Pages

Tuesday 25 September 2018

Page 57 of soyayyar mi

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page 5⃣7⃣ √... Visit ganariousblogspot.com/ for the latest release. ** ** ** Wata sa'in yakan so ya fahimtar da zuciyarsa da cewan "ai duk laifin ta,duk itace ta sayawa kanta abinda ke faruwa da ita, amman wata bangaren zuciyarsa kan ki amincewa da haka. Duk kokarin da yake yayi wa su naziha bayani a banza sabida sun ki su bashi daman haka, daga baya ma cin mutunci Amarah take masa. Hakan kuwa ba karamar batawa abokansa rai yake ba, sona jin haushi da takaicin abokin su. Ganin bashi da mafita, duk inda yabi a toshe ya sanya shi zuwa ga Dr. Abdul'Afeez yayi masa bayani komai ya kuma shaida masa iham ta daina zuwa lectures. Ya nemi alfarman da Dr. Abdul Afeez ya taimaka masa yayi kiranta ta don ya bata hakuri. Nan dr. Abdul Afeez yayi masa alkawarin gobe da yardan Allah zai kira ta. Washe gari Dr. Abdul'Afeez yayi mata aike. Da farko ta so tayi biris da kiransa, amman ganin yanayin da su Naziha suka shiga damuwa suna fadin zata jawo kanta wata matsalan yasa ta amince da zuwa amsa kiran. Su Naziha sun rako ta har cikin office dinsa. Sun jima tsaye bai bi ta kansu ba, nan Amarah ta ji haushi ta juya zata fito. Come back here, ya fada fuskan nan nasa a murtuke. Ta dawo tayi tsaye. Nan ya shiga yarfa masu bala'i, yana me ganin laifinsu cewan su suke zuga ilham ta daina zuwa lectures domin kawai su cutar da ita. Nan suka shiga rantse rantse suna fadin "wallahi ba laifin mu ba ne" Bayan ya gama yi masu fada, ya koma yayi masu nasiha sa'anan ya sallame su amman banda ilham. Nan ya bar ta zaune ba tareda yace mata uffan ba. Sai da ya gama yan rubuce rubucensa sannan ya dauki wayarsa yayi kira. Jim kadan aka bude kofa tare da sallama. Tana juyawa suka hada ido, don haka ta kauda kai. Bayan ya gaida Dr. Abdul'Afeez ya bashi izini da ya zauna. Bayan ya zauna Dr. Abdul'Afeez ya shiga yi masu Nasiha mussam ita ilham, yana cikin magana wayarsa ta soma ruri ya daga yana amasa kiran. Da alama ana nemansa ne a wani gurin don haka ya mike. "toh ni yanzun ana jira na ne, don haka gaka ga ilham...duk na san baka da laifi a abinda ya faru, amman kuma kana son bata hakuri, don haka ka bata hakuri ku sasanta juna kafin na dawo.. Yana fita Ameer ya matso da kujerar sa, yana facing na ta. Kafin duk ya bude baki da niyar yi mata magana, ta tofa masa yawu... A hankali yasa hannunsa ya goge,ya dube ta tare da fadin kiyimin duk abinda kika gan dama, kiyi abinda ya fi wannan idan har zaki ji sassauci a ranki, ki kuma yafe min please. Kallonsa batayi ba, balle ta saurare shi. Hakan ya bashi damar saukowa daga kujerar sa ya duka a gabanta. 'ya ke Aisha ki gafarce ni, wallahi bansan zanyi hurting dinki hakan ba, tunda nake a rayuwata ban taba sa wani ko wata yayi hawaye ba shiyasa na kasa rasa sukuni ganin kin zubda hawaye sabida ni....please kiyi hakuri ki yafe min. Ganin bata da niyar yin magana ya ci gaba da fadin "please dont skip your lectures all because of me, i feel guilty." ya cigaba da rokon ta,. Sai shesshakar kukan ta kawai ya ji, nan ya shiga rudani, ya ma rasa abinda zai yi ko fadi " i hate you, i hate you ta fada tana dubansa. Bazan ta'ba yafe maka ba, da ka sauya min halayena....i hate you ta kara fadin Ido kawai yasa mata,sabida kukan ta ya dagula masa lisafi. Suna a haka Dr. Abdul'Afeez ya shigo tare da wani, don haka ya sallame su . A tare suka fito daga office dinsa , da sauri su ilham tare da nura da abokansa suka nufo su. Ganin yanayinta ya sa Nura shan gaban Ameer "me kayi mata? Ba tareda Ameer ya amsa masa ba ya nemi da ya kauce,nan ma Nura ya sake shan gabansa. Kai ku zo nan, murayn Dr. Abdul' Afeez suka ji. Don haka suka nufi gunsa gaba daya. Ya kai duban sa ga ilham, ban gama case dinku ba, amman sabida bakon da nake dashi yasa na sallame ku, don haka daga yau kar ki kara skiping lecturea infact kullum safe kiyi report a office dina sabida na san da zuwanki. Kina ji ko? Kai ta daga, tareda fadin yes sir. Ameer ya ji dadi sosai a ransa da jin abinda dr Abdul afeez ya fada, bashi kadai ba, harda masoyinta Nura da kawayenta.
