Pages

Thursday 22 February 2018

SOYAYYAR MU 37

*SOYAYYARMU 👫*
By Ganarious.
         Page3⃣7⃣

√• Mutan *KENYA*,One lovvvve💝

√• *HIDAYAT ABIODUN YUSUF* u r kinda of  perfectly lady every good man is praying for.!...I pray u meet a perfect spouse as u..Ameen ya'rab.

√• visit 👉🏼 ganarious.blogspot.com/,for your skin Kia tips,hair treatments tips and all others.

             ***         ***
Kwana uku ilham tayi,a ranar da ta dawo mamee bata tunkareta da maganar su Hisham suka zo mata dashi ba,sai kashe gari bayan ta huta gajiyan tafiyat.

Zaune suke a falo,a yayin da mamee ke operating wayarta,ita ma ilham haka.
Shi kuwa abba ya kan dinning table ya na karatun littatafansa.
Wayar ilham ce ta shiga ruri...tana da'gawa ta fara magana ba tareda da ta bari anyi magana da'ga  dayan bangaren ba..'i'm discussing something very important with my mum,will surely get back to u when i'm done'..abinda ta fada kenan ta kashe wayar.
Hakan ya sa mamee suspecting dinta don daman bata ta'ba haka nan ba...
A hankali ta mike ta haye sama,satan kallonta mamee keyi,sai da ta shige dakinta sa'anan mamee ta mike ta lallaba ta bi bayan ta.
A bakin kofan ta tsaya tana me sauraron,domin kuwa waya take,sai dai me!...maganar da take yi a wayan bashi da ha'di da maganar su Hisham.
BAyan ta tabbatar da cewan ilham ta ga'ma wayar tayi sallama ta shiga dakin...gefen gado ta zauna,jiki a sanyaye ta dubi ilham,itama din mamee take kallo.
"Naji labarin mahaifinki yana tsare gidan kurkutu ko?"
Kallon mameen take,ba tare da ta amsa ba.
GANin bata da niyar yin magana ya sa mameen fadin "zani so ki je ki duba shi"
Tsubul ta mike kamar wace maciji ko kunama ta sara..gaban mamee ta dawo ta durkusa,gwiwowinta duka biyu a kasa..."ban ta'ba kin bin umurninki,ko sa'bq maki ba,haka zalika baki ta'ba sanya ni yin abu na ki ba,ba na kuma fatan Allah shi nunamin ranar da zani sa'ba umurninki......please and please mamee ina neman alfarma,don Allah kar ki tilasta ni yin hakan,wallahil azeem,har ga Allah bani son ganin mutumin nan....ta rike hannun mamee tare da cigaba da fadin "please mamee kar ki tursasa ni.

Ajiyan mamee tayi.."shikenan,ba zani saki dole ba.amman fa karki manta uba,ubane koman lalacin sa ubanki ne...sa'anan hannun mutun baya rubewa ya cire ya yadda.
Lokaci na nan zuwa da zaki fahimci haka,don haka bazani saki ala dole sai kin dubo shi ba...sai dai abu daya nake so dake.
fiddo ido tayi tana me sauraro me memee ke shirin fadi kuma.
"Idan har kinsa kina da hannu ko kume ke ce ki ka sa aka tsareshi,ina me umurtan ki dakiyi gaggawan sanya wa a sake shi ,kuma duk wani plans da kikayi ko kike shirin yi akan su,tau ki wargaje su.
Shiru tayi,sai idon da ta sawa mamee.

...." kina jin abinda nake fa'da maki kuwa?
Eh....naji mamee,amman....
Da hannu mamee ta dakatar da ita, "bani son jin wani abu,rashin dakatar da wadannan plans dinki zai sa nayi fushi dake,fushi kuma na hakika..don haka zabi ya rage naki.'kar ki manta rashin jin maganar mahaifiyata abinda ya janyo min'..
Tana kaiwa nan ta mike,har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyi tana duban ilham,tate da fadin"ina fatan zuwa gobe zani ji fitowarsa ko?

