Pages

Sunday, 28 January 2018

KAZAMACE MATATA Page2

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
*KAZAMACE MATATA*
        πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
      By Ganarious
Page2

√gaisuwa ga jama'an kontagora.

√kuna rai na Hajiya Fatima A.Bayero, Nazhee yareemaπŸ˜„πŸ‘πŸΌ, Amina muhammad(jago) jagoness dita😘

                *****
       *BAYAN SHEKARU*
Tun bayan tafiyar munir kasar Paris, bai tako nijeriya ba sai da ya kammala karatunsa.

Ya tarar da wasu canji  a mutanensa,don kuwa mahaifinsa tsufa ya fara ja,kanwarsa kuwa khadija ta haifarwa alhaji suleiman mijinta ya'ya uku,..kuma ta dauke farida daga gidansu inno zuwa nata gidan,a yayinda shi kuma alhaji suleiman ya sanya Abdulwahab a makarantan kwana....sai dai inno kam tana nan da halinta sai abinda ya karu...
Munir yayi farin ciki tarar da wadan nan canji daman kuma adduansa kenan komai ya zamto daidai.

Ko huta gajiyar tafiya munir baiyi ba...domin kuwa washegari ya kwashi kwalifications dinsa ya nufi government house da su don neman aiki.
Ganin kwalifications dinsa yasa basu bata lokaci ba,suka bashi aiki dakuma babban matsayi lokaci guda....sunyi hakan ne sabida sun jima suna neman me irin fasahnsa a fagen naurorin komfuta,don haka basu son ya kubuce masau.

Allah ne me bayarwa! Allah ne ke nufan ka da Arziki,Allah ke daukaka bawan sa..ya kuma yi wa  engr.munir wadannan ababen da na lissafo.
Lokaci kadan ya budewa munir hanyoyin arziki,ya kuma daukaka shi..
Ta ko'ina kamfunoni masu zaman kansu sukan so ace dasu munir yake aiki,amman haka bata yiyuwa,sai dai idan suna da matsala fanin saita masu komfuta,ya kan taimaka a biya shi.

Engr.munir ya gyara gidan iyayensa, ya sa kannensa a makarantu ta kudi sa'anan ya baiwa matar ubansa inno jari.
Haka engr.munir bai bar yan uwan mamansa da suke kauyen dakin gari ba..yakan je masu ziyara ya kuma kai masu abin arziki.

Bayan ya gama da iyayensa,duk da ba'a gama hidiman iyaye..ya ginawa kansa gida.
Gidan engr.munir gida ne  da sai ka zagaye fa'din birnin kebbi baka gan irinta ba ko ma shigensa ba.
🏑 engr.munir ya zama *Topic*a gari,ya zama abin magana  da kwatance, yanπŸ‘±πŸΌ‍♀πŸ§•πŸ»πŸ§πŸ»‍♀πŸ‘©πŸ»‍πŸ’Ό kuwa sai mafarkin shiga gidan suke..uwa'uba,idan sun gan shi kansa me gidan..subhanalillah,sai kiji suna fadin dama ni zai aura ya saka ni a wannan gidan nasa,wata kuma tace ita tafi dacewa dashi da gidan sa..da dai sauransu

Haka yan matan birnin kebbi suka rinka ciwon kai sabida son kasancewa da engr. Munir,...ba yan matan kebbi kadai ba,duk garin da yaje sai yan mata sunyi rubibi a kansa..
Munir ya zama celebrity ga kwarjini,duk inda ya taka jama'a maza da mata na son kusanci ko abota da shi..yan matan social media kuwa sukan baro garinsu su zo birnin kebbi ko Allah zai sa suyi dacen ganinsa.

Ganin ya ajiye komai na rayuwa amma ba mata yasa yan uwan marigayiya mahaifiyarsa sunyi kiransa suka yi masa zancen aure,yayi masu godiya da alkawarin zai yi auren nan ba da dadewa ba.

Munir ya kasance yana neman mace mai tsafta,mai ladabi da biyayya,me kuma tsoron Allah wace zata tallafawa rayuwarsa, ta kuma bawa ya'yansa da zata haifa mashi tarbiya.
Tsai da mace yayi masa wuya,sai yake ganin kamar samun macen kirki a zamanin nan zaiyi wuya...ransa na bashi duk wace zata so shi don wani abu nasa zata so shi ba don Allah ba.
Yan mata kuwa da yake tunkara,nan da nan su sadaukar da komai nasu gareshi,ga rawan kai da rawan jiki,ba ko dan aji,hakan ko baya birgeshi.

Haka munir ya cigaba da neman mace tagari,a ransa kuwa cewa yake mata masu aji sun kare ne!...

          **   **     **.
Duk ranar jumma'a  idan an sauko daga masallaci gidan babansa yake wucewa.
Yau ma hakan ta faru,can ya nufa bayan an sakko sallar jumma'a.
a waje ya hadu ba mahaifinsa,suka gaisa.ya karasa cikin gidan nan ya tarar da inno tana fadi in fadi da diyarta habibatu,sai masifa take yi muryar ta na tashi.

Habiba na ganin munir tayi shiru,domin kuwa duk fadin duniyar nan ba wanda take shakka ko girmamawa kamar munir...shima kuma yasan da haka.
Ya baiwa inno hakuri yayiwa habiba nasiha da ta daina hakan.....
Yayi mata sallam zai tafi sai kuma ta tsai dashi,ya koma ya zauna yana ssuraron ta,a daidai lokacin mahaifinsa ya kunno kai ya shigo dakin da sallamansa.

"Yauwa malam,gwara da Allah ya kawo min kai,"
Cikin anashuwa yace tau tau tau...ta samu ne.?
Daman  wannan dan ,ta nuna munir da yatsa,   na samowa mata!...na gan alamar bashi da niyar bamu jikoki mu mora!
SHiyasa a matsayi na na uwarsa  nagan dacewan da na samo mashi mata..ko yaya ka gani?
Cikin jin dadi tare da wage baki yace " hakan yayi dai dai,kin kyauta.Allah shi saka maki da alkhairi...ya dubi munir da kansa ke kasa tunda ta fara magana yace kana jin abin alkhairi da inno tayi maka kuwa?.
Murmushin dole ya kago domin kuwa maganarta ta sanyai shi zazzabi.
Ya dago kai..yayi mata godiya.

Yauwa Allah shi yi maka albarka, ta fada sannan tace masa "idan ka tashi sai kazo isah ya yi maka rakiya zuwa gidan su yarinya,sunanta SUWAIBAH..ni da mahaifiyarta mun gama magana,saur su malam.

Daga gidansu,gidan su alhaji suleiman ya nufa.
Zaune ya tarar da su,a yayin da khadija take gyara masa farcenta.
Suna gama gaisuwa kahadijah ta dubi shi tace yaa munir lafiyar ka lau kuwa?
Me kika gani?..shima ya tambayeta
Ni ce fa khadija,na san yanayin ka idan kana cikin ko wani hali...kallo daya zanyi maka nasani.
Dariya alhaji suleiman yayi yace tau kalleshi ki fadaman yanayin da yake ciki

Ahhaaabb.....yaa munir cikin damuwa yake wallah..tana fadin haka tamike ta shiga kitcen
Ta fito rike da tire,ta jawo stool ta ajiye a gaban yayan nata tace masa bisimillah yaya.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.