Pages

Friday 16 February 2018

KAZAMA CE MATA TA5

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
*KAZAMA CE MATA TA*
           ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
Written by GANARIOUS.
Page5

√•Awwwww๐Ÿ˜˜✌๐Ÿผ,mutan *Kenya* one love keep us 2geda.

åina maku fatan alkhairi masoyana,na Gode sosai da addu'oin ku.

√•feedback,& suggestions din ku r higly welcome a  ๐Ÿ‘‰๐Ÿผ ganarious.blogspot.com/ ,thanks

åmarubuciya *A'ishah zahraadeen*,Allah shi Kara basira.

        **          **         **
   Washegari,bayan ya dawo da'ga masallaci ,dakinsa ya nufa tare da samun guri ya natsu.
Hisnul-muslim dinsa ya dauko ya shiga karantawa.....bayan ya ga'ma azkhar din ya dauki al'qur'ni me girma tareda budo suratu yasin,dukhan,rahman,waki'ah da suratu mulk..al'adar sace karanta wadannan surorin kullum safe.
Hannayensa ya da'ga yana me kwararo addu'oi,sannan ya shafa tare da mike wa.
    Ya isa gun wardrob dinsa ya fiddo riga marar hannu da waando 3quater.
Bayan ya sa kayan ya fito daga dakinsa..kitchen ya fara zuwa da niyar daukan tsintsiya.ya ci karo da kwalayen su kuloli,plates da dai sauran su..da suka zubda a nan bayan sunyi mata jere.
Ya tattara su ya kwashe su zuwa bola,ya dawo kitchen din ya share tare da goge inda ke da bukatan a goge.
Yana ga'mawa da kitchen din,ya nufi filin gudansa domin kuwa yan kawa amarya sunyi masa datti da gida,na ledar biskit nan ledan pure water da sauran su.
Gaba daya zagayen gidan sai da ya share shi.

Engr. Munir mutun ne me tsaftan gaske,ko wasa baya son datti, ba kuma yayi shiri da me kazanta,duk wanda ya sanshi ya sanshi da tsafta,hakan yasa abokansa dayayi karatu da su atare sukayi masa lakani da mr. Clean.

Bayan ya gama sharan filin gidan ya nufi falonsa,ya yi shara sa'anan ya shiga goge goge...da shike ra'bin falonsa duk gilashi ne,duk wani abun ado na falonsa gilashi ne,hakan yasa kullum safe kafin ya  tafi office sai yayi goge goge tukun.

Yana tsaka da goge gogensa yaji kamar motsin tafiya,da sauri ya waiga.
Suwaiba ce....kayan jiyan shine a jikinta har yanzun.,ga alama tashiwarta kenan da'ga bacci.

Kwan lahiyaa....tace dashi,a yayinda take murza ido.
Lafiya lau ya gajiya?
Gajiya kam ya bi jiki.......goge gogena kakai da sahiyan nan?....ta tanbaya da alaman mamakinsa.
     Shiru yayi na dan lokaci,sa'anan ya ce "al'ada ta ce kullum safe na goge gidan.!

Tabdi....ai kam an gaji...ta fadi haka a yayinda take shirin juyawa zata koma sashenta.."nikam nayi ciki zuwa yin sallah"
Subhanalillah...ido waje yace taho nan niyanga,shin wace sallan zaki na yi?
Sallan sahe mana..
Duban agogo yayi,10:09am...ya nuna agogonda yatsan sa "dubi"....karfe goma har da yan mintuna kike fadin zakiyi sallan asubahi?
Tau mi??....ta maida masa
Girgixa kai yayi tare da shan mur..."haka kukeyi a gidanku?
shiru tayi bata amsa ba ganin yanda ya murtuke fuska ya ba'ta tsoro

" toh wallahi ba zani daukan maki wannan a gida na ba...sam,ya fada yana yarfa hannu.
Karki manta kin dawo karkashina,don haka duk abinda na saki ya zaman maki dole kiyi shi.
Yin sallah a cikin lokAci yana daya daga cikin dokan da zani shinfida maki,sabida tarbiyan da nake son bawa gida na kenan...don haka da'ga yau kar ki sake
A sanyaye tace "tau,ba zani sake ba, kuma kayi hakuri".
Nayi...ya fada a dakile,da'ga idan zaki kwanta ki kwanta da niyar tashi yin salkan asubahi...infact ni da kaina zani dunga ta'da ke
Tau.....ta sake fadi.
Ma'za jeki kiyi sallan.

