Yau daya ga watan February, a shekran dubu biyu da ashirin da biyar, Aisha M. Gana ta kwankwaso maki kofa domin ta yi muhawara da ke, tare da yi maki tambayoyi, duba da ganin cewan ke din abin koyi ce ga mata, musamman masu tasowa.
Mun dade muna bibiyar ki, muna kuma kallon yanda kike gwagwarmaya tare da gudanar da kasuwancin ki gwanin ban sha'awa. Wannan dalilin ne yasa muka tunkare ki, ki bamu dama muyi maki virtual interview.
Sunana Aisha M Gana.. Ni ce ke da Ganarious blog inda za mu wallafa labarinki.
(1) Da farko de za mu fara da introduction da kuma son sanin background.
Ko zaki fada mana sunan ki, Garin ki, Yaren ki, Shekarar da aka haife ki, Marital status, da kuma educational background dinki?
Assalamu alaikum Waa Rahmatullah Sunana Ummulkhair Abubakar,yar asalin sokoto haifaffiyar garin Bida jihar Neja.
An haife ni talatin da daya ga watan December 199_
Na tsaya karatu iya sakandiri Wanda na gama tun shekara ta dubu biyu da sha biyu,Wanda duk yanda naso ga ci gaba Allah bai nufa ba amma in shaa Allah ban cire rai na komawa ba nan gaba kadan.
(2) Shin, ta ya ya akayi kika fara kasuwanci? Me ya faru?
Ya ya business idea din ya zo maki?
2 Eh toh, na fara kasuwanci ne tun bansan menene kasuwanci ba wato lokacin kawai ba wani uzuri gareka ba na taso da shaukin son Sana’a ne saboda mu gidanmu ba a talla, kuma abun na ban sha’awa a lokacin idan na ga wasu na talla😅(saboda quruciyana lokacin).
Na taso bansan komi bane sai karatu, Ina kika fito karatu Ina zaki karatu tun Ina qarama, Wanda har mutane ke ganin mahaifiyata tana takura ma qwaqwalwata da yawan karatu na boko da addini (Ashe Komi lokaci ne😔) idan muka tafi makaranta tun safe ni da mahaifiyata (can take koyarwa itama) sai la’asar zamu dawo saboda in an tashi Ina tsayawa lesson, da mun dawo aka dan ci abinci zan saka uniform din makarantan hadda na a cikin Leda in wuce dashi Islamiyya, daga islamiyyan zuwa makarantan haddan namu yafi kusa akan in dawo gida, kuma muna tashi Islamiyya 6pm hadda kuma mu tafi bayan magrib.
Tau idan aka tashi islmiyya kowa ya watse sai in shiga gidan qawar mamana(maqota da makarantan) in canza kaya zuwa na hadda in wuce sai 10pm za’a tashi in dawo gida, washegari ma haka za’a sake fita, tau rayuwar dai haka akayi ta a lokacin quruciya.
Duk yanda muka so ci gaba da karatuna na gaba da sakandiri Allah bai nufa ba(Wanda tabbas akwai wani tanadi da yayi mani a gaba kuma ko yanzu Alhamdulillah bai bani daman ci gaba da karatun boko ba amma ya bude min wata qofar ni’imar bai barni haka ba)
Bayan na gama sakandiri da shekara daya cikin biyu mahaifiyata ta nema min wani institute na computer domin ta lura nima zaman hakan na damuna,a take naje nayi diploma a Amitech computer training institute dake birnin minna.
Tundaga lokacin sai na sake mayar da hankali ga karatun addinina musamman duba da boarding school nayi Ana wuce ni sosai a hadda, saboda wadanda muka faro tare tun muna yara a lokacin ma sunzo sun riga ni haddace Qur’ani gaba daya, sai na ga tau ai dama ne yanzu na samu in mayar da hankali sosai wajen Neman ilimin addini.
