Pages

Saturday 13 January 2018

Page 24.OF SOYAYYARMU👫

SOYAYYAR MU👫.
      By A'isha M. Gana
            (Ganarious)
2⃣4⃣
Kai da komowa nake a falon,komai ya tsaya min na rasa daga inda zani fara.
Mafarkin danayi kuwa sai yawo yake yi a kwakwalwata.
11:59pm dai-dai fillo ya shigo gida.
Ina ganinsa na nufeshi ina tambayar sa ko lafiya?
Ya dube ni kamar me son tuna wani abu,ya kaiwa goshinsa mari tare da fadin oops.
A tare muka zauna ,na kara tambayansa ya'ya kuka yi da mahaifin Hajiya zubaida?
Bai dubi inda nake ba ya amsa da fadin "ya bani aiki ne"
Aiki?.na fada ina me mamaki,sannan na ciga ba da fadin daman kana neman aiki shine baka fada min ba!.
Shiru yayi bai amsani ba,ya dai tsirawa kasan kafet ido.
Na cigaba da fadin "ka rasa gun wanda zaka nemi aiki sai a gun mahaifin Hajiya zubaida?
Sai a sannan ya juyo ya dubeni tare da fadin "miye aibunsa toh...haka kawai ki tsani mutanen da basu ma san dake ba!..minene don ya bani aiki!..
Yana kaiwa nan ya mike zuwa daki.
Mamaki ce ta hanani da'gawa da gun,tunda mukayi aure da fillo magana me dadi ce a tsakaninmu.
...a lokacin da na ankara na bi sa zuwa daki,na tarar baccinsa yayi nisa.

Daga wannan ranan na dinga fuskantan rashin kula daga fillo.sam bashi da lokaci na da na yara.
Ga rashin zaman gida,ya daina hira dani...idan ya dawo aiki sai ya shige daki yayi baccin sa.
Ba tambayar duniyar nan da banyi masa ba akan ko nayi masa laifi ne..
Sai yace ba komai,a duk lokacin da zani tambayeshi.
nace masa ya shirya muje ya sanar da iyayena aikin da ya samu,yace min ba yanzun ba!
Cikin kankanuwa lokaci na fita hayaci na,na rame na lallace.daman kuma bani iya shiga damuwa ba.
tun ina kukan har na daina yi.
Abinda ya daure min kai shine sauyawan samarin gidan, kusan duka samarin gidan sun chanza halayensu,kiyayya da bansan daga inda ta samo asaliba suke min..ba kamar Yusuf da salisu(Lamido karami)..da zaran sun hange ni,ko muka hadu sai su sha mur su daure fuska.
Yau fillo na nan,gobe baya nan.jibi ya tafi wannan,ga'ta yana wancan kasan.

Kwance nake ina fama da rashin karfin jiki,asalima da zarar na tashi,jiri nake gani..
Yayi sallama ya shigo,daga kwancen nayi masa sannun da dawowa ya amsa ba tare da ya dubi inda nake kwance ba,ya sa kai ya shige daki a hanzarce.
Bai fi kamar minti goma sha biyar da shigansa ba, ya fito.
Ya chanza kayan jikin sa, sai kamshi ke tashi,alaman ya sakeyin wanka kenan.
ya yi hanyar fita sai kuma ya dan dawo baya,amman duk da hakan yan nisa dani sai ji nayi"tafiyata kamani zuwa kasar croatia" sai na dawo.
yana fadin haka ya ficewarsa.
Nan da nan naji kamar zuciyata zata fashe,sai hawaye suka biyo baya.

