Pages

Saturday 27 January 2018

SOYAYYARMU 31

*SOYAYYARMU👫*
   Written by Ganarious.

👉🏼Annabi(s.a.w) ya kasance yana bude addu'arsa da *SUBHANA RABBIYAL ALIYIL A'ALAL WAHHAB*...Ahmad da hakim ne suka ruwaito shi daga maslamata dan akwa'i(r.a)

ganarious.blogspot.com/ ki shiga nan din ki duba yanda zaki gyara gashi da yin maiyukan gashi da kanki...nagode🤝🏼

3⃣1⃣
Ihu nakeyi,ina fadin noooo...no,nooo please don't do this to me.

Yana kaiwa inda nake daya daga cikin su ya zo a guje tare da dakatar dashi.
Yare suke ta yiwa junansu,ni dai ban fahimci abinda suke nufi ba,sai kawai binsa nake da ido.
Suna gama maganarsu suka fashe da dariya har shi me rike da takobin.
Nayi ajiyar zuciya a yayinda nake hamdalah a zuci.

Shi wanda ya dakatar da me takobin,ya karaso gaba na ya kama min hannu wai muje,da shike shi yana jin turanci...mu tafe yana min hira tare da fadamin sunansa...nan na tambayeshi yanda akayi na tsinci kaina anan.
Dariya yayi sosai yace "idan ka koma inda ka fito za'a sanar da kai.".

Tafiya muke ba kaukkautawa,munyi tafiyar da ta dauke mu kamar minti arba'in da takwas,ba mu hadu da mashin ko mota ba.
sai da muka bulo babban hanya sa'anan catapila ya zo wuce wa don haka macheal ya tsai da shi muka hau...yare yayi masa shima,da alama ya fadama sa inda zamu saukane.
Ganin mun shiga wani kauye ya sa na fara jin sanyi sanyi...
 Muna sauka meacheal ya nufi filin jirgin kasa dani muka shiga harda shi.
Awan mu shidda a hanya ga yunwa a tare da ni,ga salloli a kaina...muna cikin tafiya na tambayi mecheal wani gari ne nan?..yace min nan kasan Philippine ne.
Ido waje nace philipphine?
Yace eh...
Sai a sannan na tuna "bet" dina da ilham.

Mamaki ya cikani yanda akayi ilham ta kawoni kasar philippine..yaya akayi haka ta faru bani sani ba🤔!.. sai dai idan maganin bacci ta bani🙄

Babban birnin Manila muka sauka,watau capital din philipphine din kenan..muna sauka mecheal yayi kiran waya bayan ya gama magana a wayan ya jani zuwa wani gefe yace mu jira kadan.
Muna nan wata mota ta zo,don haka yace mu tashi mu shiga motan  a kaini masallaci nayi sallah..nayi masa godiya nace kamar kasan abinda nake tunani kenan.
masallaci suka nufa dani,sun kuma jira har na idar da salloli na, sannan suka nufi wani gida dai,ni dai sai bin su kawai nake amman a tsorarce nake.

Gidan kamar guest inn ne,muna shika nunamin toilet wai na shiga na hanzarta yin wanka sabida jirgin da zani shiga zai tashi nan da awa daya.
Ba nemi sanin inda kuma  za su kaini ba na shige toilet don yi wankan...sai a lokacin nake tunawa da wayata hakan yasa na sanya hannuna a aljuhun wando don ciro wayar ,ba waya a ciki sai wata yar gutun takarda me dauke da rubutun ilham tana cewa "da fatan kana jin dadin yawon?

Na fito wanka na tarar da su ajiye min abinci,sai dai abincin ba irin wanda zani iya ci bane,don haka na tsattakula na bar sauran a gurin.
Daga nan manila airport muka nufa.
Cikin dare jirginmu ya tashi ba tare da nasan inda muka dosa ba,addu'ata dai Allah shi sa london zani koma.

Ganin ba airpot din da na saba sauka bane ya sa na kariya..araina kuwa nace "ilham kin cuceni".

