Pages

Thursday 10 May 2018

PAGE 41,OF SOYAYYAR MU👫

*SOYAYYAR MU👫*
         By Ganarious.
Page4⃣1⃣

        **         **        **
Har cikin ransa yake jin kukanta, ji ya'ke kamar ya tashi ya rungumeta ya lallashe ta,sai dai ba hali ganin mamee da Babanta.
Su mamee kuwa,idanuwansu sunyi jajir,sai tunanin zuci su kai.
Ganin gari ya fara duhu,ya sanya Baban mamee lallashinsu, yana me yi masu nasihohi,daga karshe yayi wa margayiya addu'a sannan suka tafi....
Daga mamee har ilham basu runtsa ba a daren ranar, kowa da abinda yake rayawa a ransa.

Washegari bayan Hisham ya gama waya da ilham ya tabbatar tana lafiya,ya mike tare dayin wanka ya shirya..kai tsaye gidan kakaninsa ya nufa.
Yana shiga yayi karo da Baba yusuf...
Da sallamarsa ya shiga,wanda maimakon baba yusuf ya amsa, sai ya shiga yayyafa masa masifa,zaginsa yake sosai cikin da'ga murya...ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,tashin murya sa ne ya fito da malam Lamido(kakan Hisham)...sai da malam Lamido ya baiwa baba yusuf hakuri sa'anan ya sassautawa Hisham.
sai bayan yayi shiru sannan hisham ya risina yana gaida su, nan ma bai amsa ba.
Malam Lamido ya amsa tare da tambayarsa lafiyarsa kuwa?...kwana hudu kenan ,muna nemanka,babu kai ba labarinka hakan yasa hankulanmu sun tashi, gashi kuma ba'a samuka a waya...ina ka shiga??
Kuyi hakuri...tafiyace ta kami ni ba zato,kuma inda na tafi din babu network..shiyasa ba ku samu na a waya.
yana kaiwa nan Goggoji ta shigo..tana ganin Hisham ta shiga yiwa Allah godiya, da farin cikinta ta shiga tambayarsa abinda ya faru.
Hisham dan lelen Goggoji,cikin kankanin lokaci ta hada masa abinci kala kala..ko wani idan ta shigo ta ajiye a gaban sa sai ta ta'ba shi ko tace me kake so dan nan?
shi ko a takure yake,duk ya matsu ya gan wucewar Baba yusuf..
Suna a haka wayar Baba yusuf ya shiga ruri.
Farin cikinsa ya bayyana ganin Baba yusuf ya mike,yanai wa malam Lamido sallama.
Ya kai bakin kofa sai kuma ya dawo,yana me nuni Hisham da dan yatsa"karfe takwas yayi maka a gida na,katin gayyata suna gu na,don haka ka zo ka amsa."
Toh ya fada...a yayinda kirjinsa ke bugun uku-uku...ba abinda ke zuwa masa a rai,sai amincewan da ilham tayi da aurensa.
Mikewa yayi ya nufi inda goggoji ke zaune, tana kwa'don zogale..ganin Hisham na sanya ta farinciki,don haka ta shiga yi masa murmushi a yayinda take mika masa kujeran zama...."ka gaji da jira ne ka biyo?

A'a .....wata magana nake son zamuyi da ke.

Toh..toh ango.
Shagwabewa yayi.."gaskiya da wace nake son na aura,don Allah kar su tilasta min auren wace bana so."

Ta kwantar da murya tace 'idan baka so toh babu me tilasta ka....

Zaki tsaya min kenan?
Kai ta daga..."kwarai kuwa dan nan,mud'din ina raye,ba bu me saka dole.
Ya mike ya rungumeta tareda sumbatar ta a goshi."Allah shi bar min ke"
Ameen,ta fada tana dubansa.

Ya koma gun zamansa ya zauna,yana me sosa keya....."yauwa goggoji, hummm kinsa tun tasowa ta da girmana ban taba rokon ki wani abub ba ko?

