Pages

Saturday 20 January 2018

27-28 of SOYAYYARMU.

: *SOYAYYARMU*👫
      By Ganarious
Page 2⃣7⃣.
Sai bayan sallar isha'i Babana tare da hajiya suka shigo,a lokacin kukan ya lafa...sai dana sanin abinda nayi wa fillo nakeyi.
Tunaninsa nakeyi,ina kuma jin haushin kaina bisa ga abinda nayi masa.
Ina ganinsu na risina ina me gaida su.
Babana ya danyi shiru na dan lokaci,sannnan ya nemi da yasan me ke faruwa.
Ba komai na ce dashi..
Ba yanda basuyi da ni ba da na fadi abinda ya faruwa,sai ce masu nake ba komai,hakan ya batawa mamata rai tace "tashi ki bar mana gida tunda haka kawai kika zo don ki tada mana da hankali.
Hakuri na shiga bata...,Babana kuwa shiru yayi bai ce komai ba.

Washegari da safe ya sake shigowa ya matsamin da na fadamasa nace ba komai baba.
Ranar da na cika kwana hudu a gidan mu,Babana ya aika a kira masa fillo don ya neme shi a waya bai samu ba.
Ashe wai fillon ba ya gari.

Zaune nake ina yankewa mujaheed farcen sa..ba abinda nake tunani sai fillo..
Binta ce ta shigo da  sallamarta .
Cikin fara'a na amsa mata,yara kuma suka nufeta aguje sunai mata oyoyo..
maman ilham kin barni da ke'wa.! Fadin Binta.
Na basar da maganar ta,na dauko wata zance.
Na tambayi lafiyan mutan estate tace min suna nan kalsu.

Shiru-shiru..ba wace ta kara magana...can ta nisa tace maman ilham wani abu ya faru  tsakaninki da Baban ilham ne?
na da'go  ina kallonta tare da tambayarta "me kika gani?'
Hmmm...kananan maganganu da tseguma ne suke yawo a Estate,na kuma shaida maganar nan ba da'ga bakin ki suka fito ba.....kawai shairin mutanen na.
Da sauri nace wace irin magana ce?
"Cewa sukeyi wai kin ce a tashi maki a gida,ma'ana mutan estate din su kwanshi kayansu su bar nan din...shine fa salisu da yusuf suka matsawa mutane wai a kwashe cikin satin nan...wallahi Goggoji tun shekaran jiya take koke-koke wai ita ba inda zata tafi,su kuma sun matsa mata ,domin mahaifi hajiya zubaida ya riga ya bada gidan da zata zauna.
....shiru nayi,zancen ya daure min kaina,"Allah ya sauwwake"kawai na fada.

Shiru shiru har na shiga sati na uku fillo bai zo ba,Babana ya sake aikawa a nemo shi,wannan karon anyi sa'a.
Karfe hudu ya iso gudan mu.a falon Babana aka yi zaman.
Babana ne yake bayani akan zuwa na gida,kuma sun nemi su san dalilin haka nace ba komai,..ya kara da fadin "kai kuma muna ta sa ran ganinka shiru,shiyasa na sake aikawa a nemo min kai
Bai boyewa Babana komai ba ya sanar masu abinda ya faru a tsakaninmu....ya kuma sanar masu gida ne mahaifin hajiys zubaida ya bashi,don haka yake son ya kwashemu ya maida can din.
Babana ya girgiza kai yace "amman dai kuwa bakayi min adalci ba,ai kafin ya baka gida ni na baka...jeka ka sake shawara da iyayenka,duk abinda kuka yanke sai ka dawo ka dauki matarka.

Mikewa nayi na bi bayansa sa'anda zashi tafi,sai da ya kai gun motansa ya tsaya...ya juyo ya dubeni ba tareda ya ce wani abu ba.,ganin haka yasa nace masa amman fa baka kyautawa babana ba wallahi..
Eh...Na sani,ya maida min
Ido waje nace "ka sani fa kace?
eh,ya da'ga kai.
Toh wallahi tunda a sane kake bakanta min rai bazani bika zuwa wannan gidan ba,sai dai kuwa mu rabu.
🤷🏻‍♂ya da'ga hannuwansa biyu tare da make kafada,yace "anyway,shawara ta rage gareki,ni dai na baki nan da sati biyu ki harhada kayanki da na yara,idan kuwa bakiji ba duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki.
...a hasale nace 'ma cuci...butulu kawai,idan har sai na koma gidan wannan shegiyar,tau gwara mu raba hanya...ko kana tunanin bazani iya rayuwa ba da kai ba!
Ya shige motarsa ,ya tafi..ya bar a nan inata surutai na.
Na juya zani shiga cikin gida,na gan babana tsafe bakin kofar falonsa ya rungume hannayensa yana kalo na.

