Pages

Friday 26 January 2018

KAZAMACE MATATA 1

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
*KAZAMACE MATA TA*
       ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
Written by A'isha m.Gana
         (Ganarious)

√godiya ga Allah (s.w.a),da ya bani ikon rubuta wannan labarin.

√sadaukawar ga kanwata abin alfarinmu HADIZA MUHAMMAD GANA,karamar "yar sanda ta kasar najeriya..your inspiration shall reign.

√gaisuwa ta musamma ga makaranta har da marubutan.

√princess UMAYMAH BASHIR GWANDU,na mika gaisuwarta ga ma'karantan SOYAYYARMU.

√ina  marhaba da comments dinku,gyare-gyare,ra'ayinku,da dai sauransu a ๐Ÿ‘‰๐Ÿผ ganarious.blogspot.com/ na gode๐Ÿค๐Ÿผ

      **        **      **
Munir dogone,shi ba fari bane, ba kuma za'a ce masa ba'ki ba...yana da idanuwa masu girma,ga eyelashes dinsa cike kuma da tsayi.
Kana iya hangen daga inda karan hancinsa ta fara,lebensa kuwa ba'a maganarsu..sajensa ta faro da'ga gefen kunnensa ta zagayo ta kasar bakinsa, zuwa dayan gefen kunnen..
Yana magana gefen kumatun sa na lotsawa ciki.
Karya ne munir yayi magana baka sa masa ido ba,yana maganar yana lausaya idanunan nasa kamar me jin bacci...munir perfect example da yan mata suke mafarkin samu, suke kuma kira da *my dream partner*,ba wace zata kalli munir bata raya a zuci cewan da" ace itace the lucky lady ba..nima din me bada labarin sai da na kyasa๐Ÿ˜œ.
Munir zai kai kimamin shekaru talatin da daya-xuwa da biyu da haihuwa.

  Mahaifiyarsa ta rasu tun yana shekara goma sha hudu, shi da kannensa uku ta bari a gun matar ubansu...munir da kannensa sun dandani kuncin rayuwa daga gun matar ubansu wace suke kira da inno..
Wulakanci,cin zarafi da mugunta ba irin wanda basu gani ba,inno bata kaunar ganin suna farinciki ko da na sekan ne,sai dai su kasance cikin bakin rai da bakin ciki,sai dai me,Allah yayi wa munir da kannensa hakuri.
Munir jarumine,duk da ababen da yake fuskan ta bai sa shi ya kariya ba,gwagwarmaya yakai,   dafi tashi don  ganin shi da kanensa sun sami ingantacen ilimi.
Munir bashi da daki a gidan ubansa,bashi da abinci a gidan ubansa bashi matsayi a gidan ubansa,amman wadannan ababen ba abinda suka dame shi ba ne,asalima idan ya tashi da safe,yayi wa inno share share sai ya fita gari neman inda zaiyi shara,ko wanki ko dai wani aiki a biyashi,idan ko ya dawo da kudin aikin sa gida,sai inno ta kwace..
Ganin haka yasa shi dabaran raba kudin gida biyu, rabi ya baiwa mahaifin abokinsa ajiya,rabin kuma ya kawo gida.

Munir na kammala makaranta ta sekandiri,ya sayi fom din makaranta ta gaba da kudin da yake tarawa...cikin sauki kuwa ya sami karbuwa a makaratar,amman mahaifinsa ya hana shi zuwa,wai bashi kudin bashi..munir ba kariya ba yace wa mahaifin sa shi zaya dinga nema wa yana biyawa kansa kudin makaranta..
NAn ma bai amince ba,wai inno tace idan shiga makarantar baza shi dinga kawo mata kudi ba..domin kuwa kudin da zaya dunga kawo mata shi zai kashe a makarantat...
YAYi kuka,yai bakin ciki da'ga baya ya roki Allah ya yayi masa alkhair.