Shiru tayi tana dubansa,sai can  tace "toh fadi, me kake so yanzun?
Kujerar sa ya matsar gab da nata "so nake don Allah ki gayyaci duk'kanin dangin mu zuwa wannan gidan ranar asabar, masu mata kuma su zo da matan su.
Da mamaki goggoji ke dubansa "akan wani dalili?

Wata muhimmiyan sanar wa ce ta taso,don haka kar ki samu damuwa,ki gayyatou su kawai.

Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin "toh shi kenan,na yi yanda kace din.
Cikin farin ciki ya sanya hannu cikin aljuhunsa ,dubu goma sha biyar ya fid'do, gashi ki sayi goro.

"Kai dan nan....ina kake samun kudi ne?
Keya ya shiga sosawa a yayinda yake kokarin mikewa..."zan fada maki,idan na sake dawowa.

Daga nan,gidansu ilham ya nufa.
Ya dade tsaye yana matsan kararrawa,ba'a bude masa kofa ba.
Ya taka zuwa gun megadi yana me tambayarsa "mutan gidan na ciki kuwa.?

Eh toh....hajiya dai bata nan,amman ina da tabbacin ilham da me aiki suna ciki.
Godiya yayi...sa'anan ya ciro wayarsa don yayi kiran ilham.
A dai-dai lokacin kiran ke shiga,suka ji horn,ya juya yana duban gate a yayinda me gadi ya ruga zuwa bude gate din

Motan mamee ce ta kunno kai,ilham ce ke tukin gefenta mujaheed ne,sai mamee da abba da ke zaune gidan baya.

Bayan motan ta tsaya,ya nufe su.
risinawa yayi don gaida mamee.
Abbane ya fito cikin hanzari ya makalkale shi.
Ya mika wa mujaheed hannu sukayi sallama,yana meyi masa barka da isowa.
Ya kai kallonsa ga gimbiyar sa,wace tunda ta fito daga motan shi take kallo.
Gira ya da'ga mata ba tareda yace mata wani abu ba.
lokaci daya suka shiga falon su duka,sai dai mamee ta riga su shigewa.
Kalolin abincin da blessing ta shirya basu kirguwa,mamee ce ta bada ordan da tayi su mussamman domin tarbon mujaheed...don haka ta shiga jero su a  tsakiyar falon domin kuwa dining table bai daukan su.

MAmee ce ta mike,ta shige dakinta, bayan da sun gama ciye-ciye, da shaye -shayensu.
Shima mujaheed ta tashi ya nufi dakinsa,don hutawa.
Ilham da Hisham sai abba ne a falon.
Wayar ilham ce ta shiga ruri,ta sa hannu ta janyo jakarta,ta ciri wayan.
Ganin me kiran yasa ta yin dariya tana duban hisham,shima din ita yake kallo.
"Guess who the caller is"?
Uhmmm....u know I'm good @ dat, amman waye...
It's naaazeeee....
Dariya ya shiga yi,ya mike ya dawo gab da ita,"dauka ki sa a handsfree"
"Hey u darling"...ilham ta fada cikin muryan zolaya.

Mtsssssw.....r u tryinna make fun of me,wallahi i'll definately slit ur throat...fadin naziha daga dayan bangaren.
Naziha yusuf yareema,kawar ilham ce...a makaranta suka hadu,sun kulla abotane a lokacin da suka fahimci cewan a garin kaduna suke zaune,duk da nazeeha ba yar asalin garin bace.

Kafin ilham ta amsa,Hisham yayi karaf....."har kin gama fushin kenan?
Oh i see...abinda zaka fada kenan?.
Nan nazeeha ta kashe wayarta ba tareda ta jira abinda zasu fada ba.
Dariya suke yi....'i cant wait to see my darling,nazee" fadin ilham.
Yaushe zata dawo ne..
May b sai hutu ya kare.....