       **       ***     ****
A haka na kara yin sati uku a gidanmu.fillo ki wani daga cikin yan uwansa basu zo ba.

Zaune nake ina gyaran farce,sai naji sallama,na amsa tareda ba da izinin shigowa.
Me wankin Babana ne ya shigo rike da wata katuwar envelope... bayan ya gaisheni ya mika min envelop din wai wani ne ya kawo yace a bani..na sa hannu daya don karban envelop din sai ya kubcemin sabida nauyi,na sa hannu na jayo envelop din kusa dani domin kuwa ya fara yagewa..ba tareda nayi tunanin wani abu ba.
A inda na na gama gyaran farce,a nan bacci yayi awon gaba dani...ban farka ba sai da naji yars nayiwa mamata oyoyo..
A hankali na bude ido,ina me yimata barka da dawowa.
Ta amsa tare da fadin kin kuwa yi sallan azahar kuwa?
:ido waje nace laaah..ashe lokacin sallah,yayi.
Tana me kallona tace yayi ko ya wuce?.."kina bacci baki ma san da dawowan yara  ba.
Na mike na shige dakina don sauke farali.
Ban fito daga daki ba har sai da na tabatar na gabatar da sallan la'asar.
    Zaune na tarar da mamata tana shan kayan itace...yara kuwa sun baibayeta,tana basu a baki.
..idon ta ya kai kan envelop din,tace "me ke cikin envelop din can,tayi nuni da hannunta.
Hmmmmm...ni ban ma san me ke ciki ba,dazun nan malam Abdullahi ya shigo dashi wai wani yace a kawomin.
Tauu...bude mana ki gan abinda ciki!.
Toh mama!.
A hankali na yage shi,sabida daman can ya fara yagewa.
makullai ne suka zubo kasq,cikin mamaki na daga su sama ina kallo,na juya na kalli mamata,itama ni take kallo....na ajiye makullan na duba envelop din,takkadu ne a ciki da wata karamar envelop din kuma.
Na ajiye takkadun gefe na bude karamar envelop din,dan takkardace a ciki me dauke da rubutu layi biyu...ganin abinda ke rubuce ya sanya nayi ihun fadin "WHAT"...!!!
mamata ta taso ta karbi takardan,tana dubawa.
Innalillahi wainna ilaihiirsjiun kawai take fadi.
JIki a mace ta zauna kan kujera rike da takkardan.
Daga ni har ita din ba wace ta sake magana,sai dai surutun yara.
Kafin mangrib Babana ya dawo...a zazzaune ya tarar da mu yace 'ince dai lafiya ko?
Mamata bata tsaya wata wata ba ta mika masa takkardan.
SHIma din sakatsi ya shiga yi,ya dube ni ya ce "Haka Allah ya nufa!
Shima din guri ya samu ya zauna...kiran sallah ya ta dashi,ya mike zai tafi masallacin,ya gifta ta gefe na sai kuma ya dawo ya risina ya dauki sauran takkadun dake gefe na.
..murmushi yakeyi yana duba takkadun..can kuma yace "Dan Adam kenan".
Sai bayan da na idar da sallah wata irin kuka mai tattare da tausayi ya xomin.
NAyi kuk,nayi kuka kamar idona sasu fito.
washe gari kuwa mamata da babana basu je gun aiki ba,asalima ko abinci ya gagare su ci.
Yara ma ba wanda ya bita kansu har sai da hajiya tashigo..
Tace yau yan makaranta basu zo sallama ba,ashe basu je makaratan ba,injin dai lafiya?
mamata ta sauke numfashi tace lafiya kau kawai dai na tashi  jikin ba karfi ne,mamarsu kuma yanzun haka na san ba'a hayyacinta ta ke ba balle ta shiryasu.
cikin mamaki hajiya tace "lafiya?
tauuu lafiyan kenan...mijin ta ne ya aiko mata takkadar saki jiya.
Saki fa kikace?
Eh fa...
Ah'ah'ah....
Amman dai wannan yaron bashi da mutunci, fadin hajiya
mutuncin kenan ai...har fa takkardun Estate ya maido.
Nan hajiya ta shiga yin salati..tace yaushe hakan ta faru?
Da yammacin jiya
..ina daki,ina jin duk wani abu da suke fadi..
Suna gama magana hajiya ta karaso cikin dakina ta zauna....tana zama na fashe mata ds kuka,nan ta shiga lallashi...
washegari mama ta shirya yara suka tafi makaranta,amman ita bata tafi aiki ba.

