Pages

Thursday 25 January 2018

29-30 of SOYAYYARMU

*SOYAYYARMU👫*
           By Ganarious
Page2⃣9⃣
👉🏼Annabi(s.a.w) yace "sunan Allah mafi girma wanda idan aka roke shi dashi yake bayarwa,yana cikin wannan ayar: *kulillahumma malikal mulk*" surah Al imran,26:...Dabarani ne ya ruwaito shi daga dan Abbas(r.a).

Gaisuwa ta mussaman ga masu karatun *SOYAYYARMU*,.ina me marhaba da COMMENTS, dinku ko opinions ko gyaregyare a Ganarious.blogspot.com/    Nagode🤝🏼🙌🏼

          **        **       **
Mama.!Mama!! Mama!!! Kawai nake kira,Babana kuwa jarumi ne,domi kuwa yayana yana parkin ya fito ya bude gefena zai dauke ta baba ya dakatar dashi sai ce mashi yayi shiga mota mu koma gida.
Cikin da'ga murya yace sabida me Baba!,mun iso asibiti sai kuma kace a komar da ita,alhalin ko bude ido batayi.
Shiru baba yayi,a lokacin shi kuma yayana yana kokarin fito da ita zai dauke ta zuwa cikin asibitin.
Babana ya sake umurta sa da ya shiga mota,a koma gida...sai a lokacin ya fahimci me baba ke nufi da hakan,don tabbatarwa ya kunso kai dai-dai gun fuskarta ya kiran Mama.! mama!!...mama don Allah ki karya tashi,bude ido ya gani..sai jijjiga ta yakeyi yana surutai tare da fashewa da kuka.nan nima na fahimci abinda ke faruwa...na shiga yin kuka sosai ina me nadama..
wata sabuwar kuncin rayuwa na sake shiga,mutuwar mamata ta tabani sosai...gashi yannena da kanina al'ameen sun tsaneni,wai ni na kashe mama,don haka ba abinda ke hadani dasu sai Allah shi isan masu...
..kowa ba cewa yake bakin cikina ne ya kashe mama,duk sun juyamin baya..ba su kaunar ganin na.hatta hajiya bata sake min fuska kamar da.
Babana sai yarana kawai suke harka dani

A kodayaushe ina kunshe a daki,banida aiki sai kuka da nadama,gashi baby Muhammad kullum cikin kuka yakai,sabida bai saba dani ba sai mama da baba.
Haka na ci gaba da zama  cikin kuncin da hantara.
Yan uwan mama da suka ji ciwon zuciya ne ya kashe ta,sukayita Allah shi waddai da halina na rashin jin magana.

Ako da yaushe bani da aiki sai kuka da kuma sa ran ko mamata zata dawo,domin na bata hakuri ta yafe min...hakan yasa na fara surutai kamar me tabon hankali,ganin ina neman zaucewa ya sa babana ya daukeni muka je ganin likita.
Ya sanar wa Babana ,lafiya lau nake amman fa idan har na cigaba da haka har zuwa wani lokaci tauuh fa sannu a hankali zan fara hauka,don haka yake bada shawaran ayi me yiyuwa.
A daren ranar Babana ya zaunar dani cikin kwantar da murya yake maganar..
"Haba Aisha..! Ki tausayamin mana! Ko so kike na bi mamarki?
Da sauri na girgiza kai ina fadin a'a Baba..kai kade ka ragemin,don Allah kar ka wuce ka barni.
yayi ajiyar zuciya "ki saki jiki,ki koma kamar yanda kike a baya,ki daina takura kanki da tunane tunane kinji ko.
Na daga masa kai.
Jin dadinsa ya bayyana a fili,ya kara fadin "kiyimin alkawarin cire fillo a rayuwarki,ki manta shi..nasan hakan zaiyi wuya amman ki kokarta kinji?
Na sake daga masa kai.
Yace yauwa me sunan mamata.
Daga wannan lokacin na fara kokarin sakin jiki tare da ganin na dawo dai-dai...
Yannena da kanina da suke nunamin tsana,Baba na ya zaunar dasu yayi masu fada,ya kuma tunashe su matsayi a gunsu sa'anan ya fadamasu lokacine yayi shiyasa mama ta tafi,don haka idan zun cigaba da nunamin tsangwama toh fa dan Allah suke shi da ya dauki abinsa.

