Pages

Friday 9 February 2018

Page 35 of Soyayyarmu

SOYAYYARMU 👫
     By Ganarious.
Page3⃣5⃣

💞so da kauna ga mutan *Kenya nairobi*💞
.         **         **        **
Mahaifin haj. Zubaida zaune,yana yi wa bokansa bayani rai a bace..sai huci yake.
Yayi masu bayani cewan ya tarar da surukinsa ya ba'tar da takkardun kanfanin da aka aiko.
Bayan sun gama sauraronsa,daya daga cikin su yayi mass jajen kudinsa da ya aika,ya kuma bada shawaran da ya ajiye surutaka a gefe,ya matsawa Alhaji buba ya fito da takardun.
sauran mutanen sun goyi bayan shawaransa.
Alhaji Buba da ke zaune cikinsu yayi gyaran murya yace "wallahi sace takardun akayi'
Tsawa mahaifin haj. Zubaida yayi masa..ya shiga zaginsa yana fadin "macuci kawai,na dade da samun labarin cutar dani da kakeyi sabida kana son ka mallaki dukiyoyi na ta wata hanya ko!..yan uwan duk ka sayan su hanyar sace min dukiya,ko kana tunanin banda masaniyar haka ne....toh wallahi wannan karo kam,ba zaka tsira ba matsayaci kawai.
Talakan banza...idan ta kama zani raba aurenka da diyata.
Kuma na baka yau zuwa jibi ka fito da takardun nan,idan ba haka ba  ko!..duk abin da ya biyo baya kai ka saya..don sai na sa an rufemin karkakaf din matsiyatan dangin nan naka,hatta jariri bazani sarara masa ba.

Alhaji Buba ya koma gida yana me jin zafin cin mutuncin da surukin sa yayi masa..
Ko kadan baya san abinda za 'a ciwa dangun sa zarafi balantana akai ga wulakantasu.
  Hajiya zubaida ne ta zo kusa dashi ta zauna,tana me bashi baki akan ya kwantar da hankalinsa za'a gan takardun.

      **       **       **
Hisham zaune tare da su kareem.
Kaseem ya dube shi yace "daga jiya zuwa yau ka faa'da.
Hmmmm...ba dole ba! Idan ma akace ina dauke da ciwon zuciya,ba zani mu'sa ba,wallahi na shiga damuwa sosai,yau fa saura kwana biyu sati biyun da ilham ta kudirta ya cika.
Kamanta mamarta ta tabbatar mana ba abin dai faru?

Hmmm...zuciya ta,ta ki amincewa da haka...ilham sai ya aikata.
Kareem yayi ajiyar zuciya yace ka kwantar da hankalinka guy! Mu bari zuwa jibi tukun
Gaskiya ka kwantar da hankalinka..ka gan yanda ka koma kuwa.
Ya taba kuncinsa yace "ai dole na rame ko don auren dole da suke sonyi min.
Dariya sukayimasa....suna fadin wasa daiiii.
Wasa???.....idan baku sani ba,yanzun ku sani har sun sa ranar auren nan da wata biyu.
Idanuwa waje suke ce yaushe  akayi haka?
Ranar da kuka kai ni gidan,daman kiran da sukeyi min kenan.

Tabdijam....da basuyi maka adalci ba gaskiya.
Lokaci ya kai da mahaifin haj. Zubaida ya diban ma Alhaji Buba,kuma ba alamun ganin takardun.

TUnda bayan dawowansa daga masallaci ya kasa samun natsuwa,sai addu'a yake Allah shi fisshe shi daga wannan tozarcin dake shirin afkuwa masa.
Karfe takwas dai dai,me gadi ya buga masu kofa.
Hajiya zubaida ce ta tafi bude kofsn...a yanda ta gan fuskan me gadi ta fahimci ba lafiya.
CIKin tashin hankali yace hajiya ga yan sanda can kofan gida fa.
Batayi mamaki ba, domin kuwa mahaifin ta ya sanar ma ta abunda zai biyo baya idan har Alhaji buba be kawo takardun ba.
Tana tsaye gurin ya karaso,shima din baiyi mamaki ba,domin kuwa da shirin sa yake.
Ya shiga daki ya chanzo kaya,ya dawo gun hajiya zubaids yana me neman alfarma da ta rokan masa mahaifinta kar ya ta'ba masa yan'uwa.
Ta rike shi gam...ba inda zaka tafi,yana jan hannunsa tana ja itama..
Suna cikin haka yansanda suka shigo..tureta suka yi sa'anan sukatafi dashi.

Mahaifin haj. Zubaids ya bada umurni da su horeshi har sai ya fadi inda takardun suke...kudi masu yawa ya bawa yan sanda,sun ji dadin haka sabida haka suka shiga gallaza masa azaba iri-iri.
Ssi da yayi kwana uku a hannun yan sanda sa'anan hajiya zubaida ta sanarwa yan uwansa.

Nan da nan labari ya kai kunnensu gabaki daya,ciki harda Hisham.
sun shiga tashin hankali marar misaltuwa sabida sakon da mahaifin hajiya zubaida ya aiko masu da su kasance cikin shiri,mudin Alhaji buba bai fidda takardun ba,toh ko jariri ba zaya ragawa ba.