 Hajiya tareda Babana suka shigo dakina ..na risina na gaishe su.
Babana yace subhanalillah!!! Kuka kikayi haka?..kin gan idanuwanki yanda suka koma kuwa?...haba mamata!
Kukan dai nakeyi masu,ba yanda basuyi ba na daina kukan,  amma kukan ya ki dainuwa.gashi idanuwan sun kumbure sun rufe,da kyar nake bude su sabida nauyi.
Ilham da mujaheed sun shigo gida a guje,sun zo suka rungume babana,yayi masu barka da dawowa,sun gaida hajiyaq da mama daga nan sukayo kaina....da shike mujaheed na da son jiki,zuwa yayi ya haye cinyata ya kali fuskata yace"mamee idonki na ciwo ne?...ya fadi hakan yana taba min idon.
Eh na da'ga masa kai,ya marairace fuska kamar me shirin yin kuka.
Ilham dake tsaye gefe tana kallona tace " sorry mamee"..
Ita ma kai kawai na da'ga mata..
Hajiya ta umurce su da su tafi su sauya kayansu..mujaheed ya mike yana cewa mamata "wa zaiyi mama na wanka toh"..shiru tayi bata amsa shi ba,ya kara fadin ko mu sa kaya hakanan!
Mama ta amsa eh,ai yau bakayi datti ba,jeka kasa kayan haka nan.har sau fita daga dakin mama tayi kiran ilham tana tambayarta ina Hisham.
Ta bata fuska tace uncle salisu ya daukeshi sun tafi.
Kuma...! Fadin hajiya.
Babana ya nisa yace ku kyalesu kawai,zan nimesu anjima.
[1/20, 8:22 PM] Aisha Gana: *SOYAYYARMU👫*
       By Ganarious.
Page2⃣8⃣
👉🏼Annabi (s.a.w)yace hakika addu'ar dan uwana Annabi Yunus(a.s) tana da ban sha'awa da mamaki,farkonta Hailala(kalman shahada),tsakiyar ta tasbihi,..karshen ta kuma tabbatar da laifi(ikrari)..wannan addu'an itace *La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimina*..wani ma'abocin bakin-ciki,ko ma'abocin bacin rai,ko ma'abocin damuwa,ko wani mai bashi,ba zaiyi addu'a da ita ba face sai an amsa masa..!dailami ne ya ruwaito shi daga Abdurrahman dan aufin(r.a)
           **        **       **
Babana da kansa ya tafi "my precious Estate".
A gate din shiga estate din masu gadi suka sanar dashi ba kowa a a cikin estate din....sai dai gidan malamai.
Tsaye yayi yana mamaki,ya zuciyasa yace miye abin mamaki,tunda sun aiko makullai!..ya tambayi masu gadi ko sun san sabon gurin da suka koma?
Suka ce a'a,basu da masaniya,amma wata kila malaman zasu sani...don haka babana ya karasa cikin estate din.
Malaman sunyi farin cikin ganinsa,nan yake tamabayarsu ko sun san inda masu gidan suka koma?
Suma din sunce basu sani ba,nan sukayiwa babana fatan alkhairi ta tafi.
Lambobin wayansu duk ba sa zuwa,amman baba bai fidda rai ba..kullum trying yake ko Allah zai bashi sa'a.