Abin da wuya,amma alhamdulillah,...na fara komawa,mutun..matsala dayace baby muhammad da idan ya fara kuka baya jin lallashi,don haka kukan sa kan tuno min mamata,sai ni ma na kama kuka ina zancen zuci tare fadin "da mama na nan da za tayi ka za" da mama na raye da zatayi masa wannan da wancan" haka dai nake har na fara saba wa.

Bayan rasuwar mama da kamar shekara daya da rabi,..na fadawa Baba na cewan inason na nisanci gida,sabida wasu ababe da sukan dawo min sabo wata sa'ain.
Ina kike son zuwa? Ya nemi sani.
Da so samu ne na tafi American,can din ma ba wai zama zani je yi ba,karatu nake son naje na karayi fannin ilimi,ka gan da haka idan na dawo,sai na nemi aikin koyarwa..idan har ina zuwa gun aiki a koda yaushe bazani rasa abin yi ba hakan zai kawar min da zaman tunane tunane..
kwarai da gaske!..Babana ya fada cikin farin ciki..da alama maganar ta matukar sanyi farin ciki.
Ba'a bata lokaci gurin yimin abinda ya kama ta ba,don haka shirina ya kammala,na kwashi yara muka tafi kasar turawa sai mai aiki me suna Blessing da aka hadani da ita zuwa.
Allah da ikonsa da taimakonsa na gama karatuna na dawo gida,a zaton Babana a gida na na estate zani zauna don haka ya sa akayiwa gidan gyare gyare,aka sauya komai na gidan..nayi wa Babana godiya tare da fada masa yayi hankuri ba zani zauna a wannan gidan ba don haka ya bani daya daga cikin gidajensa,a yanzun haka cikinsa muke.

Mamee ta dago tare da dubansu,tace wa Hisham "ba wai naki kabane,ko wani abu,ba ni dai son ina harka da mutanen nan ne kawai"...tayi shiru na dan lokacin sa'anan tace "kuyi aurenku,Allah ya sanya albarka."..ta mike zata tafi daki,nan tayi karo da blessing ido jajir tasha kuka ma'ishi.
tayi  kalleta tare da yin murmushi ta shige.
Kuka takeyi sosai....
Hisham ya tashi ya koma  inda take zaune,ta dubeshi cikin ido tace "why...oh why..!..meyasa sukayi mata haka? Eyeeeh.meysa?
Tana fadin haka tana kuka me ban tausayi,
Hisham ya rungumeta ta yi lamo a kafadarsa,tana kuka, yana shafan gashin kanta.
sai da tayi ya isheta,sannan ta dago tare da daure fuskarta..tace "wallahi sai na dau fansa"...yanda ta dandani kuncin rayuwa sabida su,wallahi'azeem sai nasu ya ninka nata,mahaifina kuwa sai yayi da nasanin barin don wata.!ita kuwa hajiya zubaida! Soon,and soonest zata gwammaci lahira da duniya.
Da sauri hisham ya rike ta yace haba ilham! Abinda ya wuce ai ya wucen ne..please let it be.
Ta fizge hannunta da karfin gaske tare da kara murtuke fuska tace"kaiii....dont tell me that!,idan baza ka iya taimakamin da komai ba,tauh kayi shiru da bakinka.
Tana kaiwa nan ta mike ta shige,nan ta barshi....ya Santa fiye da kowa,idan tace zatayi abu, ba makawa sai tayi yi,don haka ya fara shiga rudani tun batayi ba.
Ya kai kimamin minti talati zaune a indata barshi sannan ya mike ya nufi gida.
A daren ranar,Hisham bai rintsa ba.tunane tunane kawai yake...domin kuwa duk wanda yasan ilham bayansa yake...idan tace zata yi abu tau ba fashi,ya zaunu kenan a zuciyarta!.tunani kawai yakai,yanda zai shawo kanta ta share zancen mutanen,don kuwa shi har ya fara tausaya masu,idan bata hakura ba...tsuki yayi,tare da gyara kwanciyarsa,..oh ooo Allah,ka taimake ni,ilham ce matsala ta kawai yanzun.da haka har bacci yayi awon gaba dashi.
Itama ilham ba ta rintsa,sai juyayin abinda mahaifinta fillo yayiwa mamee takai...ta kasa gane tsakanin mahaifinta da hajiya zubaida wa ya fi kuntatawa mahaifiyarta..tayi tsuki tace "gabaki dayanku zaku gane kuskurenku.


