Pages

Tuesday 15 May 2018

Page 43of SOYAYYAR MU 👫

SOYAYYAR MU👫
      By Ganarious.
4⃣3⃣.


---- *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN*...ALLAH ka bamu ikon ganin farkonta,izuwa karshenta cikin koshi lafiya,ya kuma bamu ikon Yin ibadu.......

       **        **       **
3:08pm Hisham ya iso,sabida sun ajiye magana shi da ilham cewan a yau za su tafi don yin komai,na tafiyarta da iyayenta.
Tun bayan sallan asubahi yake trying lambarta bata zuwa.
Abba da mamee ke a falon,ya risina ya gaida mameen.
Cikin sosa keya yake fadawa mamee tun a daren jiya yake trying lambar ilham bata shiga ba ko lafiya?
Ok, bara na dubo maka ita ko?
Ta jima tana buga kofa,ba ta bude ba sai da tayi kiran sunanta sa'anan ta bude.

Subhanallah ta fada a rude....rike hannunta tayi suka koma cikin dakin tare da zaunar da ita bisa gadon.
Ta dubi ilham tace "kuka kikayi haka?...mamee ta mike ta mikar da ita, gaban dressin mirror dake dakin ta nufa da ita,"dubi fuskarki".
"Kiyi hakuri....kiyi hakuri mamee,nasan nayi ba dai dai.ina neman gafararki,na sanya ki cikin bacin rai jiya,please kiyi min afuwa ki kuma auna yanda soyayyarki da mahaifinki yake.ki misalta yanda kike jinsa a ranki watakila nima haka nake jinsa....haba mamee.......mahaifina kike cewa ka'to?....nan ta fashe da kuka me karfi.
Banda kallonta ba abinda mamee take yi.

"Tacigaba da fadin duk abinda suka faru ba laifinsa bane..kar ki manta abinda ke rubuce a wasikar ko don wannan zaki tausaya masa,ko ba komai tsakaninku,mu kuma fa?

"Toh me uba....yanzun me kike shirin fada min?

Kiyi hakuri,don Allah ki fahimce ni..na ji zafi sosai da kika kira mahaifina da ka'to,ki kwatanta sanya kanki a yanayin da nake ciki.

"Naji...zan kwatanta...ta mike ba tareda ta kara wani abu ba.
Kije Hisham na falo.
Hijabi ta sanya ta biyo bayan mameen suka fito.
Rudewa Hisham yayi,ya manta da mamee a gurin don da saurin sa ya kama mata hannu yana fadin "whats wrong?
Ta kwace hannun ta,ba tare da ta amsa ba ganin haka yasa mamee ta bar masu falon
Dawowa yayi gefenta "please tell me what the problem is"
Ta sanya dan yatsa ta share hawayenta,nan ta kwashe abinda ya faru a daren jiya ta sanar masa.
Shiru Hisham yayi sabida ya rasa abin fadi.
Ta cigaba da fadin "gaskiya naji zafin furucin mamee...a son rai na na dai daita tsakaninsu kafin na koma makaranta.

"Me ye mafita?"....Hisham ya fada murya kasa kasa.
Kai ta girgiza, na rasa
Ki kwantar da hankalinki, inn'shaa'Allah komai zai zo karshe.

 Tun bayan tafiyan Hisham ,ilham ta zurfafa a tunani, tana me neman mafita.
A daren ranar bata runtsa ba,a matse take ta gan wayewan gari.
  Bayan sallan Asubahi ta shiga wanka ta shirya tsaf, sannnan ta shiga kitchen ta hada masu abin kari ta jera a dining table.
Dakin mamee ta nufa ta tarad-da idon ta arufe,ganin haka yasa ta juya zata koma.
"Karaso mana"....mameen ta fada.
Na dauka bacci kikeyi....inakwana.!
Lafiya lau,da fatan kin sami isashen bacci ko?
Eh..na samu.
Toh,maa'shaa'Allah.

"Inason zani je gidansu Amarah,da'ga nan zan je cafe.
Ido waje mamee take duban ta, da sanyi safen nan zaki je gidan mutane?
Amarah zatayi tafiya ne,jirgin karfe tara zata bi,shiyasa .
Tau a dawo lafiya.
Gidansa Amarah ta nufa,ta amshi wasu takardu sa'anan ta tafi gidan mahaifin mameen.