Mamee tayi shiru na dan lokaci,ta dubi Hisham da ilham,ita suke kallo. Gaba dayansu idanunsu yayi jajir,ba kamar ilham da hawaye  ya kusan sauka bisa kuncinta.
...mamee ta cigaba da fadin "na fita hayyaci na,na lallace,kamanni na ya sauya,na zama zautata abin tausayi.
Bana ci bana sha,ibada ma na neman gagarata,sai da kyar.
Bani da aiki sai kuka da tunane-tunane,kullum ina daki ko falo,bana fita cikin gida ballantana cikin gari..
Iyaye da abokan arziki sunyi ban hakuri,sunyi lallashi,sunyi nasiha,sunyi ban baki,sunkawo ayoyi da hadisai akan na dauki al'amarin a matsayin kaddara,amma abu ya ki yiyuwa domin kuwa a koda yaushe wata irin sabon son fillo nake tashi dashi..soyayyarsa sai huruwa take.
Babana ya daina fita,zama yakeyi dani a daki,gudun kar na yi wa kaina wani abu.
Mamata kuwa ta dade da fita harkata,duk da abin yana damun ta..fushi take da ni wata sa'in.
Nan ma mamee ta sakeyin shiru ta share hawayen da suke zubowa..ilham kam tuni ta fara kuka itama.Hisham kam namiji ne,hawaye na makele a idon sa ya daure yace mamee munajinki.
Ta share hawayen ta cigaba da fadin "na kasance makauniya, domin kuwa bana ganin halin da mamata ta shiga sabida ni.
Wasu daga cikin yan uwa da suka sami labarin abinda ya faru dani,sunyi murna har sukan kira mamata suce 'darasin rayuwa ce'..wasu suce  idan da ya'nazeeru na aura,sun tabbata hakan ba zai faru ba....kowa da abinda yake tofa wa lamarin..
Masuyi mata yi mata fata nagari,kadan ne....akwai wace don rashin imani ma tace Allah shi maimaita,duk fa mamata suke fadawa wannan sabida naki auaran ya'Nazeeru..ire-iren wadannan maganganu sun sanyata tunani,ta fara fita hayyacinta itama gata  da rike magana.

Ya'Nazeru kuwa tunda ya rasani ya kiyin aure,yan uwa sunyi sunyi ,sunyi korafi,sunyi fada gami da nasiha ya ki sauraronsu,asalima yason anayi masa zance aure.
Yana jin ance mijina ya sake ni,ya zo gidanmu don ganewa idonsa,ya na koma kuwa yace shi fa da so samu ne da zarar na haihu a daura masa aure dani...iyayen sa sunyi allah shi waddai,ba kuma zasu amince ya aureni ba...shi kuma ya dage sai ni,sannu a hankali suka amince badon suna so ba.

Watarana bayan na ci kukana,na mike zan shiga toilet,sai nakejin jiri,maimakon na koma na zauna sai na ci gaba da tafiyat,ban ankara ba sai ganina nayi zube a kasa,duk da ban san wata duniyar hankalina yake ba,zani iyacewa inajin abu kamar ruwa ruwa yana bin cinyoyina.
Na dade a haka,ba wanda ya sani domin kuwa babana dake zama dani ya tafi massalaci.
Wata irin azaba nake ji,tun ina ji har na daina ji.
Farkawa nayi na ganni a gadon asibiti.
hajiya da babana ne zaune gefe na,ina bude ido suka mike.
Baba na cikin rudewa yace yaya kike ji yanzun?
Binsa kawai nake da ido,ganin haka yasa shi barin gurin don kiran likita.

Kwana hudu nayi a asibiti suka sallame ni...likita da kansa yayimin nasihohi,ya kuma shaidawa Babana  da na dinga cin abinci,sabida yaron cikina yana tattare da yunwa...ya ce ba fata yakeyi ba amman yanada masani casa'in da tara akan yaron nan na dauke da ciwon yunwa.
ya kuma shaidawa baba na da zarar na shiga watan haihuwa ma'ana nan da sati biyu kean su kawo ni a cire yaron,sabida halinda nake ciki bazani iya haihuwa ba,asalima "tana iya rasa ranta da zarar tayi nakuda na dan  lokaci.
Godiya sukayi,muka nufi gida...
Daga wanna lokacin Babana yake kokartawa don ganin na ci abinci,sa'anan da yammaci ya rikemin hannu mu shiga cikin gida muna zagayawa,sabida shawaran da likita ya bada akan na dinga yi excersice.
Babana bai taba minti talati batare da ya shigo duba ni ba,har cikin dare yana kan zo dubiyata sabida haka ne baya samu isashe bacci.