Ta ja kofan bayan ta fito da'ga dakin,labewa tayi tana jiyo ilham din tan bugun kasar dakin ta tana fadin "oh my Gid,oh my god mamee why..ta mike ta shiga shurin gadon ta da kafafunta.
Mamee dake labe ta fashe da dariya,sa'anan ta nufi Dakinta.

Anyi transfering alhaji buba,da surukinsa.watau mahaifin hajiya zubaida zuwa abuja sabida shirin shigar da case dinsu babban kotu.....
A ranar da kotu ta umurci da a zo dasu,ake sanarwa da babban lauya cewan an ba'da umurni da'ga embassy cewan a kyalesu,domin kuwa me karan ya gan takardunsa.
Nan ta ke kotu ta ba'da umurni da a sake su,sai de masu tsoron nasu sunce sai akan beli za'a sake so,don haka kowa ya kawo lambar wanda zai zo belinsa.
Mahaifin hajiya zubaida ya bayarda lambar abokinsa, ayayinda shi alhaji buba ya bayr da lambar Baba yusuf.
Ana sanarwa alhaji yusuf yayi kiran yan uwansa ya sanar da su ba'a ba'ta lokaci ba kowa ya harhado abinda ke gare sa,don haka ya dauki hanyar kaduna tare da baba lamido da kuma Hisham.
Sun jima zaune ba'a bi ta kansu ba har sai da abokin mahaifin haj. Zubaida ya iso,sa'anan yan sanda suka saurare su...bayan yan rubuce rubucen da suka yi,da'ga karshe su bada izinin cewan kowa ya tafi da nasa..

Murna gun yan uwa da abokan arziki.
A gidan goggoji yan uwa suka hadu tarban Alhaji Buba.

Gidansu kareem hisham ya nufa cike da farin ciki..a nan din ya tarar da kaseem,ya sanar masu da labarin abinda ke tafe dashi, ya kuma nemi alfarma da suyi masa rakiya zuwa gidan mamee domin yi mata godiya.

Yau din ma a falo suka tarar da ita.
Zaune take kan lallausar kujeranta ta alfarma, a yayinda abba ke kwance tare da daura kansa bisa kafarta yana me karanta mata fairly tales,tana sauraro,a yayinda take shafar kansa.

Abba yanajin muryam hishma yayi sallama,ya mike,a guje ya karasa gun hisham din ya rungume shi..
Hisham ya rike hannunsa suka karasa cikin falon inda mamee ke zaune.
A tsanake suka gaida ta,sa'anan suka zauna.

Cikin farin ciki Hisham ya shiga yi mata godiya bayan gaisuwat...na yake sanar da ita an saki baba buba da surukinsa.
tayi mada barka tare da fadin yanzun dai kam za'a dunga cin abinci ko?
keya ya shiga sosawa yana me yin murmushi.
Da haka har lokacin sallah ya gabato,mikewa sukayi sukayiwa mamee sallama.
abba na makale da hisham,suna fita waje ,hisham ya duka dai dai kunnesa yana meyi masa rada.."wai ina ilham ne"
ta'be baki yayi yace tana dakinta.
Ido waje😳...Ashe tana cikin gidan nan ,duk dadewar da mukayi shine bata fito ba..
SAKE Dukowa yayi "nuna min windon dakinta a nan.
Juyawa abba yayi, a yayinda yake nunin sama,inda dakinta yake "gaaa......",ganin be karasa maganar ba yasa hisham da'ga kansa yana duban inda abba ke nuni.

👸🏻gimbiyar ce tsaye rungume da hannayenta,ta zagaye kirjinta da su...duk abinda sukeyi akan idon ta ne.
Murmushi yayi mata,ya aika  mata💋 kiss da'ga inda ya,ganin bata motsa ba yasa shi nuna kansa🖕🏼🙅🏻‍♂👉🏼,ma'ana *I love you*...
Ta fahimci abinda yake nufi sabida yasa ba da hakan tun suna makaranta...barin jikin windon tayi ganin kareem da kaseem ma ita suke kallo.

