Pages

Tuesday 25 September 2018

Page 56of SOYAyYAR MU

SOYAYYAR MU👫 By Ganarious. Page5⃣6⃣. √... Gaisuwa gareku makarantan ~SOYAYYAR MU~🤝🏻 √... Gaisuwa gareku mabiyan blog dina. √...fatan alkhair gareku yan'uwa maza da mata. *Don Allah a dunga hakuri da spelling errors, sentence errors,typing errors da dai sauran su*😎. A ko dayaushe zaku iya samu na a Ganarious98@gmail.com na gode. ** ** ** Guy wai me ke going on ne? Tunda ka fito da'ga kurkutun nan kake wani shiru-shiru, kana avoiding long conversations...me ke faruwa? Eh fa..! Ni ma na lura da hakan. Fadin yusuf Yayi ajiyan zuciya tare da fadin uhmmmm.....i don't know, i just know, i'm feeling guilty. Nan gabaki dayan su suka maida kallonsu gareshi. Guilty? Of what? Ahmad ya tambaya cike da mamaki. "Na sanya yarinyar nan a wani hali, da yanayi. A lokacin da na kyatta ido na gan hawayen ta, da ga lokacin na rasa sukuni a zuciyata, sabida nine sanadin hawayenta, nine sanadin sanya ta a halin da ta tsinci kanta. Image din hawayen ta na reflecting a ido na every second,nakan kuma tsinci kaina da jin zafin haka....i just dont know. Tsukin da yusuf yayi ya sanya shi yin shiru yana dubansa. Idan bak da reasonable dalili, toh kayi shiru. Atoh....inji Ahmad, ya kara da fadin ai wannan shedaniyar yarinyar bata gan komai ba tukun, sai munyi maganin ta a wannan makarata, she started a fight she can't finish.... Tun ba'a yi nisa ba ta soma hawayen makirci don a tausaya mata,a'a wallah yanda ta dauko yin yakin sai an kai karshe da ita. Dariya suka soma yi, a yayinda Ameer yake bin su da kallo ba tare da yace wani abu ba. ** ** ** Washe gari ta kama ranar laraba, a ranar kuma Ameer zai yi wa yan ajin su ilham lectures. Tun da sanyi safiya ya kammala shiryawa tare da yin kari, sa'anan ya nufi cikin makarantar. Dayan bayan daya yake duban dalibai masu shigowa suna kuma gaida shi. Har ya soma koyarwa bata shigo ba, bai kuma fidda ran zuwanta ba har sai da lectures ya kai karshe. Da haka ya koma hostel, yana me rayawa a ransa sai jumma'a kenan za ta zo. Ranar jumma'an ma bata zo ba. Ya tsinci kansa da rashin jin dadin haka..a ransa kuwa yana me fatan ba sabida shi bane take kin zuwa lectures. Kwanar ilham takwas a clinic, likita ya shaida masu 'stress' ne ya kawo mata hakan da shike jikin ta bai saba da wahala ko ta ciki ko ta waje ba. Asalima bata taba sanin menene wahala ba a rayuwa sai yanzun da ta dandana a kurkutu. Duk zaman da tayi a clinic ta kiyin magana da kowa. Idan su Naziha sun matsa mata da magana shine take fadin yes ko no, sai kuma daga kai shikenan. A ranar da aka sallame su suka koma hostel, Amarah ta zauna gab da ita. 'haba ilham....wai shin yaya kika dauke mu ne? Ba bu yanda bamuyi ba, da ki fada mana abinda ke damun ki.. Ciwonki, namu ne gashi kin barshi yana ta cin ki ke kadai, please ki fada mana abinda ke damun ki, ko bamu magance maki abin ba, atleast zamu baki shawarari. Nan fa Naziha da yusrah suka tofa Albarkashi bakin su suma. Kuka ta soma yi, suna lallashinsa. ""ina mamaki da kuma takaicin yanda na sauya hali cikin kankani lokaci. Ba ni da halin fada, bani da halin musgunawa mutun, bani da halin ramuwa, amman wai duk sun zama halayena yanzun. Na tsani yaron nan, na tsane shi.! Duk a dalilinsa na zama haka, bazan yafe masa ba a dalilin sauya min halayena da yayi... Ta dan yi