Ina shiga watan haihuwa da kwana goma Babana ya umruci su hajiya da su shirya ni a tafi dani asibiti.
A ranar da suka kaini,a ranar akayimin tiyata aka fiddo yaro.
Da' namiji Allah ya bani,tunda muka koma gida Babana ke kokarin neman daya daga cikin yan uwan fillo,bai samu ba,don haka ya hakura ya aikawa fillo gun aikinsa cewan matar sa ta haihu....shiru shiru ba alamansa.
Ni kuwa tunda na haihu nake sa ran ganin fillo,nasan ko ba komai zai zo duba dan sa.
Har ana gobe suna ba fillo,kuka ya dawomin sabo...kewar fillo kawai ke damuna.
Babana ya tambayeni ko da sunar da nake ra'ayin a sawa yaron!.
Nace masa "muhammad"sunar baban nawa kenan.
Don haka ranar suna yaro ya ci sunarsa muhammad.
Bayan an watse taro,wasu daga cikin yan uwan mamata,su kawo zance na da na ya'nazeeru....mamata bata son maganar amma ba yanda ta iya da su....ce masu tayi zatayi shawara da babana.

      **          **           **
Yaron nan tunda na haifeshi bazani iya tunawa ko sau nawa ya sha nono na ba...bani da lokacin abinci balantana ya sami kulawata,kulawarsa ta koma gun mamata.
   Tun bayan da aaka gama suna, na dauki wata hali na kyaluwa...ba wanda nakeyi magana,a ko dayaushe ina kunshe a daki...
mamata wata sa'in idan zatayi aiki ta kan kawo jaririn guri na ta kwantar dashi,amma fa ko da jaririn nan zai shekara yana kuka ba zani daga shi ba har sai ta zo ta daukeshi..tayi fada ta gaji don haka ta daina ajiyeshi guri na..wani lokaci ma sai na kwana biyu ban sa shi ido ba,sai idan babana ne ya shigo rike dashi.
Ganin na ki koma wa dai-dai kuma abin nawa kara ci yake,ya sa mamata ta baiwa Babana shawara da akaini asibiti,wata kila kwakwalwata ba lafiya..bai ki shawaranta ba,don haka suka dauke ni zuwa kasar waje.
Gabaki dayan mu muka tafi can don dama yara na hutu.

Sun tabbatar masu da cewan lafiyata kalau ba abinda ya sami kwakwalwat,sai dai damuwa..suna kuma bada shawaran da na daina damuwa,idan ba haka ba zai kawo min ciwon xuciya ko mutuwa gefen jiki.
Sati uku mukayi a can,sannan muka dawo gida..mun dawo ba da dadewa ba mamata ta fara rashin lafiya.
Ta nemi nemi izini gun Bab na cewan zata koma kasar london inda muka baro don ganin likita.
Day su ilham ta tafi,har da jaririn,a lokacin kanina ya dawo gida domin kuwa ya gama karatunsa,don haka ni dashi da su hajiya ke gida.
Watan mamata daya a can ta dawo,ta bar ilham gun yayana dake da zama a can.
Sauki kam alhamdulillah ta samu.
Bata wani dade da dawowa ba ta sake komawa,wannan karon ma da yaran ta tafi,Ba yanda babana bai yi ba akan ta tafi ta bar yaran,tace Allah ya sauwake ta barmin yara.
Karon nan ma ta dade kafin ta dawo,sai dai da ta dawo jiki ya sauka,ma'ana ta rsn rame,idanuwanta kuma sun shishige ciki...
Ya ya jiki kawai nace da ita,ta amsa min da alhamdulillah.

Mamee ta kara share hawaye tacigaba "Mamata kenan!..son kai da son zuciya ya hana na fahimci cewan tana cikin matsanacin hali...duk sabida halin da nake ciki.
Babana ya bukaci da ta nuna masa sakamakon rashin lafiyar da suka bata..
Tace ce masa ba wani abu bane face ciwon yunwa da ya kamata sosai..nan ya shiga fada..
Daga wannan lokacin itama yake saka ta gaba sai ta ci abinci.
Haka babana ya zama abin tausayi,baya nan baya can...ga tsufa ya fara kamashi.
   Watarana Babana ya matsamin da na fito falo,sabida idan zai fita guri me nisa sai ya matsamin na fito falon,wai na tsaya gun mutane gudun kada wani abu ya sake faruwa ba kowa kusa.
Mamata zaune tana baiwa baby muhammad madarars hajiya ta shigo da sallamarta,tana zama ta dubi mamata tace "kai..kai...kaiiii...!maman Aisha kin rame dayawa!..da fatan ba damuwa bac kika sanyawa kanki ba dai ko?
Mamata ta ta'be baki tace "Allah dai yayi mana sauki"
Ameen ...hajiya ta amsa,tana ci gaba da fadin don Allah ki cirewa kanki damuwa...itama Aishan addu'a zamuyi mata.

