Pages

Tuesday 18 September 2018

Page 54 of soyayyar mu👫

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page5⃣4⃣ √... Special greetings ga masu patronizing blog din, ina godiya. √... Mss_Ganarious, a instagram. √... Ganarious98@gmail.com don korafe korefe. ** ** ** Mutan kontagora, one love keep us together.💞 Ex_students especially (2009 graduates) ta G.G.U.S.S Bodinga, sokoto state,ina mika gaisuwata gare ku. ** ** ** Bayan sallan isha'i suka hadu gurin zaman su. Ko kunsan abinda shaidaniyar yarinyar nan tayi yau? Wa? Mutuniyar ka? Idan ba ita ba toh wa, nan ya kwashe yanda sukayi da ilham ya sanar masu. Ya kara da fadin Allah ya taimake ta, ta fita a ajin, da abinda zan yi mata har mutuwar ta baza ta mance da ni ba. Gaskiya kam, kayi maganinta don abin nata yana neman wuce gona da iri. Nan suka soma bashi shawarwari akan yanda zaiyi dealing da ita. Nura ne zaune da abokansa, shi daman bashi da magana sai ta Ameer. A duniyar sa bashi kaunar jin ko ganinsa. Haka kuma tun daga lokacin da ya gano ilham bata da alaka da Ameer yake matukar kaunar ta. Asalima bai taba yiwa ya' mace irin son da yake yiwa ilham ba. Ji yake kamar ya hadiye ta, komai na ta na birgeshi, mussaman irin kiyayyar da takeyiwa Ameer ba karamar yi masa dadi yake ba. Haka yasa ya sanya wasu yan eyes service duk abinda ya faru tsakanin ilham da Ameer sai labari ya kai kunnensa duk inda yake kuwa. Zaune suke suna labarin abinda ya faru tsakanin ilham da Ameer. " kai, babe din nan tana. Birge ni wallahi, ina matukar son ta...infact ina gama makarantar nan zan aureh ta... Gaskiya kam, babe din tayi, tayi sosai. A gani na ita ce zata magance mana wannan dan iskan. Cikin buga kirji Nura yace ta ma gama dashi ai. Ire-iren wadannan firan sukayita yi, daga karshe Nura yayi alkawarin ganin karshen Ameer idan har bai zo ya bashi hakuri ba. Tun da sanyi safiya tayi wanka.as usual ta bi ilahirin jikin ta da kayan kamshi sa'anan ta fiddo kayan sawayarta. Da farko english wears ta ciro, sai kuma ta maida su ta fiddo doguwar jallabiya.wace baza'a kira dark pink ba, ba kuma za'a ce purple ba. Anyi wa rigar ado da lace baki, da kuma stones. A gaskiya kayan sun fito da ita sosai Bayan ta kammala shirin ta , ta nufi dakin su yusrah nan ta tarar da Amarah ta na shiri don haka ta nemi guri ta zauna tare da fadin ku nake jira dai. Tare suka jero zuwa cikin makarantan. A dai dai inda zasu rabu, sukayi karo da Nura da abokan sa. Bayan sun gaisa ya dube ta, cikin kwantar da murya yace na sayi wannan wankan. Murmushi tayi masa ba tare da ta ce masa wani abu ba. Har kofan ajinta yayo mata rakiya, a nan suka riski Ameer yana waya, da alama, ya fito daga ajin ne don yin waya. Suna ganinsa suka rage tafiyarsu, taku suke yi suna fira irinta masoya. Duk da ta iso gab da ajin, sai ta ki shiga ajin , Har sai da wata yar ajinsu ta zo ta rike mata hannu suka karasa cikin ajin. Bata fi minti hudu da shiga ajin ba ya shigo. Wace ce ta shigo yanzun? Ya nemi sani. Wace ta rikewa ilham ta mike tace daman ina cikin ajin, na fita yin wani abu ne, sai kuma Aisha Mustapha da muka shigo a tare. Wace ce Aisha Mustphan? Gaba daya yan ajin suka juya suna duban ilham wace ta daura dayan kafarta saman daya tana karatun litafi. Wani da ke kusa da ita ya dan taba ta.... "anayi maki magana, ya fada. Ta dago ta dubi Ameer. Wanda ransa ya bacci matuka, ji yake kamar ya shake ta Gira ta daga masa tare da yatsine fuskarta. 'pick ur bag and live my class" Bata musa ba ta maida takardan ta cikin jakarta tare da mike wa. Ta nufo sa, a yayinda ita kadai yake kallon tana isa gab da shi, ta dube shi tare da fadin "take this mr. Lecturer" tana fadin haka ta tofa masa miyau(yawu) a fuska. Gaba daya aji suka hada baki da fadin 'huuuunnnh😱"...... Cikin mamaki wasu suka mimmike, wasu kuma dafe da kirji suna jinjna wannan al'amarin. Hannu yasa ya share yawun, sa'anan ya dago suka hada ido. Ta juya zata fita, ya riko rigarta ta baya tare da fisgota da karfinsa har sai da ta kusan faduwa. Tas_tas kake ji ya sharara mata mari. Nan dalibai suka rikice suka hawo saman idan al'amarin ke wakana. Duk da marin da ya sharara mata, bai sa ya ji sauki ba a zuciyarsa sai kawai ya hau dukanta. Nan aji ya rikice, ilham me taurin zuciya ce, tun sa'anda ya kai mata dukan farko ta yi nasarar damkan yatsar sa, ta kuwa murdashi sai da ta ji kamar kashin sa ya kare, sa'anan ta saki. Ganin basu iya rabon wannan fadan, yasa wasu daga cikin daliban fita zuwa neman taimakon malamai. Ajin da ke kusa da su, shine ajin abokan tafiyar Nura don haka hayaniyar da suka ji, ya sa yan ajin fitowa don zuwa ganin abinda ke faruwa.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.