Sai bayan sallan i'shai Hisham yayi masu sallama,har zuwa gun motan sa ilham tayi masa rakiya,nan yake shaida mata ranar asabar danginsa zasu hadu a gidan kakaninsa,da yardan Allah
Cikin farin ciki,tace Allah shi kaimu.

       ***        ***      ***
Ranar asabar bayan sallan asubahi ,daga masallaci Hisham ya garzaya zuwa gidan kakaninsa.
A saman dakali ya tarar da inna,mahaifiyar mamansa Binta,ya gaidata,tare da tambayarta goggoji.
"Tana daki,ta maida masa.
Ya tarar bata dakin nata,sai dai dakin cike yake da danginsu na rugga...wasu na bacci wasu kuma idon su abude,don haka ya gaida su sa'anan ya fito ya nufi cikin gida,inda yake sa ran ganin goggoji.

Zaune take tana wanke wake,da alama kosai take shirin yi

A hankali yake taku,ba tare da ya bari taji takunsa ba....har ya iso bata san da zuwan sa ba,don haka ya sanya hannuwansa ya rungumeta,tare da sumbatar gefen kuncin ta.

Kai...kai.....da sassafen nan?
Dawowa yayi gabanta "ya akayi kika san cewan nine?
Sabida duk fadin duniyar nan,babu me sumbatata,idan ba kai ba...don haka ko cikin mafarki naji an sumbace ni,toh lallai kai ne.

Dariya ya shiga yi"har a mafarki fa kikace?"

Kwarai kuwa dan nan.
Ya dora hannunsa bisa kafadarta tare da kwantar da kai,"kin san me?

A'a dan nan, sai ka fada.
Ko kin san da cewan wannan sumban da nake yi maki shi ne jigo da kuma karfafa soyayya da shakuwarmu?...a duk lokacin da zani sumbaceki,zaki ji soyayaar da kike mun ya karu.na kasance ina sumbatarki tun ina dan karami,hakan yasa soyayyarki a zuciyata ta bambamta da ta sauran dangi....bani da kamar ki,har cikin raina nake jin ki fa....kuma na san da cewan a gunki ma haka abin yake.

Haka abin a dan nan,....a koda yaushe soyayayrka na da'da karuwa ne....bani da kamar ka duk cikin ya'ya da jikokina.ban baiwa kowa matsayin da na baka ba....don haka inai maka fatan alkhairi a kodayaushe,Allah shi albarkaci rayuwaka.
Ameen ya fadaa.

TOH yanzun me ke tafe da kai da sanyi safiyar nan?
Hummm....na zo duba ki ne kawai,na so zuwa jiya, amman Allah bai nufa ba,shi yasa nayi maki sammako don da ke na kwana a rai na...
Na kuma kawo maki lemuka da zaki baiwa baki.
Toh.....ta fada a takaice.
Ya bakin? Ya sake tambayawa....
Lfiya lau,kusan dukan dangi sun zo,yan cikin gari ne ba su isowa,suma ina sa ran isowar su zuwa nan da dan lokaci.
Allah shi kawo su lfy....ya fada yana shafan fuskarsa da hannayensa.
Ni zani tafi,sai zuwa anjima zan sake dawowa.
To shi kenan,Allah shi tsare min kai.
Ameen ya fada a lokacin da ya soma tafiya.

Yayi taku kamar biyu zuwa uku,sai kuma ya dawo, "ba wani abu da kike bukata?
"A a ....
Yayi murmshi...ba kuma wata matsala ko?
A a dan nan, babu sai su kawunka da suke haukan banza,wai ala dole na fada masu dalilin tara jama'a

Kar su damu,saura kiris..
Ya maida mata.
Yana fitowa daga cikin gida ya yi kiran ilham a waya,bugu daya ta dauka.

