Pages

Sunday 24 September 2017

SOYAYYARMU👫

         By Ganarious.
15
Haka mukayi ta rayuwa kullum safe sai na kaiea fillo abinci kafin na tafi makaranta,idan kuma na dawo sai na shiga gun sa munyi hira kafin na shiga ciki.idan kuma na shiga ciki Allah Allah nakeyi na idar da sallah na dibi abinci na a plate natafi dakin sa na zauna ina ci muna hira.duk da kashaidin da mahaifiyata tayimin.
Weekends kuma mu tafi yawon ganin gari da sayayya,a maimakon librabrin da muke zuwa da safiya.

   Wataran mun dawo daga sayayyar,motanmu na gaba na mamata na biye da mu.mallam iro na parking itama tayi parking a tare muka fito,tana ganina tare da fillo fuskar nan  tasauya,gaisuwar ma bata amsa ba sai cewa tayi mu biyo ta.
Muna biye da ita har zuwa fallonta,bayan mun zauna ta kalleni rai a bace tace"a yanzun dai ina kyautata zaton kinsa abu marar kyau"! Kai na daga mata don kuwa ina tsorarce da yanayinta.
Takara da cewa last warning dina kenan.ki natsu kiyi karatu idan ki bahaka ba zaki gan ba daidai ba.nayi maki iyaka da wanan yaron,bana son na kara ganinku tare balle naganki hanyar dakin sa....kinji ni ko?
Nan ma kai na daga mata....ta maida kallonta ga fillo shima kallonta yakeyi. Ta tambayeshi sunar sa.
Ya fadamata...nan take tambayarsa me ya kawo shi kaduna.
Ya juyo ya kalleni muka hada ido,sai ras-ras zuciyata keyi.
Batare da ta jira amsar sa,tace ba lallai bane nas an abinda ya kawo ka sai dai ina neman alfarmarka.dafatan zaka fahimce ni?
Eh zan fahimce ki inji fillo.
Ta bashi shawarwari akan ya natsu yasa kai akan abinda ya kawo shi a zaton ta ya neman aikin yi ne....sa'anan tayi mashi kashedi cewan bata son ganinmu tare don ina bakutan lokaci don shirye shiryen jarabawa...tayi fada ta kumayi lallashi da shawarwari daga karshe ta sallami fillo nikuma ta cigaba da bani shawarwari.
   Bana samun natsuwa,tun daga wannan ranar da tayi mana fada ta samin ido sosai,motsi kadan sai tace ya'ya!..haka zamanta ya dawo falo,wata sa'in ma idan tana falon takan ce na kwaso takardu na nayi darasi tana duba min.