Mahaifiyar hajiya zubaida tana sane da dawo wan mijin ta don haka take shirya masa bala'in da zai tarar,....banda hakuri da ban baki ba abinda haj. Zubaida kiyi.
Ganin mahaifiyarta ba'ta da niyar sakko wa yasa ta ji haushi. Fiiszqn jakkarat tayi,tayi hanyar fita don zuwa gida tarbon mijin ta.
tana fitowo tayi karo da mahaifinta tare da abokansa ,ta karasa gunsu cikin farin ciki tana yiwa mahaifinta barka.
sallamarsu yayi daidai da fitowar mahaiyar haj. Zubaida rike da karamar bokiti.
Ganinta yasa shiyi mata murmushi yana me murnan ganin matansa.
A tsakiyar falo suka ga'me a yayinda abokansa ke shirin zama.
shi kuwa tsaye yayi yana wage hakoransa,bokitin ta da'ga ta kwara masa daga saman kansa zuwa kasa...ALLAH ya taimake shi ya dukar da kansa.
MIYa ce a cikin bokiti.
"Azzalumi,munafikin,macuci kawai....mazinaci me ya'yan banza".
Haj. zubaida ta karaso gaban mahaifiyarta,hannun ta sa tana me toshe mata baki.
KOKAri takeyi domin ganin ta cire hannun haj. zubaidan,ita kuma ta ki cirewa a yayinda take fadin "haba mama"
Cikin sa'a ta samu ta cire hannun haj. zubaidan,tare da ture ta da karfin ta,kafin ka sani haj. Zubaidsn ta zube a kasa.
'Shege me shaggu...ta shiga tafa hannunwata a yayinda take cin mutunci cikin da'ga murya.
...."mazinaci me shaggu,hu hu hu kaji kunya azzalumi kawai,da yardan Allah sai ka tozarta a nan duniyar har lahira..sai kayi da ka sanin dawowanka wannan gidan don da zaman ka kayi a kurkutu zaya fi maka.
Ganin zagin cin muyunci ba sassauci ya sanya hajiya zubaids mikewa,ta rike mahaifiyatya tana janta da karfi...da kyar da kokawa ta samu ta shigar da ita cikin dakinta.
sololo...yayi,a yayinda abokanss suka yi mutuwar tsaye sabida abin al'ajabin da suka gani a yau......sun dau lokaci ba wanda yayi magana ko motsi cikinsu,sai da'ga baya daya daga cikinsu ya karasa gun mahaifin haj. Zubaida ya dafa shi.
"Ka daure ka shiga ciki don tsaftace jikin ka.
Hakan ya sa sauran sanya baiki,suna kuma bashi baki akan kada ya biye wa mahaifiyar hajiya zubaida....suna tsaka da bashi shawarwar da nasiha haj. Zubaida ta fito,..nan suka shiga bata baki da kuma gardadinta akan cewan tayi iya kokarinta dun ganin cewan wani mumunan abu bai faru a tsakaninsu ba.
godiya tayi masu, sa'anan suka sallami mahaifinta zasu tafi...ba su kai ga fita da'ga falon ba mahaifiyar haj. Zubaaida ta fito a guje rike da tabarya.
Yana hango ta ya ruga a guje,haka abokansa ma..da gudu suka fita daga falon a tunaninsu ta fara hauka ne.
Hajiya zubaida ta biyo ta cikin da'ga murya tayi ihun fadin "mamaaahh..."
Kiran da tayi mata ya razanar da ita,tsak.! Ta tsaya don ganinta yi kamar ta hau iska ne.

Mahaifinta da abokansa ma tsayawa sukayi chakk!..yanzun kallo ya koma kan hajiya zubaidan....
Ganin haka yasa fasheda kuka tana meyiwa mamar ta fa'da...
Ita ma din ta fashe da kuka,tana fadin duk abinda zani yi wa mahaifinki,ban rama kwatan abinda yayi min ba,toh menene na ganin laifina?.
Ganin tana cikin hankalinta yasanya abokan matsowa,suna bata hakuri duk da basu sanda abinda ke faruwa ba.
Nan ta shiga yi masu bayani...hakuri suka shiga bata suna bata baki da nasiha,daga karshe sukayi mata alkawarin zai yi mata bayani,su fahimci juna.
     "Bana son bayanin sa,idan har yaran nasa ne toh wallahi idan ya tunkare ni da zance bayani zan kashe shi".