Kashe gari bayan ta idar da sallan asubahi,ta nufi  dakin mamee,zaune take kan abin sallah..da alama bata tashi ba tunda ta idar da sallah...,as usual,wayarta take daddanawa,ta durkusa ta gaishe ta,itama mameen ta amsa.
Shiru shiru...basu sake magana ba,mamee dai ta cigaba da abinda takeyi sai kuma ta dago ta dube ta tace lafiya dai ko?
Lafiya lau mamee...so nake nace maki mun gode,mun gode sosai akan tarbiyan da kika bamu,za kuma dawainiyanmu daga sa'anda babanmu ya gujeki...ba abinda zamu saka maki sai mafificin addu'a.
Mamee tayii murmushi...tace "come on babyname sake",kin manta ku amana ne daga Allah(S.w.a)? Da baza na iya ba,da bai bani ku ba..don haka godiya ga Allah.
Ok mamee,duk da hakan zani gode maki...
Shiru shiru bata tafi ba,kuma bata sake magana ba..
Mamee ta dago tace "anything more".
hmmm......yes! Ta daga yatsa...tare da saukowa daga kan gado ta rungume mameen.
"I love so much,so sorry for what u had gone tru because of us....ina kuma baki hakuri bisa ga ciwon kan da nasa ki akan Hisham,inn shaa Allah ba zani sake ba.
Mamee ta cire ta daga rungumar,suna fuskantar juna tace"Allah ne ya hadu ku,ba wanda kuma zai shiga tsakaninku.
Jikin girgiza kai ilham tace a a mamee,nifa na fasa auran Hisham.
Sabida me?😳...mamee ta nemi sani.
Sabida gabaki dayansu families din nan na tsane su...fadin ilham.
Har da ke kanki kenan?
Yes!...idan ta kama...,nu fa bazani boye maki ba,tun jiya nake da na sanin hada jini da su.
Mamee ta toshe mata baki,tana fadin dont be like this,ba wai na fada maki labarin bane don ki tsane ko wani abu....bata karasa maganar ba baby muhammad,watau dan autan ta,wanda take kira da abba ko Babana ko dady, ya fara motsi,tasa hannu a lebenta tana yiwa ilham alamar tayi shiru kar ya tashi.
Ilham ta bata fuska ta fice daga dakin..
Tun bayan rasuwar mahaifiyan mamee, mamee take tausayi baby muhammad,tausayinsa yasa ta shagwaba shi sosai..ga soyayya da kauna da take nuna masa,ga bauta masa da takeyi duk wai sunan so...hakan na matukar batawa ilham rai,taki jinin ta kalli abba yana shagwaba,da girmansa mamee na goyashi,ita ke yimasa komai,sabida ba ya son na kowa sai nata..duk ranar da ta barshi da ilham kuwa,dakansa take idan yayi mata wannan shagwaban don haka ke tsoronta idan mamee bata nan.

Dakinta ta koma bayan ta bar dakin mamee,cike take da takaicin abba sabida ya tsinke mata maganar da take sonyi da mamee.
Ta zauna tana nazari,can kuma ta mike tana fadin ya zama dole na fadawa mamee tun da wuri don haka ta nufi dakin mameen.
ta taras da mamee na mikar da abbab daga saman gadon shikuwa yana wani yauki yauki..cikin bacin rai ilham tace "mamee saukowan ma,sai kin taimaka mashi?
Idan baki iya kallo,ki koma dakin ki...fadin mamee.
Ta kara daure fuska,tace daman so nake na fadamaki zan je u.k
Mamee ta juyo ta dube tace ba lokacin hutu bane kenan?...me kike son kije kiyi a can,hutun ki bai kare ba.
Hmmmm.....akwai abinda nake son yi ne can.
Me kenan?..mamee ta nemi sani.
Ta shagwaba fuska,tace mamee don Allah ki bari naje,idan na dawo zan fada maki....nasan idan nayi maki karya zaki kama ni,shiyasa ban yi shi ba.
Tauww ai kuma baki fadamin dalili ba,don haka ban yarda ba.
Ta cije lebbanta,ta juya ta fita.a zuciyar ta na fadin mamee ta bata first steps of plans dina,amma zani san abinyi.
*SOYAYYARMU👫*
       Written by A'ishah
            (Ganarious)
Page 3⃣0⃣