Read More »

Page 56of SOYAyYAR MU

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page5⃣6⃣. √... Gaisuwa gareku makarantan ~SOYAYYAR MU~🤝🏻 √... Gaisuwa gareku mabiyan blog dina. √...fatan alkhair gareku yan'uwa maza da mata. *Don Allah a dunga hakuri da spelling errors, sentence errors,typing errors da dai sauran su*😎. A ko dayaushe zaku iya samu na a Ganarious98@gmail.com na gode. ** ** ** Guy wai me ke going on ne? Tunda ka fito da'ga kurkutun nan kake wani shiru-shiru, kana avoiding long conversations...me ke faruwa? Eh fa..! Ni ma na lura da hakan. Fadin yusuf Yayi ajiyan zuciya tare da fadin uhmmmm.....i don't know, i just know, i'm feeling guilty. Nan gabaki dayan su suka maida kallonsu gareshi. Guilty? Of what? Ahmad ya tambaya cike da mamaki. "Na sanya yarinyar nan a wani hali, da yanayi. A lokacin da na kyatta ido na gan hawayen ta, da ga lokacin na rasa sukuni a zuciyata, sabida nine sanadin hawayenta, nine sanadin sanya ta a halin da ta tsinci kanta. Image din hawayen ta na reflecting a ido na every second,nakan kuma tsinci kaina da jin zafin haka....i just dont know. Tsukin da yusuf yayi ya sanya shi yin shiru yana dubansa. Idan bak da reasonable dalili, toh kayi shiru. Atoh....inji Ahmad, ya kara da fadin ai wannan shedaniyar yarinyar bata gan komai ba tukun, sai munyi maganin ta a wannan makarata, she started a fight she can't finish.... Tun ba'a yi nisa ba ta soma hawayen makirci don a tausaya mata,a'a wallah yanda ta dauko yin yakin sai an kai karshe da ita. Dariya suka soma yi, a yayinda Ameer yake bin su da kallo ba tare da yace wani abu ba. ** ** ** Washe gari ta kama ranar laraba, a ranar kuma Ameer zai yi wa yan ajin su ilham lectures. Tun da sanyi safiya ya kammala shiryawa tare da yin kari, sa'anan ya nufi cikin makarantar. Dayan bayan daya yake duban dalibai masu shigowa suna kuma gaida shi. Har ya soma koyarwa bata shigo ba, bai kuma fidda ran zuwanta ba har sai da lectures ya kai karshe. Da haka ya koma hostel, yana me rayawa a ransa sai jumma'a kenan za ta zo. Ranar jumma'an ma bata zo ba. Ya tsinci kansa da rashin jin dadin haka..a ransa kuwa yana me fatan ba sabida shi bane take kin zuwa lectures. Kwanar ilham takwas a clinic, likita ya shaida masu 'stress' ne ya kawo mata hakan da shike jikin ta bai saba da wahala ko ta ciki ko ta waje ba. Asalima bata taba sanin menene wahala ba a rayuwa sai yanzun da ta dandana a kurkutu. Duk zaman da tayi a clinic ta kiyin magana da kowa. Idan su Naziha sun matsa mata da magana shine take fadin yes ko no, sai kuma daga kai shikenan. A ranar da aka sallame su suka koma hostel, Amarah ta zauna gab da ita. 'haba ilham....wai shin yaya kika dauke mu ne? Ba bu yanda bamuyi ba, da ki fada mana abinda ke damun ki.. Ciwonki, namu ne gashi kin barshi yana ta cin ki ke kadai, please ki fada mana abinda ke damun ki, ko bamu magance maki abin ba, atleast zamu baki shawarari. Nan fa Naziha da yusrah suka tofa Albarkashi bakin su suma. Kuka ta soma yi, suna lallashinsa. ""ina mamaki da kuma takaicin yanda na sauya hali cikin kankani lokaci. Ba ni da halin fada, bani da halin musgunawa mutun, bani da halin ramuwa, amman wai duk sun zama halayena yanzun. Na tsani yaron nan, na tsane shi.! Duk a dalilinsa na zama haka, bazan yafe masa ba a dalilin sauya min