Ta roki kakanta watau mahaifin mamee, da ya yafe wa baban ta...nan yake sanar mata ai ya  yafe masa,ya kuma tausayamasa tun bayan da ta karanta masa wasikar kakarta.

Daga gidan kakanta,cafe ta nufa,tayi scanning wasikat sa'anan ta turawa karkaf din dangin mamanta wasun su ta e-mail ta tura masu,wasu kuma ta whats app.
Ta nema da suyi masa afuwa....ta jima zaune bayan da gama turamasu,tana tunanin abin yi....
Da'ga cafe gidan su goggoji ta nufa,a waje ta tarrar da Malam Lamido yana ssuraron radio,ta risina ta gaida shi, cikin sakin fuska ya amsa mata.
me ke tafe da ke yar'nan?
Uhmmmm...wata shawarace na zo da ita.!

Toh.ina jinki
"Me zai hana ka hada kan wasu da'ga cikin yan uwa,su je su baiwa mahaifiyata hakuri?...
Dariya yayi "kinyi tunani me kyau yar'nan,....daman kuma mun riga da mun yanke shawaran Yin hakan....gobe wasu zasu taho daga rugga,gidan mahaifinta zamu fara zuwa da yardan Allah.
Toh,Allah shi ba mu yawancin rai
ameen...
Ta mike ta shiga cikin gidan,a falo ta gan mahaifinta kwance bisa dogon kujera,da alama ya zurfafa a tunani.
Sai da ta isa gab da shi,sa'anan yasan da shigowarta.
A'isha ce...ya fada a yainda yake kokarin mikewa zaune
Nan da na tausayin sa ya lullube zuciyarta.
"Baba lafiya?...ta tambaya cikin Yanayin tausayi.
lafiya lau A'isha.!
Zama tayi kusa da shi tana me duban fuskarsa,a yayinda zuciyarta ke raya mata watakila yana tare da damuwa ko ciwo.
..
Sai bayan i'shai,ilham ta koma gida,kallo daya mamee tayi mata ta dauke kai,bayan ta gaida mameen ya haye sama tare da rufe kofar dakinta.
Dangin Alhaji Buba zun taho daga rugga....washegari su nufi gidan mahaifin mamee don neman yafiyarsa..
Daganan suka je gidan mameen,sun sami kyakyawan tarbo da basuyi zato ba,ta kuma yafe masu.

Zaune suke a dining chairs suna cin abincin dare,kararrawa ta fara ruri,gabaki dayansu suka juya suna kallon kofan,bkessing ce ta ruga zuwa bude kofan.
Bayan ta duba tagan wanda ke tsaye,sai ta dawo ta sanarwa mamee mutumin nan ne da rako abba ranan.
Nan ilham ta dubi mamee suka hada ido,dauke kai mamee tayi ta ci gaba da cin abincinta.
GANin mamee bata da niyar yin magana,yasanya ilham ta mike a hanzarce ta nufi bakin kofan.
Murmushi ta shiga yi masa tareda bashi izinin shigowa.
kai tsaye gun dining ta nufa dashi,ta jawo masa kujeran da ke kallon nata,gefen sa kuma mujaheed ne,sai da yayi sallama sa'anan ya zauna.
Ya'yansa kawai suka amsa masa sallamansa,ban da mamee.
yana zama ilham ta dauki plate ta zuba masa abinci,ta ajiye a gaban sa tareda fadin bisimillah..
Mujaheed ya mike,ya dan matsa kadan tare da fadin kowa ya dubeni...kuyi murmushi zanyi mana selfiee.
Gaba dayansu suka dubeshi dauke da murmushi a fuskarsu...

Bisimillah baba....ilham ta kara fadin,ganin bashi da niyar cin abincin.

Gyaran muryan yayi yace alhamdulillah,ban sani ni zaki zubawa abincin ba ,da nace karki zuwa domin kuwa a koshe nake.
Daman nazo ne na sanar dake,zani rabu da hajiya zubaida,kuma inason duk wani abu nasu dake gurina ,ko gurin wani nawa na maida masu.
        Ban manta ba mahaifinta ya tura makudan kudi a lokacin da aka kawo masa tallan wannan kafanin....ina fatan kina da masaniyan inds kudaden suke don haka inason ki taimaka ki mika min wannan kudin na hada na maida masa.

