Pages

Tuesday 30 January 2018

SOYAYYARMU 32

*SOYAYYAR MU👫*
         By Ganarious.
Page3⃣2⃣

Wannan page din naku ne,mutanen KENYA (NAIROBI)...ALLAH shi barmani ku.🤝🏼

        **      **       **
GAnin bata da niyar tashi,yasa na mike tsaye .
Na mika mata hannu,itama ta miko hannu na daga ta.
Tana tsaye nace muje ki kwanta!.
Ta girgiza kai..
A fusace na kara fadin muje ki kwanta ko!
..."ni gaskiya bazan  iya takawa zuwa dakin ba.
😳Ido waje nace sa "ya ya kenan tau?🤷🏻‍♂
Humm...🤔,sai dai ka goya ni,ko ka dauke ni.
"Raya wa nake a zuciyata ko na shake ta ne sabida takaicin ta nakeji?.
Murya kasa kasa,tace "kar kayi tunanin shakenin ko yimin wani abu fa,! Sabida mutane na kallonmu.
🙄mamaki ya cikani,yanda tasan abinda nake rayawa a raina.
Na matso gab da ita na bata bayana tare da risinawa..amman kuma ban cemata komai ba.
Ta hau bayan na kaita har saman gado.
Na sa lallausar bargon da ke saman gadon na rufe mata jiki sabida dakin ya garwaye da sanyi.
Na zari pilo,na koma saman kujera don kwantawa,sai na ji tana fadin "ka dawo nan mu kwanta
Hasbunallahu wani'imal wakil kawai nake fadi,ba tare da na amsa ta ba.
Ka dawo nan ka kwanta, ko kuma wani abu ya faru yanzun nan ...ta fadi hakan rai a bace.
Nan da nan na mike domin tsoron abin nan da tace zai faru,wata kila ta taramin jama'a gani ba ni da kowa a kasar.

Bargo ta sa tarufe mu ...tare da fadin kar kayi tunanin yi min wani abu".
Sannan ta juyamin baya,ni ma bayan na juya.
A daren ranar ban runtsa ba sai addu'oi nake...domin kuwa ilham ta daina bani mamaki,sai tsoro,sa ran nake tana tare da mutanen boye shiyasa take haka.
 Gab da kiran sallah bacci yayi awon gaba dani.
Ina farkawa muka hada 👀,ni kawai take kallo...zaune take saman kujera ta hade hannayenta tare da rungumarsu,ta daura kafarta bisa dayan..muna yi👀,gaba na yace ras!..a zuciyata ina fadin yo ko me wanna gimbiyar take kunsawa a ranta?
Na lalubo wayata domin duban lokaci,mikewa nayi a hanzarce ganin goma ta wuce,na shiga bathroom nayo alwala,sannan na gabatar da sallah,ranar ta farko kenan da na taba missing sallan asubahi tun tasowana.
Ganin bata motsa da'ga inda take zaune ba,yasa nima ban motsa ba tunda na idar da sallah sai rokon Allah nake da shi tsare ni a duk wani abu da take shiryawa a ranta...yanayinta kawai ya tsorota ni.

