Pages

Saturday, 13 January 2018

20-23 COMPLETE OF SOYAYYARMU

[: SOYAYYAR MU👫.
  By A'ishah M.Gana
         (Ganarious)
2⃣0⃣

  Na cigaba da zama a gidan mu sabida jikina ya ki komawa dai-dai..yau lafiya,gobe ba lafiya.
Idan fillo ya zo gari sai ya zo gidan mu ya duba ni.
Sai da cikin ya shiga wata na biyar sa'anan na sami sauki.sabida haka  mamata tace na koma gidan mijina..babana bai ji dadin haka ba.
 Tunda na koma gida fillo ya maida kaduna da zaria kamar daga nan zuwa can. Kullum sai ya tafi ya dawo,idan kuwa jikina baiyi min dadi ba,toh fa ba zai tafi makaranta ba ko da kuwa na matsa mashi akan ya tafi.
Mamata tare da hajiya suke zuwa dubani bayan kwana bibbiyu.shi ko mahaifi na kullum dare sai yazo dubani.
 A koda yaushe Binta da danta suna sashena ,ita keyimin komai daga kan wanke-wanke zuwa su goge goge duk da mamata ta samo min wace zata dunga yin ayyukan.
Hisham yaro ne me kwazo da tausayi,kuliyaumi yana like dani,duk inda na shiga yana biye dani,idan na zauna ya zauna,idan na tashi ya tashi,idan ina a kwance shima zai kwanta....wata sa'in sai yayita matsamin kafafuwana yana ja min yatsunsu.
    Watarana ina zaune na mimike kafafuwana a lokacin cikina ya fara girma ko nace ya girma sabida yana watanin bakwai zuwa takwas,hisham na kwance ya tsiramin ido,nayi masa tambayar duniyar nan" hisham menene?" Menene Hisham?...ko kifta idonsa baiyi ba ya cigaba da kallona.mamarsa kuwa sai dariya takeyi.
Nima sai na sa mashi ido ina kallonsa.
Sai ganinsa mukayi ya mike yazo inda nake zaune ya shafamin ciki sa'anan ya koma ya kwanta ya cigaba da kallona.
Dariya sosai mukayi ni da mamarsa,tun daga wannan lokacin mamarsa takeyi  masa wasa tace matarka tana cikin cikin nan.
 Idan kuwa kana son ganin kukan Hisham ko rigimar sa kace mashi zaka cire matanshi na cikina ka tafi da ita...toh fa kuka zai shiga yi ya kankame ni wai don kar a cire cikin...sai idan nace ba me taba maka mata sanan fa zai yi shiru.
Tunda mutane suka gane  haka,idan dai sun shigo sashen suka iske  Hisham,wasan da suke masa kenan...ko ba komai yanayinsa zai baka dariya.
...shi yasa nace soyayyarku tun ilham bata zo duniya ba aka halicce shi..
 Watarana Buba fillo ya dawo daga makaranta sai ya tarar Hisham na gutsu gutsu da buredi duk yabi ya ba'ta guri..sai ya fara yimasa fada wai ya bari,shi kuwa Hisham din yaki bari a dai dai lokacin ni kuma na fito daga kitchen, fillo na hange na,yayo kaina ya da'gani sama yana fadin tunda ka ki dainawa zan kai ta a cire a cire matarka na kuma yi kyauta da ita.
Bani kadai ba,har shi fillon din sai da ya raza da irin ihun da hisham yayi..ya yi fa da kofin shayi da ke hannusa ya buge tv sai tass..mukaji.
 Da sauri fillo ya ajiye ni,yayi kansa ashe harda fitsari yayi.
Fillo ya fusaka,nan ya fara dukansa....da kyar na kwaceshi.

Cikina na shiga watan haihuwa Babana ya matsawa mamata wai ta dauko ni,ita kuma ta fadawa hajiya.don haka itace tazo ta tafi dani gida.
            **         **           **
Ranar wata juma'a,misalin karfe uku,nayi wanka tare da yin kwalita na tarbon miji na,don nasan ko wace juma'a yake zuwa dubiyata.
KWance  nake a dakina mamata kuwa tana da ba'ki a falonta..cikin baccin da bai kai minti uku zuwa hudu da farayinsa ba naji kamar an sara min baya da gatari.
Ihun sosai nayi...sai ga mamata a rude ta shigo tana fadin lafiya?
cewa nake "wayyo bayana zan mutu."..a ruden take fadin kiyi addu'a innshaa'allah bazaki mutu ba.
Sai a sannan na fara adduoi<Allahumma rahmataka arju fala takilnee illa nafsee tarfata'ain,wa'aslih lii sha'nee kullah la'illah illa ant><Allahumma anta'adudii,wa'anta naseeri bika ajuulu wabika asuulu,wa bika uukaatilii.duk addu'an da tazo bakina alokacin yinta nakeyi.
Mamata ta hanzarta komawa dakinta ta sanya mayafi tare da dauko wasu abubuwan da za'a bukata a asibiti,ta kira daya daga cikin ba'kin ta tana fadin haihuwan ta zo.
     A kofar gida muakayi karo da Babana tare da hajiya sun dawo anguwa.yana ganin an riko ni yayo kai na sai cicciba ta yayi ya sanya ni a motarsa muka nufi asibiti.
 Tun bayan isawar mu asibiti,ban kara sanin abinda ya faru ba sabida nafita hayyaci na.
  Kiran sallah nake ji kamar a mafarki,hakan yasa na bude idanuwana a hankali tare da ambatan salati.
HAJiya babbace na gani kwance kan doguwar kujera,da alama ita ma kiran sallan ce ta ta'da ita.
Kafin na mike ta karaso tana tamabayata "ya'ya"..ya ya kike ji yanzun?
Cikin kokarin mikewan nake fadin inason tuna abinda ya farune.
Ta koma dayan gefe inda  wata karamar gadon jarirai ke ajiye ta sanya hannu ta dauko jaririya dunkule cikin showels.
  Gashi!.tana me mikomin jaririyan tare da fadin Alhamdulillah.Allah ya saukeki lafiya an sami diya mace.
