Pages

Thursday, 16 January 2020

RIKICHI 6

RIKICHI
  Episode 6
      By Aisha M. Gana

Na rasa sukini a safiyar ranar, komai nakeyi sai mafarkin nan ya dunga fado min... Duk sai na matsu Sameer ya shigo na sanar masa.
Iyaye ne na lura jikin su a mace yake, na basar ina tunanin wata kila gajiya ce bata bar jikin su ba.
Har izuwa karfe goma sha dayan safiya, Sameer bai shigo gidan mu. Wanda wata sa'in daga masallaci ya ke gangarowa yazo muyi karatu tare. Ganin haka yasa na dauki wayar (line-line) nayi kiran sa, shiru ba'a daga ba. Na dawo kan computer ta na aika masa sako, nan ma shiru...nan na futa ina fadin "ni Sameer zaiyiwa banza?"
   Jira nake hade da tsirawa hanyansa ido, amma babu alamun sa... Na kasa jurewa, na nufi gidan su.
Mahaifiyarsa ce na hanga tana tare da wasu mutane, tana hango ni ta shiga yiwa mutanen yaren su, suka bar gurin ita kuma ta nufo ni tana me murmushi muka hade.
Bayan mun gaisa, nake tambayarta, yau sameer lafiya? Nayi kiransa bai da'ga ba, kuma yau bai zo ba, jiya kuma bai fada min za shi wani gurin ba.
   Asshaahh.... Ta fada! Tare da chigaba da fadin "kin ganni ko, na sha'afa ya bar sako na baki. Bayan ya dawo daga gun ki jiya, aka yo mai waya daga can, wai ya zo. Tou da shike akwai wadanda zasu tafi gida a yau, sai aka shirya mai komai a darwn jiyan, suka kama hanya yau.
A sanyaye na dube ta tare da fadin "tou yaushe zai dawo?
Ban sani ba, amma ba zai dade ba.
Haka na koma gida jiki na a mace.....
Bayar na baro gidan su Sameer din, umman sa ta fashe da kuka "" mutuwa me yankan kauna....kuka take tana fadin mutuwa ka raba Hafsat da Sameer! Hafsat abin tausayawa ce.
Ranar dai na kasa barci, a matse nake gari ya waye, na sanarwa iyaye na su shirya mun tafiya.
Ina idar da sallah asubahi na shirya kaya cikin akwati, na fiddo takardun tafiyata.
Bayan na kimtsa na kwashi visa da sauran takardun tafiyat na nufi dakin Umma ta. Nan na tarar ba ta cikin dakin, na dawo ta mahaifi na, nan ma ba su ciki, cikin mamaki na shiga dube dube ina tunanin ina suka nufa da sanyi safiyat nan... Bayan na duba lungu da sakon gidan, na gan babu alamun su sai kawai na sa kai zuwa gidan su Sameer.
Ina kaiwa koridon da zai sada ni da dakin umman Sameer sai na hangi takalmin Umma ta... Don haka na karasa zan shiga dakin, amma maganar da naji sunayi ya bani damar dakatawa na saurare su.
Umman Sameer ce ke  fadin "hanzarta ki tafi kar ta farko baccin ta duuba ba ta ganki ba.
Uhmmm... Umma ta ta nisa hafe da fadin 'ni fa a  takure nake'
"yi hakuri, halin da yar' nan zata shiga idan ta sami labarin mutuwar Sameer  shi nake hangowa.....
Ban san yaya maganar su ta kai karshe ba, amma bude ido nayi na gan kaina a gadon Asibiti.
A takaice dai, nayi shekara ina jinya, domin kuwa na koma kamar wace ta samu tabuwar hankali. Bayan ma na sami sauki iyayena sukayi-sukayi na koma makaranta, na ki sabida babu abokin tafiyata, da haka nayi shekaru uku zaune gida, daga baya dai na koma..... Tayu ajiyar zuciya sa'anan ta ce "kaji dalilin kenan"
Cikin tausayawa ya sa hannunsa ya share mata hawayen da suka zubo mata a kunci.
"Allah sarki, wannan labarin da ban tausayi yake! Nayi maki alkawari da yardan Allahu idan da namiji kika haifa Sameer Zamu sanya masa. Allah ubangiji shi kuma Yiwa sameer rahma, yasa Aljanna makomarsa!
"Aamiin'' ta amsa.

      **      ***         ****
Allah da ikonsa, Hafsat ta haifi da' Namiji... Tou ina ganin bazan iya misalta ko baki labarin irin farin ciki da murnan da suka tsinci kansu ba, a lokacin.
Wannan da da Hafsat ta haifa, shi ne babban yayan mu "SAMEER"
  Bayan haihuwan Sameer da kamar wata biyar, akayiwa mahaifinmu transfer zuwa lagos tare da karin girma a gun aikin.
Hafsat tayi sallama da iyayenta sabida su ma din iyayen zasu koma kasar su da zama.
   Ba su jima da komawa lagos ba, yan uwan abba suka soma yo masa saki da korafi, wai ya ki kawo dan sa su gani.
  Nan wasu suka shiga jigilan zuwa, duk kwana bibbiyu, wai suna zuwa duban yaro... Ganin haka yasa mahaifinmu neman transfer zuwa Minna Niger state.
   Hafsat da danta Sameer suna samun  kyakkyawan kulawa daga wajan mahaifin mu.. Yana son sameer kamar ransa, idan da yana da iko, tou da ko ku'da ba zai taba yaya Sameer ba.
Suna zamar lafiyar su, abokiyar (kishiyar) kakan mu ta kawo shawaran da ya dace auri wace suke yare daya (watau bagwara kenan) wai shine mutuncin sa. Bayan da mahaifin mu ya sami labarin haka, yace masu shi mata daya ta ishe shi, kuma suna zamar lafiyar su don haka a janye maganar nan.
Ita dai mahaifiyat mahaifinmu (kakar mu kenan) ba ta ce komai ba, sai kishiyarta ce ta shiga babatu harda yar kwalanta wai don ba itace ta haife she a cikin ta ba shi yasa shawaran ta bai zaman masa dole ba..... Kin ji fa!
Mahaifin mu ba ya kaunar yagan ya sabawa iyayensa, balle har su kai ga zubda hawaye akan sa, don haka dole ya amince ba don yana so ba.
 Hajiya Asabe, watau kishiyar kakan tamu itace da kanta ta zabawa mahaifin mu mata.
Diyar kanwar ta da suke uba daya me suna Rakiya( wace a yanzun muke kira Mummy) itace aka aurawa mahaifin mu.
  Tun zuwan Rakiya zama yaki dadi... Zaman lafiya da kwanciyar hankali ya bar gidan mahaifin mu.
Hafsat ba ta jin dadin zaman gidan kwata kwata, ga shairi da makirci wasu abun ma a gaban Abba akeyi mata, amma kuma bashi da ikon magana.
Kowa yasan Mummy ta Asirce Mahaifin mu.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.