halayena da yayi... Ta dan yi shiru na lokaci, tana me sharan hawaye. Na yanke hukuncin barin wannan makaranta, sabida har ga Allah bazan rubutu masa wasikar ban hakuri ba... "zaki bar makarantan fa kika ce? Yusrah ta tambaya cikin yanayin mamaki. Zan bar masa makaranta, idan ba hakan nayi ba, bazan daina tunani ramuwan abinda yayi min, wanda a hankali halayena zasu sauya gabaki daya. Haba dai..! Sabida yaron nan zaki yi quitting schooling din? Nan fa suka shiga ban baki akan ta hakura da barin makarantan. Kusan sati na biyu kenan bai sa ta ido ba. Duk inda yake tunanin zai ganta yana bi da dube dube amman ko inuwarta bai hanga ba. Hakan ya sosa masa zuciya, ya na me fatan Allah shi sa ba a dalilinsa ta daina zuwa lectures ba. Yau din ya fito ne daga koyar da yan ajin su. Tafiya yake a hankali zai koma ajinsa, don daukan darasi. Kamar ance ya waiga, sai ya hada ido da su Naziha, da alama maganarsa sukeyi don har nunashi sukai da yatsa. Ya birki tare da juyawa zuwa inda suke zaune. "Assalamu alaikum......" yayi masu sallama. Fuskokin su a daure, ba tare da sun amsa ba, yusrah ta mike tana fadin 'ku tashi mu tafi ko? Nan ya sake yi masu sallama....."haba yan uwa? Sai kace ku ba musulmai ba? Kun kuwa san muhimmancin sallama kuwa? Yana rufe baki Amarah ta haushi da masifa kamar jiraye ta ke dashi. Banda kallonta ba abinda yake yi. "toh zata bar maka makarantan, burin ka ya cika ko? Ka ji dadi yanzun? Kallo daya zaka yi masa ka fahimci tashin hankalin da ya shiga karaf daya. Ya matsa gab da Amarah...." please dont tell me" Tsuki tayi tare da barin gefen sa "ku zo mu tafi" ta fada. Biye yake da su yana me rokon su da su tsaya su saurari abinda zai fada masa . Sai da suka kai bakin hostel, sannan ya hakura. Shit ya fada tare da rike goshinsa. A daren ranar Ameer bai runtsa ba....zancen zuci kawai yakeyi, yana ganin laifinsa. Shi daman a rayuwarsa baya son ganin hawayen mutun, especially mace. Bashi kuma kauna a dalilinsa ka shiga wani yanayi, shiyasa baya fada a rayuwarsa. Allah Allah yakeyi gari ya waye....don haka da sanyi safiya ya nufi hanyar hostel dinsu. Ya kai kimamin awa biyu tsaye idonsa akan gate din hostel, yana me duban masu fitowa. Yana hango su ya nufe su....."Assalamu alaikum. Yauma basu amsa masa sallamarsa ba. Don Allah ku saurare ni mana, da haka har suka shiga cikin makaranta yana biye da su. Kai...!wai ma kake so ne? Inace burin ka ya cika yanzun? Zata bar maka makarantan kamar yanda ka bukata? Nazhiha ce ke masa wannan maganar. Wallahi i never meant it....ni karan kaina banyi zaton abin zai kai haka. Itace ta dauke shi da zafi haka. I"'m very very sorry, please Yana rufe baki Nura tare da tawagarsa suka karaso gurin. Nan suka gaisa da su Naziha, cikin yanayin damuwa yace 'wai me ke faruwa ne, ilham bata da'ga wayata? I'm so worried gashi bata shigowa school, hope ba ciwon bane ya yi tsananii ko? Lafiyar ta kalau, tana neman hutu ne kawai yusra ta maidawa Nura. Sai a sannan ya kai dubansa ga Ameer "wannan pig din kuma fa? Me yake yi anan? Ya na fadin haka ne a yayinda da yake nunin Ameer da yatsa. Ohoo masa.! Amarah ta fada tana me hararan Ameer. Dan Allah ku zo mu tafi,nan suka watse suka barshi tsaye shi kadai. Daga wannan lokacin Ameer ya rasa sukuni. Ya rasa yanda zaiyi ya ganta domin ya bata hakuri.