Binta ce meyimin komai tun bayan tafiyar sa.
ba yanda batayi ba wai muje asibiti,na ki yarda sabida bani son naje su ce damuwa ce.
Kwanansa hudu ya dawo.
Kwance ya tarar dani, ya sami kujeran da kegefe na ya zauna.
na mike daga kwancen na zauna ina me kallonsa..."sannu da dawowa baban ilham"
Sai a lokacin ya dubi inda nake "yauwa sannunki"ya fada.
Na tsira masa ido...ina me mamakin sauyawan fillo cikin kalilan lokaci.
...na sanya dan yatsa na share hawayen da ke shirin zubowa.
..na daure nace masa "wai don Allah na tambayeka mana!
Ya juyo yana me kallona ba tare da yace komai ba.
Wai me ke faruwane Baban ilham?
Kamar me fa?..shima yayi min tambaya maimakon amsa...sai kawai naji raina ya sosu.
kana nufin kace baka da masaniyar me nake nufi da tambayar?..nayi maganan ne a fusace.
Kai ya girgiza.
Na yi shiru na dan lokaci kamar bazani sake magana ba,sai kuma nace "fillo ya sauya"..kai ma kasan da haka! Ka chanza gabaki dayan ka...kamar ba kai ba.
Na kasa amincewa cewan kaine..don Allah ka fadamin laifin da nayi maka da har ya shafi yara na.
Tunda na fara magana har na kai karshe idonsa na kaina... sai kallona yakeyi....can,yace ni fa yanda nake haka nake har izuwa yanzun...
Zai sake magana wayarsa ta shuga ruri..yan dauka yayi hanyar waje.
Ban gan fillo ba sai karfe goma sha biyun dare.
Kashe gari da sassafe ya hada kaya a karamar jaka wai tafiya ta kama shi.
Nan na sashi gaba ina me yi masa kuka irin me taba zuciya.
"Kiyi hankuri maman ilham,idan na dawo zamuyi magana.
Ya na kaiwa nan ya fice abinsa.
nayi kuka kamar ba gobe ,abin bakin ciki shine yaransa da baya damuwa da su.ko tambayarsu baya yi.

Kashe gari na tashi da masifar ciwon kai,ga kasan marata da ta addabeni,ba abinda nake tunani sai mutuwa,don ganin nake zan mutu.
Ban bata lokaci ba na shirya,na nufi sashen Binta na kwashi yara muka tafi gidan mu.

Babana ne zaune cikin abokansa a gun da aka kebe don hutawa.
Yana gan shigowarmu,ina ganinss naji kamar na koma sabida banyi zaton yana gurin ba....sai kame kame nakeyi,shi kuwa tunda muka budo kofa idonsa  ke kanmu..
..ya mike ya nufo mu.
Kallo daya yayi mi yace subhanalillah!
Aisha ke ce?
Murmushin karfin hali nayi,nace nice Baba.
Yace lafiyarki?
Na sakeyin murmushi nace masa lafiya lau Baba,na dan yi zazzabi ne kwanar nan,amma alhamdulillah sauki ya samu.
Baba na bai sake bin takan abokansa ba,sai ya bi mu cikin gida.
Muna isa hanyar da ta raba tsakanin sashen hajiya da ta mamata,muka tarar da su zaune,da shike gurin akwai rumfan kara da kujeru.
Hajiya ce ta fara ganinmu ta taso a hazarce,ta taremu tare day rikemin hannu tana fadin..."lafiyarki kuwa? Tana meyimin kallon mamaki.
..lafiya lau hajiya,dan rashin lafiya dai nayi,amma alhamdulillah.
Tace oh oh...yar'nan,cikin ne ke wahalar dake haka!..duk kamaninki ya canza.
Sashenta ta kaimu,bayan mun gaisa da Mamata.

Abinci me yawa ta dibo ta ajiye a gabana.....murya a sanyaye nace 'hajiya bana iya cin abinci ai.'
Shi yasa kikayi wannan rama tunda baki cin abinci.
Babana da ya kafa min ido tunda muka zauna,ya matso kusa dani...
Cikin laLlashi yace ki ci abinci mana mamana...
..tauww Baba,nace dashi
Madallah.....ki ci ina kallonki.
Na tursasa kaina cin abincin,ina me kokarin boye hawayen da ke makale a idanuwata.

Ina gama cin abincin,na mimmike a gurin,sai bacci..
Na dade ban sami irin baccin ranar ba..
Sai washe gari na koma sashen mamata
Ina zaune falonta tashigo tare da samun guri ta zauna.
.."ashe mijinki ya sami aiki?
Ras-ras naji kirji na nayi...dajin tambayar nan nata.
Eh mama...ya so ya zo ya fadamaku,amman tunda ya sami aikin bashi samun zama.
Tohh Allah ya sanya alkhairi
Ameen ameen na amsa ta.

A rana ta uku,kwance nake a falon mamata,ta gyara min gashin kaina,ta shafesu da mayyuka masu gyaran gashin.su ilham kuwa suna sashen Hajiya babba...wayata ce naji taa ruri, ganin me kiran yasanyani yin murmushi da tsintan kaina cikin annashuwa.
Ina da'ga wayan muka gaisa,murta can ciki-ciki daga alama ba lafiya, hakan yasa na nemi sani..."safiya da wata matsalan ne?