A hankali nake taku zuwa inda aka tanadar don tarbon matafiya..gaba na sai dukan uku-uku yakeyi sabida ban san inda zani dosa ba kuma idan securities ko polisawa suka lura da hakan,zasuyi zaton wani abu su kama ni,gashi bani da wata shaida ta shiga kasar,ba i.d card ba komai..Allah yasa jirgin ta yan kasuwa ce da masu bincike sun tsai dani.
Mutane sai tarban yan uwa da abokan arziki sukai ni ko ba alaman wanda na sani a guri,haka na cigaba da tafiya kamar hawayniya..wata yar budurwa ce ta taba ni,tace lafiyar ka kuwa?..maimakon na amsa ta sai nake tambayarta wani gari ne nan.
Huhh...ta fada ayayin da ta fiddo😳 idanunta waje  tana me mamanki tanbayata..
Kana nufin kacemin,baka san kana a dubai bane?..

oohps🤦🏻‍♂....sorry ba tanbayar da nake son yi maki bane kenan..
Tayi shiru tana jiran na tanbaye ta,rasa abin tanbaya nayi don haka nayi mata sallama kawai.
Sololo...tayi tana me kallona,nidai nan na barta,kafin ta tara min jama'a.

Ina barin gurin na hango kamar sunana,da sauri na tafi gun tabatarwa,..hakan dinne sunan ne rubuce barou  barau a katuwa takarda an daga shi sama,sai dai takardan ta rufe rabin jikin wanda ke rike da shi don haka ban gan ko fuskar ba...a rai na nace toh ko wa zani hadu dashi kuma?
Ina isa gurin nace "hi"
A hankali aka sauke takardan.

Ilham ce tsaye..tayi wurgi da takardan ,ta daka tsalle sai saman jikina...ta shiga sumbatata..,niko sololo nayi,ina dubanta.
Dariya takeyi sosai tare da rikemin hannu muka fito wajen airport inda ake ajiye motoci.

A zatona zatayi shatan motane,sai ganin nayi ta bude min gaban mota ta umurce ni da na shiga ita kuma ta zagaya gefen direba ta shiga...mamaki ya cika ni,yaushe ilham ta san dubai da zatayi tuki a gari...kai wannan tana tare da yan boye.
Kallona tayi ta fashe da dariya,tana fadin lots of talks ko?
Ban amsa mata ba sai kallonta kawai da nake.

Wata katuwar hotek ta nufa,wanda idan nace zan kwatanta maku kyau da tsarinsa tau fa sai gobe ko jibi zani gama baku labarin,muna shiga haraban hotel din tayi parking ta fito tareda zagayo ta gefe na ta bude min kofa,ta rikemin hannu na fito muka shiga ciki.

Cikin hotel din ma abin kallo ne,dakin da ta shigar dani kuwa ba'a cewa koamai...tsaye nayi ina waige waige,ta karaso inda nake ta rungume ni gammm..kamar ance mata za'a raba mu ko za'a sace ni.
Kan ta na saman kirji na,sai fadin take "i missed u,i missed u alot.....mun kai kamar minti shidda a haka,hannu na sa na cire ta daga jiki na ina me kallonta cikin ido..

TA fashe da dariya irin ta cin nasaran nan .banda kallonta ba abinda nake cos i was speechless..
ta sa yatsarta saman lebena tace "shiiiii🤫......I know  it all,u don't have to say it.
Sai lokacin na sami karfin yin magana.na ce da ita"ya'ya kikayi haka ilham"?

Ta sake yin dariyan..."kar ka ce komai".
Nop....ki fadamin yanda kika yi,na wayi gari a kasar philipphines,da kuma wadanda suka taimaka maki.
Dariya tayi tace, bazan ce maka komai ba yanzun,don haka dont ask..tana fadin haka ta mike. Sai ga ta ta dawo rike da wayana da kuma wallet dina,da sauri na karba wayat ...ta shiga dakin kuma ta fito.."tashi kayi wanka,ba tareda na amsa ta ba,na mike ina biye da ita har bathroom din,...zan ajiye maka kayan sawa asaman gado,idan ka fito ka sa..
.
Bayan na fito wanka na sa kayan,tsaye nake gaban madubi ina me kara kallon kaina,..budo kofa tayi ta shigo.
Wow..looking sweet ba laifi,ta karaso ta sumbace ni a kunci na,tareda rike min hannu muka fita.