 Na karbi jaririyan tare da tsira mata ido.
Na dade ban cire idona gareta ba kamar me son tunano abu.
Hajiya dai ni take kallo,na dago na kalleta,na maida kallon ga jaririya...na kuma kara kallon hajiya sa'anan nace da hajiya "itace na haifa kuwa?
Murmushi tayi tace mikika gani
Uhmmm...hajiya wannan ai..sai kuma nayi shiru.
Ai me?..inji hajiyan
Shiru nayi ina me kara kallon wannan jaririyat.
...ba'a mamaki da ikon Allah! Tabbas ke ce kika haifeta.
  Tasbihi na soma yi...karo na biyu kenan da nake gani wannan irin kyan haliytan..abin mamakin kuma shine halittan farko da ta biyun akwai kamanni,watau Hisham da ilham.
    Ranar suna kuwa anyi shagulgula dayawa sabida sunar da taci.sunan mahaifiyar Babana muka sanya mata "A'ishatu.
jama'a daga waje da ciki,lungu,sako duk sun zo taron sunan Aishatul-ilham...wasun su sun zo ganin kyan jaririyan ne don gani ya kori ji.

Duk soyayyan day iyayena sukeyimin sun raba shi gida biyu suka baiwa ilham rabi...haka buba fillo,ilham ce kawai ke gabansa.
Bayan wata uku da haihuwan ilham na koma gidana na estate, alokacin ne muka sanya Hisham makaranta
A koda yaushe idan Hisham ya dawo daga makaranta a guje yake shigowa ya zo ya rungumi ilham,idan ma ya tarar tana bacci sai ya ta'da ita,idan ko a bayana take sai dolena na sauke ta sabida ya dinga ja mata kafa kenan.
Hisham baya kaunar wani yazi yace zai fita da ilham,ko da nan da bakin kofa ne.....da rigimarsa sai yace zai dauke ta,daganan sai ka gansu kasa tare.idan ta fara kuka shima fa sai ya tayata.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har na yaye ilham.
Bayan nayaye ta na nemi yardan fillo don nayi makarantan da mamata ta samomin,shima ya ji dadi.
cikin kankanuwa lokaci akayi komai na shiga makaranta,sai shirye shiryen barin kasa.
A gun mamata na bar ilham,na tafi kasar germany don karo basira akan tukin jirgin..da kyar,da yaki na yakinci kaina sa'anan na cire tunani da zancen yar kyakyawan jaririyata da babanta,na sami natsuwa domin yin abinda ya kawo ni.
  BAYAN WATA TAKWAS.
Bayan wata takwas mukayi hutun sati biyu,munyi waya da Babana ta ta offishinsa sabida ba wayar hannun a lokacin.nan na sanar dashi munyi hutu sai yake fadin ko zaki zo ganin takwararki ne.
  Har cikin raina naji dadi kuma na so hakan sai dai kuma daga wanna hutun sai jarabawar gama makarantan.
Na daure nace masa a a sai na gama duka-duka zan dawo.
Yace toh shikenan.
     Saura kwana hudu hutu ya kare,inakwance ina karatu,gefena hoton ilham ne da nake kallo a ko da yaushe...
Karan buga kofa naji,a natse na tashi na sanya doguwar riga da dankwalinta sa'anan na taka zuwa ga kofar na bude.
Direban kamfanin Baba ne na fara gani don shi ne gaba bayansa fillone sa'be da ilham a kafadarsa.nayi tsale na rungumosu mukayi ciki.
Bayan munci abinci,muka shiga fira nan yake shaida min Babana ne yayi masu komai domin su zo su ganni.
Ranar da hutu ya kare suka koma.

Cikin ikon Allah har mun fara jarabawa na barin makarantat,...na bada himma don ganin na zama tauraruwa.
Haka kuwa ya faru domin kuwa nice gaba da kowa daga kasar nigeria..
Taro yayi taro,yan uwa da abokan arziki duk sun zo ciki har da Baba Lamido,binta da danta Hisham.
        **         **         **
Gidan mahaifina na sauka..sai da nayi sati biyu sannan na koma gida.
Tun bayan kammala makaranta ta zaman gida nakeyi.muna haka har ilham ta cika shekaru uku,fillo ko sai dai yazo weekends ganinmu,idan kuma yasamu hutu sai ya dawo.
Mahaifiyata ta fara damuwa da zamar banzan da nakeyi,hakan yasa tayiwa Babana magana da na fara aiki a daya daga cikin airport din kasar mana.
Ya kwantar mata da hankali da fadin aiki kam kamar ta samu.
ba a jima ba kuwa Babana yayi nasarar nema min aiki,sai dai kashh!...gun screening suka gano ina dauke da cikin wata uku,wanda nima din ban san dashi ba.
FIllo yayi murna sosai da ya sami labarin cikin nan.
Ilham na cika shakara hudu,shi kuwa fillo a lokacin za ya shiga ajin karshe a makarantan A.B.U....tunda fillo ya shiga shekarar karshe na lura wasu daga cikin halayyensa na ccanzawa.
 Yana daya daga cikin halinsa,duk weekends sai ya zo dubani da diyata amman sai ya rage zuwa shigar sa ajin karshe.
Da farko ban kawo wa raina komai ba sai nake tunanin watakila yana son bada himma ne yasa kai ga karatun sosai tunda shekarar karshe kenan.
   Ranar wata asabar ina zaune tare da Hisham da ilham suna wasansu,tun da safe nake sa ran ko fillo zai zo sabida sati na hudu kenan bai zo duba mu ba....har bayan sallah la'asar bai zo ba sai kawai naji bacin rai,ba don cikin jikina ya tsufa ba a lokacin,da binsa zanyi ko zan sami natsuwa...na tashi na shirya su Hisham na kwashesu zuwa gidanmu.
  Ko da muka isa gidanmu karfe biyar ta wuce,Mamata tayi mamakin ganin da yammaci tace lafiya!
Nace lafiya lau mama.
Sai bayan magriba Babana ya shigo muka gaisa...bayan gaisuwan yace amman dai nan zaku kwana ko?