Hmmmm...ai ki tambayi kanki,haba Aishah!..yaushe zakidauke ni yar'uwa?,ni wallahi ba abokiya na daukeki ba,ji nake kamar ciki daya muka fito.
Dariya nayi sosai,sa'anan nace tohh Hajiya safiya!..yau kuma laifin me nayi?
cikin fusata tace ba maganar waya bace,da ta waya ce,da ba zani baro abuja zuwa kaduna ba..mussam don ke na shigo gari,don haka kina gida yanxun?
Eh bana nan,amma kina iya samu na a gudan Babana.
Toh shikenan.gani nan zuwa.
Cikin farin ciki nace safiya kenan.
Ba'a dauki tsawon lokaci ba kuwa ta iso da ledojin su biscuits da chaculates ta kawo wa yara.
Ta shiga dakin mama ta tarar bata ciki,sai ta nufi kitchen,a nan suka hadu suka gaisa.
Ta dawo falo inda nake,fuska a daure ta sha mur...hakan yasa na fashe da dariya.
Guri ta samu ta zauna tana kallona tace"nasan hakan zai faru ai..dube ki? Dube ki don Allah A'isha.
Ta ta'be baki..tana me huci
kiyi hankuri nasan bana kyautawa..amman yanzun dai ki fadamin wata irin katuwar laifi nayi maki ya tasoki daga abuja.
Ta harareni,tace kina nufin baki san laifinki ba.?
Kai na da'ga mata kawai...nace sai kin fada.
Ashe mijinki zai kara aure shine baki sanar da ni ba,kina nan kina shanye bakin cikin ke kadai ko?..ko ba komai,zani baki magana ta kwantar da hankali.
..nifa har yanzun ban gane inda maganarku ta dosa ba.
ta sa hannu cikin jakkarta ta fito da katin gayyata tare da miko min...tace'duba ki gani,wannan ba katin gayyatar auren mijinki bane.
Ina karban katin idona ya kai gun sunar hajiya zubaidah,sai na kuma daga farkon rubutun.
Tabbas sunar fillo ne....da karfi nace innalillahi'wa'ina ilaihirraji'un.
Mamata dake bakin kofa tana sauraron duk wani abu da muke fadi,rike take da tiren kayan marmari da kofuna akan tiren da alama safiyace zata kawowa..
Ihun yasata sakin tire..
ITA kuwa safiya rude wa tayi,ta mike tsaye da rasa abinyi.

Tunda nayi wanan ihun,ban sake fadin wani abu ba.sai da'fe kirji nayi.
Mamata ba ta damu da kwalaben da suka fashe a gabanta ba,ta tsalake su ta yo kaina,ta dafa kaina tsna me kallona cikin rudani domin kuwa ta rasa abinyi ko fadi,ta cire hannun da na dafe kirjina dashi ta sanya a nata.
Shiru shiru ....sai ta fara kiran suna na a hankali.
Ban amsa ba,ban kuma kalli inda take Ba,domin kuwa ban san inda hankalina yake ba ...
Ganin haka yasa ta mike da sauri tayi hanyar waje,a hanya sukai karo da Babana zai shigo.
Lafiya?..yace da ita ganin yanayinta.
Ba ta amsa shi ba tayi masa nuni da yatsa tare da rikeshi zuwa falon.
A hanzarce ya karaso yana fadin subhannalillah,me ye sameta?
...ya tattabani,ya girgiza ni,shi din ma rasa yaya zsi faro yayi..ya dubi safiya miye same ta?.
cikin rudewa da in-inniya tace ni wallahi bani da masaniyar cewan bata san da maganar ba.
Ya kara duban ta da kyau yace maganar me?
katin kawai ta mika masa,ba tare da tace wani abu ba.
Duk da yanayin da nake ciki,ssi da na gan tashin hankali a idon Babana..idanuwansa su ka'da sunyi jajir.
Dirshan ya zauna,ya dade bai cire idonsa daga katin ba...mamatace tayi karfin hali ta shiga yimasa bambami..,sai a sa'anan na fara kuka me ban tausayi.
Gaba dayansu suka shiga lallashi.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.