Bayan rabuwan Hisham da ilham a gidan mamee,basu sake haduwa ba...ko kiranta yayi bata dauka,idan text yayi mata batayi masa reply.
Hakan yasa duk hankalinsa a tashe,ba  shi da sukuni.,don haka yau jumma'a ,yana dawo wa daga masallaci ya sake watsa ruwa ya canza kaya,tare da feshe jikinsa da kalolin turaruka.
Ya fizgi makulin motarsa ya fita..kai tsaye gidansu ilham ya nufa.
Sai dai me! Kunya ya hanashi shiga..gashi yana ta kiran wayarta ta ki dagawa..zaune yayi cikin motan,ya na tunanin mafita.
Yana tsakiyan tunanin,mai gadi ya wangale wa mamee gate  zata fito..
Da saurinsa ya fito daga motansa, ya nufo gun gate din, tana ganinsa kuwa ta tsaida mota
   Cikin fara'a ta amsa masa gaisuwa,bayan ya gaishe ta,sai ya kama sosa kai..
     Ta dubeshi,tace "ya ya dai Hisham?.
.....hmmm ba komai mamee.

Murmushi tayi tace feel free..idan da wani abu ka fada naji.
Har zuwa wannan lokacin ya soshe soshen kansa,sai kuma ya ce kawai dai....
..kawai dai me? Ta tambayeshi.
Ilham ce ta daina daukan  calls dina,tun bayan rabuwar mu a nan..ba ta kuma amsa min messages dina,abinda ya fi damuna shine "fansar da tace zata dauka.
Yanayin maganarsa ya baiwa mamee dariya, ta da'rah sannan tace fansan me kuma.

Wai zata rama duk wani abu da iyayena,da dangina sukayi maki..

Dariya ta koma yi,tace "kar ka damu,ba abinda ilham zata iyayi...tausayi da bakin ciki ne suka sanya ta yin furucin,na tabbata ilham ba zatayi komai ba...rashin daukan wayarka da batayi,kazo gobe..ga ka ga ta zanyi mata fadan haka.

Haka ya koma gida jiki a mace,kwarai da gaske ni kadai nasan ilham,hatta mamee da ta haife ta bata san ta kamar yanda na santa ba....
  kwance yake,amman kuma idonsa a rufe suke kamar mai bacci,yana ta zancen zucin shi kadai,daga shi sai singlet da boxer..cikin sa a kife yake kan lallausar kujeran sofa.
kaseem da kareem ne suka shigo da sallamarsu,daga kwancen ya amsa masu,ba tare da ya da'go ko ya bude ido ba..

Samun guri sukayi suka zauna,kareem ya mike ya nufi inda frij yake ajiye ya dauko masu drinks,..a yayin da kaseem yake cewa hisham"lafiya kuwa  abokina?..tunda ka dawo tafiyar nan muke ganin ka haka,me ke faruwa ne.

A sanyaye ya mike zaune,ya dauki pilo ya rungume.

Wai me ke faruwa ne??...ilham din ce k? Fadin kaseem.
   Ya daga masu kai daga  baya,yace itace wallahi.
   Sun fashe da dariya,sabida yanayin da yayi maganar..sai da suka gama dariyansu,sannan suka ce toh yaya?...mahaifiyar tata ce taki amincewa har zuwa yanzun?

Ya kada kai.."ta amince ai.
Cikin daga murya suka ce maa'shaa'Allah,ka isa barka.
 Hummm...kawai yayi
Kaseem yace yanzun dai me ye matsalan?
Ya nisa yace' abinda kenan,shine bayan na dawo saudiya na tafi gidansu,don daman tace idan na dawo na zo,toh shine fah take ba mu tarihi da labarin zaman da tayi da iyayena,da dangi na ga baki dayansu...
A gaskiya ba su yi mata adalci,shine yanzun ilham ta dauki alkawarin ramawa mamanta abinda sukayi mata.

