Pages

Monday 17 September 2018

Page 52 of soyayyarmu

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page5⃣2⃣ √... ganarious.blogspot.com/ ** ** Bayan da Dr. Abdul'Afeez M.D ya yi masu nasiha,ya umurce su da su tafi su chigaba da amsan darusa. Suna fitowa da'ga office dinsa ilham ta sha gabansa.."kar kayi tunanin zan fasa yi maka abinda nayi niya, sabida anyi mana nasiha. A'a, a'a... Ta fadi hakan ne tana yarfa hannunta, shi kuwa ban da kallonta babu abinda yake yi. "mahaukaciya".... Ya fada bayan da ta juya zata tafi. Nan ta sake juyawa, tare da kusantowa gab da shi.. "sake maimaita abinda ka fada yanzun" Ya bude baki da niyar yin magana, suka ji magana a bayan su "ku tafi aji mana" fadin Dr. Abdul'Afeez. Murmushi yayi masa tare da fadin 'ok sir',sa'anan ya bi hanyar ajinsu. Naushi yake kaiwa tafin hannunsa, da dayan hannun. Yana safa da marwa. "Guy wai me ke faruwa ne?... "yarinyar nan, yarinyar nan mana..! Na kasa yin maganinta, so nake na nuna mata ni ba tsaranta ba ne. Dariya suka soma yi masa... "me kuwa zaka yi mata.? Fadin yusuf, ya kuma ci gaba da fadin ai wannan yar' da'ga alamu she'daniya ce, don haka kawai ka fita harkanta. A gurin da suke haduwa idan sun sami dan hutu(break) bayan lectures, nan su Amarah suka tarar da ilham rai ba'ce.... Ko ba'a fada masu ba, sun san ranta a ba'ce shike, Naziha ta zauna kusa da ita tare da da'fa kafadarta "ya ya dai?" Mtssss...tayi tsuki, yaron nan na neman sauya min halayen Wa kenan? Wannan Ameer din mana. Dariya sukayi..."ki ce dai mutumin ki, zamu fi gane hakan" Daga nan suka soma tattaunawa akan wani topic da wani malami ya baiwa yan ajin su Amarah,da suyi bincike akai. A kodayaushe da Ameer take farkawa a zufiyarta, burin ta bai wuci ta gan ta musguna masa ba. Kulli'yaumi da sabon tunani take tashi, 'idan mun hadu, zani yi masa kaza da kaza. Sai dAi Allah cikin ikon sa, bashi basu damar haduwa, sai dai su hangi junarsu daga ne'sa. Shi Ameer din ma haka tunaninsa yake, 'yayi alwashin ba zai yafe ma ta ba, sabida a duniyarsa ba'a taba raina masa wayau ba sai ita.. Wataran su ilham na daukan darasi akan cututtukar fata, wanda mr. Williams Collins ne ke daukan su wannan kos din. Bayan ya gama yi masu bayanai, ya kuma amsa tambayoyin su sa'anan ya soma yi masu jawabi kamar haka. Ku bude kunnuwan ku don sauraron gargadi da kuma abinda zan fada maku. Tafiya ce ta kama ni zuwa kasar china, inda ni da wasu kwararun likitoci da malamai daga kasashe dabam-daban na duniya, zamu hade acan domin yin research(bincike) akan wata cutar fata da ta sauka a kasar china din. Wannan tafiyar ta sati uku ce. Don haka nake son sanar da kuma gabatar wanda nake son zai cigaba da koyar da ku. Sunar sa Abubakar shima dalibi ne kamar ku. Ba kuma sabida nace masa dalibi kamar ku ba zai sanya kuyita abinda kuke so a aji a yayinda yake koyarwa. Ina son ku sani shi wannan dalibin daban yake da duk wani dalibi a fadin makarantar nan,ina matukar girmamashi ,ina ganin kimansa da mutuncin sa. Don haka bani son reni a tsakaninku,idan kuka sa'ba masa kuwa duk hukuncin da ya yanke ina marhaba dashi ba kuma zanyi biris da shi ba...idan kunne ya ji?? "jiki ya tsira"....fadin daliban aji, ayayinda suke hada baki. Nan ya juya ya fita, jim kadan ya shigo. Ameer ne biye dashi, a tsakiyar ajin suka yi tsaye a yayinda mr. Williams ya sake gabatar masu da Ameer a matsayin wanda zai cigaba da koyar dasu kos din sa. Ya kum ja masu kunne da kar su soma su rena masa wayau don ganin shi da'libi ne.daga nan yayi masu sallama da fatan alkhairi sa'anan ya rike wa Ameer kafada suka fice daga ajin. Suna fita ilham tayi yar siririya tsuki wanda yasa wadanda suke kusa da ita juyowa suna duban ta.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.