Jin motsin mikewarta yasa na saci kallonta,nan da nan ta juyo muka hada ido,nayi saurin dauke kai na.
Bata jima ba ta dawo rike da tire,ta ajiye a gaba na tace "inakwana"!.
Dar'dar na amsa mata da lafiya lau.
Zama tayi,ta dibo abinci ta kai baki na....haka na dunga cin abincin ina kallonta.
Ta gama bani abincin ta umurce ni da na shiga wanka..ban mussa ba nayi yanda tace😄.
Na fito wanka na tarar ta ajiyemin kayan sawa.
Bayan na saka kayan na zauna,ina tunanin yau kuma me take shirin yi.
Muna nan a haka,ba me ce da wani qalah,sai satan kallonta nake,ita kuwa tana gyaran farce.
A haka har lokacin sallah yayi,ta mike tace mu tafi masallaci..bayan mu dawo daga masallacin tayi ordering abinci anan hotel din,ba da jimawa ba suka kawo.
Bayan gama cin abincinmu,ta tashi zuwa inda kayanmu suke ta harhada jikin jakkuna..ta tako zuwa inda nake tace tashi mu tafi..
A raina nace "yo ina kuma zata kaini".
Airport muka nufa,ganin mun bi layin masu zuwa uk,na tsinci kaina cikin farinciki da godiya ma Allah.
Jirgin mu na sauka na ra'ba jiha da ilham..shatan mota nayi,duk da bani da kudi,amman nayi kira abokaina da su fito da kudi su jirani a bakin hostel dinmu.
Daga ranar da muka sauka,duk wani abu da zashi hadani da ilham ina kaudashi,fushi nake da ita sosai,hakan yasa na yanke duk wani mua'ammala da ita....hakan yana bakanta mata rai.
Ta kai gayimin txt,Amman ban amsa mata ba,sabida cike nake da haushinta.🙄
SAti biyu ina avoiding din ta...wataran zaune nake cikin abokaina sai ga ta ta zo gun.ta zo dai dai inda nake tace ashe kudi zai shiga tsakani na da kai...tayi ta surutan ta ba tare da na amsa mata ba..
Tana barin gurin da kamar minti goma,naji text a wayana,a zato na itace...sai da aka dauki lokaci sa'anan na duba wayar..'Bank alert ne' sunyi min refunding kudade na,an maida min da komai yanda yake a baya.
Mamaki ya cikani,na rasa abin ce wa,ina cikin haka text ya sake shigiwa kuma...wannan karon itace.
You've fail'.🙅🏻‍♀.shine abinda ta rubuto.
NAN take hankalina ya tashi,na shiga neman ta a waya amman ba ta dauka..na shiga tunane tunane yanda ilham ta sami kudin da ta maida min a account.
Haka ilham ta cigaba da gara ni kafin,sai da na garu sannan ta hakura muka maida *SOYAYYARMU*

Hisham ya dubi kaseem da kareem yace kunji dalilinda yasa na dage da cewan zata aikata duk abinda tayi niya.
       😄😅😂🤣dariya suka shiga yi masa sosai,tun can da yake basu labarin dariya suke masa.
Ya daure fuska yace idan baku da abin cewa,ku tashi ku tafi,ku barni nayi tunani abinda zan ce mata kafin gobe.
Yauwa!...kaseem ya fada,a yayin da yake nuna hisham,..idan zaka je gidan gobe,ka kira mu mu tafi tare.
Idan ta gan idanunmu dolenta ta saduda,ko kuwa ya dubi kareem.
Haka ne abokina,kasan sarkin yawa ya fi sarkin karfi....

Washe gari bayan sallan la'asar kareem iso daukan Hisham da motansa,daga nan suka nufi gidan su kaseem.
   Sunyi sa'a kuwa domin mamee na gida...ssi da hisham yayi tope-tope😃,sannan suka matsa bell..kareem da kaseem kuwa sai dariya suke masa..
Basu jima a gurin ba blessing ta zo ta bude masu kofa.
Da sallamarsu suka shiga falon,nan suka tarar da mamee zaune.
Tayi masu marhaba da zuwa,cikin fara'a..ta kuma umurci blessing da ta kawo masu abin sha🍷🥂🍸🍹🍾
Wayarta ta dauka tayi kiran ilham wai ta sauko kasa,ba tare da ta sanar da ita su Hisham ne suka zo ba.
A hanzarce ta fito daga dakin ta,sai dai kafin ta sauko sai da ta duba kasan falon tukun sa'anan ta fara taku daddaya,ganin Hisham ya sata ta hada rai.
Sannu a hankali take takowa kuma cikin takama da kasaita...daya bayan daya take sauke kafarya daga steps din,fuskar nan kamar ka gudu,sabida yanda ta hada rai.
Yanayi ya baiwa Hisham tsoro,su kareem da kaseem kuwa a ransu sai cewa suke wannan 'dodo ce'.
A yayinda idon mamee ke kan wayarta,bata san wainar da ake toyaa ba.
Kamshin turaren ta kawai ya sanar da isowar,mamee da dago ta dube ta.
"Sannu da hutawa mamee"..ilham ta fada,tana me shirin zama.
Yauwa sannunki..fadin mamee.
ta juya garesu,suka hada ido da hisham yayi saurin dauke kai.
"Sannunku da zuwa" ta fada cikin sanyin murya.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.