Ina son karatu sosai gaskiya shiyasa da bokon bai yiyu ba sai na nema ma kaina makarantan hadda ya zama Ina zuwa makarantan hadda biyu kenan(da asalin Wanda na fara tun Ina yarinya da kuma Wanda na saka kaina)karatun sai ya zama yana rage min kewa bani da lokaci sai kokarin ganin baa sake wuce ni ba, hadda bibbiyu sama da qasa nake koya a makarantu biyu, haka dai aka ci gaba da rayuwa bayan sakandiri.
Akwai wani lokaci da muka je wata makaranta yin Dawrah a lokacin Ina sanaan su Aya mai sugar Ina sarin su charbin malam Ina yin su bambara da Gurasa, ranan da muka fara zuwa makarantan na ga anguwan baa sayar da irin abun ci hakan nan babu ma shago a kusa sai anyi tafiya mai nisa,gashi in munje tun 9am sai 5pm zamu tashi.
Ai Ina dawowa gida ban Bari kaina yayi murfi ba😂na ce ma mahaifiyata ta fara yin zobo da pure water da ginger ni zan dinga su Aya dasu Bambara Ina kaiwa wajen 😂.
Ranan da na fara Kai Kaya an fito break kafin kice me Kayan nan duka sun qare😅haka na ci gaba da yi, har watarana an idar da salla malam nayi mana nasihohi ya basu misali Dani yace ga Ummulkhair nan riba biyu take ci ga neman ilimi ga sanaanta 😅shikenan malam yayi ma kowa allura kowa ya zabura ya fara kawo abun sayarwa.
(3) Ma Sha Allah🤗 wannan labarin yayi dadi sosai. Jiya muna hira da wata, sai ta ke ce mun tana tsoron fara kasuwanc. A matsayina na wace take da ilimi akan kasuwanci, ina ganin wannan common issue challenge ne da diyawa mutane suke fuskanta. Wasu zaki gan suna tsoron kar suyi production a ki saye wanda haka zai janyo masu asara. Kowa de da tasa irin tsoron. Shin, lokacin da kika fara business, kema kin tsinci kanki a irin wannan yanayin tsoron?
Idan kin amsa da "Eh," zamu so muji yanda kikayi overcoming wannan tsoron.
A zahirin gsky bani da tsoro na fara business kuma nima bansan dalili ba, muddin zuciyata ta raya min inyi abu tau wlh in shaa Allah sai nayi kafin inyi zaki sha mamakin irin hidima da nake wa abun nan na addua, Hana idona bacci nakeyi inyi ta adduan ya samu karbuwa kuma cikin hukuncin ubangiji muna samun albarkan Allah a ciki.
(4) Tambaya ta gaba bayan Self-doubt shine: Criticism, watau masu cewa "Ayi de mugani" ko masu yiwa mutun dariya idan ya fara business ko wani abu can daban. Ganin suke shirme kawai yake yi, ko bashi da na yi ne, ko abinda yake yi ba zai je ko ina ba. Ko kin tsincin kanki a cikin irin wayannan mutane a lokacin da kika fara kasuwancin ki? Idan kuwa kin ce eh, yaya kika tsaya akan ra'ayinki amaimakon ki zama discouraged ko ki yi give up?
Hmmmm a lokacin da na fara sanaan abincin gargajiya farko farko ne na samu ire iren izgilancin nan. Akwai wanda qiri qiri ya gayamin wannan sanaan su bambara da nakeyi yaushe zai ciyar dani har yarinya in banda tarin wahala?(bambara wani abincin marmari ne da ake yi a jihar Neja, abincin gargajiya ce na nupawa) a lokacin naji ciwon abun nan a raina kuma na roqi Allah ya nuna min ranan da wannan zaici arzikin wadannan sanaan, zancen da nake miki yanzu tun baa Kai ko Ina ba a wancan lokacin sai da yaci arzikin su dambu😅ko a iya haka Alhamdulillah ya tabbatar ba aikin banza nakeyi ba sbaoda da sanaan su bambara aka fara sanina sosai sannan da sanaan Bambara daidai da omo na wanki bana roqa a bani ni nake wa kaina komi da kaina
Ma sha Allah. This is inspiring.