Na cigaba da mamakin ilham,sabida sai da muka yawo ce kwatan garin nan,da farko Burj khalifa park muka fara zuwa,sannqn muka nufi down town da uptown, muka nufi desert safari,..anan take ce mani  ko ta sake batar dani ne nan...shiru nayi ina kallonta.
Ta sa hannu daga goshina zuwa kasan hanci na tace ko bazani iya ba?👱🏼‍♀....zaki iya wallahi🙄nace da ita..
Daga nan muka nufi fairy tale palace,hotuna kawaai mukayi anan sa'anan muka nufi masaukinmu,shima din sabida mangrib ya karaso ne.
Masallacin da ke cikin Burj khalifa hotel muka nufa,da shike akwai sashen mata...ba mu koma daki ba sai da mukayi sallan isha'i.
A falo na yadda zango,ita kuma ta shiga ciki tayi wanka ta fito.
Zaune nake ina operating wayana,sai gata..ta zauna saman kafafuna tare da kwantowa da jikinta saman nawa jikin.
Duk jiki na a mace yake,na kasa magana sai binta nake da ido.
.ta kawo bakinta setin kunnena ta radamin "idan na fada maka abu ka yarda kawai,don't doubt it"...abinda naso nayi maka ya fi haka,amman i dont want to miss....ta mike,ta taka inda rediyo yake a ajiye ta kuna wakar celinedion....duk dai idona na kanta,ta zo gurina ta rike min hannu tana fadin tashi muyi rawa..
Kallonta nake,ba tareda na tashi ba.
Ka tashi mana!!....ta sake fadi.
Nan ma ban tashi ba,ta bata rai tace wallahi zan sa a kullemin kai yanzun.
Da saurina na mike....sabida tuno maganar da ta gama rada min a kunne yanzun.😅
Dariya ta shiga yi tana fadin kace bani iyawa mana.
NA Girgiza kai nace kina iyawa ilham.

Muna tsakiyan rawa,tace daga yanzun sweet -moon din mu zai fara..ko ka manta na ce maka zamu zo sweet moon?.
A'a ...kawai na fada.

SAI da ta gaji don kanta sannan ta ce mu zauna...
Kwantar da kanta tayi saman kafafuwana....ilham kamar 🐈 take,akwai son jiki.
Muryana can kasa kasa na ce da ita,ina bukatan kiyimin bayani daga likacin da kika bani sweet din nan zuwa yanzun.
Tayi murmushi trace bayanin me kuma?.
...hmmmm amman dai kin bani kunya!,basiran kenan batar dani ba cikin hankalina ba?
Mikewa tayi zaune tana kallona tace wa ye fada maka,ba cikin hankalinka kake ba.?.
Eh mana ,sai da kika bani wani abu tukun.
Hummmm...hisham kenan, ok,lets do it this way,tunda ka kasa tuna komai,ka duba wayatka zaka gani..kuma yanzun tunda kana cikin hankalinka mu sake wata "bet din".
A'a nace da ita,ina me girgiza mata kai.
Murmushi tayi tace ka ji tsoro kenan.

Naji...naji tsoro din.yanzun ki fada min inda kika sami kudin nan da kike watangale dashi.
Ina na samu?
na daga mata kai,eh ina kika samu.
Ba wani kudi bane face kudin da ka bani mana.

Cikin  rudewa nace nace yaushe na baki kudi?😳.
Kai fa kace na kwashe duk kudin da ke account dinka sabida deal din yayi alrmashi.

Ban tsaya sauraronta ba na hanzar ta bincike ta wayanaa.
tsullll namike tsaye ina salati,ganin babu ko sisi a account na,ta wawushee komai.

Zufa ke karyowa ta ko'ina  a jikina,cikin yanayi tashin hakali nace "yaya kikayi ilham"
ta tabe baki tace ,kai fa kace na kwashe kudin,kuma dashi nake komai na deal dinmu,jirgin da ya kaika philipphine jirgi ne ta yan kasuwa,mu kadai ya kwasa,ya kuma maidani a ranar,ka gan kenan dole na biyasu kudinsu,wayanda sukayi yi maka komai ma a can,sai da na biyasu.,zuwa dubai dinka,wannan hotel din da muke ciki duk a cikin kudinka ne.

Salati na shiga yi,na sulale zaune,kai na rike ina tuna nin yanda akayi tasan passcode da secret number dina,wanda shike ban fadawa kowa ba sai mahaifiyata.

Mun dade zaune ba wanda yace wa wani qa'lah.
zuciyata kuwa tam take da takaicin ilham.
Mikewa tayi tana fadin tashi muje mu kwanta dare yayi...wani irin kallo na jefe ta dashi me dauke da sakuna,a raina kuwa kamar na shaketa..
TA kara magana karo na biyu,
na girgiza kai ina fadin bazani iya kwana daki daya dake ba.
Sabida me,? Baka yarda da kanka ba kenan.
Shiru nayi ban amsa ta ba.
"Ka tashi mana muje"..ta kara faDi.
A hasale nace jeki ki kwanta,ni bazani kwanta daki daya dake ba.
Tayi fushi,ta koma ta zauna tana cewa ni ma bazani iya kwana a dakin ni kadai ba

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.