Kareem yayi guntun tsaki,yace tau miye damuwarka???...ai wannan bai shafe ka ba,tunda mamarta ta amince,idan ta gama daukan fansarta ba sai kuyi aurenku ba..besides me wannan yar ilham din zata iya🤷🏻‍♂

Ido waje Hisham yace me zata iya fa kace??...Tabdi..,wallahi what ilham is capable of doing ya wuce tunanin wani dan adam,nasan ilham,nasa abinda zata aikata...infact nasan ta fiye da kowa a duniyar nan..duk abinda tace zata yi, tau fa sai tayi shi.

Kana wani magana can😏,auren ma tace ta fasa...duk da nasan ni kadai take so...don haka abinda fi damu na shine yanda zan shawo kanta ta yafewa iyayena da dangi na.

Kareem,yake sa baki yace"na fada maka ba abinda zata iya yimasu"

A hasale Hisham yace kaiii...wai kodai na baka labarin ilham ne kafin ka yarda?
Ilham mace ce da idan tace zatayi abu sai tayi shi.
Ba sau daya ba,ba sau biyu ba ta sha tace min zatayi abu,idan nace baza ki iya ba sai tace muyi "bet"...da ikon Allah kuwa sai tayishi.
Wani lecturern mu ya taba kashe kansa sakamakon,duk da bansan me ilham tayi masa ba,ta dai dau alwashin sai ya gwammaci lahiransa da duniyan,sakamakon fyade da yayiwa daya daga cikin kawayenta.

Ilham takan bani mamaki akan hakan,sai dai bani daukansa serious,kullum cewa nake baki iya wa,...na daina fadin hakan domin kuwa nima ya kawo kaina.

Watarana,nazo school,amman tunda nazo ban ganta ba,al'adarmu kuwa bamu shiga class sai mun hadu da juna,don haka na nufi hall din da nake sa ran ganinta..gaba daya dalibai suka juyo suna kallona,shiki lecturer ya tambayeni me nake nema?  Nace masa ba komai don haka na fita daga hall din,..ina cikin tafiya na ji an rike ni,juyowar da zani sa kawai na gan ilham ce rike da jakkarta.
Cikin bata fuska nace meya sa kika fito alhalin ba'a gama maku lectures ba.
Ta shagwabe tare da marairacewa tace "ko da na zauna ma bazani fahimci komai ba,tana maganar tana lallausa idanuwanta.
Ido waje nace sabida me?
Hannunta ta yi nuni kirjina dashi..ban nemi karin bayani ba,na rike mata hannu muka tafi.
Gurin da aka kebe ko donyi karatu,ko me son hutawa ko shakatawa, ko kebencewA,nan muka nufa,ina zama na janyota ,ina fadin zo ki zauna.
..ta make kafada tace ita baza ta zauna a nan ba,nace tau ina kike son zaman,?
Tace saman kafafuna..
ido waje nace kafafun basu da karfi,don Allah ki tausayamin....ganin bata da niyar zaman yasa na janyota ta zauna bisa cinyar nawa...na sa hannuwa na zagaye cikinta dasu tare da kwantar da kaina a gadon bayanta,murya kasa kasa nace kina ganin mutane mu suke kallo?
Toh ina ruwanka da su? Ta fada.
"Kinsa da ganinmu za su fahimci mu yan nijeriya ne,especially ke! Kuma ansan mu da kunya,don mun zo cikin su ba shi zai sa muyi koyi da al'adar su ba,su yakamata suyi koyi namu.
ba tare da tace min wani abu ba,ta cire min hannuwana,ta dawo gefe na ta zauna,tare da kwantar da kanta a kafada ta.
Magana irin ta masoya mukeyi,tana yai min zancen yanda zamuyi zamantakewar aurenmu...daganan ta dauko maganar ya'yan da zamu haifa, tana fadin  Allah shi sa yaranmu su biyo basirah da fasahan ta.
Dariya nayi mata nace ke har wata fasaha ne da ke? Kiyi fatan su biyoni dai..nan dai muka shiga musu,ita ala dole tana da fasaha.
Cikin dariya nace da fasahanki,da basiranki kike bacewa a gari?
Itama tayi dariya,tace wallahi wannan  bacewan da gangan nayi kuma sabida kai.
Ba wani nan...ke dai fadi gaskiya!.
Da gaske fa nakai,sabida kai na bacce...ko da gaba dayan duniyar nan zani shiga bani bacce ba.
Dariya ta bani sosai nace " ko a makarantarmu ina iya batar dake fa,kuma ki batu.
haba dai....sai dai ni na batar da kai.
ni din...? Ya fada
EH kai din fa.
Kaiiii....yarinya kinyi kadan da ki batar dani.
Haka kace?
Nace mata eh,kinyi kadan wallahi...bari ganin komai kikace zakayi Allah ba baki sa'a, this is me!...ina fadin haka ina bugun kirjina.
Tayi kuttah tare da mikomin hannu wai muyi "bet"..munyi bet akan zata batar dani,idan kuma baki batar dani kin zama tawa har abada tace eh ta yarda, tace idan kuma na batar da kai ba kai ba kallon wata mace a duniyar nan sai ni kadai...nima nace mata na yarda..da haka hiran yazo karshe..
Nayi mata rakiyah har izuwa baki gate din hostel din su,mukayiwa juna sallama,na juya nazi tafi tayi kira na don haka na taka zuwa inda take tsaye,tayi murmushi tace ka kasance cikin shiri don da zaran anyi hutu zaka bace.
Dariya nayi,na shafa kanta nace da sauranki yarinya.

