RIKICHI
Episode 4
By Aisha Gana (Ganarious)
||if you're interested in the continuation of SOYAYYAR MU, please send a message to ganarious98@gmail.com thank you||
Ciwon kakan mu yaki ci, ya ki cinyewa. Gashi ba wanda ya taimaka masu cikin yan' uwa ko mutan gari.
Sun nemi taimako har sun gaji. Haka yana matukar bakantawa Hajiya Asabe rai, sai ta kuma fara rayawa a ranta, cewan akwai sa hannun mutane. Daga nan kuma duk wayewar gari sai tayi ta maganganu,tana bace bace.
Tafiya tayi nisa, anzo lokacin da abin ci yake gagaran su a gidan,duk da manya ya'yan sun mike da nemowa!
Shekarun mahaifinsu hudu a kwance, sai ranar wata alhamis ,da yammaci yace ga garin ku nan.
Rayuwar yunwa da talauci su abba suka tsinci kansu da shi. Yayunsa mata da kannensa, suk wace ta sami miji ba ta bata lokaci.... Mazan kuwa ko wannensu ya dage da nema, daga mai zuwa yin dakko, sai masu tura baroo da dai sauran su.
Abban mu na cike shakaru Ashirin, ya shiga garin minna nemawa kansa aikin. Cikin nasara kuwa ya sami aikin wanke motoci, sai dai shi a gidan mutumin da ya dauke shi aiki zai zauna sabida mutumin ya bukatan a wanke masa mota ko wace safiya kamin ya tafi aiki.
Alhaji yunus, shine wanda ya dauki Abban mu aiki, matar sa daya da kuma dan su kwaya daya tak! Alhaji yunus mutun ne me kirki da daraja dan Adam.
Idan me karatu zai gan yanda yake wasa ya kuma sakewa abba ka ce ko dan'uwan sa na jini ne!
Nan da nan abba ya goge kamar ba shi ba. Tou yana samun lafiyayar abinci ga kuma kwanciyar hankali.
Albashin abba naira hamsin ne a lokacin (A lokacin kudi na da darajansa), bayan albashin, su suke ciyat da shi, su kuma tafafar da shi. Haka idan anyi hutu za shi ganin gida, matar alhaji yunus zata dibi kayar sawan ta, da na dan ta hade da na alhaji yunus din ta bawa abba ya kaiwa yan uwan sa! Ba kaya kadai ba har da su mayukan shafawa, sabulai da dai sauran su.
A duk lokacin da me koyar da dan Alhaji yunus ya zo, sai abba ya dauko littafi shima ana koya ma shi.
Da Alhaji yunus ya lura da hakan sai ya tambayi Abba ko yana da ra'ayin karatu ne, amma yace eh, inason karatu sosai, sai dai hakan bazai samu a rayuwata ba!
Sabida me? Alhaji yunus ya nemi sani
Cikin sosa ke ya abba yace sabida shekaru na oga!
No! Shekaru ba za su taba hana ka karatu ba, idan dai kana da ra'ayin karatun ni me taimaka maka ne!
Nan abba ya nuna farin cikin sa, tare da fadin ya amince, zai yi karatun.
A cikin satin nan, Alhaji Yunus yai masa komai na makaranta. Sai da abba yayi kwala, sabida farin ciki, da kuma godiyar Allah da ya hada shi da mutun irin Alhaji yunus.
Abokan Abba da suka ji labari, dariya sukai ta yi masa, wai bashi da hankali.
Abba na akwai kaifin basira, duk da shekarunsa, kwakwalwarsa tana da kaifi. Ganin kwazon abba ya sa Alhaji Yunus yana ta tsallakar da shi daga wannan ajin zuwa wancan aji. Don haka shekaru biyu da rabi abba yayi a primary.
Da taimakon Allah da taimakon Alhaji yunus abba ya gama secondary cikin kankanin lokaci, yana gamawa Alhaji Yunus ya nema masa aikin yi ya kuma nema masa gida.
Bai jima da fara aikin ba suka maida shi portacort, yana aiki kuma yana zuwa makaranta watau university kenan.
Cikin kankani lokacin Allah ya Azurta abba. Hakan ko bai sa ya manta yan'uwansa ba, duk bayan kwana biyu yake yi masu aike, ko kuma ya zo da kansa.
Abba ya gina masallatai, ya gyaran gidan su, yayi kannesa maza gida sa'anan matan ya basu jari.
Ganin haka ya sa mutanen gari kawo masa tayin ya'yansu.
A portacourt din abba ya hadu da "Hafsat"
A ranar wata asabar, da sanyi safiya abba ya fito zai tafi gun aikinsa, sai ya hange ta saman keke, da alama tana motsa jiki ne. Tana isowa dai dai gun sa ya tsayar da ita, bayan gaisuwa bada bata lokaci ba abba ya shigar da kansa domin kuwa idon sa na kaiwa kanta ya ji babu wace yake so sai ita.
Murmushi tayi masa, hade da fadin zanyi tunani.
No comments:
Post a Comment