Read More »

Saturday 22 September 2018

Page 55 of SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page 5⃣5⃣ ** ** ** ** ** Wasu da'liban sun rike ilham, a yayinda wasu su ke rike da Ameer, suna tausasa masa zuciya. A lokacin da ilham take kubce kubce wai ita ala dole su sake ta ta dambata dashi, a lokacin wasu malamai suka iso. Tsawa daya da'ga cikin malaman ya daka mata, sai A sa'annan ta natsu. "what is going on inn here? Ya fada yana duban ilham. Kafin duk ta amsa masa, fada ya barke bangaren inda Ameer ya ke a tsaye.... Ashe Nura ne ya shigo ajin rike da belt, yana hangen Ameer ya nufesa ya wasga masa. Nan abokan sa suka kama masa, ai ko kafin ka sani ajin ya rikice. A gaskiya Ameer yayi ta maza, su kusan shidda akan sa, amman sai da ya raunana wasu daga cikin su. Duk kokarin da malamai sukai don ganin sun raba wannan fadan, abin ya ci tura don haka sukayi kiran securities na makarantar. Cikin kankani lokaci labari ya cike makarantar. Labari na kaiwa ga Abokan tafiyan Ameer, suka fito a fusace ....." yau kam sai munyi maganin yan iskan nan" Suna isowa bakin ajin su ilham, sukayi karo da securities sun fito da abokan tafiyar Nura, da shi Nuran, da kuma ilham ciki har da abokinsu. Basuyi tsaya wata-wata ba, suka hau dukan abokan Nuran har shi Nuran ma. Securities sunyi kiran yan uwansu da su zo su tafi da abokan Ameer. Tunda aka jefa su a kurkutun makaranta, ba'a sake bin ta kansu ba.. Har sai washe gari. Shugaban makaranta, da sauran manyanyan malamai na kings college ne zaune a *special staffs meeting room*,inda suke sauraron wani malami wanda aka bashi mukamin *idon makaranta* (ma'ana duk abinda ya faru a makaranta shi zai kawo labari.) Bayan ya gama jawabinsa, a fusace shugaban makarantar yace a tafi a zo masa da su. Cikin kankani lokaci aka fito dasu, izuwa hall din. Ilham ce mace a cikinsu, idanun nan nata duk sun sauya, sun yi jajir ga girman da sukayi, da alama ta sharbi kuka. Ita ce ta fara isowa gurin tare da security mace. Dr. Abdul'afeez yana ganin ta ya mike tare fadin 'you again?? Yana rufe baki securities suka shigo da Nura da abokansa, da kuma Ameer da Abokansa. "All of them are blacks.! How rude..." fadin shugaban makarantar, har huci yake yana zagin su,yana tsaka da zaginsu idon sa ya kai kan Ameer. 'Abubakar'.....ya fada cike da mamaki a yayinda yake nuninsa da yatsa. Dnt tell me you among. Nan malamai suka shaida masa fadan ai nasa ne. Yayi kiran Ameer da ya dawo gabansa yayi masa bayani. Yana gama sauraron Ameer ya shiga zagin ilham, daga karshe yace gaba ki dayan su za'a kore su a makarantan, banda Ameer din. Ya juya ga Nura yana nunashi da yatsa....'maganar ka ta ishe ni a wannan makarantar, don haka za'a zauna da board managements akan ka, yazama dole kai da abokanka ku bar wannan makarantar....'i can't continue to keep people like you.' Ya dubi sauran malamai, yace za'a sake zama meeting akan su, amman kafin nan a maida su prison, amman ba da Ameer ba. No sir, that would be unfair, don Allah kayi hakuri bazan fita a gurin ba tare da abokaina ba...a dalilina suke gurin, don haka bazan ji dadi ba idan na fita, su aka rike su.... Ajiyan zuciya yayi yana duban Ameer 'shikenan.! Yanzun yaya kake son a yi? Ameer ya nisa yace a sake su , su tafi. Ni a bar ni a nan. Shugaban ya yi shiru na dan lokaci, sa'anan yace toh ayi yanda yake so din. An saki abokan Ameer suka koma Hostel, a yayinda aka komar da sauran. Hukumar makaranta ta hana kowa zuwa gunda aka tsare su Ameer. su Naziha sun yi roko, sunyi magiya akan a basu dama don su ga'nah da abokiyar su, sai dai duk rokonsu a banza sukayi sabida ko kallonsu securities ba suyi ba ballantana su saurare su. Da haka suka hakura suka koma hostel cike da tausayin ilham. Sai da suka cike kwanaki biyar a cikin kurkutun, sa'anan shugaba ya bada damar a fito da su. Bayan zaman shawar-wari da sukayi tsakanin malamai. Da kyar take da'ga kafar, kallo daya zakayi mata ka fahimci cewan a wahalce take. Duk da karfin halin da takeyi sai da tafiyarta ya dunga karkacewa kamar wace ta shaa, ta bugu. Itace aka fiddo karshe, don haka meeting hall ta tarar da abokan fadan ta. Tana shiga ta nemi guri ta zauna. Dr. Abdul'Afeez ya daka mata tsawa. 