Pages

Thursday 8 November 2018

MUMUNAR KARSHE.!😥

~MUMUNAR KARSHE!😢~ Rukai'yah ta kasan ce cikakkiya. ga ilimin addini da ta boko. Ga biyayya da tausayawa. Mahaifinsu ya rasu, a lokacin tana j.s.s3, ta na da kanne hudu, uku mata, sai dan autan su. Rayuwa tayi masu tsanani, duk da hakan mahaifiyarsu ta kasance mace me wadatar zuci, tana kuma horon ya'yanta da su kasance haka,su kuma dunga godewa Allah a duk yanayin da suka sami kansu. Mahaifiyarsu ta kasance tana tuyan masa tana saida wa,fatan ta,ta ya'yanta su sami ingantaciyar ilimi don haka ba ta yarda suyita tangaririya ba a gari. Duk inda zata tafi,ko ziyara da ya'yanta take zuwa hakan yasa shakuwa da sabo a tsakaninsu. Bata da kawaye sai ya'yanta, haka su din ma. Duk idan sun tafi makaranta ko islamiyah, Allah, Allah suke su dawo gida sun rungume mamar su. Da haka Rukai'yah ta gama makarantar sekandiri. Ga ta da kwazo da basira, amman ba halin cigabawa sabida rashi. Shekarar ta daya tana zaman gida bayan da ta kamala sekandari. Amman kuma bata yi zaman banza ba, sabida ta shiga haddah(al-qur'ani). Ta kuma kasance tana suyan warah a kofar gidansu da yammaci. Mukthar makwabcin su ne,mahaifinsu ya rasu ,su dinma talakawa ,sai dai kannensa mata uku da sukayi aure,mazajensu masu kudi ne don haka suka gyara masu gida. Mukthar ya kan zo siyan wara a gun Rukai'yah. Ya kasance yana sonta sosai, amman bai taba fadawa kowa ba, bai kuma sanar da ita ba, ko da alama..ya barwa zuciyar har sai ya sami abin yi, sannan ya fada mata. Wataran ya zo gun mahaifiyarsu Rukai'yah sayan wainar masa, sai yake tambayarta ya labarin makarantar Rukai'yah? Tayi ajiyar zuciya tare da nisawa tace ..."toh ga mu ga Allah, amman ina iya kokari na don ganin ta ci gaba da karatu, sabida Rukai'yah yarinyace me kwazo...na kuma yarda ta ita. ...toh mama Allah ya shige mana... Bayan sunyi sallama ya tafi gida. Kwana uku a tsakani, ya sake zuwa ya sanar da mahaifiyar Rukai'yah da su kawo takardun makarantar ta. Tayi farin ciki sosai sannan ta nemi sanin yanda zai taimaka masu. "mijin kanwata yana daya daga cikin masu ba da 'schoolarhip, don haka nayi masa magana.' Ba'a bata lokaci ba aka hada masa komai da suke bukata. Bayan dan watanni ya sanar masu su kasance cikin shiri, Rukai'yah ta sami karbuwa, sai dai ba cikin garin ba. Ma'ana zata tafi wani gari makaranta. Mahaifiyarsu Rukai'yah tayi farinci har sai da tayi hawaye. Tayi wa Mukthar godiya, tayiwa Allah godiya.Don haka suka soma shiryawa, duk da ba wani shirin kirki zasuyi ba. Ana sauran kwana hudu Rukai'yah ta tafi, mukthar ya zo gidansu. Bayan sun gaisa yayi mata nasiha hade gargadin cewan tasan kawayen zata bi.... Godiya tayi masa...sannan ya dauko jakka....'gashi kayan sayawa kannena suka hada maki, don students suna son saka kaya. Nan ta sake yi masa godiya cikin farin ciki. Yasa hannu a aljuhunsa ya ciro envilop, tare da mika mata...."ingo wannan ki kara! A ranar sai da mahaifiyarta tayi hawaye sabida farin ciki. Daren ranar da zata tafi ba su rintsa ba, ta kwanta lamo akan cinyar mahaifiyarta , a yayinda mahaifiyar ta ke shafar kanta. ..."mama...! Na'am Rukai'yah.... Inn'shaa'Allah hutu zai zo maki,nan ba da dadewa ba! Murmushi mamar tayi..."na sani, na sani Rukai'yah, nasan kalar yar' da na haifa, na yarda dake dari bisa dari, don haka fatan alkhari da addu'a kawai kike bukata.... Washe gari duk idanuwansu sunyi jajir sabida kukan rabuwa, Rukai'yah ta kasance tana tunasar da kannenta da su kyautawawa mahaifiharsu da haka suka rabu ta tafi. Tunda ta sanya kafarta cikin makarantar, bata shiga sabgar da ba nata ba, daga masallaci sai daki... Bata da kawaye sabida bata