Albishir yayi mata,ya sanar da ita burin zai cika, don haka bayan sallan azahar ta shirya zai zo ya dauketa.
Bayan sun gama wayan tayi ajiyan zuciya,tana me kara tausayawa babanta  wanda soyayyarsa ta mamaye zuciyarta,tun bayan da tasan abinda haj.zubaida da mahaifiyarta suka aikata akansa.
Tana matukar tausaya masa da danasanin kuncin da ta sanya shi,duk ta karamar lokaci ce.
ta mike tana me tunanin ko ta sanar da mamee abinda take shirin aikatawa...
Kaita girgiza...nop,mamee baza taje ba,ko ta tafi zata batamin tsarin abun.
Dakin mujaheed ta nufa,rubuce-rubuce ta tarar yana yi,ta jayo kujera gabansa
"Me kuma ake rubutawa"?
Kin mance ni young scholar ne....ya tattara takardun ya maida gefe.
Ya maido hankalinsa gunta "da magana ko"?
Kai ta da'ga ,ta sa dan yatsa ta share hawayen da suka tarun mata a ido.
Cikin yanayin tashin hankali yace "whats wrong"?
Ka shirya zamu tafi wani guri,tana fadin haka ta mike.
mikewa yayi ya sha gaban ta..."whats wrong"?
Zanyi maka bayani idan mun dawo.
Daga dakin mujaheed,dakin mamee ta nufa, kwance suke ita da abba.
A sanyaye ta haye gadon ta shiga tsakanin mamee da abba.
A duk lokacin da ilham da hau bisa gadon mamee toh tabbass da abinda ke damuwarta,ko idan bata da lafiya.

Ganin haka ya ss mamee ta juyo tana dubanta...."ya ya dai? Ta fada.
Ta sa dan yatsa ta share hawaye...."hajiya zubaida ta cuce mu! A sanadiyarta mun rasa kulawa da soyayyar uba.

HAnnunta mamee ta rike"ki daina fadin haka,ki sawa ranki haka Allah ya rubuto zai faru da ku..duk da na fahimci abinda kike nufi,amman fa karki wasu suna tare da iyayensu,ko nace mahaifinsu kuma basu sami gata,tarbiya so da kulawa irin wanda kuka samu ba.a duk lokacin da na gan ki kina kukan rashin uba sai nake ganin kamar baki gode da fadi tashi da nayi da ku ba...nayi iya yi na don kar kuyi rayuwa maraici did i not try?

Rungume mamee tayi ta shiga rera kuka.."kinyi kokari sosai mamee,Allah shi kadai zai iya biyan ki,please kiyi hakuri ba zan sake fadan haka ba...

NO..no...na fahimce ki namesake,just that inaso kema ki fahimce ni,bani son wannan feelings ya zama part of u..u understand.?
Kai ta da'ga..na gane mamee bazan sake ba.

DA haka mamee ta dunga bata magana da nasihohi masu ratsa jiki tana kuma bata misalai,suna haka mujaheed ya shigo da sallamarsa.
Ganin yanayinsu yasa shi karasowa saman gadon.
Daya bayan daya yakebduba fuskokinsu....whats happening here? Ya fada
Ilham ce ta mike tana tayarda abba daga baccinsa...tashi ka shiga wanka ka shirya zamu fita.
Ya mike cikin gigin bacci ya fada bayin mamee.

Bara naje nayi wankan,nima.
zo mana.....mamee ta fada a yayinda take kallon ilham cikin ido.

TA dawo ta risina gabanta....
"Kina ganin bani bukatan sanin wani abu?
ta murmusa,domin kuwa tasan inda maganar mamee ta dosa.
"Kinsan bani boye maki komai,inason zamu fita da kannena,idan mun dawo inn'shaa'Allah zan sanar maki.
Shikenan Allah ya tsare.
Ameen ta fada tare da ficewa daga dakin.

Bayan da ilham ta fito wanka ta da'de tsaye gaban wardrob dinta ta na me tunanin kayan da ya dace ta saka don  birge babanta....amman kuma kayan ya zamana very simple.
Ta ciri kaya sunfi a kirga,duk basuyi mata ba...don haka ta maida su.tare da yanke shawaran zuwa gun mamee don tambayar ta wacevirin kaya take sakawa ta birge mahaifinta.