'would you get up and stand on your feet?".. Da taimakon securities ta mike. Hawaye cike da idon ta, a yayinda take mikewa. Bayan ta mike ta sanya dan yatsar ta tana share hawayen, tana janye yatsar tare da bude idon ta, ba zato sukayi ido hudu da Ameer.. Idanuwansa na dauke da sakonni wanda a lokacin baza ta iya gane ko na me nene ba. Ta kauda kai, a yayinda hawayen suka cigaba da bin juna saman kuncin ta. Dr. Abdul'Afeez ne ya soma jawabi akan hukunce hukuncen da ya dace su fuskan ta, amman sabida wasu dalilai an yafe masu, akan sharadin kowannensu zai yi rantsuwa da alkawarin ba zai sake sa'bawa dokar makaranta ba, idan kuma haka ta faru duk abinda makaranta ta yanke masu su, suka saya... Bayan nan malamai suka shiga baiwa ilham shawarwari a yayinda wasu suke aibanta halin ta suna fadin itace silan abinda ya faru. Sun kuma umurce ta, da ta rubuta wasikar ban hakuri kala uku. Daya zuwa ga malamai, daya zuwa ga shugaban makarantat, daya zuwa ga Ameer.. A lokacin da suke tofa albarkacin bakinsu duk akanta wata sabuwar kuka ta zo mata.sai sharan hawaye takai....... Jikin ta ya raya mata ita kadai ake kallo, amman ta kiyasta akwai wani me kallon ta wanda shike a dalilin tsareta da idonsa ta kasa dagowa. Naziha tareda Amarah da yusrah tsaye dan ni'sah da meeting hall. Fitowar ta suke jira. Suna nan tsaye idon su kan kofar hall din, suka hange ta tana fito wa. Da gudun su suka karasa gun ta,suna tamabayar lafiyar jikin ta. Kuka ta saki, me ratsa jiki kuwa. Su ma din nan da nan jikinsu yayi sanyi, nan suka shiga lallashin ta. Tare da kama hanunta suka nufi hostel. Ruwan wanka suka soma hada mata, sa'anan suka taimaka mata tayi wanka. Hidayata wace suke daki daya,ita ce ta fiddo mata da kayan sawa. Bayan nan suka shirya mata abinci, da kyar da kuma magiya ta ci abinci. Tana ci, tana hawaye. Ba wace ta nemi da ta san dalilin kukan ta, duk jikinsu ya mace sai kallonta sukeyi suna tausaya mata. Tana tsaka da ci, ta mike a guje, toilet ta nufa inda ta dunga amai. Sannu ilham...."sannu kinji ilham! Shine kawai abinda ke fitowa a bakinsu. "wani gurin na maki ciwo ne? Fadin Amarah. "jiri nake gani..... Nan suka taimaka mata, ta kwanta, ba'a fi minti hudu da kwanciyarta ba, jiki yayi zafi. Suna jin haka suka nufi school clinic da ita inda aka basu gado.
Read More »

Tuesday 18 September 2018

Page 54 of soyayyar mu👫

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page5⃣4⃣ √... Special greetings ga masu patronizing blog din, ina godiya. √... Mss_Ganarious, a instagram. √... Ganarious98@gmail.com don korafe korefe. ** ** ** Mutan kontagora, one love keep us together.💞 Ex_students especially (2009 graduates) ta G.G.U.S.S Bodinga, sokoto state,ina mika gaisuwata gare ku. ** ** ** Bayan sallan isha'i suka hadu gurin zaman su. Ko kunsan abinda shaidaniyar yarinyar nan tayi yau? Wa? Mutuniyar ka? Idan ba ita ba toh wa, nan ya kwashe yanda sukayi da ilham ya sanar masu. Ya kara da fadin Allah ya taimake ta, ta fita a ajin, da abinda zan yi mata har mutuwar ta baza ta mance da ni ba. Gaskiya kam, kayi maganinta don abin nata yana neman wuce gona da iri. Nan suka soma bashi shawarwari akan yanda zaiyi dealing da ita. Nura ne zaune da abokansa, shi daman bashi da magana sai ta Ameer. A duniyar sa bashi kaunar jin ko ganinsa. Haka kuma tun daga lokacin da ya gano ilham bata da alaka da Ameer yake matukar kaunar ta. Asalima bai taba yiwa ya' mace irin son da yake yiwa ilham ba. Ji yake kamar ya hadiye ta, komai na ta na birgeshi, mussaman irin kiyayyar da takeyiwa Ameer ba karamar yi masa dadi yake ba. Haka yasa ya sanya wasu yan eyes service duk abinda ya faru tsakanin ilham da Ameer sai labari ya kai kunnensa duk inda yake kuwa. Zaune suke suna labarin abinda ya faru tsakanin ilham da Ameer. " kai, babe din nan tana. Birge ni wallahi, ina matukar son ta...infact ina gama makarantar nan zan aureh ta... Gaskiya kam, babe din tayi, tayi sosai. A