Pages

Thursday 9 August 2018

KAZA MA CE MATA TA page9

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
*KAZAMA CE MATA TA*
           πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
Written by *Ganarious*
Page9

√...Makarantan SOYAYYAR MU one love.

√... *Anty ubaida* wannan page din naki neπŸ’

√...mss-ganarious, a instagram.
√...ganarious98@gmail.com
√...Ganarious book series, group din mu ta facebook.

       **        **        **
  Tsaye yayi na dan lokaci yana dubanta, hade kuma da jin haushin kansa, na rashin yi mata tayi, tun kamin ya fita daga kitchen din.
  "dauko plate ki biyo ni"...shine abinda ya fada tare da daukan fork ya fice.
Dan karamin plate ta dauka,ta bi bayansa.
Tana isa gunsa tayi tsaye, shi ko ya mika mata hannu ba tare da ya dube ta ba.
Ta mika masa plate din, ya raba abincin gida biyu ya zuba mata a plate.
"zauna ki ci anan" ya fada a yayinda take shirin komawa kitchen bayan ya mika mata plate din.
Ta jawo kujera ta zauna ta soma cin abinci,shi ma din abincin yake ci cikin natsuwa.
Itace ta fara mikewa,sa'anan shima ya bi bayanta.
Ya wanke plate din da ya ci abinci da tukunyar,sa'anan ya goge saman inda ya dafa abincin....binsa take da kallo tana fadin  *iya yi  dai,ace duk abinda mutum yayi amfani da,sai ya wanke anan ta ke?tabijam! Ni kam dai.....

A kwana a tashi..... Suwaiba ta cike watanni takwas a gidan engr. Munir.
Sai dai kuma ba abinda ya sauya daga cikin halayenta na kazanta da ko'na kula.

    Kamar yanda engr. Munir ya fada mata da ta dunga yin abincin ta ita kadai, shi yana nasa..haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a tsakaninsu.
Aikace aikacen gida kuwa, kamar share share da goge goge shi ta sakar ma wa. Sashenta ne kawai baya gyarawa.

    Zaune suke shi da amininsa Sa'ad.
Sa'ad ya dubi abokin sa yace "da alama kana cikin damuwa,har ka rame fa.!
Siririya tsuki engr. Munir yayi tare da fadin ai dole na yi rama...wallahi bani ko son na wayi gari mu hada ido da ita.
Sanin abinda ke faruwa ya sa sa'ad dafan kafadarsa yace ''why not ka kara aure toh''
Wallahi nayi tunanin haka,matsalan shine bani da ra'ayin mata biyu ko fiye da haka.
Toh yanzun miye mafita?
Kawai sakinta zani yi idan har zan sake aure.
Nop....ba ka yi haka ba.....
Ai dole hakan ce mafita,idan ma banyi hakan ba ina kake tunanin zani saka matar da zan aura? Ko ka manta yanda tsarin gida na yake ne?
...ganin hankalinsa na neman gushewa sabida bacin rai,yasa sa'ad ya shiga kwantar masa da hankali, da haka har sukayi sallama ya nufi gida.

   Daga wajen gidansa yake jin hayaniya,sai mamaki yake 'anya daga gidana ne kuwa?'  don haka ya nufi hanyar sada shi da cikin gidan a hanzarce.
Baje suke,su da ya'yan su, a yayinda wasu kwance saman kujerun wasu zazzaune saman kafet,ya'yan nasu ma wasu tsatsaye sukayi saman kujerun suna tsalle, suna guje guje.
Da sallamar sa ya shigo..nan wasun su suka shiga gyara zama,ana rufe jiki.
"sannunku dai""...engr. munir ya fada a yayinda yake kara kallon yanda suka maida masa falo.
Nan suka wage baki gaba dayansu, suna amsa masa Gaisuwan.
Bayan yan gaishe gaishen, ya nufi sashen sa.
Zama yayi saman gadonsa tare da da'fe goshinsa. Ya kai kimamin minti goma sha shidda a zaune, sa'anan ya mike ya shiga bayinsa.
Jim kadan ya fito ya sanya kayansa marar nauyi, sa'anan ya nufi kitchen.
Ganin yanda suwaiba ta bar masa kitchen kaca-kaca, alhalin ya tsabtace shi kafin ya tafi gurin aiki.
Ransa ya baci sosai, ji yake kamar ya tafi falon ya riko mata kune yana ja,har sai sun iso kitchen din.
Tsuki yayi,yashiga gyaran kitchen din...bayan ya maida komai inda ya dace,sai ya daura ruwa dai-dai wanda zai dafa masa kus-kus dai dai cikin sa.
Nan yayi tsaye yana me jiran kus-kus din har sai da ta dahu.
Yana cikin zubawa a plate suwaiba ta shigo.
"sannu da aiki."  ta fada.
Kallo ma ,bata ishe shi ba, ballantana ya amsa mata gaisuwan.
"daman kai suke ta jira fa tun  da'zun"
Nan ya da'go yanai mata kallon kasa-kasa 'su wa kenan?
Yan'uwana mana.!
Ni suke jira?
Eh....sun zo neman taimako ne.suna cikin mawuyacin hali na yunwa ga shi azumi ya zo, shinnasa suka garzayo nan...

Minana.!.....wata murya suka jiyo
A lokaci daya engr. Munir har suwaiban suka juya bakin kofa.
Inno ce tsaye..fuskan nan a murtuke,ko da me karatu zai dube ta a lokacin sai hanjin cikinsa ya ka'da
Nan ta karaso cikin kitchen din, inda engr. Munir da matarsa suwaiba suke tsaye.
Sannu da zuwa inno...fadin engr.
Ba tare da ta amsa masa ba, ta dubi suwaiba. "mi kunne na ke ji? Ya taimaka wa yan uwanki? Ci da sha,da dawainiyarsu kike son daura masa? Toh ba zai yiyu ba. Kuma ki saurara ki ji'yah.! Ke ce dai kinka zama tilas ya ciyar,don haka kar ki fara ki da'ura masa wani nauyi...inno na kaiwa nan ta harari suwaiba, tare da nunin kofa da hannunta "je ki ma'zah ki watse su,su koma inda sunka hito"
Cikn bacin rai suwaiba ta raba gefen inno, ta turo baki ba tare da tayi magana ba.
Sha sha sha kawai ta fada a  yayinda take duban engr. Munir, nan ta shiga yarfa masa nasa masifan " kai kuma.! Kar ka sake ka yarda su maida ka wawa.,kana ji ko?
Kai ya da'ga mata.!
Da gunguni suwaiba ta shiga falon,idanun ta sunyi jajir.
"lafiya dai"....sun fada.
Ku tashi ku tafi, umurni ce daga uwar miji na.
Toh..!
Kar ku damu,inn'shaa'Allah zan biyo ku.
Nan suka mike ko waccensu ta shiga hada tarkacen ta.
Inno ce ta shigon falon ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana me duban su kasa-kasa, ba tare da ta tamka masu ba, su din ma haka.
Hakanan kuma da zasu tafi, basuyi mata sallama ba,ce cewa suwaiba kawai sukayi" toh muntafi" nan tayi masu rakiya .
Rai bace ta shigo falon, bayan da tayi masu rakiya,kai tsaye hanyar dakin ta ta nufa.
Keh....zo nan.!
Da kamar ba za ta je kiran innon ba, sai kuma ta nufi inda take zaune, a dai dai lokacin engr. Munir ya fito daga inda yake la'be yana kallon duk abinda ke faruwa.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.