Hisham ya shiga tashin hankali,ya rikice,ya rude...ba abinda ke fito wa abakinsa sai"ilham y..ilham why..
WAyar sa ya dauka yayi kiran kaseem da kareem.
Cikin dishewan murya yace kudirin ilham ya tabbata..haka kawai ya fada masu ya ajiye wayar.
Ba'a dauki tsawon lokaci ba suka iso.
Nan ya shaida masu abinda ke faruwa.
Mamaki suke...abinda ya daure masu kai, shine mahaifinta da ta fara dashi.

🤦🏻‍♂dafe goshi hisham yayi.."washh washhh..
a hanzarce suka matso gab dashi,suna tambayar lafiya?
Ya rike hannun kareem,ya ce jiri nake gani,gashi kaina na barazanar fashewa.

Ba su tsaya tunanin wani abuba,sun kamashi zuwa gun mota,daga nan suka nufi asibiti da shi.
Likita ya gama gwaje gwajensa ya dawo gare su.
YA shaida masu jinin sa ne ke son hawa...kuma ina me baku shawara da ku fadamasa ya rage tunane tunane.,ya kuma dunga samun isasshen baci
a ranar likita ya sallame su,ya kuma basu maganin da hisham zai dunga hadiya.

A hanyar su ta komawa yace wa kaseem su kaishi gidan baba Lamidi(kakansa)..domin sanin halinda suke ciki.

YA tarar da iyayensa da yan'uwa anyi chirko chirko, kamar an aiko masu mutuwa..nan ya shiga tausaya masu..
Hisham mutumine da Allah ya hallici ce shi da wani abu wai tausayi...
Ya nemi sanin police station din da aka tsare Alhaji Buba,
Ko ka tafi baza su bari ka ganshi ba fadin baba lamido.

TAFe suke akan hanyarsu ta maida hisham gida..kaseem ya nisa "yanzun menene abinyi?
A fusa ce kareem yace kawai a sanar wa mahaifin hajiya zubaida cewan su tuhumi ilham domin kuwa itace sanadin komai.
Kana ganin haka zai yi?...fadin kaseem
Me zai hana.
Tau ai ba wata kwararriya shaidan da zai nuna cewan itace ta aikata haka.
mu dai gwada yi haka don ceto bawan Allah,don da Alam wannan ilham din bata da imani.
har cikin ransa yaji furucin kareem,amman ya daure.

KASeem ya nisa yace mudai bita a hankali,domin kuwa wace zata iya aikata wannan abun komai ma tana iya wa kenan..

Suna kaiwa gidan hisham sakon text message ya shigo wayarsa.ganin ilham ce yasa shi saurin budewa jiki na rawa.
"Next person" shine kawai abinda ta rubuto masa.
Ya da'fe kirjinsa tare da jingina jikinsa a motan.
ganin haka yasa kaseem karasowa da sauri ya rike shi.
YA AMshi wayar ya karanta abunda ke a rubuce.
Da taimakon su hisham ya karasa falonsa.
 Zama sukayi,bayan sun zaunar dashi.
Gaskiya ya kamata ka sanarwa iyaye da yan uwanka abinda ke faruwa.
Ya fahimci qbinda kaseem ke nufi da haka,ya girgiza kai yace " soyayyar da nake yiwa ilham ya wuci haka...babban kuskurene sanar da su abinda ilham ke yi akansu..

So kake a kyaleta ta cigaba da saku cikin kunci?.
Kuyi hakuri,inn shaa'Allah zuwa gobe i will come up with a plan,yanda zamu dakatar da ita.
A ranar da alhaji buba ya cika sati,mahaifi haj. Zubaida ya baiwa yansanda cin hanci da su kamo baba yusuf su tsare shu,wata kila ba zai  rasa sanin inda takardun yake ba.
Hankula sun kara tashi,sai jeren giyan zuwa gidan mahaifin haj. ZUBAida suke,domin bashi hakuri da neman afuwa.
yayiwa megadi kashedi akan kar ya sake barin su shiganmasa gida,sai dai idan da takardu suka zo.

WASA wasa har Alhaji buba yayi satibiyu a gidan kurkutu.
Mahaifin haj. Zubaida zaune yana banbami wai alhaji buba ya ki fitowa da takardun,matarsa kuwa sai lallaminsa takeyi...suna tsaka da haka yan sanda tareda airforce suka faso cikin falon.
Ganin ka'ten maza yasa su jin tsoro.
Takarda suka ciro,suka bude tareda nunawa mahaifin haj. Zubaida.
Wannan warrant ne da ya bamu daman kama ka,akan laifin  amsan takardan kanfani ba tare da sa hannun me shi ba..
Embassy na japan dake wakiltansu a nan najeria,da kuma shugaban airfoce suka sa hannu domin a tafi da kai.
Babban police headikwata na birnin tarayya aka tafi da shi.
sun sanar dashi laifinsa shine amincewa tayi da kuma karban takardun da aka sato alhalin me kanfanin bashi da masaniyar haka.

Mamaki sosai yayi jin cewan me kanfanin na raye...yayi Allah shi waddai da rashin binciken da baiyi ba.
ya sanar da yansanda daga farko har izuwa halin da suke ciki na bacewan takardun...nan babban ogan yan sanda ya sa aka taho masa da Alhaji buba
Tambayoyi yayi masa daga nan yasa aka tafi da su kurkutun garin lagos kafin su gama bincike a shigar da kara kotu.
Hajiya zubaida ta shiga rudani, gashi da alama karamar hauka ta kamata.surutai kawai take,..sai fadin take mutane biyun da ta fiso a duniya ake shirin rabata dasu.
Nan da nan gari ya dau gulmace gulmace da labarai akan zance mahaifin haj. Zubaida da mijinta.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.