Pages

Friday 23 February 2018

SOYAYYARMU 38👫

SOYAYYARMU 👫
    Written by Ganarious.
Page3⃣8⃣.

√•…KENYA NAIROBI,I ❤ u people.

√•…Labarin *KAZAMA CE MATA TA*..Yana nan a ganarious.blogspot.com/

          **          **         **
Hello aka fada daga dayan bangaren.
Muna magana na ne A'isha Al-Mustapha?.
Eh....A'isha Al-Mustapha ke magana da ku.

Ok...kina magana ne da mr. Wiliams daga House of P.O.P ta kasar landon.
Ok...ok..,ta fada a yayinda take da'ga kai kamar yana gurin.
Shekarun baya da suka shude, akwai wata mata me suna Hadiza muhammed, tayi ajiya anan house of p.o.p din.
Wannan ajiyan kuma tayi shi mussaman don ke....a opinions statement sheet din ta,ta rubuta cewan wannan ajiyan za'a baki shine ranar da kika cika 23yrs a duniya...kuma notifications dinmu sun nuna nan da wata biyu zaki cika 23din .
Personal information dinki sun nuna kina zama ne a kasar naijeriya don haka muke sanar maki da ki gaggauta shirin zuwa nan kafin ranar,sabida wasu gwaje gwaje da za'a yi don tabbatarwan ke ce.
Suna gama fadin haka suka kashe wayarsu..
Shiru ilham tayi,ta na son tuno wani.
Mahaifin mamee ya matso kusa ita yana tambayar lafiya? Suwaye ne suke kira?
Sai da ta juya ta dubi Hisham tukun wanda shike idonsa na kanta,sa'anan ta rike hannun kakanta suka karasa kan kujera.
      "Kaka.! Mamar mamee ta kan tafi dani u.k ko?
Kai ya da'ga..."eh, tana zuwa dake, meya faru? Ya sake tambayawa cikin matsuwa.

Tayi ajiya ne a house of p.o.p dake kasar london,ta kuma sanar dasu da cewan su mika mani ajiya a ranar da zani cika shekaru 23 a duniya,shine suke kira don na zo.
Ahaaf...kaji mutanen banxa,ba sai su aiko maki ba,da su ce ki tashi daga nan har kasan landan.!

Dariya tayi masa..."ah'ah kaka ba laifin su bane.
Watau gurin kamar gida ne ko nace kamar banki,zaka iya ajiya anan domin wani ko kuma wa kanka...idan karamin abu zaka ajiye kamar su takarda ko zinari ko lu'u lu'u da sauran su za'a baka akwati da lambar akwati din,dakuma komai na akwatin tau ba me iya bude ta sai kai din,ba'a kuma iya satan akwatin sabida a jikin bango aka kera ta..
Sa'anan idan ababe masu yawa ka kawo,kamar lodi lodi kudi,sai su baka daki,wannan dakin kofar ta ta computer ce,pin din da duk ka sa shi zaka bude ta dashi.
Shiya sa baza su iya aikomin dasu ba,yanxun ma naji suna fadin nazo nayi thumb print,shi yasa nake tambayarka ko mamar mamee tana zuwa dani landan,domin kuwa na tuna mu taba zuwa wani guri da nayi thumb print,alokacin ban san me hakan ke nufi ba,idan har gurine,tau fa lallai sai na yi thumb print din sa'anan zani samu access din wannan abin da ta ajiye din.

Ajiya zuciya yayi "tau gashi kuma kawunki na can,ya baro kasar".
Ahahh..ka manta can nake karatu?

Ah..haka ne fa kuma,tau shi kenan,idan kin koma gida sai ki sanar da mamanki,kiyi shiri ki tafi.
Sai bayan sallan isha'i, sa'anan sukayiwa kaka sallama.
Hisham ne ya maida ta gida.

Jikin mamee yayi sanyi lakaas da ilham ta sanar mata da abinda ya faru a gidan babanta.
tunanin mamarta ya sake dawo mata sabo,ilham bata kan so mamee na yawan tunanin mamarta,domin kuwa duk ranar da ta tashi da tunanin mamarta su kansu basu gane kanta har sai ta kwana da kwanki a sanyaye kuma ba walwala,wata sa'in kuma tayita koke koke.
ko yanxun da ilham ta sanar mata,idanun ta sunyi jajir,ta mike a sanyaye tace wa ilham ta kasance cikin shiri,zata shirya mata komai na tafiyar.

        **         **           **
Ganin mahaifiyarta bata da niyar sassautawa babanta, ya sa ta bashi shawaran da ya bar mata gidan na dan lokaci ya koma daya daga cikin gidajensa.
yaji dadin shawaran da diyarsa hajiya zubaida ta bashi..daman ko ya rasa kwanciyar hankali,ta kowani bangare baya samun sauki ga mutanen gari har na anguwa da suka sa shi gaba ana fadin daman sana'a 419, ya ke ya tara dukiyoyi haka?,yan uwa ko dariya suke masa, ga matar sa  da tun ranar da ya tako kafar sa gidan ta hanashi sukuni.
Sai da hajiya zubaida ta tabbatar da tafiyar mahaifinta sa'anan ta kwashi kayanta ta sallami mahaifiyarta.
gidanta ta nufa,da isar ta ta tambayi me gadi ko alhaji buba ya zo?.
A'a,bai zo ba ...me gadin ya maida mata.
Cikin gida ta karasa,ta tarar masu aikinta sun gyara ko ina tas.don haka ta shiga kitchen ta daura girki.bayan ta gama,ta shirya kulolin abincin a basket.
Kai tsaye gidan goggoji ta nufa da kulolin.
A falo ta iske Alhaji buba,da mahaifiyarsa goggoji,da kuma wasu jikokinta.
Ta samu guri kusa da alhaji buba ta zauna suka kara gaisawa.
Bayan nan suka shiga yin hira,irin ta anjima ba gan juna ba din nan....a cikin hiran take tambayar sa dalilinsa na rashin zuwa gida.
Shiru yay bai amsa ba.
sai da gari ya fara duhu,sa'anan ta ce da alhaji buba da ya tashi su tafi gida.
Kai ya girgiza tare da fadin, "gidan nan ba gurin zuwa na bane....nan ya sanar da ita duk abinda mahaifinta ya fada..
Ta shiga lallashinsa tana fadin bacin rai ne ya sanya shi fadin haka,yan kam kowa ya san baka da laifi a abinda ya faru.

