Pages

Friday 21 July 2017

SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫..
  By Ganarious.(Al-Ansar writters)
4⃣
Na jima zaune ina jinjina wannan Al'amarin..har na matsu na ji wannan labarin.
    A GIDAN BABA YUSUF.! Hisham ya tarar da baba Lamido bayan ya gaishe su cikin girmamawa,Baba Lamido yayi mashi nuni da gefe kusa dasu wai ya zauna.
 Ya batun tafiyarka ta zuwa yin aikin umurah ? Baba lamido ke tambayar Hisham.
Yau ne tafiyan inn shaa Allah.
Toh madallah..Allah yasa aje a sa'a ya kuma karbi ibadun.
  "Amin baba"
Dalilin kiranka shine ni da sauran yan'uwa mun yanke shawaran hada ka aure da hindo yar gidan gwaggo kulu...ita ma yar uwarka ce don haka ka bar zance waccen Ilham din tunda uwarta taki bamu hadin kai.
 Cikin wani yanayin tashin hankali Hisham ya dubi Baba Lamido yace... A... Gaskiya baba bani iya auren wata mace idan ba ilham,kuyi hankuri ku canza shawara don Allah.
  Haba wa...ai nan da nan baba Lamido ya shiga balbalo mashi masifa,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba...Aurenka hindo kamar anyi angama don haka ka dawo da shiri...tashi ka bamu guri.
Cikin sanyi jiki Hisham mike tare da yi masu sallama,Baba yusuf ne ya amsa mashi tare fadin a dawo lafiya.
Garden ya nufa ya zauna a daya daga cikin kujerun ya zauna yana me jinjina maganar Baba lamido.ya kai kimamin minti Arbain da uku sa'anan yayi tsuki ya fiddo wayarsa don kiran Abokansa watau KAREEM da kASEEm....bugu biyu zuwa uku kacal  yaji andauka..
Dude yane ?
Me kuke nufi !. Yafa kamata ina Airport yanzun
Kwantar da hankalinka...Gamu nan tafe...zamu zo maka da wata labari mai dadi.
Ba ruwana da wani labarinku nidai kuzo ku kai airport
Bayan ya kashe wayar yashiga duba sakonin da suka shigo,nan ya ci karo da message din ilham...gaban shi na bugun uku-uku ya bude.
 "YAUSHE ZAKA DAWO ? "abinda ya gani kenan...mamaki kawai yakai ya tasan zaiyi tafiya ? Sai kuma ya tuno yafada mata zaije kasa me tsarki donyi masu addu'a...yana cikin tunani wayarshi tayi ringing,yana picking yaji ance fito muna waje.yana fita ya nufi gurinda suka yi parking mota ya bude gidan baya ya shige.ba tare da sunyi mashi magana ba kareem ya ta'da mota sai hanyar airport.
sai bayan tafiya tayi nisa sukajiyo Hisham na tanbayar wata labari kuke dashi ?

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.