Kai na daga mashi..
ashe mamata tana lura dani,tace ai ko baki fadamin zaku kwana ba.
Shiru nayi bance mata komai ba.
Bayan sallah isha'i,tayiwa yara wanka suka kwanta,ta sani gaba tana tambayata lafia kuwa?
Nace mata lau lau mama.
Ta girgiza kai tace ko dai jikin ne?
Nan ma nace mata a'a.
Allah dai ya raba lafiya ta fada.
Daren ranar ban rintsa ba,tunanin fillo kawai nakeyi...kashegari da safe na tashi da ciwon mara amma na daure ban bari mamata ta gane ba,don ina zaton damuwa ce ta kawomin hakan ba haihuwa bace.
Tun ina daurewa har na kasa,a gun da na idar da sallah azahar a nan na durkushe rike da ciki,ina cikin haka binta tayi sallama ta shigo..
Ban amsa mata sabida tsananin ciwon da ya ad'dabe ni,ita kuma da ga shigowarta ta fara fa'da wai na tafi ban sanar da ita ba,kuma ban taba haka ba don haka hankalin kowa a tashe yake shiyasa ta zo nan din don tasan bazan wuce nan din ba...
Tayi ta surutan ta taji shiru ban amsa ba,sai ta karaso inda nake ta leka fuskata sai a lokacin ta fahimci cewan bana hayyacina nan ta yi waje da hanzarinta don kiran mama ta.

Karon dan ba'ki sa samu,sai dai gashin kansa da lebensa abin kallo ne,bani da abincewa sai godiyan Allah...
Sai bayan na haihu da kwana hudu sannan fillo ya zo dubanmu.
Ranar ce ta farko da na canza masa fuska kenan tunda mukayi ban taba fushi da shi ba haka ban taba daure masa fuska ba.sai a ranar.
Kallo daya yayimin ya fahimci cewan ina fushi dashi,sai bayan mutane sun watse sannan ya shigo dakina rike da jaririn yace min ya jiki?.
Ba tare da na dubeshi ba nace Lafiya lau.
Cikin sanyi jikiya tashi ya ajiye jaririn cikin gadon sa sannan ya dawo gefena ya kamo hannuna ya sanya a cikin nasa.
‬: SOYAYYAR MU👫.
     By Ganarious.
2⃣1⃣
Ki yanke min ko wata irin hukunci amma karki yi fushi dani....ni kadai nasan yanda naji a raina ganin ki haka.Don Allah ina rokonki kar ki karayin irin wannan fushin,nasan nayi laifi kuma a shirye nake da na dauki hukuncin da za'ayimin amma ba da wannan ba.
 Ba san sa'anda hawaye ya zubomin ba,ina me kallonsa nace "kafada min dalilinka na rashin zuwa duba mu..kuma yaushe kaji na haihu?
  Ya sa hannunsa ya sharemin hawayen,sannan yace Bani da lafiya ne!.
Nan da nan na rude,na kuma shiga tausaya masa ..ina fadin "ya jikin?
Na ji sauki hamdala...
Nan ta'ke mu manta komai muka shiga hira irin ta masoya masu shaukin juna...sai da yaro ya fara kuka sannan fa muka tuna yana gun,fillo ya taka zuwa gun gadon ya dauko shi.
  Ya dawo gefena yana me kallon jaririn,nikuma ina shafa kansa(shi jaririn).
Yayi murmushi yace tabdijam...wannan d'an kam ba'ki ne,muka tuntsire da dariya sabida yanayin da yayi furucin.
 Ai nice sak...wannan ba'kin nawa ne....sabida haka sai kawai ka sanya masa sunnan baba na.
 Da sauri ya kalle ni,yace kin so kanki da yawa! Duk da nima zan so haka  .
Wannan kam Baban mahaifiyata ne domin kuwa shima din ba'kin buzu ne ,kamar wannan jaririn.
Ahmadu shine sunan da aka sanyawa yaron,sai nake kiransa da MUJAHEED..wannan  jaririn shima akwai shi da shiga rai.
  Wata biyu nayi na koma gida.
Abu kamar wasa tunda muka koma gida fillo bai leko mu ba,har zamu shiga sati na uku..sai nake tunanin wata kila bashi da lafiya ne kuma...
Sabida tunanin haka na shiyar ranar asabar,tare da yin girke-girke don kaimasa.
Hisham da ilham sashen binta na kaisu sannan na nufi zaria.
Gidan da nayi zama alokacin da nake karatu nan yake zaune shima,don haka ban wani yi wahalan neman gida ba.
Na tarar da gidan a rufe,da alama baya nan kenan.
Na dade tsaye ina tunane-tunanen abinyi sai wata zuciyar na rayamin wata kila yana hanyar kadunan....
A zuciya ta nace ko da yana garin ban san lokacin dawowansa ba...ina cikin wannan tunanin mujaheed ya fara motsi,ya tashi daga baccin kenan.
Wai waiga  na gani ko zan sami gun zama,ai ssi nayi ido hudu da fillo cikin mota.
Motan nan tana gun sa'anda na  wuce domin kuwa ta gefen ta na bi amman tunani bai bani da na kalli cikin motan ba balle mutanen cikinsa.
    Wata fara mace ce a gefe,daga alama itace mai motar don zaune take a kujeran direba.
Muna hada ido da naji zuciyata na ras-ras da karfi...
Kallonsa nake shima hakan,sai kuma ya maida kallonsa ga matar suka ci gaba da maganarsu.
  Na da'de ban dauke idona daga gareshi ba,har sai da mujaheed ya fara kuka...
 na rasa mafita gashi ba gun zama,gashi fillo bai zo ya bude mana kofa ba...duk sai na rude cikin kankanin lokaci.
Kuka yake sosai..niko sai girgiza shi nakeyi ba tare da na sa'ko shi daga baya na ba...muna cikin haka fillo ya fito daga motan,ita kuma ta ja motan ta wuce.
Ya karaso inda nake tsaye ya amshi mujaheed ya bude kofa yashiga ciki ya kwantar dashi.
Ya dawo ya kwashi kaya ya shigar.ya sake dawowa har zuwa wannan lokacin tsaye nake bani ko motsawa.
