Global opportunities| Business/Entrepreneurship| Fashion/Beauty| Health/Wellness| Inspirational Stories| Interviews| Guides.
Saturday, 22 September 2018
Page 55 of SOYAYYAR MU👫
SOYAYYAR MU👫
By Ganarious.
Page 5⃣5⃣
** ** ** ** **
Wasu da'liban sun rike ilham, a yayinda wasu su ke rike da Ameer, suna tausasa masa zuciya.
A lokacin da ilham take kubce kubce wai ita ala dole su sake ta ta dambata dashi, a lokacin wasu malamai suka iso.
Tsawa daya da'ga cikin malaman ya daka mata, sai A sa'annan ta natsu.
"what is going on inn here? Ya fada yana duban ilham.
Kafin duk ta amsa masa, fada ya barke bangaren inda Ameer ya ke a tsaye.... Ashe Nura ne ya shigo ajin rike da belt, yana hangen Ameer ya nufesa ya wasga masa.
Nan abokan sa suka kama masa, ai ko kafin ka sani ajin ya rikice.
A gaskiya Ameer yayi ta maza, su kusan shidda akan sa, amman sai da ya raunana wasu daga cikin su.
Duk kokarin da malamai sukai don ganin sun raba wannan fadan, abin ya ci tura don haka sukayi kiran securities na makarantar.
Cikin kankani lokaci labari ya cike makarantar.
Labari na kaiwa ga Abokan tafiyan Ameer, suka fito a fusace ....." yau kam sai munyi maganin yan iskan nan"
Suna isowa bakin ajin su ilham, sukayi karo da securities sun fito da abokan tafiyar Nura, da shi Nuran, da kuma ilham ciki har da abokinsu.
Basuyi tsaya wata-wata ba, suka hau dukan abokan Nuran har shi Nuran ma.
Securities sunyi kiran yan uwansu da su zo su tafi da abokan Ameer.
Tunda aka jefa su a kurkutun makaranta, ba'a sake bin ta kansu ba.. Har sai washe gari.
Shugaban makaranta, da sauran manyanyan malamai na kings college ne zaune a *special staffs meeting room*,inda suke sauraron wani malami wanda aka bashi mukamin *idon makaranta* (ma'ana duk abinda ya faru a makaranta shi zai kawo labari.)
Bayan ya gama jawabinsa, a fusace shugaban makarantar yace a tafi a zo masa da su.
Cikin kankani lokaci aka fito dasu, izuwa hall din.
Ilham ce mace a cikinsu, idanun nan nata duk sun sauya, sun yi jajir ga girman da sukayi, da alama ta sharbi kuka.
Ita ce ta fara isowa gurin tare da security mace.
Dr. Abdul'afeez yana ganin ta ya mike tare fadin 'you again??
Yana rufe baki securities suka shigo da Nura da abokansa, da kuma Ameer da Abokansa.
"All of them are blacks.! How rude..." fadin shugaban makarantar, har huci yake yana zagin su,yana tsaka da zaginsu idon sa ya kai kan Ameer.
'Abubakar'.....ya fada cike da mamaki a yayinda yake nuninsa da yatsa.
Dnt tell me you among.
Nan malamai suka shaida masa fadan ai nasa ne.
Yayi kiran Ameer da ya dawo gabansa yayi masa bayani.
Yana gama sauraron Ameer ya shiga zagin ilham, daga karshe yace gaba ki dayan su za'a kore su a makarantan, banda Ameer din.
Ya juya ga Nura yana nunashi da yatsa....'maganar ka ta ishe ni a wannan makarantar, don haka za'a zauna da board managements akan ka, yazama dole kai da abokanka ku bar wannan makarantar....'i can't continue to keep people like you.'
Ya dubi sauran malamai, yace za'a sake zama meeting akan su, amman kafin nan a maida su prison, amman ba da Ameer ba.
No sir, that would be unfair, don Allah kayi hakuri bazan fita a gurin ba tare da abokaina ba...a dalilina suke gurin, don haka bazan ji dadi ba idan na fita, su aka rike su....
Ajiyan zuciya yayi yana duban Ameer 'shikenan.! Yanzun yaya kake son a yi?
Ameer ya nisa yace a sake su , su tafi.
Ni a bar ni a nan.
