Pages

Thursday 15 February 2018

KAZAMA CE MATA TA 4

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
*KAZAMA CE MATA TA*
             ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
  Written by Ganarious.
Page4

√ *NAZIHA YARIMA✌๐Ÿผ*
√ *HIDAYAT ABIODUN*,.ONE love shall keep us together.

√jinjina ga yar'uwa *HADIZA GANA*

         **        **        **
Tun bayan da ya baro gurinta yake tunanin suwaiba ba irin macen ds ya ke so bane...qualitiez din da ke bashi sha'awa a mata ma, ta rasa su ko daya bata dashi.
   ...tsuki yayi"inna na neman ruguzamin farin cikin da nake hange a rayuwata.

Sai da engr.munir ya dauki tsawon lokaci, sa'anan ya sake zuwa gunta.....wannan karon shi kadai ya tafi.
Yau ma kamar ranar farko....shanya shi tayi,sabida ta dade bata fito ba,har ransa ya baci,yana tunanin ya tafi sai ga ta ta fito.
Gefen windon sa ta zo tare da kwankwasa masa gilashin,ya sauke gilashin yana me kallonya..."zagaya ta can,ki shiga gaban mota,
Allah ya taimake ta ta iya bude murfin,motan๐Ÿ˜œ..tana zama ta buga kofan da karfi wai ita nan ta rufe murfin motan.
Ta dubeshi tare da gaida shi,shima din ya amsa yana me kallonta.

Gaba dayan motan ta dauki warin hayaki...sai rayawa yake a ransa wannan wata irin yarinyace haka me halin * "ko'in'kula...ko irin kwas kwariman da yan mata sukeyi idan zasu fita ta'di,ba tayi.

Maganar tace ya dawo dashi da'ga duniyar tunanin da ya tsunduma.
"Mahaifina  yace na fa'da maka ka turo iyayenka sabida nan da wata biyu za'a yi bukin kanwata kuma yana son ya hada da nawa.
Sai da ga'ban sa yayi ras...jin maganarta,shiru yayi na dan lokaci sa'annan yace 'toh naji...ya sake yin shiru na dan lokaci sai kuma ya dube ta "miyesa baki sa turare ne?...
Juyowa tayi tana dubansa....tau kaka kake son nayi,tinda bani da shi?
Amman ai na baki kudi ki saya ko?
Eh....walla kudin nan abubuwa dayawa munkai dasu.,ta murmusa sanna  ta cigaba da fadin idan nace zani lissafa maka abinda munkai da kudi,duhu zai cimmana,ba tareda na gama fado su ba.
Yayi ajiyar zuciya yace "ni me son turare ne,idan kuma kina son mu shirya dake ki dunga sanya turare kuma ki zamto me jin magana.
Tau na ji'yah...zan duba ko zani samu ko da ta dari ce,ko ta dari da hamsin.
Jin takaicin ta yasa son barin gurin,don haka yayi mata sallama ba shiri.....dubu daya ya ciro ya mika mata "gashi ki sayi turaren"
Farin ciki ta shigayi,tare da yin godiya.
"A gaskiya idan na sake zuwa,ban ji kamshin turare ba raina zai baci..
"Innshaa'Allahu ka gama jin kamshin turaren....

Gidansu inno ya nufa bayan yabar gurin suwaiba..
Ya sanar da ita sakon mahaifin suwaiba,da ta fadamasa.
Inni cikin wage baki tace "toh toh madallah, ka gan kenan lokaci kadan ya rage, sai ka kasance cikin shiri..ka kuma bada abinda ya saukaka don a sayi kayan laifeh..
Tau inno, gobe inn'shaa'Allahu zani kawo kudin afara sayayya.
Yayi mata sallama sannan ya nufi gidan kanwarsa khadija.

Ya sanar mata komai game da zancen suwaiba,da kuma yanda sukayi da inno.

"Kenan ka amince da auren yarinyar nan?...cikin ba'ta fuska take maganar.
Kai ya girgiza...tau yaya kike son nayi?kin fi kowa sanin inno,rashin amincewa ta da hakan ma zai zama mani wani salon tashin hankali ne,gwara hakan dai.