 Abinci ma kani na ne ke kaiwa fillo,kullum idan ya kai sai yace mashi ka kira min Aisha mana amma ba daman fita hakan ka sosa min zuciya don nakan rasa inda keyimin dadi.
tsananin ya kaiga mamata ke kaini makaranta kuma ita din ke dawo dani haka na cigaba da rayuwata har mukayi hutu..bata so naje hutu ko ina ba,sai da i wasu yan uwanta da suke lagos sun matsa mata wai lallai na zo hutu gun su.
Ta sanar da mahaifina ta kuma umurceni da banso hakan ba.
DUk kokari da dabarun da nayi don samun ganin fillo a banza nakeyi,daga baya na aiki kanina ya bashi hankuri ya kuma sanar dashi zanyi tafiya,kuma ba zan dadeba ya jirani inn shaa Allah idan na dawo zamu gan juna. Nayi wa kani kashedi da maganar ya zamto tsakanin mun biyu.
Kashe gari Babana dasu hajiya aka tafi kaini airport don hawa jirgi zuwa lagos.
             A  LAGOS
 Uncle Ahmad da matar sa Anty Amina yan'uwa ne.watau cousins ne su.kuma duk su biyu cousins din Mamata ne.
Ya'Nazeer shine baban dan uncle Ahmad,shine a airport yana jiran isowata.nayi murna ganinsa shima haka.mun shaku sosai har akance mana mata da miji.mamar sa kuwa da gaske takeyi wai nice matar sa...
Sai da ya kai ni nayi ciye ciye sa'anan muka tafi gida....a gida kuwa wata irin liyafa suka shiryamin sai kace matar wani minista ce zata dira a gidan.ban iya con wani abin kirki ba Don cite ciyen da nayi kafin mu iso gida..kannen ya'Nazeer basu ji dadin haka ba....
Duk sun lura da yanayin da nake ciki.a koda yaushe nakan so kebe kaina don tunanin fillo ko kuma idan ana wasa da walwala sai nayi shiru-shiru.Anty amina ce ta fara tambayata wai ko anyimin wani abu ne don ba haka na saba yi idan na zo hutu nace mata a a ba komai.
Shima ya'Nazeer din yayi juyin duniyar nan nace mashi ba komai sai ya dauki wata al'adar fita dani kullum zuwa guraren shakatawa ki zan saki jiki....
Muna ta hira sabida gobe zan koma gida sai anty Aisha ta kawo zancen kawarta wace take son ya'Nazeer,sai ya ce ki fada mata ta daina sona sabida ni Aisha nake jira...dariya nayi bayan mun hada ido.
Tare da su anty maryam da sauran yaran gida akayi min rakiya zuwa airpot,ba abinda ke raina sai kawai na gan fillo....
Mallam iro ya zo daukana..na kuwa ji dadi sosai don kuwa muna isa gida nagan alamar motan mamata bata a parking space hakan na nufin bata gida kenan sai na sami kwarin gwiwa wucewa dakin fillo.
Nayi sa'a kofar dakin sa a bude take...sallamata tayi daidai da dagowar fuskarsa sai kawai ya kura min manya idanun nan nasa,nima shi nake kallo....daga bisani da kallo-kallon ya ishe ni nace na dawo!
Ajiyan zuci yayi sa'anan yace sannunki da isowa ransa a bace.
Kana lafiya? Nace dashi
Jam....tare da samun guri ya zauna da kyau.
Hamdala....nima guri na samu na zauna ....daga nan ba kara kallon inda nake ba balle yayimin magana,sai kurawa  kasa ido da yayi.ni ko shi nake kallo.
  Mun dauki lokaci a haka kafin nace ma sa fillo buba baka ji kewata bane?.
Ya dago ya kalleni,ya kara maida kai.
"Ka amsa ni mana"!
Ya sake dagowa yace ya'ya kikeson nAyi
Niban ce kayi komai ba amma ka fadamin cewa kaji kewa ta.
Toh naji kewan ki...kuma sosai fiye da yanda kike zato,toh amman ya kike son nayi!....yanayin maganarsa yasa na tsinci kaina da tausaya masa.
Da kyar ya saki jiki muka fara fira kamar yanda mukeyi a da...a firan yake fadin kin tuna a rugga na tambayeki ko iyayenki zasu amince na aureki.!
Eh na tuna .
toh baki cemin komai har   yanzun.kuma no in as on na koma rugga,sai mu koma tare idan na aureki.
ka kwanatar da hankalinka...zan aure ka amma ba yanzun ba.
Yayi baro baro da idanun nan nasa yace"yo sai yaushe toh"
Sai na gama karatu tukun
Shi karatun yaushe zaki gama shi?
Na kusa inn shaa Allah.
toh shikenan,zan tafi rugga,idan kin gama sai na dawo na aureki.
Da sauri nace don Allah kar ka tafi bazan iya jure rashin ganinka ba.
"Yo ai ko ina nan innarki bazata bari ki ganni ba.
Kar ka damu zanyi kokarin nagan cewa ka ganni a koda yaushe...farin cikinsa ya bayyana don na fadi haka.
Kiran sallah ce ta ankarar damu,dani dashi muka mike,ni na nufi cikin gida shikuma yayi massallaci.
    A falo na ci karo da mamata,kallo daya nayi mata,sai da zuciya ta tayi ras ras..gaisu... Read more

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.