10:30am isa ya iso gidan engr. Munir da kula me dauke da wainar masa...inno ce ta aiko shi.
Engr.munir bayan ya gama aikinsa yayi wanka,tare da feshe jikinsa da ture me kamshin gaske.
     Lekawa yayi falin suwaiba,ba ta gurin don haka ya dakinta.
Sallamarsa ya sa ta da'go kai daga kwancen.
Kallonta yake cikin mamaki..."miyasa bakiyi wanka ba?"ya fada cikin da'ga murya
Kalonsa take yi bata amsa ba.
"Baki ji nane?....
Ta mike"yanzun da man nake da niyar yin wankan.
"Ina jiran ki a falo,idan kin fito wanka  ki xo mu ci abinci.

Baifi minti shida da zamansa ba sai ga'ta tafito.
kai ya daga ya na me duban ta cikin takaici,wai amarya kenan fa,fisabilillah,ki irin kamshi da amare keyi bata yi..siririn tsuki ya yi ba tare da taji ba.
abincinsa ya zuba ya turama mata kulan.
Har yayi nisa da ci,ba ta dibi abincin a plate dinta ba.
ya dube ta yace "ki zuba abincin mana,yanda zaki iya ci.
Plate ta dauka ta zuba abincin ta fara ci.
dubanta yake ....sam sam wannan ba ajina bace,yanda nake komai cikin class,ita ko wannan bata dashi ko kadan...wannan ba irin matar da nake son nake kasancewa da ita har tsawon rayuwa ta bane....a duk lokacin da zamu hadu sai rai na ya bacci..haka zamuyi rayuwar auren....duk a zuci ya ke wannan zancen....tsuki ya sake yi wanan karon kam a fili yayishi.
Kai ta dago tareda fadin lafiya dai?
daure fuska yayi ba tare da ya amsa ta ba.

Tana gama cin abincin ta mike zata kwashi plates zuwa cikin..
"Zauna muyi wata magana"....ya fada fuskan nan ba sassauci.
Tau...ta fada tareda koma wa ta zauna.

kina son aminci a zaman auren mu?
Eh...walle ina so.
Hakan zai samu ne idan har kin saureri ni kuma kinyi amfani da duk wani abu da zani fada maki.
akwai ababen da bana so,meyinsa ma bana sonsa balle na shirya da shi.
๐Ÿ‘€kallonsa kawai take,tana me sauraronsa.
Abu na farko,shine me wasa da ibada kamar yanda kikayi da'zun,ina fatan baza ki sake ba,idan har hakan ya faru gaskiya bazaki kwashi me sauki ba.
Sa'anan abu na biyu,ni mutun ne me tsafta,duk me kazanta bana shiri da shi....da fatan zaki kiyaye hakan,
Kai kawai ta da'ga masa.
Shiru yayi na dan lokaci,ya dube ta yace ababenda nake ki' suna ds yawa amman idan kin kiyaye wadannan biyun sauran basu da matsa.
kin fahimce ni ko.?
Eh ....ta fada cikin sanyi murya.

ABIncin rana da ta dare duk inno ce ta aiko masu.
Bayan sallan isha'i engr. Munir ya nufi gidansu inno,yayi mata godiya tare da sanar da ita zancen tafiyar sa zuwa potakot gobe....addu a tayi masa.
Kudi ya ciro ya mika mata"gashi,koda suwaiba zata bukaci wani abu,duk da ba dadewa zaniyi ba.
cikin wage baki tace tau tau madalla....inno abinso ya samu.
Bayan ya dawo yake sanar wa suwaiba ,dubu goma ya bata yace ko da zata bukaci wani abu bayan tafiyarsa,sa'anan idan dubu goman be isheta ba,ta iske inno,idan ma wata matsala ce ta iske inno.
Washe gari yazo sashenta yi mata ssllama,yauma kwance ya tarar da ita,ya girgiza kai tare da kuntsa kansa cikin dakin.
"Kayan tea  na kitchen na sayo,ki hada tea ki sha,ni kam na tafi.
ta mike tare da yimasa a dawo lafiya..
Tir da wannan irin matar,ko irin rakiyan nan babu...ya fada a ransa.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.