Da kyar suka shawo kanta da lallashi ta shiga cikin gida,tare da yi masu alkawarin baza tayi masa komai ba.

Hajiya zubaida na son zuwa ganin rabin ranta,watau alhaji Buba amman ba bu da'ma,sabida gudun kar ta tafi ta barsu suyiwa junasu illa.

     Zaune take duk lissafinta a da'gule take,tsuki tayi tace" kai mamee...naso na ganar da mutanen nan kuskurensu,na so su zo gaban ki su durkusa suna masu baki hakuri,sabida cutamaki da sukayi ammamn kuma ki tsinkemin lisafi....karan kararruwan falon ya tsinke mata zancen zucin da takeyi.
A hankali ta maida dubanta ga kofa,da shike ba'a rufe ta ciki ba.
Hisham ne ya turo kofan...ya kunso kai cikin falon da sallamarsa,yana me yi mata murmushi.
Kallonsa takeyi ba tare da ta dauke idon ta ba, ba ta kuma amsa masa sallamar da yayi ba...
Har ya karaso gunta bata dauke idon ta gareshi ba,hakan yasa shi xuwa gabanta,yatsar sa ya kawo gun idonta,bata kifta ba,ba kuma ta daina kallonsa ba.
Ya duko gab da fuskarta,fuskar sa  na fuskantar nata,yana kallonta cikin ido,ita ma din kwayar idonsa take kallo...sun dade a haka,sai kuma ya kai idonsa kan lebenta yana me kallonsu,da'ga baya ya shiga matsowa da nasa leben.
TAna jin le'bensa akan nata,ta kauda kai.
Murmushi yayi ya kuma dawo gefenta ya zauna gab da ita....ya kai bakinsa dai dai gun kunnenta ya rada mata "i missed those memories we had in school"...Nan ma bata amsa amsa ba,ya kwantar da kansa bisa kafadarta..yayi hakan ne don tayi magana,amman ta kiyi.ya mike ya dawo gabanta ,ya durkusa tare da daura hannayensa bisa kafarta.."come on ilham,ni ne fa Hisham,mutumin da kike si,can you please talk to me?.
ya juma a hakan yana me rokonta akan tayi masa magana,ta ki....yana a durkushen mamee budo kofa.
rikicewa yayi,ya rasa gun zama,ga kunya.
ganin yanda ya rude,ilham ta shiga yimasa dariya ba tareda ya ganta ba.
Mamee ta karaso cikin falon,da sauri Hisham ya durkusa yana gaisheta. Ta amsa masa cikin farin  ciki.
bayan sun gama gaisuwarsu da Hisham,sa'anan ilham tayi mata barka da isowa .
mamee ta dubi ilHam a yayinda take kokarin mikewa "Babana yace na fadamaki wasu mutane sun kira shi da'ga u.k,wai zasuyi magana dake.
Ya fada masu baki kusa,amman su kira karfen tara,gobe da safe.don haka gobe da safe idan ALLAH yasa muna raye sai ki tafi.
tau .....ta fada tana me mamakin wanda ya kirata a tsohon line-line telephone na gidan kakanta,wanda shike bata san lambar ba balle ta baiwa wani.
har mamee tayi nisa,sai kuma ta juyo,ta dubi Hisham tareda tanbayarsa ko anbashi abin shaa me sanyi.
dukar da kansa yayi cikin kunya ba tare da ya amsa mata ba.
ta kai duban ta ga ilham..."sai ki tashi ki kawo masa lemu ko?.