(5) Da babban jari kika fara kasuwancinki? Ko zaki fada mana yanda kika fara kuma ya girma?
Eh toh,yanzu dai ba za’a saka da sanaan su Aya da charbin malam da nayi tun kafin inyi aure ba saboda a lokacin ba ma zan iya tuna jarin ba.
Amma dai zan iya tuna jarin da na fara riqewa a dunqule shine bayan na haifi diyata ta farko, in laws dina suka kawo mana ziyara sukayi mani kyauta ni da yarinya dubu talatin.
Ko a lokacin Ina sanaan sarin su spices daga Kano sannan na fara harkan dan pre order kadan kadan kafin in haihu.
Da nazo na haihu na samu wancan kudin sai ya bani daman yin order ta farko da kudina ba sarin sari ba. Nayi order lokacin wasu bed side lamp ne a lokacin duniya na kwance😅ko ni 3000 nayi sayar dasu😅.
Tundaga lokacin sai na ba ma harkan pre order qarfi (Duk da ban wani samu support din babanta a lokacin ba, amma dai bai hana ba, shi dai lokacin baya so gani yake kaman ya rage ni da wani abu ne yasa nake son business) amma as time goes on ya ga ba wasa nakeyi ba da kanshi ya dauki 70k bana taba mantawa ya bani yace in qara jari
Oh Ma Sha Allah.
(6) Kin taba zuwa, ko participating a wani business school ko training a yayinda kika fara kasuwancinki? Idan kin amsa da "Aa," ta yaya kika san yanda ake sanyawa product price, book keeping, financial management da sauran ababen da ba'a koyar da su ko ina sai a business school ko business training?
Ban damu da zuwa workshop na business ba saboda ni da kika ganni nan confidence dina iya inyi business ne duk abunda zai sa ace in fito inyi magana gaban Jama’a bani da wannan confidence din yanzu jikina zai fara rawa, shine dalilin da ko za’a yi workshop bana son zuwa saboda banso ace in tashi inyi magana, vwara ma idan Ina daga zaune inda nake zan iya awa hudu Ina magana akan business ban gaji ba akan ace in tashi inzo in bada jawabi.
Na koyi yanda ake saka riba da sanya farashi ne tun shekarun da na fara harkan pre order shekara biyar baya kenan a wani group na wata baiwar Allah Aysha suraj (duk da yanzu ba zance ga inda take ba saboda nazo nayi rashin tsohon wayana da layina)
(7) Ina sunan business dinki ya samo asali?
Sunan business dina ya samo asali ne daga sunan diyata da suna na wato UMM AMATULLAH Duk da last 3yrs naso canza sunan amma printer na ya ban shawaran kada in canza saboda idan yana min aiki a shagon shi mutane suka shigo suna yawan santin sunan suce ya musu dadi.
Naso canzawa ne lokacin da na fara bibiyan su Ayeesh A Sadeeq dasu Likitan Sanaa akan muhimmancin saka business name qarami kuma unique wanda ba zai wahalar da mai karantawa ba, ni kuma na duba na ga nawa yayi tsawo gashi in ba mu ba yawanci qabilu zasu tsinci sunan da musu wahala,haka dai na haqura nayi register da wannan sunan.
Alhamdulillah Duk da naso canzawa Ina Jin dadi yanzu yanda mutane da yawa da sunji Umm Amatullah ni nake fara zuwa ransu har sunan ma yana neman rufe asalin sunana.
(8) Duk me kasuwanci, yanada kishiya. Ma'ana competitors kenan. Ta yaya kike banbanta kanki da competitors dinki? Me kike yi daban da nasu?
Qoqari wajen riqe sirrin sarrafa kayana da zai iya bambanta ni da saura(kinga kaman misali,kamfaninmu na cikin Sahu na farko da muka fara gabatar da shampoo mai hadin karkashi da kanumfari a social media). Mutane da yawa sun san shampoo amma lokaci daya muka goge musu hadda muka hada namu shampoo din da sinadarai da zai tashi daga normal shampoo (Duk da yanzu munyi yawa sosai masu shampoo na karkashi amma still bai hana a bambance mu ba, sai dai muna nan muna wani shirin da in shaa Allah zamuyi mashi wani kwaskwarima daban mu sake bambanta).