Ya matso gaba na,muna dab da juna domin ina jiyo numfashinsa.
  A hankali yace 'mu shiga ciki ko!.
Nan ma ban motsa ba,gashi sai ihu mujaheed keyi.
 Ya rikemin hannu ya jani zuwa ciki.
da kansa ya zaunar da ni,ya nufi gun a.c ya kunna sannan ya dawo ya dauki mujaheed yana lallashi,duk da haka yaro ya kiyin shiru.
Ya dawo gefena yana fadin don Allah ki saurari wannan yaron..
Ko kallonsa banyi ba balle na amsa shi. Shi ke kidansa,shi ke kuma rawansa...
...sai da maganar sa ta isheni na na mike a hasale,na fizgi mujaheed ina kokarin goya shi.
Shima ya mike cikin mamaki,yana kokarin rike ni,na fizge hannuna.ya sake kamo hannuna  yace don Allah kiyi hankuri kiyi min magana...
Kuka irin ta ban tausayin nan ce ta ci karfi na ...sai kawai naji ina tausawa kaina.
Da dabaransa ya samu ya zaunar dani.mujaheed kam yayi kuka har ya hakura.
ya sani ga'ba ya kallon ina kuka har sai da nayi me  isa ta.
Sai da kukan ya lafa sannan yace "haba Aisha"....nasan dai kishi ne,amman a duniya kinsan bani da kamar ki kuma ba kuma zan sami  kamar ki ba..a tunani na kin fi kowa sanin abinda zan iya yi,da wanda bazan iya ba.
Yayi shiru na dan lokaci,ni ma din har zuwa lokacin ban kalli inda yake ba balle na amsa shi.
ya kamo hannun na ya matsa yatsu ...kar ki sawa ranki komai wallahi ba abinda ke tsakani na da ita.
Wannan baiwar Allah da kika ganni cikin motanta,yar ajinmu ce tare muke karatu.
Ta zo ne domin mu nemi mafita kan wata matsala da nashiga..wallahi taimako na take son yi.
..cikin dishewar murya nace "taimako?
Giransa ya da'ga tare da fadin eh.

Bana son ki tada hankalinki shiyasa ban sanar dake matsalan danake ciki ba!
Ya cire idonsa daga kallon da yake min sannan yace "na sami matsala a makaranta semestan can har hukuman makaranta na shawaran kora ta daga makaranta.
Cikin gwalalo ido nace "garin yaya?

Cikin sanyi da taushin murya yace labarin na da  tsawo,amman zan dan takaita maki yanda zaki fahimce ni.
Wasu mata ne suka kullamin shairi a lokacin ana jarabawa,da sanin wasu mallamai,da kuma hadin kansu.
Wadannan matan,matan banza ne.tun a shekarar farko suke nema na  da harkan banza duk da wasu tsakanin su da Allah suke sona,sai dai basu sami hadin kai daga gu na ba...sunyi iya yinsu,ko wacen tayi kokarin ganin ta karkato hankalina gareta,amma sam na ki.
Akwai wata a cikinsu da take min son gaskiya,na sanar da ita ni mai mata ne,bana kuma ra'ayin yin mata fiye da daya,..ashe ita wannan din akwai daya daga cikin mallamai dake nemanta ,ita kuma bata son sa,asali ma bata bashi fuska wai duk a dalilina...a dalilin haka mallamin ya sanya min ido na neman abinda zanyi ya gasa ni.
Wata matan auren kuma ta sanya ni gaba,ala dole sai na so ta,nan ma ba amince ba...sabida ni wannan baiwan Allah take barazanar kashe aurenta.
Ire-iren matan nan ne suka sanya ni gaba,har sun sa nayi suna malamai kuma na takaici na.
Rashin amince masu ya sanya su son ganin na wulakanta.
   Muna jarabawa wancan semestan da ya kare,kwatsam sai na gan an gefe ni da wata takardan da ta fada a dai dai kafa ta...idan ba hadin baki ba,suna wurgo takarda wani malami ya iso gaba sai ya sa hannu ya dauki takardan ya bude ba tare da ya karanta ya gan me ke ciki ba ya jawo hankalin sauran mallaman wai su zo ya kama wani na satan amsa.
Lecturori kuwa sun taru akai na suka ta'da ni tsaye tare da amsan takardata,kowa sai fadin albarkacin bakinsa yakai,nayi masu bayani,nayi ranstuwa sun ki yarda..don haka aka yo waje dani za'a kaini babban offish.
Sun sa ni gaba muka fito daga ajin jarabawa,nan muka hadu da wani mallami,shi wannan malamin yana bani girma sosai a duk cikin dalibansa,ya tambaya abinda ke faruwa aka sanar da shi.nan yace su bashi takarda ta da nake rubuta amsoshi aciki,da takardan da nake satan amsa da shi.
An mika masa,nan ya shiga dubawa,bayan ya gama dubawa yace amma ai abinda ke takardan satar amsan da na takardan amsoshin sa basu ko bi hanya daya ba ma'ana ba wani abu da yayi shige balle suce na saci amsa...ganin ya fara walwale masu shiri ya sanya suka daure fuska,tare da fadin ai dai an kama shi da takardan don haka bashi da wata mafita,sai abinda hukuman makaranta ta yanke masa.
  Bayan wannan jarabawa,wasu daga cikin dalibai suka yi zanga zanga zuwa offishin da ke kula da jarabawan dalibai,suna fadin baza mu yarda ba!!! Kullin shair akayi masu!!.
Baza mu yarda ba idan har ba'a bashi hakin sa ba.
Da haka suka jawo hankalin manya manya mallamai,don haka sukayi shawaran su zauna akan batu na.
NI kuwa a lokacin ina cikin mawuyaci hali,ke kadai ke raina,ke kadai nake son gani,ke kadai ce nake son fadawa banyi satan amsa ba! Amma kuma me!..na tsincin kaina da rashin son fadamaki don zaki ta'da hankalinki. Ba kuma zan so ace Babanki yaji wannan zancen ba.
Wannan matan da kika ganin ita ce kan ga'ba don ganin an bani hakkina.
