Pages

Tuesday, 13 February 2018

SOYAYYARMU 36

SOYAYYAR MU👫
      By Ganarious.
Page 3⃣6⃣

        **       **         **
Mahaifin haj. Zubaida bashi da aiki sai tsinewa Alhaji Buba, ya na me da na sanin shigowarsa a rayuwar sa.
      Yan sanda ko na aikinsu na horansu,akan su fiddo takkardun.
Bincike ya nuna masu lallai takardun na hannunsu..
Mahaifin haj. Zubaida ya shaidawa Alhaji Buba da cewan da zarar sun fita daga nan kurkutun,tau za shi raba auren Alhaji Buba da na yar sa,ba shi ba,hatta abinda duk ya mallaka Alhaji Buba da yan uwansa,yana son a maida masa..

Mahaifiyar haj zubaida ce zaune tayi tagumi,abin duniyar duk ya sha mata kai, ya chikwikwiya mata..a yayin da ita kuma haj. Zubaida ke zaune gefen ta tana surutan ta.

Mama!...haj. zubaida tayi kiran uwar.
Ta juyo,ta dube ta ba tare da tace wani abu ba.

Gaskiya ki zo mu tafi gun bokan ki na nijar yayi mana aiki, duk wanda ya sace takardun nan ya maido su.
Mmmmmhhhh...haka ne fahhh,kinyi gaskiya.tunanin haka bai zo min ba,da ba'a tafi da mahaifin ki ba.

Me zai hana muje gobe?
Shikenan,muje gobe din...zuwa anjima zani je nayi mata shatan private jet.
Hajiya tayi murmushi "bazan kyale wannan barawon ba,wallahi sai na sanyawa ko wanene gu'ba ya sha"

Washegari sun shirya suna zaman jiran lokaci.karfe 12:00pm jirgin su zaya tashi wanda zai kai su har inda za su tafi,ya kuma dawo da su.
Hajiya zubaida ke fadawa mahaifin ta irin wulakanci da tozarci da zatayi wa duk wanda ya saci takardun nan....
....hayaniyar da suke jiyo wa daga wajen gate ya sa ta dakatar da maganarta,sun dan saurara "kamar muryan mace ki? Hajiya zubaida ta fada,a yayin da ita kuma mahaifiyarta ta kasa kunne ta ji da kyau..
Me gadi da ne fa nake tunanin yana sa'in sa da wata.
Mahaifiyar haj. ZUbaida tayi kiran me aikinta tare da umurtan ta da ta tafi bakin gate ta dubo abinda ke faruwa anan.

Jim kadan me aikin ta dawo" wata mata ce megadi ya hana ta shigowa shine suke sa'insa.
Ta mike ta fita zuwa bakin gate din....ta tadda matar tayi dammara,sai kokawa takeyi da me gadin...tsawa tayiwa me gadi ayayin da take kokarin raba su da hannunta...
..."bakubda hankali ne"..ko mahaukata ne ku??.
Matar da da'ga mata hannu,cikin tsiwa tace "bashi da hankali dai,mahaukacin megadin  da kuka ajiye..wallahi sai na koya masa darasin da bazai manta ba a rayuwa,tunda kaki ka sauri ko ni wacece,balle ka san matsayi ga me gidanka.
    Ganin fitsara da rashin kunyar matar ya sanya mahaifiyar haj. Zubaida yin shiru,sai bin ta take da ido,tana me mamakin dalilin zuwan mahaukaciyar nan gidanta.
Hajiya zubaida cevta iso cikin takama da isa.
"Kehh kehh kehh...ta fada a yayinda take dakatar da matar.
A wulakance ta dubeta da samanta zuwa kasa ta watsar...."mahaukaciyan ina ne ke,da zaki zo gidan mutane kina hauka?.

Kehh zubaida...matar ta fada cikin da'ga murya, ayayin da kuma take nunin haj.zubaida da yatsan ta.
   "Ni kike kira da mahaukaciya?!.toh ki sani watarana sai kinyi da kin sanin fadin haka don sai na tabbatar kinyi haukan nan da kika min kirari da shi.....wannan gidan da uban da kike takama dashi na baki aronshi ne na dan lokaci domin kuwa ni da yarana zamu kwaci incinmu nan ba da dadewa ba.
Ta cire dammara daga kugunvta,ta dubi mahaifiyar haj. Zubaida da take a daburce
"Na zo dubiyan uban ya'yana ne sabida kwana biyu naji sa shiru,da fatan ba mutuwa yayi ba....idan ko haka ne ,tozarci ta riske ku,domin kuwa sai na wulakanta ku yanda baku ta'ba zato ba.