Rashin algusu(Wanda har ta Kai mutane ko kashi zan kasa in sayar in shaa Allah zasu saye nan take saboda yarda da sukayi mani da dukka products dina)
Sirrin hoto(yana taka muhimmin rawa wajen bambanta ni)Duk inda aka ga salon hotona ko da ba kayana nayi ma hoto ba za’a ce Umm Amatullah tayi hoton nan.
![]() |
Before: Hair Care |
Ma Sha Allah. Na ji dadin jin haka. Sai tambaya na gaba: (9) Akwai ranakun da mutun yake tashi ya ji baya son yin komai, ko ya ji abubuwa sun fita masa a rai sun dame shi... Kina tsintan kanki a wannan yanayin? Ya kike handling din irin wannan challenges din?
Break nake zuwa. Idan na shiga cikin yanayin nan na kan dan je hutun sai in dawo da qarfina lokacin qwaqwalwata ta huta zata dawo da qarfi.
(10) Hausawa suna cewa "Hannun da ya kirga riba, watarana zai kirga hasara" haka ne?
Kin taba yin hasara a kasuwancin ki wanda ya girgiza ki? Wani darasi kika koya daga wannan hasaran da kika yi?
Hmmmm muna adduan Allah yasa ya zama kaffara garemu😂😂ko last 2 yrs nayi wani asara da ya girgiza ni in ba yanzu ba ba wanda ya sani sai yan gidanmu. Shea butter da na saba kawowa bayan naje nayi siyayya na riga kayana wuto wa saboda in iso da wuri sai aka samu akasi an rasa daga Ina aka canza min buhun shea butter dina har buhu hudu aka bani Wanda bai da haske😓Kayan basu iso ba sai after 8 aka dauko min washegari na kwance buhu in fara aiki na ga shea butter babu haske, dole na karya musu farashi sosai in samu in rage asara.
Tundaga lokacin muddin zan riga kayana isowa yaron da ke min aiki sai ya tabbatar yaga shigan kayana mota sun tashi sannan na riqe driver guda daya wanda shi ke kawo min kaya .
Sai kuma qananun asara na production da baa rasawa Alhamdulillah da mun gano inda matsalar suke sai muyi kokarin ganin mun magance shi
Muna rokon Allah ya chigaba da kiyayewa. (11) menene "WHY" dinki? Kinsan bature yace komai da mutun yake yi, ya kamata ace yanada "WHY"
Me ke baki karfin gwiwa ki chigaba da kasuwanci ko da kinji kamar kiyi give up?
Babban WHY dina a business in canza background dina meaning in kawo sauyi a cikin rayuwata da ta iyayena da ya’yana da qannena.
Kaman yanda rashi ya hana ni ci gaba da karatu a wancan lokacin duk soyayyata da son karatu hakan ne ke bani daman jajircewa wajen yin Sana’a don canza ma qanne na nasu rayuwar su samu wadataccen ilimi.
Sa'anan ina da zuciya shiyasa nake da gudun abunda zai iya sa wani ya wulaqanta ni. Ban yarda da roqo ba kuma gashi Ina son cin dadi 😂😂shiyasa na dage in nema in samu in biyawa kaina buqata infi qarfin buqatuna in shaa Allah
Ma Sha Allah.
(12) Ko zaki iya fada mana Wacece role model dinki? Ina nufin wace idan kika dubeta ko da a hoto ne, ta ke baki sha'awa har kike son ki zama kamar ta, ko kike sha'awan kaiwa matsayinda take, kuma kike bin sahun ta.
Maryam Gatawa
Tun shekarun baya itace role model dina saboda a shekarun baya muna business kusan iri day na garin danwake da su yaji yanda take tafiyar da kasuwarta sai abun na ban sha’awa da burin nima watarana infi haka in shaa Allah.
