Pages

Monday, 20 January 2020

YANDA ZA'A MAGANCE WARIN BAKI.

   ABABEN DA KE SANYA WARIN BAKI, DA KUMA YANDA ZA'A MAGANCE SHI!

Ina fatan duk mun san me ake nufi da warin baki? Warin baki shine wani iri doyi ko iska barar dadi da ke fitowa daga bakin dan' Adam. A gaskiya duk wanda yake fama da warin baki zai kasance yana jin kunya ko nauyin yin magana gurin taro, ko yin magana da abokan sa, sabida a duk lokacin da yai numfashi iska ta fito, tou lallai kuwa duk wanda yake kusa dashi zaiji babu dadi.
Kada daga cikin ababen da ke sanya warin baki sune kamar haka:
~Rashin shan ruwa,
~ulcer na ciki da makogoro,
~yawan cin danyen albasa,
~cin daddawa,
~rashin wanke baki, ko kurkure baki a yayinda aka gama cin abinci me dauke da su daddawa da sauran su.
  Wadannan da aka lissafo sune mafi kuma kadan daga cikin ababenda suke kawo warin baki... Tou idan ana fama da warin bakin ga yanda za'a kawo karshen sa.
  Da farko ga ababen da za'a Bukata:
~kanufari
~danyen citta(Ginger)
~cinnamon
~Ruwan kal
~mint leaf.
   Ina fatan mun san duk ababen nan da aka lissafo? Kanufari shine babban makamin mu a nan! Kanufari yana maganin ababe da dama, ciki har da ciwon hakori... Ku lura kasashe ketare kamar india da sauran su, basuyin maclean ba tare da sun sanya kanufari a ciki ba. Don haka kanufari ba warin baki kawai yake magance ba, har da ciwon hakori idan aka dace.
Idan hakori na ciwo, a sami kanufari a sa a baki a tattauna(a cikin baki) idan yayi lukui, sai a ture shi daidai inda ke ciwon a barshi na dan lokaci sai a tofar, idan kuma anan fama da warin baki, maimakon a tofar sai a hadiye.

  Sa'anan za'a sami roban ruwa me kyau da marfi sai a jika kanufari, da citta, da cinnamon idan ya jiku sosai a tace a zuba ruwan kal , a sami kuma roban ruwa me kyau sai a zuba... Tou da wannan hadin ne za'a dunga kurkure baki safe da dare.
Sa'anan anfanin peppermint shine a dunga tattauna shi.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.