Pages

Tuesday 18 September 2018

Page 53 of SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫 By Aisha M.Gana (Ganarious) √... Aisha M. Gana Facebook. √... Mss_Ganarious Instagram. √... Ganarious98@gmail.com ** ** ** Gurin haduwansu ta nufa, bayan da ta fito lectures. Zaune ta tarar da su, a yayinda suke jiran fitowar ta. "salam ta fada tare da neman guri ta zauna. Wa'alaikumussalam....sannu da isowa kawas...fadin yusrah a yayinda take mike, tana me kokarin mikawa ilham sponge cake da shike shi suke ci. Nop, thanks ta fada ba tare da ta dubi cake din ba ma. What? Why?...yusra ta nemi sani cike da mamaki. I'm not just in the mood.....ilham ta maida mata. Cikin yatsine fuska Amarah tace "sabida ke fa muka aika neman shi cikin gari, sabida babu a makaranta, mun kuma san yanda kike son cin sponge cake sosai... Eh wallahi,...ba na jin cin komai ne kawai. Shiru sukayi suna duban juna. Sun kai kimamin minti biyar ba wacce ta sake magana, sai daga bisa ni Naziha ta mike ta dawo ta zauna kusa da ita. 'waye ya ta'ba mana ke kuma yau?... Uhmmm..... Kawai ta fada ba tare da ta dubi fuskar Naziha ba. Da magana kenan.... Nop, ni dai kawai bana jin dadi ne. Daga Nan suka mike zuwa Hostel. Bayan sun taso massalaci daga yin sallan i'shai, tafe suke suna fira cikin annashuwa, alokacin ilham ta warware, ba kamar lokacin da suka fito lectures ba. Guys kun san wani bu? A'a, sai kin fada.... Nan ta sanar masu duk abinda Mr. Williams ya fada a aji game da tafiyarsa, da kuma koyar dasu da ameer din zai dunga yi kafin ya dawo. Tabdijam...no wonder kinyi shiru dayawa dazun.fadin Amarah. Dariya naziha tayi tare da fadin 'daman dai nayi shiru ne, amman na shinshi ni hakan, wannan ameer din dai zamuyi maganinsa. Toh yanzun ya kenan? Uhmmm.....ni dai gaskiya, bazan zauna wannan yaron ya koyar dani, me ya sani da zai sanar dani. Duk da bana son mssing kos din Mr. Williams amman gaskiya bazan zauna wannan yaron ya koyar da ni ba, sai dai ni na koyar dashi. Nan suka fashe da dariya har suna tafawa. Kwance ta'ke tana me dannar wayar ta, da sanyi safiyar labara.... Naziha da tare da Yusrah suka kunno kai da sallamar su. Dagowa tayi tana duban su..."kun fito kenan? Eh, bamu son mu makara... Ok, sai kun dawo. Ban gane sai mun dawo ba, ke fa? Ni? Tabdi! Ai ni daga yanzun na yafe lectures din mr williams har sai shi ya dawo ya soma yi da kansa. Kar ki ba da mata mana, besides you are the one to loose..don haka ki ajiye duk wani abu da ke tsakaninki da wannan guy din, ki shirya mutafi. No, wallahi wannan yaron bai kai matsayin da zai koyar da ni ba, please believe me. Ba yanda su Naziha ba suyi da ilham ba, akan ta tashi ta shirya su fita lecture,amman ta ki ta cigaba da dannar wayarta. Ganin da gaske takeyi, yasa sunyi mata sallama suka fice abinsu. Bayan fitar su da kamar minti goma, wata tunani ta fado mata, a yayinda zuciyarta ta shiga rera mata "ki tashi ki tafi lectures din, wannan ce damar da zaki samu ki wulakanta wannan shegen nan" A hanzarce ta mike tana murmusawa ta shiga wanka. Tana fitowa ta shafe jikin ta ma mayukan kamshi tare da bin jikin ta da turaruka. T-shirt ta sanya hade da wando wanda ya kame mata kugu, ga shi daman kugun nan sai hamdalah sabida ki'ransa.bayan ta sanya T-shirt din tayi stoking , ta dauko rigAr jeans me dogon hannu ta dagwara akan T-shirt din, sai dai shi wannan rigar ya sauko ya rufe bayanta...amman kuma bata rufe botur ba, ta barsu a bude. Ta gyara sumar kanta tayi parking a baya, sa'anan ta dauki face-cap ta kafa. Sneaker masu kyan gaske ta sa, sannan ta ja jakarta sai cikin makaranta. Ko da ta isa aji sunyi nisa da lectures, cikin isa da takama take taku, tun shigowar ta yayi shiru tare da binta da ido. Dai dai ta isa gun kujerar da take da niyar zama yace 'hey u' Dagowa tayi ta dubeshi, sannan ta kauda kai tare da zaunawa. " ke ! Da ke nake magana, pick your bag and leave my class right away. Duban gunsa ma batayi ba, balle ta sanda mutun na magana. Littafi da ciro tana me dubawa, ya sake dubanta a fusace "ki fita mun a aji nace. Nan ma bata mike ba, tayi biris da shi. Ya hada takardunsa tare da duban daliban cikin ajin,idan har bata fita ba, toh ni kuwa bazani koyar da ku ba. Nan yan ajin suka shiga rudane, suna son ilham sosai ba su kaunar abinda zai bata mata rai, gashi kuma a dadilinta zasu loosing wannan lectures din. Nan wasu suka soma gun guni, suna shawaran abinyi. Ta juya ta dubi fuskokinsu, sai kawai taji zuciyarta ta kariya, don haka mike tare da daukar jakkarta ta fice daga ajin. Gurin haduwansu ta nufa, ta tarar da yUsrah har ta fito lectures. Kai kai kaiiiiii.....babe kin ganki kuwa? Kamar na hadiye ki. Tsuki tayi a yayinda take shirin zama. Tana zaunawa Naziha ta iso gurin.."wa nake gani haka,? Kin hadu fa...ina ce ko kince kin yafe lectures din mr. Williams? Nan ta zayyana masu dalilin fitowarta, da kuma abinda ya faru a tsakaninsu. Cikin jin haushi da takaicin Ameer suka soma zage zage...."A gaskiya ya kamata mu taka masa birki, abin nasa na neman wuce gona da iri. Ai zai gane kuran sa, ba dai jibi jumma'ah muna da lectures din sa ba, zanyi masa abinda ba zai ta'ba mantawa ba a rayuwarsa.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.