sa ba da yin kawaye ba tun a gida, duk da tana birge wasu matan, suna kuma son yin abota da ita sai dai ta ki basu fuska. Su biyar ne a dakinsu. Rukai'yah da wace ake kira da Fateemah sune yan' year1, 100level kenan. Sumayyah da Aisha sune yan 2, sai grace a cikin su yar' shekarar karshe ce ita. Rukai'yah ta kasnace bata son kazanta, don haka ita ke sharan daki ta kuma zubar da datti, ganin haka yasa suka bar mata sharan dakin, ba wace keyi sabida girman kai....da alama fateemah itace kawai yar masu kudi a cikinsu, sauran kuwa yan karyane! Sai karyan arziki da samun guri. Duk wasu ababe da akeyi a hostel ko cikin makaranta, idan dai ba ta addinin ba ce, Rukai'yah bata zuwa. Shakatawan dare bata zuwa, so dayawa sumayyah takan gayyace ta su je party.amman sam.! Akwai ranar da daga ita da fateemah suka kwana a daki, sauran duk an tafi yawon holewa. Rukai'yah ta dade tana mamaki da tir da halin wasu matan university. Idan kuwa waya suke, sai ta ji kamar ta nitse ba kamar fateemah wace babu ruwanta da yawoce yawoce, amman soyayyar waya kam,itace ta farko. Da haka semestan ta kare, ko wacensu ta nufi gida. A kwana a tashi hutu ya kare sun dawo. Fateemah ce kawai bata dawo cikinsu ba. Hidimomi sumayyah ta yo wa Rukai'yah, ta yo mata sabbin kaya, hade da takalmomi da jakkuna. A gaskiya Rukai'yah tayi farin ciki sosai, hade da yi mata godiya. Satin su hudu, fateemah ta dawo. Don haka sun ci gaba da komai as usual, Rukai'yah ce me shara. Idan sun dawo yawon su, su sayo mata kayan dadi. Tun bayan da sumayyah ta karanci cewan fa Rukai'yah yar talakawa ce, ta soma kunsa kanta tana bata shawarwari da ta dunga bin maza ta na sami kudi. Rukai'yah tace sammmmmm....! Allah shi tsare ta, ita ba irin wannan kudin take so ba. Duk da hakan sumayyah bata hakura ba,ta dunga bin Rukai'yah da wannan maganar da ga karshe Rukai'yah ta daina zaman daki, ta tare a massallaci sabida sumayyah. Idan ta shigo daki, lallai kaya tazo sauyawa ko kuma zata ci abinci, da haka fa har suka shiga shekara ta biyu. Duk da haka sumayyah bata hakura ba.... Wataran Rukai'yah ta shigo daki sai ta tarar suna firansu na yan duniya, sauri ta soma yi tana son ficewa, ganin haka yasa Aisha mikewa ta rufe kofa, ta juyo ga Rukai'yah tate da ta'ba mata kirji "ki rantse ke budurwa ce"...ina nufin baki ta'ba sanin namiji ba. Cike da mamaki Rukai'yah ke binsu da kallo ba tare da ta furta komai ba, sai dai lebenta na alaman motsin neman tsari. Gira Aisha ta da'ga mata...."sarai kin san abinda nake nufi. Nan sumayyah ta mike, wannan bakauyar yanzun zata ce ita ustazuwa ce...ustazuwar karya! Nan Rukaiyah ta ra'ba gefe zata fita, Aisha ta sha gaban ta. Saurara.....wai ya ya zamuyi da ke na? Muna son mu wayar maki da kai amman gaki dai kamar wata...... Nan Aisha ta kama mata hannu ta zaunar da ita.....ta soma magana murya kasa kasa...."wai kuwa Rukaiyah kin san baiwan da Allah yayi maki kuwa?dube ki fa! Dube ki fa!...wallahi da nice me irin jikin nan naki da yanzun na sayi wannan gari. Wannan jikin naki ba karamar arziki asset bane.. Ki dube mu daga ni har Aisha ya'yan talakawa ne kamar ki, amman da jikin mu, mun farantawa iyayen mu. Don haka muna son mu taimaka maki mu wayar maki da kai,kema ki shiga yayi ki sharewa mahaifiyarki hawaye , ki hole rayuwarki... Sun jima suna bata shawarwari, ita ko banda kallonsu ba abinda takeyi. Rukai'yah ta kauracewa dakin sam....haka suka soma jin takaicinta. Wataran ta shigo daki cin abinci, sai ta tarar da fateemah, bayan sun gaisa fateemah ta dubeta,tare da fadin "wai sabida su Aisha kika kaurace wa dakin nan? Shiru tayi bata amsa ba, Uhmmm.....Rukai'yah kenan! In