shiru na lokaci, tana me sharan hawaye. Na yanke hukuncin barin wannan makaranta, sabida har ga Allah bazan rubutu masa wasikar ban hakuri ba... "zaki bar makarantan fa kika ce? Yusrah ta tambaya cikin yanayin mamaki. Zan bar masa makaranta, idan ba hakan nayi ba, bazan daina tunani ramuwan abinda yayi min, wanda a hankali halayena zasu sauya gabaki daya. Haba dai..! Sabida yaron nan zaki yi quitting schooling din? Nan fa suka shiga ban baki akan ta hakura da barin makarantan. Kusan sati na biyu kenan bai sa ta ido ba. Duk inda yake tunanin zai ganta yana bi da dube dube amman ko inuwarta bai hanga ba. Hakan ya sosa masa zuciya, ya na me fatan Allah shi sa ba a dalilinsa ta daina zuwa lectures ba. Yau din ya fito ne daga koyar da yan ajin su. Tafiya yake a hankali zai koma ajinsa, don daukan darasi. Kamar ance ya waiga, sai ya hada ido da su Naziha, da alama maganarsa sukeyi don har nunashi sukai da yatsa. Ya birki tare da juyawa zuwa inda suke zaune. "Assalamu alaikum......" yayi masu sallama. Fuskokin su a daure, ba tare da sun amsa ba, yusrah ta mike tana fadin 'ku tashi mu tafi ko? Nan ya sake yi masu sallama....."haba yan uwa? Sai kace ku ba musulmai ba? Kun kuwa san muhimmancin sallama kuwa? Yana rufe baki Amarah ta haushi da masifa kamar jiraye ta ke dashi. Banda kallonta ba abinda yake yi. "toh zata bar maka makarantan, burin ka ya cika ko? Ka ji dadi yanzun? Kallo daya zaka yi masa ka fahimci tashin hankalin da ya shiga karaf daya. Ya matsa gab da Amarah...." please dont tell me" Tsuki tayi tare da barin gefen sa "ku zo mu tafi" ta fada. Biye yake da su yana me rokon su da su tsaya su saurari abinda zai fada masa . Sai da suka kai bakin hostel, sannan ya hakura. Shit ya fada tare da rike goshinsa. A daren ranar Ameer bai runtsa ba....zancen zuci kawai yakeyi, yana ganin laifinsa. Shi daman a rayuwarsa baya son ganin hawayen mutun, especially mace. Bashi kuma kauna a dalilinsa ka shiga wani yanayi, shiyasa baya fada a rayuwarsa. Allah Allah yakeyi gari ya waye....don haka da sanyi safiya ya nufi hanyar hostel dinsu. Ya kai kimamin awa biyu tsaye idonsa akan gate din hostel, yana me duban masu fitowa. Yana hango su ya nufe su....."Assalamu alaikum. Yauma basu amsa masa sallamarsa ba. Don Allah ku saurare ni mana, da haka har suka shiga cikin makaranta yana biye da su. Kai...!wai ma kake so ne? Inace burin ka ya cika yanzun? Zata bar maka makarantan kamar yanda ka bukata? Nazhiha ce ke masa wannan maganar. Wallahi i never meant it....ni karan kaina banyi zaton abin zai kai haka. Itace ta dauke shi da zafi haka. I"'m very very sorry, please Yana rufe baki Nura tare da tawagarsa suka karaso gurin. Nan suka gaisa da su Naziha, cikin yanayin damuwa yace 'wai me ke faruwa ne, ilham bata da'ga wayata? I'm so worried gashi bata shigowa school, hope ba ciwon bane ya yi tsananii ko? Lafiyar ta kalau, tana neman hutu ne kawai yusra ta maidawa Nura. Sai a sannan ya kai dubansa ga Ameer "wannan pig din kuma fa? Me yake yi anan? Ya na fadin haka ne a yayinda da yake nunin Ameer da yatsa. Ohoo masa.! Amarah ta fada tana me hararan Ameer. Dan Allah ku zo mu tafi,nan suka watse suka barshi tsaye shi kadai. Daga wannan lokacin Ameer ya rasa sukuni. Ya rasa yanda zaiyi ya ganta domin ya bata hakuri.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.