Daga munir har mahaifinsa hadi da kannensa tsoron inno sukai, suna matukar shakkarta, sai dai ya'yanta da ta haifa basu shakkarta,masifarta ma baya basu tsoro, asalima fadi na fada takeyi da su,ba ta magana basu maida mata ba.

Haka munir ya cigaba da rayuwa a gidan,ya na fadi tashi don ganin ya nemawa kansa da kannensa.

  Alhaji suleiman shine mutumin da munir yake zuwa gidansa tun da sanyi safiya,ya share masa gida,ya zub da sharan gidan sa'anan ya wanke masa motarsa...ba gidan alhaji suleiman kawai munir ke aiki ba,akwai gidaje da dama da yake masu aiki,amman gidan alhaji suleiman yake fara zuwa.

Alhaji suleiman ya y gama karance munir..ya lura munir me tsoron Allah ne,komai tsakaninsa da Allah yakeyi,gashi da tsafta.
   Watarana bayan munir ya gama aikinsa,yayi sallama a falon alhaji suleiman,ya amsa tare da umurtansa da ya shigo.
Ya shiga ya sanar wa alhaji suleiman cewan ya kammala aikinsa na ranar.
Godiya alhaji suleiman yayi masa,sa'anan ya umurce shi da ya zauna suyi wata magana.

Alhaji suleima ya sake yi masa godiya sannan yace na fahimci kai mutumin kirki ne me tsoron Allah kuma..ko kasan da cewan kudaden da nake bari a mota da gan gan nake barinsu! Sabida na jarabta ka,kuma ka sha ka tsallake jarabawan..a gaskiya na yaba da halayyenka,domin abin koyi ne kuma da misaltawa...
Ga ka da tsafta,tunda ka fara yimin aiki gidan ya canza,ga ka baka shiga shirgin da da ba naka,infact halayyenka is perfectly ok wallahi
Munir ya ji dadi sosai,duk da ba yau ya saba jirin irin haka ba..don haka yayiwa alhaji suleiman godiya.
Alhaji suleiman ya cigaba da fadin zan so na sami mata me irin halayyarka.
Murmushi munir yayi bai ce uffan ba.
    Allah da gaske nake fa...idan kana da kanuwa me irin halayyanka,please ka hada ni da ita na aura..
Mata ta,ta rasu gurin haihuwa ta barmin yara uku..tun bayan rasuwarta nake neman koda me kwatankwacin halayyanta ne amman ina! Matan yanzun sai a hankali..ba wai ban sami macen me halin kirkin ba,no..no.no,kawai ina son wace zata bi dokata,ta kuma rikemin yara na tsakaninta da Allah.
Ina son mace me tsoron Allah,kuma me tsafta,wace kuma zata zauna a gida,nufi na anan shine bani amincewa mata ta ta dunga aikin gwamnati,..mata ta da ta rasu,digirin ta uku wanda shike ma bani dashi amman ta bi doka ta,ta zauna zaman baiwa ya'yana tarbiya..yanzun kam wace zata tara irin kwalifications nata ta amince da irin doka ta? Da wuya ko nace babu.
Don haka macen da zata zauna a gida nake so.
 Shiru shiru munir  baiyi magana ba,hakan yas alhaji suleiman ya sake yi masa magana.
Ajiyar zuciya yayi yace inada kanuwa wace na tabbata halayyenta sunfi nawa kyau da ban sha'awa...amman...nan yayi shiru
Ahaji suleiman cikin matsuwa yace,amman me? Zata aure wani ?

Ya ka'da kai yace a'a,..bata da isashen ilimin,matar uban mu bata barin ta zuwa makaranta,sai sa'a da sa'a..nan ya sanarwa alhaji suleiman irin rayuwar kunci da suke fuskanta.
Cikin tausayawa alhaji suleiman yace' wanan na daya daga cikin dalilin ya dayasa,na natsu ina neman mace ta gari,ba wace zata zo ta sa yarana cikin wani hali ba....mata abin tsoro,yanzun kiri-kiri ta hana ka zuwa makaranta sabida wata yofin dalilinta.
Munir ya da'ga,yana me jin abin a ransa.