Balle ita din ta taba taka wani muhimmin rawa a rayuwata wanda ba lallai ta iya tuna abunda tayi min na alkhairi ba.
![]() |
Before |
(13) mun zabi muyi maki wannan interview din ne sabida muna sa ran ki zama role model ga kannen mu da yan'mata masu tasowa, su kuma bi sahunki. Kwananki mun gan wasu bloggers suna yada wasu yan'matan TikTok, wayanda suka arziki cikin kankanuwan lokaci, a yayinda wasu ma har sun mallakin gida da mota na kansu. Haka yasa nake ganin kamar wannan irin nasaran zai birge wasu yan'matan, har su ji ina ma ace su ne.
Wasu kuma zasu so su bi sahunsu domin su m su mallaki gida da mota. Toh sai ina ganin irin wannan sahun ko hanyan yana iya kai mutun ya baro shi sabida diyawan su ba ta hanya madaidaiciya suke samun wannan arzikin ba. So a matsayin ki na wace ta fara daga kasa, kuma muke fata ki zama daya daga cikin wace za'ayi koyi da ita, wace shawarwari zaki ba wa mata, musamman nasu tasowa?
Shawara na garesu sune kaman haka👇🏻.
1 HAKURI
2 JURIYA
3 JAJIRCEWA
4 NACI
5 ADDUA
6 AMANA
Kasuwanci wani abu ne me zuwa cike da qalubale wanda ba zaka fahimci hakan ba sai qalubalen tazo, sannan baka da hanyan kauce ma qalubale na kasuwanci dole duk kiyayenka sai kaci karo dashi, shawara na garesu duk wacce ta tsinci kanta a halin na qalubale ko wata hasara na kasuwa ta sani ba hakan na nufin ta ajiye tayi give up ba, a’a hakan ma yana nufin wani matakin nasara ne da bata Isa ta taka ba sai da qalubale.
Shi qalubale tamkar qofa ce na bude nasara da daukaka in shaa Allah.
Ayi addua ayi juriya ayi haquri da yanayin rashin ciniki kada a gaji idan watarana baa saye ba watarana za’a saya, duk da haka muka faro.
Dole kafin kayi building trust tsakanina da jamaan da basu taba ganinka ba basu taba sanin gidanka ba a dau lokaci, Kai zaka bada qofar da za’a aminta da kai sannan Kai zaka bada qofar a gujeka.
Ayi haquri a riqe amanan dukiyar wanda ya aminta da kai, a kawar da ido daga cin haramun da dukiyar wanda ya aminta da kai sai a kai ga cimma nasara in shaa Allah
Ma Sha Allah. (14) Muna godiya kwarai da shawarwarin da kika bayar. Sai tambaya ta gaba "Yaya kike hangen company ki nan da shekaru 5-10? Menene plans and goals dinki?
![]() |
Hair growth set. |
Nan da shekara 5-10 Ina hango katafaren gini na kamfanin Umm Amatullah wanda zai qware wajen sarrafa Kayan abinci Wanda za’a saukakawa iyalai a gida kaman su garin danwake, garin Fankasau sindaran dandanon girki da sauransu.
Ina da plans sosai a shekarun gaba game da dan jaririn brand din nan in shaa Allah da nake adduan Allah ya cika min,a ciki akwai bude shagon saloon wanda a shagon mu ba zamuyi amfani da abu ko daya na wani kamfani ba face Kayan kamfanin Umm Amatullah Global enterprises daidai da comb na kamfani zai kasance.
Daga cikin burina akwai son mallakan katafaren waje na Kayan kwalliya da qyale qyale na yara(Kinsan ni maman yara ce😅😅)
Ma Sha Allah 😁
(15) Akwai abinda kike shiryawa a boye? Ko akwai abinda kike son customers dinki suyi anticipating gani?
Time shall tell in shaa Allah 😅zamu bayyana haka idan lokaci yayi
(16) Idan mutun yana son products dinki wasu hanyoyi zaibi domin ya same su?