BAYan malamai sun taru,sukayi kirana,da wannan matan aka zauna meeting,daga karshe suka yanke shawaran cewan na sake maimaita wannan shekaran,ma'ana an maida ni baya.
Fillo na kaiwa nan ya saki wata irin numfashi mai zafi,..tare da fadin ban so kin san da zancen ba,Allah kuma ya kaddara zaki sani.
 Nayi ajiyar zuciya nace masa ai da ka fadawa babana da yasan abinyu...ya sa yatsansa kan lebe na alamar nayi shiru.
Don Allah wannan zance karki fadawa baba kinji.
Na turo mashi hannu tare da bata fuska nace ....amma ai ko wata irin hali kake ciki,bai kamata kayi mana abinda kayi a yau din nan ba..iyalanka su zamana sune gaba da komai...a gaskiya naji zafin wulakancin da kayi mana a yau.
YA kara sanya tafin hannunsa ya toshe min baki.
Tsakani na da ke ba wulakanci,don Allah kar ki kara fadin haka,yana soke min zuciya ta.
...eh mana dole na kirashi wulakanci,kana fa kallon giftawan mu ai da sai ka zo ka bude mana kofa idan yaso sai ka koma ku cigaba da tattaunawan..
ya kara matsemin baki..na ji nayi laifi,kiyi hankuri maman ilham.
na harareshi sannan nace kar a sake.
Bayan nan sai sai hira,muka manta da komai.

      ***        ***        ***
SUna cikin jarabawa makarantarsu ta shiga yajin aiki,don haka ya dawo gida....
Akoda yaushe muna cikin farin ciki da annashuwa.
a shekaran,wayar hannu watau handset ta fito.Babana ya saya mana ni da fillo ya kuma chanza min mota,shima fillo an saya ma sa.
Bazani manta ba ranar wata asabar fillo ya kwashe mu zuwa gurin shakatawa ni da kyawawan yarana.
MUna gurin ilham ta sa rigima wai ya kaisu su hau doki,dole ya kwashe su zuwa gun.
ni dai ina zaune ban ce uffan ba.a gefe na wasu mata ne zaune,tun isowar mu suke ta kallonmu da alama maganar mu sukeyi...
SUna ganin fillo ya kwashi yara ya bar gun suka taso zuwa inda nake.bayan gaisuwa suke tambayata miye alakarmu da fillo.
Cikin murmushi I nace masu ni matarsa ce.
daya daga cikin su ta girgiza kai,dayan kuma tace Allah dai shi baku zaman lafiya....amman fa sai kinyi hanakuri.
cikin yanayin rashin fahimtar me take nufi da fadin haka nace "kamar ya fa?
Sai dayan da bata ce komai ba tunda suka iso tace ciwon ya'mace,na ya'mace ne..agaskiya baza mu boye maki ba,wasu matan za su iyayin komai domin ganin sun mallakeshi,a yanda mukaji magana na yawo,akwai wata da wai ta kai sunansa gun boka.Allahu'a'alam..allah masani.
shi wannan mijin naki ba course daya mukeyi ba,amma gaba daya makarantan nan an sandashi sabida yanda mata ke fada akansa..
anyi lokacin da wasu mata sukai dambe akansa suka yagewa junansu kaya a tsakiyan makaranta...sun bani labarai da dama,daga baya sukai min nasihohi sannan mukayi sallama.
A gaskiya maganarsu ta sosa min zuciya,sai kawai naji ina tausayawa kaina.....ina cikin haka fallo ya dawo,ya dagwara ilham a wuyarsa,sai ya riko hannun Hisham
Ya na isowa mujaheed ya fara mimmika hannuwansa ma'ana a dauke shi shima...ya dauke shi sukayi ta wasan su,suna wasa fillo ya na sstan kallona yagan alaman akwai abinda ke damuwata...ya ajiye mujaheed ya dawo gefe na yace "ya'ya dai?
Na kirkiro murmushi tare da fadin "dai-dai.
haka muka nufi gidan duk jikina ya mutu,sabida  maganar matan nan.


Yajin aiki ya kare,makaranta tayi kiransu.
Ranar da za shi koma yana shirya kayansa,ni kuma inakwance sai binsa nake da ido,abubuwa dayawa suke min yawo a kwakwalwa..yana gama hada kayan ya hauro saman gadon inda nake kwance ya rungumeni..
ya ya dai maman ilham,me kike tunani?...na yi laifi ne da ba a tayani shirya kaya ba?.
     Ajiyan zuciya nayi nace ma sa..ji nake kawai kamar kar ka koma.
dariya sosai yayi yace maimakon kiyimin murna yajin ya zo karshe!.idan fa matsalarnan ta warwaru zan gama kenan.
hmmmm....
kiyi magana mana bana son ganinki haka.
Na shagwabe masa tare da cewa "ni dai bana son yan matan makarantan nan su kwace min kai..
dariya ya sakeyi tare jamin hanci yace ..ke kadai ce har duniya ta kare.
Allah ya sa! Nace da shi.
innsha'Allah wannan alkawari ce,don haka ki sawa ranki sanyi.
ya mike yace bara nayi wanka ko?
gira kawai na daga mashi.
Ya fito wanka ya same ni a inda ya barni,ya shafe jikinsa mai me suna venus sa'anan ya dauki brosh ya gyara suman kansa sukayi luf-luf kamar ta larabawa..kananan kaya ya dauko yasa.ya feshe jikinsa da turare me sanyi...duk ina nan inata binsa da ido..
yana sa agogonsa ya juyo ya daga mn gira....
haba....ai nan da naji wata irin kishi ta motsomin.
Dole mata suyi fada akansa,fillo ya goge,ya zama classic,wanda ya tashi a kasar  turai ma ba xai nuna masa iya sa kaya ba..fatar sa ta kara kyau da walkiya..
ina cikin zancen zuci ya zo dai dai kunne na tare da yimin ra'da.."wannan kwaliyan naki ne,yayi maki kuwa?
ban amsa masa ba sai hararansa da nayi.
     YA dauki jakkarsa ya miko min hannu wai na tashi muje sashen Goggoji(mamarsa kenan) zai sallameta.