Washe gari da sassafe ilham ta shirya,ta nufi dakin mamee zuwa yi mata sallama.
Tana baro gun mamee ta yi karo da Hisham a bakin kofan falonsu,da'ga alama ya jima da zuwa,tsaye tayi tana dubansa.
😉gira ya da'ga mata.
Ta dauke kai tare bin ta gefensa,ya biyota yana fadin na zo yi maki rakiya ne...
cigabawa tayi da tafiyarta,ba tareda ta amsa shi ba...
YA Rike hannunta,na ta tsaya tana duban hannunta dake cikin nasa...
Ta da'go ta dube  shi"wai dole ne sai nayi maka magana?
Ya da'ga mata kai.
Ta sake duban hannuwansu tareda fadin sake min hannu.
KIN sakewa yayi.
"Ka sake min hannu nace ko?ta fadi hakan a fusace .
ya Saki hannun,ya kuma rike kafadarta.

Uhmmmm....kawai tayi,tana me dubansa.

😉gira yasake da'ga mata.
"Wallahi abu zai faru yanzun nan,idan har baka dauke hannunka da'ga jiki na ba".
Da sauri ya cire hannunsa,ta cigaba da tafiyarta.
Me gadi dake tsaye yana kallonsu ya girgiza kai,yana me yin murmushi tare da bude mata gate,yana yi mata fatan adawo lafiya.
Tana fita gate,hisham ya shiga motarsa ya biyo ta a baya.
Taku take a hankali,wanda dayawan mutane sun dauka kirkiranshi tayi,alhalin kuwa hakan Allah yayi abinsa..
nisa da ita yayi parking ya fito daga motan,ya tako ya sha gaban ta.
"Ki bani dama na zama drivern ki a yau,please ilham"..
Ta dube shi ta watsar tare da bin gefensa,ta cigaba da tafiyarta.
Ya sake binta ya sha gabanta,wannan karon harda durkusawa yayi yana me rokonta akan bukatarsa,..
waigawa tayi,ganin su jama'an gurin da masu wucewa duk su suke kallo...
Batayi masa magana ba ta juya ta nufin inda motansa yake a ajiye,sanin nacin HISHAM,gashi ba'a turai suke ba.
Tsale yayi ya mike yana fadin YES..!💪🏻,cikin jin dadi.
Tunda suka fara tafiyar take suburbuda masa masifa,da alkawarin idan yasake yi mata abinda yayi a yau tau wani abu zai faru😁😄.
Shiko banda dariya ba abinda yake yi.
Gidan kakan ilham,watau mahaifin mamee suka nufa..
A waje suka tarar dashi yana sauraron labarai a redio,ilham ta rungume shi a yayinda take gaida shi...ya amsa yana mai yi mata wasan kaka da jikansa..
Ya kai dubansa ga hisham, ya nuna shi da yatsa yace "wannan shine HISHAM.
Ta da'ga kai....eh shine.
Ya bude hannuwansa,da nufin hisham yazo,ya zo ya rungumeshi.
"Idon ka kenan hisham?.
Kallon kaka yayi yace kayi hakuri kaka...
Ya daga kai tareda fadin nasan ba kaifin ka bane ai.....yaya kake?.
Lafiya lau alhamdulillah,hisham ya maida masa.
Madallah....
bayan sun gama gaisawa da shi,suka karasa cikin gida..
hajiya cikin farin ciki ta tarbe su,tareda umurtan me aikinta da ta kawo masu abin breakfast.
Kayan tea aka kawo masu da soyayyan kwai da ayaba soyeyye.
Ganin abinda aka kawo masu,kuma hisham baya shan tea,yasa ta mike ta shiga kitchen.
Jim kadan taa fito rike da plate,a gaban sa ta ajiye ba tare da tacemasa wani abu ba.
Sayeyyean indomie ce ta ajiye masa,ya dube ta ya dubi indomie din yayi murmushi,yasan sarai ilham ya dauke da soyayyarsa.
9:00am dai dai wayar line-line telephone dake falon mahaifin mamee ya fara ruri,duban ilham yayi yace na tabbatar mutumin jiya ne don haka matsa ki dauka.
Cikin faduwar gaba ta kafa wayar a kunne tare da fadin "hello".

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.