         **     **      **
Mun gama jarabawa da kamar kwana hudu,muna tare da ilham zancen mu bai wuci irin ta masoya ba,nan na kawo maganar "bet" din na..
Ta dube tace ban manta ba ai,kuma gobe ne ko jibi inn'shaa'Allah.
Nace tau allah shi kaimu,don na matsu ki batar dani na gani ki basiranki ba a baki bace kawai.
Murmushi tayi,tace bacewan taka ai ta yan gata ne sabida sweet-moon zaka tafi yi.
wanene sweet-moon kuma?..ko dai honey moon kike nufi?
eh..honey moon ai na ma'aurata ne,sweet moon kuma na masoyane masu shirin yin aure.

Washe gari jira nake,ilham ta zo mu fita ta batar dani shiru,don haka na dauki wayata nayi kiranta....daga bangarenta hayaniya nake ji,na nemi sanin inda take tace min tana kasuwa,ta umurceni da nazo na sameta a bus stop din kasuwa.
ban bata lokaci ba na shirya,na dauki wallet dina,da atm card sai wayata..ina isa gurin na hangeta tana zuwa inda na ke..rike take  da tsinkayen sweet,tana isowa ta mika min daya tana shan dayat.
na yi dariya nace a kasuwan nan zaki batar dani?
ba tare da ta amsa ba,ta girgiza kai.ta zauna nima na zauna kusa da ita.
bayan kamar minti goma da zamar mu a nan bus ta zo,ta rikemin hannu muka shige bus din...da shigar mu na fara ganin kamar bus din juyawa take dani,na rufe ido na ina me fadamata yanda nake ji...ta kama kaina ta kwantar a cinyarta.

Bude ido nayi,na gan ni kwance a gadon kara,na  mike da sauri na leka windon dakin ciyayi na gani,na koma dayan gefen na lekan windon,shima kamar dayan gefen ne,na dawo tsakiyan dakin na kara yiwa dakin kallon kyau duk komai na dakin da ka'ra akayi shi,kofa na  gani,shi ba'a bude ba shi ba'a rufe ba,na taka sannun a hankali zuwa gun kofan na bude...
a tsorarce nake ganin ba abu mai rai a gurin ,daji ne sosai,da alama wannan dakince kawai a gurin na waiga hagu da dama ba abinda nake ganin sai ciyayi...a raina ko addua nake,nayi taku hudu zuwa biyar zuwa gefen dakin,nan na gan hanya,sai dai wannan hanyat,mutane sukayi shi da sahun kafarsu,ba ta mota bace ko mashi,ko keke.
Na bi hanyar,tafiya me nisa nayi ban hadu da abu me rai ba,sai tsuntsaye da ke yawo a sararin samaniya...ina cikin tafiyan nagan alaman na shiga gona don ganin alkama a shuke,hamdala nayi ina sa ran ganin mai rai..cikin ikon Allah na bulo a wata gona,mutane na gani sun fi goma maza da mata,suna noma,suna gani na suka mike tsattaye,wasun su na nunani suna yare,kafin na ankara wani ya zaro takobi yayo kaina.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.