Nan ma ban mike ba,ya sake magana.
ya ajiye jakkat ya dawo gefena yace Don allah kiyi hankuri ki fadamin abinda ke damuwanki.
kallonsa kawai nake yi.ya dawo gaba na ya rusuna yace gani a risune don Allah ki fadamin.
hawaye naji sun cikamin ido,nace zuciyata na bani zan rasa ka.
come on! Ki daina fadin haka.na fada maki cewan ke kadai ce....da haka dai yayita lallashina.
tare muka shiga sashen Goggoji daga nan muka nufi sashensu baba Lamido,a can din na tarar da Binta dasu Hisham..
fillo ya dauki mujaheed yana masa wasa daganan muka fito zuwa gun motansa don dashi zai tafi makarantan.
‬: SOYAYYAR MU👫.
         By Ganarious
2⃣2⃣
Bayan komawansa mukan yi waya sau biyar zuwa shida a rana.ki ni na kirashi,ko shi ya kirani.
Ko wace ranan juma'a kuwa yana gida,lahadi ya koma.
Wataran ina zaune ina zaune sai tunane tunane nakeyi,sai kawai naji ina sha'awan koyarwa watau na zama lecturar..nan da nan na yake fadawa mamata,na dauki waya nakirata bayan mun gaisa nake sanar da ita batun koyarwan...
Tace ai baki da kwalifications na koyarwa,don haka idan har kina son din ba makawa sai kin koma makaranta fannin education da kuma koyarwa.
nace toh mama!..zan koma don yin karatun.
Tace shikenan.amman kiyi shawara da mijin naki.
         **        **      **
Bayan dan lokaci fillo ya sake halin rashin dawowa,gashi wata sa'in bana samun wayarsa,..hankalina ya fara tashi,ba shiri na nufi zaria.
Na tarat ba ya gida sai kawai zuciyata ta bani da na tafi makaratan,kai tsaye na nufi makarantan da shike nasan department dinsu,tambaya daya nayi cikin sa'a aka cemin yana gun cin abinci...
Bayan sunyi kwatance na nufi gurin,ganin motarsa a filin gurin ya tabbatar min yana ciki,don haka na sami kwarin gwiwan shiga nan.
Na shiga gurin ina dan dube-dube ko zani gan sa,sai kuwa na ganshi yana shan drinks tare da matar nan.
Na karasa gurin nayi masu sallama,ya amsa yana murmushi,ita kuwa sai kallona takeyi.
fillo ya mike ya jawomin kujera tare da umurta ta da na zauna.bayan na zauna ya nufi gurin masu abinci don sanar da su abincin da za su karo.
Bayan mikewan fillo ta kalleni muka hada ido,tattausan murmushi nayi mata,domin taimakon da takeyiwa mijina,ba ta mayar min da murmushin ba,ila daure fuskarta ta juya gefe.
Fillo da kansa ya karbo min abinci,ya ajiye a gabana tare da fadin bisimillah!.
Yana zama yace mata ga matata! Sunanta Aishah.
Ya juyo gu na yacemaman ilham ga Hajiya zubaida,itace wadda nake baki labari.
Na sake murmusawa nace ai na ganeta...
Inawuni...na ce da ita.
Tace.." lafiya"
Tana fadin haka ta mike,tace wa fillo zata tafi,idan sun kara haduwa sai su tattauna zancen.
Shikenan,na gode yace da ita.
Tana wucewa yace ki ci abinci mana.
Na harare shi,nace duk hankalina ya bi ya tashi..
Ya fahimci abinda nake nufi da fadin haka.yace oh....kiyi hankuri maman ilham wayarce nake ganin ta daburcemin.
Na kara hararansa nace "wai sai dole dole matan nan ce zata iya taimakon ka.! Ni fa a gaskiya batayimin ba,kuma hankalina bai kwanta da ita ba.
Eh toh...taimakon ne zai fi sauki daga gunta..kannen babanta da shi baban na ta sune kan gaba a harkan ilimin,nan makarantan ma ita yar gata ce.hakan yasa wasu lecturorin suna shakkanta.
Hmmm....na ji,amma ai da mun sanar da Babana  shima din zai samo maka mafita mai sauki.
Ya sanya yatsan sa kan le'bensa,alamar nayi shiru.
   Bana son Baba ya ji wannan mumunan zancen,don Allah kar yi masa wannan zancen koda da wasa ne.
 Ba yanda baiyi ba akan naci abinci amman naki ci,haka muka bar abincin muka nufi gida.
  Da taimakon Allah,da taimakon hajiya zubaida makaranta ta yafewa fillo.don haka baza shi sake maimaita shekaran ba.
Sunayin hutu ya dawo gida.daga wannan hutun ida ya koma zai gama kenan.
Tunda ya dawo,hajiya zubaida ta kan kirashi so uku zuwa hudu a rana,abin ban haushi har cikin dare ta kan kirashi.
Abin kan daure min kai har na kaiga yiwa fillo magana.."wai ita wannan matan me take so da kai"...har cikin dare fa take kiranka kuma tasan kana da mata"
SHiru yayi,bai ce komai ba.
Daman taimakon ka take sonyi,kuma tayi...miye rage kuma?
   Bayan an kwana biyu sai ta tsagaita kiransa,daga alama yayi mata magana.
Sai dai kuma me!..idan fillo ya fita masallaci sallah,sai ya dauki lokaci bai shigo ba,har sai na kirashi.
.....ranar muna zaune falo,ilham ta dauki wayan fillo tana wasa dashi,nan mujaheed ya sa rigima wai sai ta bashi,tana mika masa ya saka wayan a kofin shayin da ke gabansa..daga nan wayan bata sake kawowa ba.
kashe gari da yammaci ibrahim kanin fillo yayi sallama yashigo wai ana neman fillo a waje.
Ba nemi sanin ko waye ba ne,shi kuma ya mike ya canza kaya ya fita.
Tun abin karfe biyar har bayan isha'i ba fillo ba alamunsa.
Boys kwatas na nufa duk da nisan ta daga gida na,ga tsoro ina ji.amma ba yanda zani yi sabida inason ganin ibrahim.