Kai ta shiga girgizawa....kayi hakuri baba,banason nayi jayeya da kai,duk wani abu da saka sanya ni yi a shirye nake da nabi dokar ka.... don Allah baba ka fadi wani abu da kake son nayi maka banda wanan..sabida baza ni maida masu da wannan kudin ba
Kallonta yake yi"sabida me?
Sabida na ta'ba kudin....
Wannan bai ds matsala,zani yi kokarin ganin na maida wanda kika ta'ba,sai ki bani saura....
A'a baba..! Kayi hakuri,kudin nan ba ta koma hannunsu ba, kuma shine a matsayin ko nace shi zai fanshi rashi ko nace raba mu da tayi da kai..ni da kannena zamu raba kudin.

KAR kiyi haka ilham........nayi alkawarin zani kokarta,don ganin na share maku ababen da suka faru a baya.,ya shiga lallashinta da maganganu masuvratsa jiki.
Kuka ta saka..."kayi hakuri baba,don Allah karka tilasta ni da na maida wanan kudin, besides wannan kudin baya kasar nan,sa'anan wadanda suka tayani aikin a lokacin na biyasu,don haka Kadan ya rage...
Tana kaiwa nan ta mike ta haye sama.
Tsaye take a jikin windon dakinta tana jiran fitowarsa...ta jima a gun sa'anan ta hange shi ya fito tareda abba da mujaheed....
ajiyan zuciya tayi"kayi hakuri  babana,bana son na sa'6a maka....

Cikin satin nan Alhaji buba ya aikawa hajiya zubaida da takardan saki.Tashin hankali..🤔..

A cikin satin kuma ilham ta soma shirye shiryen kimawa makaranta,tana me takaicin yanda plans dinta ke rushewa....
Mamee ce tayi sallama ta shigo ta samu guri ta zauna tana me duban ilham har sai da ta tsargu.
"Kiyi hakuri ilham,ki bi maganar mahaifinki ki maida masu da kudin su...nan mamee ta shiga lallashinta tana me yi mata nasihohi.,kuka ta shiga yi nan ma.

A kwana a tashi yau saura kwana uku ilham ta tafi.
Ta gama aikace aikacen ciki gida,ta shirya ta nufi gidan su Amarah, daganan suka kwashi jiki zuwa gidan su nazeeha wace tunda sukayi hutu ta tafi garin su bata dawo ba sai yanzun da zasu koma makaranta.
nazeeha ta tausayawa ilham sosai jin ababen dake faruwa da ita bayan tafiyarta,nan ta shiga lallashi tare da karfafa mata gwiwa..da haka sukayi ta shawarwari da hira irinta kawaye.

Yan'uwa da abokan arziki sun yo rakiya.
A airport ilham ta tarar da nazeeha da Amarah,tare suka tafi gurin screening,bayan da an tabbatar da basu dauke da miyagun abubuwa sannan aka basu damar tafiya.

5:02 suka dira a babban birnin tarayya ta kasan landon,sikin farin ciki suka jawo jakunansu zuwa gurin screening, sai dai me, jakar ilham taki tafiya,hakan na nunin jakar na dauke da wani abu...don haka polisawa sukayo caa suka mamaye gurin domin enjinin na ta wata kara.
Bude jakar sukayi,ba su wani je da nisa ba,sukayi karo da cocaine.
Nan suka kama ilham suka tafi da ita station dinsu.
Tashin hankali da rudani sun ziyarci nazeeha da Amarah, yau wai abinda suke ji suke kallo a t.v shi ya faru da aminiyarsu.
nazeeha ta dubi Amarah tace "ki tafi makaranta da kayan,ba'ra na bi na gan wace police Station din zasu tafi da ita.

Toh nima dai nazeehan zani bi,don ganewa idona yanda za'a kwashe...kuma ku biyoni,mu bi nazeeha,ko bi Amarah zuwa makaranta

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.