Pages

Wednesday 15 August 2018

Page 50, of SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫
       By Ganarious
Page50

√...Assalamu alaikum ya yan'uwa.
Makarantan soyayyar mu,ina me roko da neman afuwa akan rashin typing. A gaskiya nima ba na jin dadin,yanda nake releasing pages., ma'ana idan na saki  wannan page, yakan dauki lokaci kafin na sake saki..
Nasani, nasani, na san dacewan hakan be dace ba,please kuyi hakuri,ku kuma yi min uzuri🙏🏼
Da yaddan Allah,zani yi adjusting.
       Na gode.!
√...ku bini a 👉🏼 ganarious.blogspot.com/ domin samun latest.

        **          **          **
Tana cikin kallonsa, ya da'go suka hada ido.
Kau da kai tayi tare da cigabawa da tafiyar ta me daukewa jama'a hankali.
  Matattala da ya dace ta bi, ba tanan ta bi ba,kuma tana sane ta bi daban wanda zai sa'da ta Ameer din.
Tana isa dai-dai gabansa ,ta take masa kafa, ba tare da ta dubi fuskar sa ba.
Ta tsallake shi zuwa gun da aka tanada don zaman yin wa'azin ta zauna.
Tunatarwa me ratsa jiki ilham ta gabatar.
Ita din ce ta rufe taro da addu'a, bayan da ta gama wa'azin,sa'anan dalibai suka soma watsewa.

    Ameerah ta bukaci masu mUkami, ciki har da ilham su tsaya,don wasu shawarwari da zasu yi bayan taron. Don haka Naziha da su Amarah, sun nemi guri suka zauna don jiran yar'uwarsu.
   Ameer ne tare da abokan tafiyarsa,suka fito daga dakin taron, nan ya dakatar dasu yana fadin "kai, ku tsaya"
Tsayawa sukayi, suna dubansa.... Ameer ya sa hannunsa ya rikewa daya daga cikin su hannu..."ku zo mu tafi karkashin bishiyan can"
"wai shin me zamuyi a can din" daya daga cikin abokansa ke neman sani.
Bai amsa ba har sai da suka isa gurin, suka zauna a kujeru da ke karkashin bishiyan
"kar ku damu,ku dan jira na dan lokaci,da abinda nake sonyi ne.

Sun kai kimamin minti goma a gurin. Yayinda shi Ameer din ke tsaye rike da kugunsa yana safa da marwa.

 Yana tsaka da haka ya hangi wasu dalibai mata sun fito daga dakin taron...tabbas sune wadannda yake jira,sabida yanayin da ya nufe su ya tabbbatar da haka.su kuwa, abokan tafiyansa suka bi sa da kallo.

 Tafiya suke suna firan su cikin anashuwa, ba tare da ji alaman takun mutum a bayansu ba...
Ji kawai tayi an rikomata kafada,hadi da janyota da karfi, kafin duk ta kai dubanta ga wanda ya janyo ta,sai kawai ta ji ta wuuf....a kasa, yasa kafa ya kwasheta.
Cikin rudewa su Naziha suka durkusa,domin kamota.shi kuwa ameer din sai neman hanyar kai mata naushi yake.
Abokansa ne suka karaso gurin a guje suna ririkeshi.....'Are crazy? U most be outta of your mind" shine abinda abokansa suke fadi, a yayinda suke kokarin tafiya dashi.
Kokari kawai takeyi, ta gan cewan ta tuge Nikab din da ke laulaye a kanta, a yayinda su Naziha sun taimaka mata  ta mike..
Tana yin nasarar cire Nikab din,ta fizgi hannunta cikin zafin nama, takalmin kafarta ta cire ta bi bayan Ameer da abokansa.
Kafin duk su Naziha su rike ta,ta ruga a guje ta isa garesu, tana kaiwa gurin su suka juyo gabaki dayansu, nan ta kwadawa Ameer din takalminta me tsini a goshinsa.

  Ya salam..! Shine abinda ya fada,tare da dafe gurin da hannunsa.
Su ko abokansa sai innalillah....suke furtawa
Nan suka rike shi,yana janye hannunsa jini ya soma malalowa kamar an bude fanfo.
Kokari suke su zaunar dashi, don yi masa first aid, amman kamar an soka masa tsinke ya zabura, yanufi inda su ilham ke kokarin kwantawa ilham da hankali, ita kuwa tana fisge fisge.
Ganin haka yasa abokansa ririke shi suna ba shi baki, amman inna idonsa ya rufe.....'no,! Ku barni kawai, wallahi sai na kashe ta yau' kawai yake furtawa..
  Guri ya soma cika da masu wucewa,kowa ya zo wucewa yagan diramar da akai, sai ya tsaya.
Ilham kam ido ya rufe,bata ji bata gani, nan ta haukace masu kamar me jinnu akai, sabida sai da ta ture su naziha ga baki dayansu ,ta cire dayan takalminta ta nufe su a guje.
Abokan Ameer na ganin haka, wasun su suka rike ta,amman sai da ta jefa takalmin, cikin rashin sa'a bai takalmin be sami Ameer din ba.
     Da kyar, da kyar da gumi dalibai sukayi nasaran kashe  wannan wutar fa'dan.
Su Naziha sun rike ta zuwa hanyar hostel,ba takalmi ba bu hijabi sai sumbatu takeyi.
Shi kuwa Ameer, yana tare da abokansa suna bashi hakuri,sai yayi fito masu baro baro da cewan shi fa bai hakura ba, sai ya koyawa yarinyar nan darasi a wannan makarantan.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.