Shugaban ya yi shiru na dan lokaci, sa'anan yace toh ayi yanda yake so din.
An saki abokan Ameer suka koma Hostel, a yayinda aka komar da sauran.
Hukumar makaranta ta hana kowa zuwa gunda aka tsare su Ameer.
su Naziha sun yi roko, sunyi magiya akan a basu dama don su ga'nah da abokiyar su, sai dai duk rokonsu a banza sukayi sabida ko kallonsu securities ba suyi ba ballantana su saurare su.
Da haka suka hakura suka koma hostel cike da tausayin ilham.
Sai da suka cike kwanaki biyar a cikin kurkutun, sa'anan shugaba ya bada damar a fito da su. Bayan zaman shawar-wari da sukayi tsakanin malamai.
Da kyar take da'ga kafar, kallo daya zakayi mata ka fahimci cewan a wahalce take.
Duk da karfin halin da takeyi sai da tafiyarta ya dunga karkacewa kamar wace ta shaa, ta bugu.
Itace aka fiddo karshe, don haka meeting hall ta tarar da abokan fadan ta. Tana shiga ta nemi guri ta zauna.
Dr. Abdul'Afeez ya daka mata tsawa.
'would you get up and stand on your feet?"..
Da taimakon securities ta mike.
Hawaye cike da idon ta, a yayinda take mikewa.
Bayan ta mike ta sanya dan yatsar ta tana share hawayen, tana janye yatsar tare da bude idon ta, ba zato sukayi ido hudu da Ameer..
Idanuwansa na dauke da sakonni wanda a lokacin baza ta iya gane ko na me nene ba.
Ta kauda kai, a yayinda hawayen suka cigaba da bin juna saman kuncin ta.
Dr. Abdul'Afeez ne ya soma jawabi akan hukunce hukuncen da ya dace su fuskan ta, amman sabida wasu dalilai an yafe masu, akan sharadin kowannensu zai yi rantsuwa da alkawarin ba zai sake sa'bawa dokar makaranta ba, idan kuma haka ta faru duk abinda makaranta ta yanke masu su, suka saya...
Bayan nan malamai suka shiga baiwa ilham shawarwari a yayinda wasu suke aibanta halin ta suna fadin itace silan abinda ya faru.
Sun kuma umurce ta, da ta rubuta wasikar ban hakuri kala uku.
Daya zuwa ga malamai, daya zuwa ga shugaban makarantat, daya zuwa ga Ameer..
A lokacin da suke tofa albarkacin bakinsu duk akanta wata sabuwar kuka ta zo mata.sai sharan hawaye takai.......
Jikin ta ya raya mata ita kadai ake kallo, amman ta kiyasta akwai wani me kallon ta wanda shike a dalilin tsareta da idonsa ta kasa dagowa.
Naziha tareda Amarah da yusrah tsaye dan ni'sah da meeting hall.
Fitowar ta suke jira. Suna nan tsaye idon su kan kofar hall din, suka hange ta tana fito wa.
Da gudun su suka karasa gun ta,suna tamabayar lafiyar jikin ta.
Kuka ta saki, me ratsa jiki kuwa. Su ma din nan da nan jikinsu yayi sanyi, nan suka shiga lallashin ta. Tare da kama hanunta suka nufi hostel.
Ruwan wanka suka soma hada mata, sa'anan suka taimaka mata tayi wanka.
Hidayata wace suke daki daya,ita ce ta fiddo mata da kayan sawa.
Bayan nan suka shirya mata abinci, da kyar da kuma magiya ta ci abinci.
Tana ci, tana hawaye. Ba wace ta nemi da ta san dalilin kukan ta, duk jikinsu ya mace sai kallonta sukeyi suna tausaya mata.
Tana tsaka da ci, ta mike a guje, toilet ta nufa inda ta dunga amai.
Sannu ilham...."sannu kinji ilham! Shine kawai abinda ke fitowa a bakinsu.
"wani gurin na maki ciwo ne? Fadin Amarah.
"jiri nake gani.....
Nan suka taimaka mata, ta kwanta, ba'a fi minti hudu da kwanciyarta ba, jiki yayi zafi.
Suna jin haka suka nufi school clinic da ita inda aka basu gado.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Designed by Jide Ogunsanya.
No comments:
Post a Comment