Yanne na da suke zaune  kasashe ketare sun hada kai suka zo lokaci daya..ciki harda dan hajiya...sun zo duba lafiyar mamata ne,su da matansu da kuma ya'yansu,har ilham ma an zo da ita..
tunda suka zo,babban yayana ta gun mamata yake jin takaici na..
ya baiwa iyayena laifi wai su suka bata ni...kallona ma baya sonyi,don duk saanda ya kalle ni sai yace dubeki,baki da maraba da yan gidan mahaukata...ya dinga tsuki kenan duk saanda ya hangi Babana ya shiga daki na ko ya fito daga dakin.
a ranar da yannena suka cike kwana hudu da zuwa,zaune suke a falon mama,ya'Abdurrahaman dan hajiya ya shigo,ya  sallami mama akan cewan  xasu tafi zaria da shi da matarsa da yara.don gaida iyayen matarsa....tayi masa addu'a da fatan su dawo lafiya.
ya shigo dakina don sallaman Baba,shima baba yayi masa a dawo lafiya.
Ya mike zai tafi,Baba ya tsaida shi yana tambayarsa da wata motan zai tafi?.
Ya amsawa baba.
Baba na ya mike ya ajiye baby Muhammad kusa dani,yana cewa ya'Abdurrahaman muje na baka makullin motan nan mercedes,sabida jiya akayimata services.
Yana fice wa baby muhammad ya fara kuka,kuma sosai yake kukan...daga kitchen mamata ta zo a guje,tana zuwa ta ganshi a gefe na,ko kallon inda shike nayi ba,balle na daukeshi..rai a bacce ta shiga fada tana fadin" ashe musuluncin ki bai cika ba!,ba ki tawakkali da abin da Allah ya rubuto!..nayi fada nayi lallashi duk baki hakura ba..toh yaya kike son muyi?ko so kike mu kamoshi a daura maki shi don dolensa?..haba Aisha!..ganin ki a haka,ya sanya mu cikin wani hali,amman duk da haka bai sa kin dai-daitu ba ko sai kin gan mun rasa ran mu tukan sa'anan hankalinki zai kwanta?
Haba...ke wace irin yarinya ce da bata tawakkali,baki yarda da kaddara ba!..fada mamata takeyi sosai hat tana sarkewa,niko kuka nasa mata.
Tana cikin magana ya'Abdul azeez ya shigo rai a bace,ya na kokarin riketa yana bata hankuri,ta ture masa hannu..tana nuna ni da yatsan tare fadin "yar nan sai ta kasheni tukun hankalinta zai kwanta,wai ace dan cikin ta......
...maganar da bata karasa ba kenan,ta da'fe kirjinta tana batun faduwa kasa,ya'Abdul azeez ya tareta yana fadin subhanalillahiii..mamah!
Ganin haka yasa na taso a hanzarce na zo gunsu ina fa din mama kiyi hakuri,ba zani sake ba!
Tuni ya 'abdul azeez ya dauke ta muka nufo waje.
Mamee kam kuka ya tsananta,wannan karon kukan da takeyi ya tabo zuciyar Hisham,shima din sai sharan hawaye yake yi.

Mamee ta ci gaba "a kofar shigowa sashen mama mukayi karo da Babana,..cikin rudani yace lafiya?
Asibiti..Baba asibiti zani kaita kawai yayana yake fadi.
Family motar mu Baba ya fito da,yayana ya sanya mama a bayan motan,nima na shiga bayan,shima baba haka ya shigo muka zauna nan..yayana ke gaba yana tuki.
A hanyar mu ta zuwa asibiti kuwa ba abinda nakeyi sai kuka ina fadin mama ki yafemin nayi nadama,bazani sake ba kinji mama!..yayana kuwa sai masifa yake yana cewa kiyi fatan kar wani abu ya sameta,don kuwa idan haka ta faru bazani yi maki da sauki ba...sai da Baba ya tsawatar sa'anan yayi shiru.
Tunda muka shiga motan idonta a rufe numfashinta ma sama-sama...shima babana a hankali yake kiran sunanta,.muna shiga haraban asibitin ta rike min hannu gam..ta bude ido a hankali tana kallona tace..' kiyi hakuri..kiyi hakuri..ta fada,zata sake magana kenan ta saki hannuna tare da rufe idonta a hankali..

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.