Alhaji suleiman ya nisa ya ce shikenan,dama akwai wasu fom dake gurina wanda gwamnati ta bayar a bawa yara masu kokarin gaske,amman kuma wadanda iyayensu ba su iya dauka nauyisu..don haka gwamnati zata dauki nauyinsu zuwa kasar waje karatu..don haka ka kasance cikin,shiri sabida zakuyi jarabawa har sau uku,kunayi ana tace wasu daga cikin ku.

Munir yayi godiya sosai yana farincikin haka.ya mike yana yiwa alhaji suleiman sallama.
Ya tsaida shi ,yace masa ya jira shi su tafi tare,sabi da yau dinnan yake son ganin khadijah.
A kofan gidansu alhaji munir yayi parking,daga nisa munir ya hange ta,ya nunawa alhaji suleiman ita yana fadin ga ta can tafe ma..
a natse take tafiyar,ita ma din doguwa,kyakyawa da ita. Banbancin da munir shine  bakar fata ce da ita...
Alhaji suleima ya gama dubanta kaf! Kafin ta karaso.
kiranta munir yayi,ta waigo sai ta nufo su, da fara'anta ta gaida alhaji suleiman sa'anan tacewa munir "yaa munir gani.
Mekika sayo?
na sayo gari ne...ta amsa,
Tau shiga ciki,nima zani shigo yanxun.

Munir ya juya ya kalli alhaji suleiman,yace ka ganta nan,itace khadijan.

Alhaji suleiman yayi ajiyar zuciya yace ,na ganta kuma tayi min dari bisa dari.....ka fadamata bukatata,idan ta amince sai nazo ganin mahaifinku.
daga nan sukayi sallama,alhaji suleiman ya mika masa kudin aikinsa na ranar,amman munir ya ki karba.
A daren ranar munir yayi kiran khadijah zuwa gefen gidansu,nan yake sanar da ita yanda sukayi da alhaji suleiman.
Tayi matukar farin ciki, addu'arta a kodayaushe Allah ya kawo mata karshen zaman ta a wannan gidan don haka tayi hamdala tare rokan Allah shi tabbatar da auren.
ganin alhaji suleiman mai maiko ne yasa mahaifinsu munir jin dadi don haka ya amince.
ba'a bata lokaci ba akayi komai da komai na auren.

An daura auren alhaji suleiman da khadijah, don haka amarya ta tare gidanta...ba abinda takeyi,sai yiwa Allah godiya da yarabata da gidan kunci,kannenta da ta baro can sune kawai damuwarta.

Munir ya dauke kafa daga gidan alhaji suleiman,aikima ya daina yimasa,sai dai ya shiga gari yana neman gidan da suke son ayi masu wanki su biyashi.
bayan haka,munir ya dage da karatu da kuma addu'a,yane me rokon Allah da ya bashi sa'a.

ALhamdulillah,anyi jarabawan gwaji har sau uku,kuma cikin ikon Allah,munir ya tsallakesu don haka yana daya daga cikin masu zuwa kasar paris.
sai da komai ya kammala na tafiyarSa,sa'anan ya sanarw mahaifinsa komai da komai,mahaifinsa yayi murna sosai tare da yiwa  alhaji suleiman godiya, ita kuwa uwar mulkin sai mita takeyi,wai wa zai dunga samo mata kudin chefanne... kaji min mata fa๐Ÿคท๐Ÿป‍♀,ga ta da yara!

Da haka munir ya tafi kasar paris karatu.
Sai da yayi hawaye ranar  tafiyarsa sabida kannesa farida da Abdulwahab da zai bari,sai dai ya barwa khadijah amanarsu.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.