Ta juya ta fara tafiyarta,a guje mahaifiyar haj. Zubaida ta bi bayanta tareda chakume ta,tana fadin "sai kin fada min hadin ki da me gida na".
Tureta ta yi da karfinta,domin kuwa saura kiris ta sha ka'sa..."kina son sanin hadi na da shi?...idan ma tafiya yayi,in ya dawo kin tambaye shi yaran sa faisal,farid da aminu da ya boye a garin Gombe...da'ga nan bata kara ba,tayi tafiyarta.
Mutuwar tsaye mahaifiyat haj. Zubaida tayi,da kyar haj. Zubaida ta shawo kanta sa'anan suka shiga cikin gida.
Tana zaunar da ita ta fashe da kuka tana me zagin me gidan ta hadi da tsine masa.

11:34am haj. Zubaida ta umurci mahaifiyarta da ta tashi su tafi airpot,sabida tafiyarsu ta zuwa nijar din.

Hawaye ta share.."wa? Allah shi sauwwaka naje nijar sabida macucin nan,sun dade  basu rike shi a can din ba.
Haba mama...haj.zubaida ta fada a yayida ta maida fuskarta na tausayi.
Wallahi ba inda zani je....sayar da komai nasa zani yi kafin ya fito,don bazani tashi a tutan babu ba, sabida ya sami ma'ga da.

Haba mama...karyiwa babana haka mana...!da'ga jin maganar wannan matar ko nace mahaukaciya sai ki dauki zafi kina zargin mijin ki.

Ba wani nan...wallahi maganar ta akwai kamshin gaskiya.
Hajiya zubaida ta kara marairacewa tana me bawa mamarta hakuri sai kam tayi nisa domin kuwa baza taji kira ba,balle ta saurare ta.

         **         **      **
   A gidan baba yusuf akayi taro,domin yin shawarwari yanda zasu bulowa al'amarin da ke faruwa a wannan familin.
Gaba dayan su sun hallara,su kuma tattauna akan al'amarin Alhaji buba da ke tsare a kurkutu.
Mafitan dai guda daya ce shine kuma addu'a,abinda kawai suka yanke kenan,su dinga yi masa addu'a har Allah ya fidashi da'ga nan.
bayan sun gama shawarwarin Hisham ya fada masu da su bar masa komai, inn'shaa'Allah zaiyi kokari ya gan cewa komai ya dawo dai-dai...
wata zuciyar ta raya mas da ya fada masu su je su baiwa mamee hakuri watAkila hakkinta ne ya kama baba buba..da sauri yace wa zuciyarsa a'a.
a karshe ya shaida masu zaya je lagos cikin satin nan don dubo baba Buba.

kai da komawa yake yiyana me cizon yatsan sa.
kaseem da kareem kuwa sai binsa suke da ido,ganin bashi niyar natsuwa ya sanya kaseem riko shi ya zaunar.
"na fada maka yanda zaka kawo karshe wannan halin da kuke ciki?
Kai ya dago ya dubi kaseem din,ba tare da ya amsa ba ya mayar da kansa.
"Ka amsa ni ma'nah...shin kana son kawo karshen wannan kuncin da kai da yan uwanka kuke ciki.
Kai ya da'ga yana m kallon kaseem din.
..."toh ga shawara,amman fa duk abinda na fada zakayi ba gardama.
Ido kawai ya sawa kaseem.
"Zuwa zakayi gun mahaifiyar ilham din, ka bayyana mata komai,ka fada mata halin ilham..ka fadamata abinda ilham keyi da kuma wanda take shirin yi..ka fadamata ilham is behind the anxiety and difficulty ur families a facing...ka roke ta da Allah da annabi da ta hana ilham abinda take yi,hakan zai sa komai ya zo karshe,domin kuwa ita kadai nake ganin zata hana ilham daukan wannan act din.

Gaskiya na goyi bayan shawaranka...hakan kuwa ya kama kayi hisham,sabida ita kadai ce zata iya stopping ilham da aiwatar da kudirinta....fadin kareem
Hisham ya yi ajiyan zuciya..."thank all for your support, inn'shaa'Allah zanyi yanda kuka fada amman sai dawo da'ga lagos .
Karfe bakwai da yammacin ranar su kareem suka yi masa rakiya zuwa airpot,sun kuma shaida masa gobe zai iske su anan din don tarbonsa.
Hotel hisham ya kama,sabida bashi da dangi a lagos sai dai abokansa da suka yi karatu tare...don haka anan ya kwana.

