Pages

Thursday 16 August 2018

Page 51 of SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫
      By Ganarious.
Page5⃣1⃣

          **      **      **
 Kwance ya ke, a yayinda idonsa na rufe kamar me bacci,sai dai da ka gan yanayin kwanciyarsa,zata san cewan ba ba bacci yake yi ba.
Bayan abokansa sun lallashe shi,su ka koma hostel.da isar su suka hada masa ruwa me dumi-dumi domin yayi wanka.bayan ya fito wankan suka cire ankachif da suka daura masa akai, tare da laulaya masa bandeji akai....idan ka ci abinci yanzun sai mu tafi clinic ko?..fadin daya daga cikin abokansa yusuf.
Ba tare da ya amsa Ba,ya haye saman gadonsa tare da rintsa idon sa.
Ababen da suka faru a tsakaninsa da wannan yarinyar da alokacin ma be san sunarta ba su ka dunga dawo masa,kamar yanzun suka faru. "wannan wace irin  shaidaniya ce, tun tasowa ta sa'insa bai ta'ba shiga tsakani na da wani ko wata ba, ballanta wai muyi fa'da,amman yarinyar nan sai da ta kaini karshe..musamman ma abinda tayi min ayau,wanda shike xani iya cewa tozarci,kai.....kai....kai....dole nayi wani abu akanta,sai na koya mata darasi.." duk a zuciya yake wannan  sumbatun...ya cigaba da shawara da zuciyarsa,nan yusuf ya katse masa zancen zucin da fadin "tashi ka ci abinci mu tafi clinic"
Sai da sukayi da gaske sa'anan ya tashi ya ci abinci,amman fa bayan ya gama ci yace shi fa wallahi ba zai tafi clinic ba, ganin yayi rantsuwa yasa suka fita harkansa.

   Bangaresu ilham kuwa, babu yanda Naziha bata yi da ita ba akan tayi wanka,ko kallo basu isheta ba, ballantana ta sauraresu...safa da marwa kawai takeyi tana sumbatu,ganin bata da niyar sauraronsu,suka nemi guri tareda da zaunawa suna bin ta da ido..a yayinda suke mamakin ilham,wace basu san haka ta ke da taurin zuciya ba, sai yau.
Kiran sallah yasa suka rike mata hannu zuwa masallaci, nan dai kam bata mu'sa ba.bayan sun dawo da'ga masallacin Yusra ta shiga rokon ilham, sai da kyar sa'anan ta shiga wankan,abinci kam ta ki ci,iya naci kam sunyi, akan sai ta ci abinci.
    Bayan sallan magriba, sun dawo da'ga masallaci ta kwanta tare da rufe idanunta, hakan yasa su Naziha sun nufi dakunansu.
Bata jima da kwantawa ba, wayarta ta shiga ruri.
A hankali ta bude idanunta tare da kai hannu ta dauki wayar, tana ganin sunar me kiran,tayi tsuki tare da kashe wayar ta mayar ta ajiye.
   Washegari,bayan sun kammala shirinsu,su ka jero zuwa cikin makaranta.
Dalibai maza da mata, sai kallonsu suke,wasun ma harda nunin su da yatsa..."Turawa fa ba isashen hankali ne da su ba" fadin Amarah.
"wai don sabida abinda ya faru jiya?
"eh...shine suke mana wannan kallon"
Uhmmm....kallo kam yanzun zasu fara shi....fadin ilham.
Da haka sukayi firan su,har suka kai gurin rAbuwa, ko wace ta kama hanyarta.

