Pages

Tuesday 25 September 2018

Page 57 of soyayyar mi

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page 5⃣7⃣ √... Visit ganariousblogspot.com/ for the latest release. ** ** ** Wata sa'in yakan so ya fahimtar da zuciyarsa da cewan "ai duk laifin ta,duk itace ta sayawa kanta abinda ke faruwa da ita, amman wata bangaren zuciyarsa kan ki amincewa da haka. Duk kokarin da yake yayi wa su naziha bayani a banza sabida sun ki su bashi daman haka, daga baya ma cin mutunci Amarah take masa. Hakan kuwa ba karamar batawa abokansa rai yake ba, sona jin haushi da takaicin abokin su. Ganin bashi da mafita, duk inda yabi a toshe ya sanya shi zuwa ga Dr. Abdul'Afeez yayi masa bayani komai ya kuma shaida masa iham ta daina zuwa lectures. Ya nemi alfarman da Dr. Abdul Afeez ya taimaka masa yayi kiranta ta don ya bata hakuri. Nan dr. Abdul Afeez yayi masa alkawarin gobe da yardan Allah zai kira ta. Washe gari Dr. Abdul'Afeez yayi mata aike. Da farko ta so tayi biris da kiransa, amman ganin yanayin da su Naziha suka shiga damuwa suna fadin zata jawo kanta wata matsalan yasa ta amince da zuwa amsa kiran. Su Naziha sun rako ta har cikin office dinsa. Sun jima tsaye bai bi ta kansu ba, nan Amarah ta ji haushi ta juya zata fito. Come back here, ya fada fuskan nan nasa a murtuke. Ta dawo tayi tsaye. Nan ya shiga yarfa masu bala'i, yana me ganin laifinsu cewan su suke zuga ilham ta daina zuwa lectures domin kawai su cutar da ita. Nan suka shiga rantse rantse suna fadin "wallahi ba laifin mu ba ne" Bayan ya gama yi masu fada, ya koma yayi masu nasiha sa'anan ya sallame su amman banda ilham. Nan ya bar ta zaune ba tareda yace mata uffan ba. Sai da ya gama yan rubuce rubucensa sannan ya dauki wayarsa yayi kira. Jim kadan aka bude kofa tare da sallama. Tana juyawa suka hada ido, don haka ta kauda kai. Bayan ya gaida Dr. Abdul'Afeez ya bashi izini da ya zauna. Bayan ya zauna Dr. Abdul'Afeez ya shiga yi masu Nasiha mussam ita ilham, yana cikin magana wayarsa ta soma ruri ya daga yana amasa kiran. Da alama ana nemansa ne a wani gurin don haka ya mike. "toh ni yanzun ana jira na ne, don haka gaka ga ilham...duk na san baka da laifi a abinda ya faru, amman kuma kana son bata hakuri, don haka ka bata hakuri ku sasanta juna kafin na dawo.. Yana fita Ameer ya matso da kujerar sa, yana facing na ta. Kafin duk ya bude baki da niyar yi mata magana, ta tofa masa yawu... A hankali yasa hannunsa ya goge,ya dube ta tare da fadin kiyimin duk abinda kika gan dama, kiyi abinda ya fi wannan idan har zaki ji sassauci a ranki, ki kuma yafe min please. Kallonsa batayi ba, balle ta saurare shi. Hakan ya bashi damar saukowa daga kujerar sa ya duka a gabanta. 'ya ke Aisha ki gafarce ni, wallahi bansan zanyi hurting dinki hakan ba, tunda nake a rayuwata ban taba sa wani ko wata yayi hawaye ba shiyasa na kasa rasa sukuni ganin kin zubda hawaye sabida ni....please kiyi hakuri ki yafe min. Ganin bata da niyar yin magana ya ci gaba da fadin "please dont skip your lectures all because of me, i feel guilty." ya cigaba da rokon ta,. Sai shesshakar kukan ta kawai ya ji, nan ya shiga rudani, ya ma rasa abinda zai yi ko fadi " i hate you, i hate you ta fada tana dubansa. Bazan ta'ba yafe maka ba, da ka sauya min halayena....i hate you ta kara fadin Ido kawai yasa mata,sabida kukan ta ya dagula masa lisafi. Suna a haka Dr. Abdul'Afeez ya shigo tare da wani, don haka ya sallame su . A tare suka fito daga office dinsa , da sauri su ilham tare da nura da abokansa suka nufo su. Ganin yanayinta ya sa Nura shan gaban Ameer "me kayi mata? Ba tareda Ameer ya amsa masa ba ya nemi da ya kauce,nan ma Nura ya sake shan gabansa. Kai ku zo nan, murayn Dr. Abdul' Afeez suka ji. Don haka suka nufi gunsa gaba daya. Ya kai duban sa ga ilham, ban gama case dinku ba, amman sabida bakon da nake dashi yasa na sallame ku, don haka daga yau kar ki kara skiping lecturea infact kullum safe kiyi report a office dina sabida na san da zuwanki. Kina ji ko? Kai ta daga, tareda fadin yes sir. Ameer ya ji dadi sosai a ransa da jin abinda dr Abdul afeez ya fada, bashi kadai ba, harda masoyinta Nura da kawayenta.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.