gani na ita ce zata magance mana wannan dan iskan. Cikin buga kirji Nura yace ta ma gama dashi ai. Ire-iren wadannan firan sukayita yi, daga karshe Nura yayi alkawarin ganin karshen Ameer idan har bai zo ya bashi hakuri ba. Tun da sanyi safiya tayi wanka.as usual ta bi ilahirin jikin ta da kayan kamshi sa'anan ta fiddo kayan sawayarta. Da farko english wears ta ciro, sai kuma ta maida su ta fiddo doguwar jallabiya.wace baza'a kira dark pink ba, ba kuma za'a ce purple ba. Anyi wa rigar ado da lace baki, da kuma stones. A gaskiya kayan sun fito da ita sosai Bayan ta kammala shirin ta , ta nufi dakin su yusrah nan ta tarar da Amarah ta na shiri don haka ta nemi guri ta zauna tare da fadin ku nake jira dai. Tare suka jero zuwa cikin makarantan. A dai dai inda zasu rabu, sukayi karo da Nura da abokan sa. Bayan sun gaisa ya dube ta, cikin kwantar da murya yace na sayi wannan wankan. Murmushi tayi masa ba tare da ta ce masa wani abu ba. Har kofan ajinta yayo mata rakiya, a nan suka riski Ameer yana waya, da alama, ya fito daga ajin ne don yin waya. Suna ganinsa suka rage tafiyarsu, taku suke yi suna fira irinta masoya. Duk da ta iso gab da ajin, sai ta ki shiga ajin , Har sai da wata yar ajinsu ta zo ta rike mata hannu suka karasa cikin ajin. Bata fi minti hudu da shiga ajin ba ya shigo. Wace ce ta shigo yanzun? Ya nemi sani. Wace ta rikewa ilham ta mike tace daman ina cikin ajin, na fita yin wani abu ne, sai kuma Aisha Mustapha da muka shigo a tare. Wace ce Aisha Mustphan? Gaba daya yan ajin suka juya suna duban ilham wace ta daura dayan kafarta saman daya tana karatun litafi. Wani da ke kusa da ita ya dan taba ta.... "anayi maki magana, ya fada. Ta dago ta dubi Ameer. Wanda ransa ya bacci matuka, ji yake kamar ya shake ta Gira ta daga masa tare da yatsine fuskarta. 'pick ur bag and live my class" Bata musa ba ta maida takardan ta cikin jakarta tare da mike wa. Ta nufo sa, a yayinda ita kadai yake kallon tana isa gab da shi, ta dube shi tare da fadin "take this mr. Lecturer" tana fadin haka ta tofa masa miyau(yawu) a fuska. Gaba daya aji suka hada baki da fadin 'huuuunnnh😱"...... Cikin mamaki wasu suka mimmike, wasu kuma dafe da kirji suna jinjna wannan al'amarin. Hannu yasa ya share yawun, sa'anan ya dago suka hada ido. Ta juya zata fita, ya riko rigarta ta baya tare da fisgota da karfinsa har sai da ta kusan faduwa. Tas_tas kake ji ya sharara mata mari. Nan dalibai suka rikice suka hawo saman idan al'amarin ke wakana. Duk da marin da ya sharara mata, bai sa ya ji sauki ba a zuciyarsa sai kawai ya hau dukanta. Nan aji ya rikice, ilham me taurin zuciya ce, tun sa'anda ya kai mata dukan farko ta yi nasarar damkan yatsar sa, ta kuwa murdashi sai da ta ji kamar kashin sa ya kare, sa'anan ta saki. Ganin basu iya rabon wannan fadan, yasa wasu daga cikin daliban fita zuwa neman taimakon malamai. Ajin da ke kusa da su, shine ajin abokan tafiyar Nura don haka hayaniyar da suka ji, ya sa yan ajin fitowa don zuwa ganin abinda ke faruwa.
Read More »

Page 53 of SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫 By Aisha M.Gana (Ganarious) √... Aisha M. Gana Facebook. √... Mss_Ganarious Instagram. √... Ganarious98@gmail.com ** ** ** Gurin haduwansu ta nufa, bayan da ta fito lectures. Zaune ta tarar da su, a yayinda suke jiran fitowar ta. "salam ta fada tare da neman guri ta zauna. Wa'alaikumussalam....sannu da isowa kawas...fadin yusrah a yayinda take mike, tana me kokarin mikawa ilham sponge cake da shike shi suke ci. Nop, thanks ta fada ba tare da ta dubi cake din ba ma. What? Why?...yusra ta nemi sani cike da mamaki. I'm not just in the mood.....ilham ta maida mata. Cikin yatsine fuska Amarah tace "sabida ke fa muka aika neman shi cikin gari, sabida babu a makaranta, mun kuma san yanda kike son cin sponge cake sosai... Eh wallahi,...ba na jin cin komai ne kawai. Shiru sukayi suna duban juna. Sun kai kimamin minti biyar ba wacce ta sake magana, sai daga bisa ni Naziha ta mike ta dawo ta zauna kusa da ita. 