Mintuna goma sha biyar suka bawa Hisham don ganawa da alhaji buba.
Yan sanda biyu suka fito da alhaji buba,sun rako shi har inda aka tanadar domin baki masu zuwa.
Hisham na hangen sa ya tsira masa ido har sai da suka kusankaraso wa gunsa,sanan ya tashi ya rungume alhaji buba cikin murna.
Suna zama ya hangi ta'bo a fuskarsa,ya duba da kyau.."baba karfe wuta suka na'na maka a fuska?
murmushi yay tare da kama hannun Hisham.."ya ya kake,ya ya mutanen gida?..da fatan ba abinda ya same su ko? Duk lafiyar su kalau ko?

Hawayene suka zubo bisa kuncin Hisham,ya sa hannuya share yace "kowa lafiya lau baba..! Suna kuma gaida ka...da fatan basu horonka ko?

Girgiza kai yayi,kar ka damu da wannan..ina muhammad kanin ilham?
Lafiyansa kalau baba..
Ina gaida  shi sosai sosai idan ka koma.
Shiru hisham yayi...daga bisani,yace "baba ko na wakilce ka,na baia mahaifiyar ilham hakuri?..watakila za'a samu sassauci ga wannan al'amarin.

Kai ya sake girgizawa,"kar ka damu ,idsn Allah yasa na fito,zamu tattauna akan wannan.
..suna baka abinci yanda ya kamata kuwa?....hisham ya nemi sani.
Murmushi yayi ya da'ga kai,zaiyi magana masu tsaronsa suka tada shi,lokaci yayi.
Rike hannunsa Hisham yayi yana me hawaye.."baba zanyi kokari na fidda ka da'ga nan.
Murmushi kawai yakeyi wa Hisham a yayinda ake turashi...ya juyo yacewa Hisham da ya fadawa yan uwa su daina sawa kansu damuwa akansa.

Hisham ya fito gidan kurkutu yana me hawaye...
Bai ta'ba jin a ransa yana jin haushi ko takaicin ilham ba kamar ta yau. Ji yake kamar ace tana kusa ya shaketa....wayarsa ya ciro tare da nemo lambarta.ya rubuta mata sako kamar haka *your iman is weak,i do wish you could see how terrible and horible your actions turns ur onw father*...ya tura sakon tare da maida wayarsa cikin aljihunsa.
Ya tari taxi,yayi shatanta zuwa airport.
Yana isa airport sako ya shigo wayarsa, ilham ce ta maida masa martani kamar haka *oh my Goodness,it's a pity u just got to know that.i also wish u could feel or imagine the situation my mum went truu years back,which result of her loosing a wonderful mother*...a sanyaye ya maida wayarsa cikin aljihun wandasa.ya karasa cikin airport din.

Kareem da kaseem ne suka zo tarban sa as usual.
Ganin yanayinsa yasa basu ce masa komai...
A hanyar su ta zuwa gidan mamee kareem ya hangeshi ta madubi yana sharan hawaye,ya tausaya masa kwarai da gaske.

Suna isa gidan mamee ana kiran mangariba.a waje sukayi parkin,ba tare da sun shiga cikin gida ba,domin kuwa me gadi ya shaida masu mamee bata dawo ba,amman yana da tabbacin duk inda take yanzun yana hanyar dawowa gida,sabida mangariba baya riskanta a waje.
Sun tambayi me gadi ko da masallaci kusa ,yayi masu nuni da masallacin suka tafi.
Bayan sun dawo sallan mangariba me gadi ya yayi masu izini da su shiga domin mamee ya dawo kuma ya sanar da ita zuwan nasu
Har sunyi nisa,sai kuma Hisham ya dawo baya gun me gadi
"Don Allah idan baza ka damu ba inason nayi maka wata tanbaya
Megadi yayi murmushi yace 'a'a badamuwa,Allah yasa na san amsar tanbayat'
" ilham na ciki?
ah'ah..tayi tafiya jiya.
ALHAMdulillah .....ya fada,yayiwa me gadi godiya sannan ya riske su kareem suka karasa falo.
 
Mamee ta dauki tsawon lokaci bata fito ba.
Sai dai me..!
Ta fito ne rike da tire a hannu,blessin na biye da ita a baya,itama din rike da tire a hannunta,a saman dining table suka ajiye sannan mamee ta umurce su da su taso suci abinci.
kin tashi sukayi,har sai da ta sake magana a karo na biyu.
A kunyance  suka mike zuwa gun dining table din.
ta zubawa kowa nasa a plate,tare da fadin bisimilan ku ko?
kareem da kaseem sunyi *bismillahir.....* suka fara ci,don daman suna tare da yunwa.
ganin shi Hisham din bashi da niyar cin abincin ya sanya tayimasa magana.
"Kiyi hakuri mamee,bani da appetite, bani iya cin abinci
😳 waje mamee tace  sabida me?