banda abinki, matsayinku daya fa,kin zo, sun zo, ba wace tafi wata....yanda suke da iko, kema haka kike da iko don haka ki daina takurawa kanki sabida su....amman kuma kin san wani abu? A gaskiya maganar da suke yi maki gaskiyace. Batayi mutuwar zaune ba, sai da taji fateemah tana waya da saurayinta ya shigo nijeriya don haka zasu hadu a abuja..nan da nan ta shirya kayanta ta nufi airport. Sumayyah da Aisha basu kyale Rukai'yah ba, sai da sukayi nasara akanta. Alokacin zata kammala shkararta ta biyu. Naseer da' ne ga wani shahararen me kudi,... Abin kunya ne fadin irin tarbiya da kuma halayensa. Garin yawace yawocensu suka hadu da abokanen abokan sa. Anan ne sumayyah taji su suna firan Naseer. Daga wannan lokacin hankalin ta ya tashi, tasan dai bata jerin macen da Naseer yake so....nan Rukai'yah ta fado mata a rai,don haka ta shiga hura mata wuta har sai da ta amince da bukatar ta😔. Sumayyah tare da Aisha suka nufi kasuwa don yi mata sayayya. Bayan sun dawo suka dauke ta zuwa sallon akayi mata gyaran kai, da farce. Daga nan suka nufi gidan cin abinci don maganar da zasuyi da ita a sirance. ..."cikin murya Aisha ta rungume Rukai'yah. Sumayyah ta soma magana, gobe idan Allah ya kaimu, zaki tafi Abuja gun Naseer. Shima gobe jirgin sa zai iso najeriya sabida ke. Naseer da' ne ga wani shahararen me kudi...ya kasance yana holewarsa da mata iri iri, sai dai tun da yake harka da mata bai taba nasarar kecewa mace budurcinta ba, haka yasa yane cigiyar budurwa fil a leda, hade da alkawarin makudan kudi wanda ya iyan sayan gari guda, kingan kenan, talaucin ku yazo karshe muma zamu ci albarkacin ki. Nan suka tafa suna darawa, a yayinda kirji Rukai'yah ke bugun uku-uku, murmushin karfin hali tayi. Kashe gari suka yi mata rakiya har tashi, sai da motarsu ta soma tafiya sannan suka koma hostel cikin murna. Kwanan Rukai''yah hudu kayi kiran tana sanar masu zata dawo. Ihu suke,suna murna....suna yi mata fatan isowa lfy. Tun da ta taso suke kira, kin kusan isowa, tace a'ah, har ta soma fadin eh...alokacin da ta iso gari sukayi waya da sumayyah ta tabatat masu ta shigo gari, yanzun zata hau adaidaita sahune ya kawo ta makaranta. Murna suke, suna wake wake....a haka har an kusan kai awa bata iso ba, don haka suka shiga kiran wayarta....shiru ba'a da'ga bah. Sun yi kira iya ba adadin, bata da'ga ba, nan Aisha ta fusata.....tabdi jam,renin wayau yarinyar nan take son yi mana fa! Nan sumayyah tace banason na yarda da abinda zuciyata ke fadamin, don ko ina iya kashe ta idan hakan ya tabbata. Ba su hakura ba, suka ci gaba da kira har sai da aka da'ga. Ba tare da sun saurara anyi magana daga dayan bangaren ba, suka soma yarfa masifa. ..."ayyah... A dunga sassauci! Wani ya fada daga bangaren, jin muryan namiji yasa suka sassauta. Ya cigaba da fadin "ko zan san alakar ku da me wayar,? Nan gabanyayi ras ! Suna tunanin ko yan fashine. Da sauri sumayyah tace mu kawayenta ne. ....a gaskiya wace kuke son kuyi magana da ita tayi hatsari dazun,tirela ya fado masu suna cikin adaidaita sahu don haka, rai yayi halinsa . Jefar da wayar Aisha tayi,hade da wata iriyar ihu me razanarwa. Ita kuwa sumayyah jikinta karkar yake,har hakoranta suna karo da juna..... Mahaifiyar Rukai'yah kuka take sosai, ta matsa kusa da gawar yar'ta ta dafa ta....tana me sumbatu,kanenta ma haka. A lokacin da za'a tafi da ita, a lokacin su Aisha suka iso, isowarsu ke da wuya aka fito da gawarta, ai nan Aisha ta ruga,da taimakon jama'a a ka kamata don an dauka ta haukace. Allah sarki Rukai'yah😢😢 Lallai wannan shine mumunar karshe..... To be continue....👌🏻

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.