Ganin bashi da niyar tashi,ya sa ta mike ta dauki jakarta tayi masu ssllama.
Ta nufi gida cike da takaicin abinda mahaifinta yayi mijin ta da take so kamar ranta.

Washe gari ta nufi gidan da mahaifinta ya koma da zama.bayan ya gama cin abincin da ta kawo masa,yayi mata godiya yana me tambayar yaya mamanki?
Cikin bacin rai ta amsa,ta kuma nuna masa bata ji dadin abinda yayi wa mijinta ba.
"Ai tau mijin naki ne sanadin duk abinda ya faru.
"Amman ai ba laifinsa bane...yanxun haka wani ne meyi maka hassada ya shirya wannan makirci din.
Shiru yayi, daga  baya ya ce zanyi tunani akan wannan lamarin.
A'a baba..! ga Gaskiya ka gani karara...ni fa bani son abinda zai girgiza min zaman aure na gaskiya, kuma mijina ya tsorarta da furucin ka.
Tau naji, yanzun me kike son nayi masa?
So nake ka bashi hankuri akan cin zarafin da kayi masa,ka kuma manta da abinda ya faru sabida ku daidaita.
Tau naji...ya fada.

Daga gidan mahaifinta,gidan Baba lamido ta nufa.
Ta tarar suna meeting akan auren hisham da hindo.
BAyan meeting din baba yusuf yayi kiran hisham ya sanar masa da cewan sun sanya ranar daurin aurensa da hindo.
Hisham ya rude kwarai da gaske,gidan mamee ya nufa,a bakin titi sukayi karo, zata fita shi kuma zai shigo,ta tsaida motar ta,shima ya tsaiyar tare da fitowa ya nufota.
Har kasa yake yana me gaida ta....kafin ya sake magana tace "su ilham na nan,ka karasa gida ko....zani na dubo babana.
"Tau a dawo lafiya,ina  kuma gaida shi.
Ya koma cikin motarsa ya karasa gidan mameen.

YAU ma kofan falon abude take,yayi ssllama tare da kuntsa kai.
zaune take kan dining chair tana shan fruits salad.
     Kamar yanda a duniya ba wanda ya kai sa sanin ilhma,haka ita ma tafi kowa sanin sa,ta san Hisham kamar yunwar cikinta.
Tana ganinssta fahimci hankalinsa ba'a keance yake ba.
Daga lokacin da yayi sallama take kallonsa har ya kai gun kujeru ya zauna.
kallonsa takeyi,tana son matsawa gunsa don jin meke tafe dashi,sai kuma ta basar.
zaune yayi yana dane dane wayarsa,sai huro iska yake ta bakinsa,daga baya yayi ajiyar zuci,
TSIntan kanta tayi da mikewa zuwa gunsa.
TA Zauna kan kujeran da ke fuskantarsa, nan ya dago kai ya dube ta tare da kirkiran murmushi
" me ke faruwa?...shine abinda kawai ta fada.
Shiru yayi bai amsa ta ba,sun dade a haka, ta kuma karanci irin yunwar da ke tare dashi don haka ta mike don samo masa abinda zaya ci.
ganin ta mike yasa shi rike hannunta,a tunaninsa fushi tayi sabida be amsa ta ba.
ta juyo ta dube shi,idanunsa duk sun canza.
"Please ilham ki ceci rayuwata ki amince da aurena....
uhmmmm.....kawai tayi ta cire hannunta daga nasa ta nufi hanyar kicin.
JIM kadan ta dawo rike da tire da abimci akansa,a gabansa ta ajiye tare da fadin bisimillah.
kai ya girgiza"bazani iya ci ba.
"Kaci mana ko da kadan ne" ta sake fadi.
Kai ya sake girgizawa ba tare da ya ce wani abu ba.
Ta sake mikewa ta nufi dinning inda take zaune kafin ya shigo,fruiys salad din da take sha ta dauko,ta mika masa tana fadin tau ga fruits.
Nan ma kai ya girgiza.
"Kasan dacewan kana tare da yunwa kuwa?...ta fada rai bace.
Bai amsa ba,kuma bai karbi fruit din ba.
Ajiyewa tayi ta nufi kitchen,jim kadan kuma ta fito rike da roba yogot da kofi,ta iso gabansa ta bul-bula yogot din cikin kofi.ta matsa kusa da shi ta sa masa kofin a bakinsa,ya dube ta tukun sa'anan ya bude baki.

6:00pm mamee ta dawo,nan ta sanar masa ai nan da kwana uku ilham zata tafi london.
Ya juya ya dubi ilhamsuka hada ido, sannan ya maida kallonsa ga mamee yace mata idan baza ki damu ba,zani so na rakata.
Mamee tayi shiru na dan lokaci,saanan tace shikenan Allah shi kaimu.
Ba tare da ya sanar wa kowa daga cikin iyayensa ki yan'uwa ba ,ya bi ilham zuwa kasaar london.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.