Ya ta'be baki..."ni gaskiya da baka amince ba".
Sai a lokacin alhaji suleiman da ke zaune yana sauraronsu ya sanya baki.
"Shawaran da zani baka shike ka yawaita addu'oi,sallalo akan Allah shi zaban maka alkhairi,idan kuma babu alkhairi a tattare da aurennan,koda kuwa kwana daya ko sekan daya ya rage a daura,Allah shi ruguza shi ko ya kawo sanadi...
Shawarwari me karfafa gwiwa alhaji suleiman ya dunga bawa engr. Munir da'ga nan aka shiga hiran duniya.
Suna tsaka da hiran khadija da dauko zancen kayan le'fe..." gaskiya yaa  munir karka baiwa inno kudin kayan nan,ka bani kawai naje kasuwa na siyo,idan na saya sai na kaimata...na san inno sarai da shegen son kudin nan nata.
"Ah'ah kar kuyi haka,yin haka zai kawo maku abinda kuke gudan ma,idan har bata sayi abin kirki ba ko ta danne kudin kanta tayiwa...wataran ka sayiwa matan idan har ita din yar' kirki ce...fadin alhaji suleiman...da haka yayi masu sallama ya tafi gidansa.

Kudi masu yawan gaske ya baiwa inno.da na kayan le'fe, da kuma na kayan miya kamar su curry da thyme da za'a yi anfani da su lokacin buki.
Ya baiwa baban sa wasu kudaden da ya gyara inda ke bukatan gyara agidan,duk da sanin cewan babu.ya kuma bashi kudin abinci da za'a ci lokacin buki.

Shima din engr.ya kara gyaran gidan sa,duk da ba wani gyara gidan ke bukata ba,sai part din amaryansa da ya canzawa fenti.

Shiri ya kankama!...ranar daurin aure kawai ake jira,domin kuwa saura kwana uku kacal.
sai dai....gwamnatin jiha,ta umurni engr.munir da ya tafi jihar potakot domin setin wasu injinaye da aka shigo dasu.
engr munir ya nemi alfarma da su bashi kwana daya,bayan daurin aurensa....dalilinsa kuwa shine hangen abinda zai faru idan bai tsaya anyi daurin auren da shi ba,sanin inno da yayi da rashin fahimatr mutun.

Yau jumma'a,bayan sallar  jumma'a aka daura auren  engr. MUNIR & SUWAIBAH,...taro yayi taro domin kuwa makil gurin daurin auren yake da mutane....
engr. Munir me jama'a, abokan sa na social media wadanda bai taba gani ba sun zo,wadanda yayi karatu dasu, da wadanda sukayi yarantaka duk sun halarci daurin auren.
Yan mata ko, ba'a ce wa komai,sabida ko wace ta kasance cikin domin jiran  ko za'ayi dinning ko wani abu da zai sa matar engr. Munir ta zo,sabida suna son ganin wace ce wannan me farin kafan...sai kash, ba abinda aka shirya bayan daurin aure,amarya kuwa ko walima batayi ba..

Taro ya watse...amarya ta tafi gidanta, dangi da yan uwa gami da kawayenta da suka raka amarya gidanta sai santin gidan suke suna rayawa a ransu "da ma nice aka kawo nan, "da nicr na sami irin gidan nan" da dai sauransu...kowa sai tofa albarkacin bakinsa yakai,tare da yimata gargadin da kar tayi sakacin abinda zai sa wannan gidan ya sub'ce mata..
Da haka suka watse, suwaiba ta zama super star a cikin dangi,karkaf din danginsu,ta wajen baba da mama, babu me kwatankwacin irin gidan suwaiba...asalima ta kowani bangaren talakawane na hakika.
Amarya kadai aka bari,a yayinda ango ke waje da abokansa.
sai goma da rabi sukayiwa juna sallama,suka tafi shi kuma ya shigo cikin gida.
Ya rufe kofofi da winduna,sannan ya kashe fitilu...har ya kai dakinsa,sai kuma ya tuna fa yau bashi kadai ne a gidan ba fa.
ya karkada kai'a ransa yana fadin ko irin zullumin nan da angeaye suke yi shi baiyi ba,sabida sam sam yarinyan bata birge shi balle ta bashi sha'awa.

Hanyar sashenta ya nufa,ganin folonta empty ya bashi mamaki,ba kujeru balle t.v da sauran ababen ado,nan ma girgiza kai yayi, ya nufi dakinta..bude ya yarar da kofan a yayinda fitilun dakin ke a kune.
Kwance take bisa madaidaicin katifa,wanda ko zanin gado ba'a shimfida masa ba,sai ledan da katifan tazo dashi..da alama tayi nisa a barcin.
Da'ga bakin kofan yake kallonta, a ransa kuwa fadin yake wannan wace iri ce!...kayan jikinta ma bata cire ba,balle ta shimfidawa katifan bedsheet....wata kila ma wanka bata yi ba.
ya da'ga kafada yana fadin"anyway wannan ya rage gareta.
Ya kashe wutan,tare da jan kofan ya rufe.
Ya nufi dakinsa.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.