Ilham bata fi minti goma sha bakwai da shiga hall ba, wata lecturer ta shigo ajin tana tambayar waye "Aisha B.Mustapha"?
Ilham ta mike tare da da'gin hannunta..."here i am ma"
Come with me kawai matar ta fada ta juya ta fice daga hall din.
Ilham biye take da wannan matan har izuwa Admin, inda office din manya-manyan lecturers suke.
A hanyar da zai sada su da office din wani babban malami suka hade da abokin fadanta watau Ameer.
Nan zuciyar ilham ta soma tafarfasa...ji take kamar ta shako masa wuya.
  A tare suka shiga fallon office din,inda matar da umurci ilham ta zauna,ta kuma umurci sekatariyar da ke zaune a gun, da ta shiga office ta sanar wa lecturer daliban sun isa, tana kaiwa nan ta yi tafiyar ta.
Daga ilham sai abokin fadan ta suka rage a gurin,  a yayinda sekatariya ta shige office din ogan ta.
Jim kadan ta fito tana dubansu, tare da fadin "ku taso"
Ilham ce ta fara mike wa,A yayinda Ameer yake biye da ita, suka bi bayan matar zuwa cikin office.
They are here sir" sekatariyan ta fada bayan da sun shiga office din Dr.Abdul'Afeez M.D
Dr. Abdul'Afeez M.D, bayarabe ne da'ga kasar Nigeria, Babban lecturer ne kuma Shine displinary leader ta makarantan. ma'ana, shi ne me kula da tarbiya dalibai.
 Bayan sekatariyarsa ta sanar masa isowar su ilham, ya da'ga mata hannu ba tare da ya da'go ya dube ta ba....don haka ta fita daga office din tareda rufe kofa.

Tsaye suke a gaban teburinsa,suna duban sa, a yayinda yake ta rubuce rubucensa ba tare da ya da'go ya dube su ba.
Kamar wasa har su ilham sun cike awa daya tsaye,wannan bawan Allah be  da'go ya dube su ba,sai rubuce rubuce yake abin sa.
Ranta ya soma baci, sai zancen zuci take tana fadin "ai wannan ma wulakanci ne"
Ga kuma kafar ta dake yi mata ciwo.
Sai da suka cike awa daya da rabi, sa'anan mutumin nan ya ajiye bironsa tare da'gowa ya dube su.
Duban su yakeyi dayan bayan daya. "gida daya kuka fito? Shine abinda ya fito bakin sa.
Kai kawai ta girgiza, a yayinda shi Ameer din yace "No sir"
Amman kun hada dangantaka ko?
Nan ma yace "no sir"
Anyway.....nasan kun san ko ni wane ko?
Yes sir suka hada baki.
Naji labarin kunyi physical fight, haka ne?
No sir, suka sake fadi?
Toh yaya abin yake? Ku nake sauraro.
Shiru sukayi,sa'anan daga baya shi Ameer din ya soma bayani.
Bayan ya gama nasa, ya bukaci ilham tayi bayani itama .
Nan ta fada masa abinda ya shiga tsakaninsu,tun farkon haduwarsu.
"shiru yayi na dan lokaci sa'anan ya soma jawabi.
"A gaskiya, bayan da na samu labari, niyata na kori ko su waye,sai dai banyi zaton kune  ba...
Kai kai Abubakar Hisham Dahiru,dalibi neda wannan makaranta ke alfahari da,a ko da yaushe muna son ka zama abun koyi ga sauran dalibai, wannan abin da kayi yana iya bata maka suna.
Ke kuma...ya fada a yayinda yake dubanta yana nuna ta da yatsan sa.
Aisha wa ake kiranki?
Aisha Mustapha sir.
Ok, Aisha Mustapha.  100level ko?
Yes sir ta fada.
Shin kina da labarin yanda makarantar nan ke alfahari da wannan kuwa? Ya maida kallonsa ga Ameer yana dubansa
Kai ta girgiza tareda fadin " No sir"
Toh tun tarihin wannan makarantan ba'a taba samu ko yin dalibi kamar sa ba, sai ke da muke sa ran zaki mamaye gurbinsa....sabida haka makaranta ke alfahari da ku, domin kuwa kun zamar taurari, haka yasa da na gan ku naji cewan bazan iya zarce hukuncin da nayi  niya akan ku...don haka ina baku hakuri da ku yafewa juna, ku kuma rike junanku hannu bibbiyu, duk da kunce ba gida daya kuka fito ba,amman ai kasa daya kuka fito?kai suka daga.
Nan yayi masa nasihohi, daga karshe ya gargade su da kar su sake ya ji wani abu makamacin haka.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.