Kwankwasa daya nayi ya bude kofar.
Bayan mun gaisa nace mashi "ko kasa waye yazo gun buba fillo da'zun?
A'a bansanta ba!
Ido waje nace mace ce?
Eh mace ce.tace min tana kiran wayarsa bata shiga.
Raina kawai yabani hajiya Zubaida ce,ita kadai ce macen da ke kiransa a waya.
 Cikin baccin rai na koma sashena,ina shiga fillo ya shigo.
Ba tare da nace masa komai ba,na shig jera masa abinci sa  a dinning table.bayan na gama na koma kan kujeran falo na zauna.
yana zaune a dinning chairs ya kai kamar minti hudu bai gan alaman zan taso ba..yayi kirana wai na taso
Na amsa shi  da ni na koshi.
Ya maida marfin kulan ya rufe sannan ya taso zuwa inda nake.
Ya dan risuno,fuskarsa na gab da nawa,ya tsiramin idanuwansa...kiyi hankuri ki tashi muje mu ci abinci..
Na hasal nace mashi bani ci ko dole ne?
   Mamaki a fuskar fillo,shiru yayi yana me kara duba na.
Ni ma din ban ji dadin yi masa haka,ranar ce farko  da hakan ta faru a zamantakewan auren mu.
Ba tare da na kalleshi ba na mike na shige ciki.
Ina daki ya shigo...al'adansa akoda yaushe shine ya rike min yatsu..idan dai muna zaune toh hannuna na cikin nasa.
Bayan ya shigo ya kamamin yatsu kamar dai kullum.
Kiyi hankuri maman iilham..kamata yayi idan nayi maki laifi ki dunga fadamin,ba kiyi fushi ki barni a duhu ba.
A sanyaye nace "kayi hankuri baccin rai ne yasa nayi maka magana haka,amma innshaa'allah haka ba zata sake faruwa ba.
Na hakura.yanzun ki fadamin miye saki bacin ran.
na kalleshi nace kana nufin baka sani ba?
Wallahi ban sani ba maman ilham.
Waye yayi sallama da kai dazun?
Tambayar ta soke masa zuciya,don na karanci haka a fuskarsa.
Ya daure ya dube ni yace yanzun na fahimci cewan babban laifi nayi...
Kiyi hankuri..hajiya Zubaida ce tazo dubani.
Duban ka fa?na fadi hakan tare da sa masa ido.
Eh... wai tana kiran wayata kwana biyu bata shiga,shine ta zo dubawa ko lafiya...na sanar ita wayan ta sami matsala,shine fa ta dauke muka nufi inda ake saida waya ta saya min sabuwar wayan.
bayan mu fito tace muje gidansu na gaida mahaifin ta,don ya da'de yana son ganina.
Zai cigaba da bayani na da'ga masa hannu ma'ana ya isa hakan...hawaye n bin juna,na sanya hannu na goge nace"tunani na a fara tabbata.
Ya matso kusa dani tare da matseni a jikinsa...tunanin me?
Da daureren murya nace zata kwacemin kai.
yayi murmushi me dauke  sauti yace maman ilham kenan...na fadamaki ba sau daya ba,ba sau biyu da ki sawa ranki ke kadai ce...kisani fa bani da kamar ki a duniya,idan aka cire iyayena....hakan dai yayi ta kwantar min da hankali d kalamansa masu dadi,da kuma kara shaida min irin son da yake min.

Mamee tayi shiru na dan lokaci tare dayin murmushi...tace bayan munyi haka dashi,sai kuma ya dauko dabi'an fita kullum dare.kafin hutunsa ya kare.
   Bayan hutunsa ya kare,ya koma makaranta da sati daya kenan sai zazzabi ya rufeni,inakwance su hisham sun isheni da hayaniya haka yasani yi masu dubaran cewa su tafi su kiramin goggo binta(maman hisham).hisham ya rike dayan hannun mujaheed,yacewa ilham ita ta rike dayan hannun suka fita.
Sun fita ba da jimawa ba suka shigo tare da binta biye dasu da sauran yaranta.
cikin farinciki binta ta shigo ba tare da mun gaisa ba tafara fadin"ashe mutanen kirki suna dayawa a duniyan ba laifi."
Binta kawai nake da ido.
ta ci gaba da fadin yau fa kawai muna zaman zamanmu Allah ya jeho mana mutuniyar kirki wai ita hajiya Zubaida.
Cikin zafin nama na mike tare da da'fe kirji ina fadin wa?
Ta fashe da dariya tace hajiya zubaid.
Na gyara zama nace mitazoyi a gidan nan.
Nan binta ta sami guri ta zauna dashike bata zauna ba tunda suka shigo duk sabida murna.
Bayan ta zauna tace wai marantarsu daya da buba,shine ta zo su gaisa da yan uwansa...ta kuwa abinda tsaraba masu yawa.ciki harda turamen zannuwa,sabulai da dai suransu.ta kuma yi rabon kudi.
samarin gidan nan marasa aikinyi kuma tayi masu alkawari sama masu aiki.
    Nima kingan abin arzikin da na samu shine nace bara nazo na nun mak,sai gashi na hade da yaran wai kina kira na.
 Binta ta kwance gefen zaninta ta ciro kudin da bansan ko nawa bane.
nan ta'ke na kar jin zazzabin,wat irin yanayin da bata misaltuwa na dunga ji..jiri da ciwon kai lokaci guda suka sauka min...na rike gishi na ina fadin 'waashh' washh..binta taimaka ki kira ibrahim ya kaini asibiti.
‬: SOYAYYARMU👫.
        By Ganarious.
2⃣3⃣
A asibiti ko,kwantar dani sukayi.
Mamata da Babana suna isowa suka nemi likita,bayan sun ga'na suka nemi sannin abinda ka damuna.
Ya fada masu wani abu bane ila cikin jikina dake barazanar zubewa sakamakon damuwa da nake ciki.
"Damuwa!..kamar ance masu get set ready go,don a tare suka furta haka.
Likita yace Eh...tana sanyawa kanta damuwa da yawa.
Bayan sun baro gun likita,gu na suka nufo...