Za'a iya samu na anan👇
Contact :07046456676
WhatsApp:07053066288
Facebook:Ummulkhair Abubakar
Instagram:Umm Jaafar
TikTok:Umm Amatullah Global enterprises
(17) Muna godiya kwarai da lokacin da kika bamu, anan muka zo karshen wannan interview din.
Munayi maki fatan alkhairi da rokon Allah ya cika maki burin ki.
Daga karshe mun baki dama nominating yar'kasuwa irinki, wace take gwagwarmaya sosai domin neman na kanta kuma wace mu ke sa ran yan'mata zasu bi sahunta.
Thank you 🤝
Nayi nominating Umm Sodeeq CEO Mahleed farms
Anan muka zo karshen virtual interview dinmu da Ummulkhair Abubakar, me kamfanin Umm Ammatallah Global Enterprises. Wani fata zakuyi mata?
Ku rubuta mana a comments section, muna kuma rokon ku da ku taya mu yada wannan interview din, fatan mu shine yan'baya suyi koyi da ire-irenta🙏
Mashallah Allah ta Kara dafawa data nafeesa aleeyu
ReplyDeleteMA Sha Allah tabbas maman a Atu mace ce abar koyi Ga qananan Yan kasuwa, ina roqon Allah ya qara WA rayuwar Ta albarka, yasa data da dukkan alkairi
ReplyDeleteMashallah Allah yh Miki jagora yh cigaba da rufa Miki asiri,Ina rokon Allah yh saukaka Miki hanyar halak yh Baki miji nagari
ReplyDeleteShe's a woman with golden heart ,mai zafin naima attimes if felt reluctant of posting she do come to my mind.
ReplyDeleteMasha Allah wlh naji Dadin krtn Nan danayi dama tana cikin role model Dina Allah y Kara daukaka yasa kufi hk
ReplyDeleteMaa shaa Allah
ReplyDeleteMaman Amatullahi Allah ya miki daukakar da baki taba zato ba ta alkhairy a kasuwancinki
Masha Allah ina rokon Allah yaqara saukaka company ki yasa masa albarka, najima ina bibiyarki sama da shekaru hudu Alhamdulillah kuma ina karuwa da ke sosai da irin kwarin gwaiwar da kike bamu ,Allah ya dafamana Allah ya raya mana Amatullah🙏
ReplyDeleteMashaa Allah. Allah Ya Albarkaci kasuwancin ki Ya cika miji buri kan ki. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum. I've been a fan for more than 2 years
ReplyDeleteAllah Ya Bamu ikon fara wa muma🤲
Masha Allah
ReplyDeleteAllah y albarkaci kasuwa yasa albarka
Allah yasa Albarka
ReplyDeleteMaa Sha Allah ubangiji ya karowa rayuwa Albarka ya Karo kasuwa me albarka ❤️❤️
ReplyDeleteMa shaa Allah
ReplyDeleteAllah ya cigaba da daga Miki ya Baki miji nagari ya raya Mana Amatullah😊
Naji Dadin wannan hora Kuma ta zaburar dani sosai
Masha Allah
ReplyDeleteAllah ya sa albarka
Masha Allah, tabbas ke din mutuniyar kirki ce wacce Babu baqin ciki, hassada ko qyashi shiyasa Allah yake duba al'amuranki. Allah ya qara dafa miki yasa kifi haka ya nuna mana aurenki da Mamman, ya raya Amatu da namu yaran baki daya 🤲🤲🤲
ReplyDeleteMa sha Allah
ReplyDeleteMasha Allah Allah yasa wa rayuwa albarka Ameen
ReplyDeleteMaa shaa Allah,muna yi mata fatan alkhairi, Allah ya albarkaci kasuwancin ta kuma Allah ya cika mata burin ta na Alkhairi, Allah yasa product din ta ya fita ƙasashen duniya
ReplyDeleteMa Shaa Allah U inspire me fatan nasara agareki
ReplyDeleteMaa Shaa Allah
ReplyDeleteMasha Allah Allah ya cika maki burika na alkhiari
ReplyDelete