr.munir ya  turawa  khadijah kudi cikin account din ta.
Ya kirata a waya ya sanarda ita yanda zata yi da kudin,ya umurce ta da ta sayawa suwaiba kayan shayi,sa'anan sauran kudin ta ba

DAga kasuwa  gidan suwaiba suka nufa.
Zaune take,ta baje sai baran gasashiyar gyada takai tana me taunawa.
duk ko'ina na falon bawon gyada ne...daga gefe kofuna ne da ta sha shayi da su,kai kuma ledojin biskit da ta sweet.
      Guri khadijah ta samu,tana me bin falon da ido.

"Anty bisimillah,ga gyada."
A'a na gode,.....a yayinda khadijan ta kago murmushi.
Ke fareeda ga gyada...

KAI ta karkada,fuskar nan kuwa a murtuke.
Ga shi,kayan shayi ne ya'munir ya ce a sayo maki,sa'anan ga wannan dubu biyar...

Ahhh'ahhh'ahhh....kai Allah me sona,toh sanunku da kokari,na gode...yaushe zai dawo ne?
gaskiya bani da masaniyar ranar dawowansa,amman dai cikin kwanaki nan zai dawo,da yardan Allah..
Fareeda dake zaune,tukun da suka shigo batayi magana ba sai a lokacin.."a jiyan da kikayi waya da shi baki samu damar tambayarsa ranar dawowansa ba,sai korafi da a baki,yanzun da ya baki kike tunawa da kiyi wannan tambayar ko?tunda bukatar ki ta biya
shiru tayi ta na duban fareedan..
Kehhh...khadija ta fada a yayinda take da'gawa fareedan hannu.
TA JUyo ta dubi suwaiban, zai dawo cikin kwanakin nan,kinji ko?
Toh Allah shi kawo shi lahiya.
Ameen,khadijah ta fada a yayinda take mikewa .ita ma fareeda ta mike tana yatsine yatsine.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.