'waye ya ta'ba mana ke kuma yau?... Uhmmm..... Kawai ta fada ba tare da ta dubi fuskar Naziha ba. Da magana kenan.... Nop, ni dai kawai bana jin dadi ne. Daga Nan suka mike zuwa Hostel. Bayan sun taso massalaci daga yin sallan i'shai, tafe suke suna fira cikin annashuwa, alokacin ilham ta warware, ba kamar lokacin da suka fito lectures ba. Guys kun san wani bu? A'a, sai kin fada.... Nan ta sanar masu duk abinda Mr. Williams ya fada a aji game da tafiyarsa, da kuma koyar dasu da ameer din zai dunga yi kafin ya dawo. Tabdijam...no wonder kinyi shiru dayawa dazun.fadin Amarah. Dariya naziha tayi tare da fadin 'daman dai nayi shiru ne, amman na shinshi ni hakan, wannan ameer din dai zamuyi maganinsa. Toh yanzun ya kenan? Uhmmm.....ni dai gaskiya, bazan zauna wannan yaron ya koyar dani, me ya sani da zai sanar dani. Duk da bana son mssing kos din Mr. Williams amman gaskiya bazan zauna wannan yaron ya koyar da ni ba, sai dai ni na koyar dashi. Nan suka fashe da dariya har suna tafawa. Kwance ta'ke tana me dannar wayar ta, da sanyi safiyar labara.... Naziha da tare da Yusrah suka kunno kai da sallamar su. Dagowa tayi tana duban su..."kun fito kenan? Eh, bamu son mu makara... Ok, sai kun dawo. Ban gane sai mun dawo ba, ke fa? Ni? Tabdi! Ai ni daga yanzun na yafe lectures din mr williams har sai shi ya dawo ya soma yi da kansa. Kar ki ba da mata mana, besides you are the one to loose..don haka ki ajiye duk wani abu da ke tsakaninki da wannan guy din, ki shirya mutafi. No, wallahi wannan yaron bai kai matsayin da zai koyar da ni ba, please believe me. Ba yanda su Naziha ba suyi da ilham ba, akan ta tashi ta shirya su fita lecture,amman ta ki ta cigaba da dannar wayarta. Ganin da gaske takeyi, yasa sunyi mata sallama suka fice abinsu. Bayan fitar su da kamar minti goma, wata tunani ta fado mata, a yayinda zuciyarta ta shiga rera mata "ki tashi ki tafi lectures din, wannan ce damar da zaki samu ki wulakanta wannan shegen nan" A hanzarce ta mike tana murmusawa ta shiga wanka. Tana fitowa ta shafe jikin ta ma mayukan kamshi tare da bin jikin ta da turaruka. T-shirt ta sanya hade da wando wanda ya kame mata kugu, ga shi daman kugun nan sai hamdalah sabida ki'ransa.bayan ta sanya T-shirt din tayi stoking , ta dauko rigAr jeans me dogon hannu ta dagwara akan T-shirt din, sai dai shi wannan rigar ya sauko ya rufe bayanta...amman kuma bata rufe botur ba, ta barsu a bude. Ta gyara sumar kanta tayi parking a baya, sa'anan ta dauki face-cap ta kafa. Sneaker masu kyan gaske ta sa, sannan ta ja jakarta sai cikin makaranta. Ko da ta isa aji sunyi nisa da lectures, cikin isa da takama take taku, tun shigowar ta yayi shiru tare da binta da ido. Dai dai ta isa gun kujerar da take da niyar zama yace 'hey u' Dagowa tayi ta dubeshi, sannan ta kauda kai tare da zaunawa. " ke ! Da ke nake magana, pick your bag and leave my class right away. Duban gunsa ma batayi ba, balle ta sanda mutun na magana. Littafi da ciro tana me dubawa, ya sake dubanta a fusace "ki fita mun a aji nace. Nan ma bata mike ba, tayi biris da shi. Ya hada takardunsa tare da duban daliban cikin ajin,idan har bata fita ba, toh ni kuwa bazani koyar da ku ba. Nan yan ajin suka shiga rudane, suna son ilham sosai ba su kaunar abinda zai bata mata rai, gashi kuma a dadilinta zasu loosing wannan lectures din. Nan wasu suka soma gun guni, suna shawaran abinyi. Ta juya ta dubi fuskokinsu, sai kawai taji zuciyarta ta kariya, don haka mike tare da daukar jakkarta ta fice daga ajin. Gurin haduwansu ta nufa, ta tarar da yUsrah har ta fito lectures. Kai kai kaiiiiii.....babe kin ganki kuwa? Kamar na hadiye ki. Tsuki tayi a yayinda take shirin zama. Tana zaunawa Naziha ta iso gurin.."wa nake gani haka,? Kin hadu fa...ina ce ko kince kin yafe lectures din mr. Williams? Nan ta zayyana masu dalilin fitowarta, da kuma abinda ya faru a tsakaninsu. Cikin jin haushi da takaicin Ameer suka soma zage zage...."A gaskiya ya kamata mu taka masa birki, abin nasa na neman wuce gona da iri. Ai zai gane kuran sa, ba dai jibi jumma'ah muna da lectures din sa ba, zanyi masa abinda ba zai ta'ba mantawa ba a rayuwarsa.