A gaban wardrob ta tarar da mamee tana nemawa abba kayan sakawa,shi ko abban akwance yake lullube cikin bargo.
Tayi tsuki sai dai be fito ba tana me karasawa gun mamee a dai dai lokacin ta ciro kayan sawansa.
Mamee..! Ilham tayi kira.
Ba tareda ta dube ta ba ta amsa.
Wani irin kaya kike sakawa lokacin baya ki birge mahaifinmu?

Bazani iya tunawa ba...ta amsa a yayinda take taimakawa abba don ganin ya saka riga.
Ilham ta dade tsaye tana duban mamee daga bisani ta juya ta koma dakinta.
Doguwa riga ce tayi karo dashi,yana daya daga cikin dogayen riguna da tayi ordering daga *GANARIOUS CLOTHING*,Bayan da ta kammala shirinta ta sauko kasa,nan ta tarar da mujaheed da abba,fitowar ta kawai suke jira.
Mu tafi ko?.....ta fada tana dubansu.

Har sun kai bakin kofa sai kuma ta dawo ta nufi dakin mamee.
.......mamee don Allah ki bamu aron motanki.
Kai ta girgiza,ba tareda ta dubi inda take ba.
matsawa tayi kusa da mameen..."please mana mameen mu.
A'a nace,nasan tukin ki,idan ba ina cikin mota ba ba amince maki tukawanshi ba.
Please mamee i promise zanyi tuki cikin natsuwa...
a'a nace,ta fada a fusace..
Nan ta mike jiki a sanyaye ...tana kaiwa baki kofa ta juyo sukayi ido hudu da mameen,nan ta marairace fuska.
Mamee ta yi mata nuni da gaban madubi..ma'ana ta dauki makullin.
"Becareful" ta fada.
"I promise "ta maida mata cikin farin ciki

Suna fita tayi kiran Hisham,ta fada masa ba sai ya zo daukan su ba.
Kasuwa suka nufa, nan tayiwa mahaifinta shopping,daga kasuwa suka tsaya a gidan su Amarah...
Amarah kawar tace da suke karatu tare,nan sukayi sallan azahar,sa'anan suka tafi gidansu Goggoji.

Jingine yake a jikin motansa,sai duban agogo yakeyi.
Daga nesa ta hango shi, ta murmusa a ranta tace "isowar mu kake jira"

Yana ganinsu ya nufe su, gefen abba ya je tare da bude masa murfin motan.
"Laah.Ya'Hisham kai ma ka zo ashe".
Eh...ai nan ne gidanmu.
Wannan mutumin ma nan ne gidansu?

Eh...idan ka shiga zaka ganshi.
Tsale ya daka'naji dadi'

TA backyard suka shiga cikin gidan,a lokacin kowa da kowa na babban falon gidan.

Dakin goggoji suka shige,nan ma ba kowa...don haka hisham yashiga falon yayi kiran goggoji gefe don sanar da ita isowarsu ilham..... ya kuma sanar da ita ilham ce son magana da yan uwan.
Cikin mamaki tace "kai dan nan,wata irin magana ce da sai an tara  jama'a har daga rugga?
Nan ilham ta matso,ta rikewa goggoji hannu "kiyi hakuri,so nake su ji maganar daga bakina.

Toh shikenan ,ku biyo ni mu tafi falon.
A' a ki fara zuwa a bude taron da addu'a ,bayan nan sai ki sanar da su yaran Alhaji Buba ne ke son magana.
Shikenan,bara na shiga na sanar da su.

Jama'a mabiyan wannan labari,ina me baku hakuri....don Allah kuyi hakuri kuyi min uzuri,inn'shaa'Allah zani yita kokari kawo maku sabuwar page.
thanks.🙏🏼🙏🏼

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.