"Wallahi mamee ina cikin damuwa,dalilinkenan da ya kawoni nan ki taimaka min ,domin kuwa ke kadai ce zaki iya magance mani matsalata....
Kafin ta yi magana,ya mike,taku biyu yayi zuwa gefenta ya durkusa gwiwowinsa kasa.

"Pls and pls mamee ki yarda da duk abinda zani fada maki,kar ki dauka maganar shirme ce.
Kallonsa kawai take yi,batare da ta ce wani abu ba.
Kamar yanda kika fada *SOYAYYARMU*da ilham al'amarin  abu ne da Allah ya kirkira.Allah kuma yasa kinsan da hakan,a duniyar nan bayan ke,duk wanda ke son ilham a bayana yake,inason ilham wanda shike bazani iya kwatanta soyayyar da nake mata ba...haka kuma na santa kamar yanda nake sonta, i'm sorry to say this,mame yanda na san ilham baki santa haka ba...nasan abinda zata aikata da wanda baza ta aikata ba.
😔Shiru yayi na dan lokaci sannan yaci gaba "nasan iyayena sun sa'ba maki,sun kuma cancanci ko wata irin hukunci,sai dai ganin wannan tsa-tsauran hukuncin da suke fuskanta ko nace suke shirin fuskanta ya ta'ba min zuciya...jini kenan.
Don Allah mamee ki yafe wa iyayena,hskan zai sa ilham ta yafe masuta kuma sassauta masu.

KALLOnsa kawai takeyi,tana me sauraronsa.
idanun sa sunyi jajir,sunyi taf da hawaye kiris ya rage su sakko.
"Daga lagos nake,naje dubiyan Baba Buba,wanda yau watansa daya da kwana hudu kenan a gidan kurkutu...ya share hawayen da suka sakko ya dubi mamee yace "Baba babu nacikin wani hali,tsorona kada ciwon zuciya ya kamashi, azaba iri iri suke horonsa da shi acan akan laifin da baiyi ba..
ya dakata da maganar sa.,ya ciro wayarsa.
ya budo sakonin ilham da tayi masa.
ya mika mata wayat tare da fadin don Allah mamee ki yarda dani.
ta maida masa da wayarsa bayan ta gama karantawa.
"Ilham tayi alkawarin duk wadanda suka sa'ba maki a baya sai ta tabbatar sun dan'dani kunci fiye da naki..
na kasa bacci sabida tace mutun biyu da zai tafi kurkutun,ba zai dawo ba iya tsawon rayuwarsa.

Shiru yayi na dan lokaci,itama shirun tayi..."don allah mamee ki taimaka min,ke kadai ce zaki hanata..iyayena da dangina suna cikin wani hali,sun rasa farin cikin su,na san nayi son kai da neman wannan alfarman,alhalin abinda ya dace da su kenan,amma na kasa jurewa na kau da kai akan halin da suke ciki.
don allah ki yarda dani,ilhamce a bayan duk abinda ke faruwa .

Gyaran murya tayi,ta umurci hisham da ya koma saman kujera.
BAYAN ya zauna ta yi nuni da plate din dake gaban sa tareda fadin 'ci abincinka,kafin yayi sanyi.
Kiyi hakuri mamee wallahi duk yanda naso cin abincin bana iyawa.
Mikewa tayi ta dawo kusa dashi ta shuga bashi abincin a baki....tana tsaka da bashi abincin abba ya shigo a guje.
runguman Hisham yayi ta bayansa.
Hisham yasa hannu ya riko shi,tare da dawowa dashi gabansa suna fuskantar juna.."kayi fushi dani ko?
Eh nayi,amman ganinka yanzun yasa na hakura na daina fushin.
☺thanks...hisham ya fada

Yauwa uncle hisham yau zamuje gidan nan ko?...sabida nayi mafarki da mutumin nan wai ya kone a fuska.
hisham cikin mamaki ya ta'ba masa kuci.."ai mutumin nan yayi tafiya,amman kafin ya tafi,yabar sakon gaisuwa zuwa gareka.
Cikin bata fuska abba ya koma gefen mamee ya zauna.
Mamee ta cigaba da baiwa hisham abincin,
...."laaahh ,ka gode anty bata nan da tace kato da kai ake bawa abinci a baki.
Kaseem da kareem dsi yan kallo ne,domin kuwa sun gama cin abincin su tu da dadewa.
sai da abinci ya kare a plate din sannan mamee ta sarara masa...tayi masa alkawari komai zai dawo masu dai-dai inn'shaa'Allah,don haka ya daina damun kansa.

Daga gidan mamee gidan kakansa baba lamido ya nufa,ya shaida masu komai ya kusan zuwa karshe da yardan Allah.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.