Read More »

Monday 17 September 2018

Page 52 of soyayyarmu

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page5⃣2⃣ √... ganarious.blogspot.com/ ** ** Bayan da Dr. Abdul'Afeez M.D ya yi masu nasiha,ya umurce su da su tafi su chigaba da amsan darusa. Suna fitowa da'ga office dinsa ilham ta sha gabansa.."kar kayi tunanin zan fasa yi maka abinda nayi niya, sabida anyi mana nasiha. A'a, a'a... Ta fadi hakan ne tana yarfa hannunta, shi kuwa ban da kallonta babu abinda yake yi. "mahaukaciya".... Ya fada bayan da ta juya zata tafi. Nan ta sake juyawa, tare da kusantowa gab da shi.. "sake maimaita abinda ka fada yanzun" Ya bude baki da niyar yin magana, suka ji magana a bayan su "ku tafi aji mana" fadin Dr. Abdul'Afeez. Murmushi yayi masa tare da fadin 'ok sir',sa'anan ya bi hanyar ajinsu. Naushi yake kaiwa tafin hannunsa, da dayan hannun. Yana safa da marwa. "Guy wai me ke faruwa ne?... "yarinyar nan, yarinyar nan mana..! Na kasa yin maganinta, so nake na nuna mata ni ba tsaranta ba ne. Dariya suka soma yi masa... "me kuwa zaka yi mata.? Fadin yusuf, ya kuma ci gaba da fadin ai wannan yar' da'ga alamu she'daniya ce, don haka kawai ka fita harkanta. A gurin da suke haduwa idan sun sami dan hutu(break) bayan lectures, nan su Amarah suka tarar da ilham rai ba'ce.... Ko ba'a fada masu ba, sun san ranta a ba'ce shike, Naziha ta zauna kusa da ita tare da da'fa kafadarta "ya ya dai?" Mtssss...tayi tsuki, yaron nan na neman sauya min halayen Wa kenan? Wannan Ameer din mana. Dariya sukayi..."ki ce dai mutumin ki, zamu fi gane hakan" Daga nan suka soma tattaunawa akan wani topic da wani malami ya baiwa yan ajin su Amarah,da suyi bincike akai. A kodayaushe da Ameer take farkawa a zufiyarta, burin ta bai wuci ta gan ta musguna masa ba. Kulli'yaumi da sabon tunani take tashi, 'idan mun hadu, zani yi masa kaza da kaza. Sai dAi Allah cikin ikon sa, bashi basu damar haduwa, sai dai su hangi junarsu daga ne'sa. Shi Ameer din ma haka tunaninsa yake, 'yayi alwashin ba zai yafe ma ta ba, sabida a duniyarsa ba'a taba raina masa wayau ba sai ita.. Wataran su ilham na daukan darasi akan cututtukar fata, wanda mr. Williams Collins ne ke daukan su wannan kos din. Bayan ya gama yi masu bayanai, ya kuma amsa tambayoyin su sa'anan ya soma yi masu jawabi kamar haka. Ku bude kunnuwan ku don sauraron gargadi da kuma abinda zan fada maku. Tafiya ce ta kama ni zuwa kasar china, inda ni da wasu kwararun likitoci da malamai daga kasashe dabam-daban na duniya, zamu hade acan domin yin research(bincike) akan wata cutar fata da ta sauka a kasar china din. Wannan tafiyar ta sati uku ce. Don haka nake son sanar da kuma gabatar wanda nake son zai cigaba da koyar da ku. Sunar sa Abubakar shima dalibi ne kamar ku. Ba kuma sabida nace masa dalibi kamar ku ba zai sanya kuyita abinda kuke so a aji a yayinda yake koyarwa. Ina son ku sani shi wannan dalibin daban yake da duk wani dalibi a fadin makarantar nan,ina matukar girmamashi ,ina ganin kimansa da mutuncin sa. Don haka bani son reni a tsakaninku,idan kuka sa'ba masa kuwa duk hukuncin da ya yanke ina marhaba dashi ba kuma zanyi biris da shi ba...idan kunne ya ji?? "jiki ya tsira"....fadin daliban aji, ayayinda suke hada baki. Nan ya juya ya fita, jim kadan ya shigo. Ameer ne biye dashi, a tsakiyar ajin suka yi tsaye a yayinda mr. Williams ya sake gabatar masu da Ameer a matsayin wanda zai cigaba da koyar dasu kos din sa. Ya kum ja masu kunne da kar su soma su rena masa wayau don ganin shi da'libi ne.daga nan yayi masu sallama da fatan alkhairi sa'anan ya rike wa Ameer kafada suka fice daga ajin. Suna fita ilham tayi yar siririya tsuki wanda yasa wadanda suke kusa da ita juyowa suna duban ta.
Read More »
Designed by Jide Ogunsanya.