A sanyaye Babana yace Aishata me ke faruwa?
Cikin yanayi rashin fahimtar maganarsa nace baba ban gane ba.
Likita yace kina dauke da ciki,kuma cikin na barazanar zubewa sabida kina cikin damuwa.
Nayi murmushin karfin hali nace bana cikin ko wata Damuwa Baba!
Ya girgiza kai yace ban yarda ba,sai kin fadamin abinda ke damunki,yau din nan a yanzun kuma....ko mijinki ne?
Na girgiza kai nace a'a Baba.
Toh me ke saki damuwa?
Baba bana cikin damuwa..likitan fa ma bai san aikin sa.
Shiru yayi yana kallona,daga baya yace nine fa Babanki me sonki,...don Allah ki fada min abinda ke damunki.
Baba nace maka ba komai wallahi.
Karya kikeyi....mamata cr ta fadi hakan daga inda take tsaye tunda suka shigo bata ce komai ba sai kallonmu da takeyi.
Wallahi mama ku yarda dani bana cikin damuwa...kawai dai tunani na bai wuci  zancen komawa ta makaranta danyi maki ba...kuma naji ki shiru,baki ce komai ba sai ina tunanin bakiyi marhaba da maganar bane.
Babana yayi ajiyan zuci yace kin tabbatar shi kawai kike tunani?
Kai na gyada masa.
Yace mamarki ta yi marhaban da zancenki,kin ji ta shiru ne sabida ba'a fara saida fom bane.
ruwan da aka sanya min ta drip na karewa suka sallame mu.
A harabar asibitin mukayi karo da fillo.
Bayan sun gaisa da babana yace ma sa yana son ganin sa anjima .
Tunda muka isa gida fillo ya kasa tsaye,ya kasa zaune.sai kai da komowa yakeyi,ni ko banda kallonsa ba abinda nake.
Muna cikin haka binta ta shigo da abinci,mujaheed biye da ita..ai ko a guje ya karaso guna ya hayemin ciki.
Nan fillo ya hanzarta sauke shi tare da yimasa gargadin hawa jikina.
Bayan isha'i fillo ya tafi gidanmu.bansan me suka tattauna a can ba dai.
Zaune ya iskoni,mujaheed na saman kafata yana baccinsa.
Gefena ya zauna yana me kallona...ya jima ya na kallona daga baya yace Aisha!
na kai dubana gareshi.
Don Allah ki fadamin damuwarki mana.
...ya marairace kamar dan shekara bakwai.
Na kauda kai gefe ,xa juyo da fuskata tana fuskantan na sa.
Ni ne fa!...nine fillonki,don Allahi ki tausayawa masoyinki ki fadamashi damuwanki.
Na sanya dan yatsa na share dan guntun hawayen da ke shirin sakkowa,na ce masa ba komai.
Cikin yanayin tausayi yace ban taba zaton zaki iya yimin haka ba..daman akwai abinda zaki  boye min.
..bazani tilasta maki fadin abinda bakiyi niya ba,amman don Allah idan har ina da hannu cikin sanya ki wannan halin,ki yafe min..hawayenki ba za su bari na sami natsuwa ba.
..hakan dai yayita lallashina yana bani magana.
Da safe bayan ya shirya zai tafi makaranta sai naji wani abu ya zokaremin kirji...na so na yimasa zancen hajiya zubaida sai kuma na fasa.
Ni ce na kaishi tasha,sabida a ru'de ya shigo gari da ya sami labarin rashin lafiyata don haka bai zo da motan sa ba.
  Tunda fillo ya tafi bani aiki sai tunanin Hajiya zubaida,na kasa gano manufarta na zuwa rabawa yan'uwan fillo kudi....ina cikin tunaninta binta ta shigo tare da su Hisham...Da shike kullum safe take zuwa daukansu sabida wannan cikin ya xo min da rashin son hayaniya,ko ba don hakan ba ma,nakan so kadaicewa a yan kwanakin..
Tana bude kofa suke xo a guje fada a jikina,da hannu nayi masu alaman kar su zo..mujaheed ne kawai da bai fahimce ni ba ya karason na rungumeshi.
bayan Binta ta sami guri ta zauna take tambayata ya jiki.
NA amsa mata da sauki.
...muna cikin hira nace mata yanzu ku kawai baku san mutum ba,baku san inda ta fito ba ,ta zo ta raba maku kudi kun karba!..har kuna wani jin dadi.
Dariya Binta tayi tace ai tayi mana byanin kanta..
Tace maku me?
Ai na fada maki,idan baki manta ba.
Eh..kin fada min,yanzun ma ki kara fadamin.
Mi tace maku yake tsakaninta da Buba?
Cewa tayi karatu iri daya sukeyi a makaranta.kuma ajinsu daya.
Aww...shikenan abinda tace?
eh...shikenan,aike maman ilham matan nan akwai kirki.ki duba fa wai har ta samawa Yusuf aiki.ta kuma ce duk me bukata ko neman aiki cikin samarin gidan nan ya sanar da ita.don ba basu lamban wayanta.
Na gyada kai ina me jinjina al'amarin.
     **       **         **
Munyi waya da fillo ya ke sanar da ni batun jarawarsu da za su somayi...nayi masa addu'a,mukayi sallama.
farin ciki na shiga yi sabida daga wannan jarabawan ya gama kenan don haka zai dawo kusa dani ya daina ganin wannan hajiya zubaidan.
...na mimike kafafuwana dakyau ina me tunanin hakan,sai wayan hannuna ta fara ruri.
SAFIYA ce!..me kiran,kawata ta tun sakadiri skul.

Ina ganin itace,farin ciki ta da'da shiga ta.kamar tana gun tana ganina.
Muna gama gaisawa ta shigayimin rashin kiranata,hankuri dai na bata kamar kullum.
Sai da hira yayi nisa,sannan take tambaya fillo nace mata yana makaranta.
..tace ko da shike baya gane ni,sau biyu muna haduwa amman bai gane ni ba.
Na tare da fadin kodai ba fillo bane?
tace shi din fa...dan filaninki.
Shiru nayi na dan lokaci sannan nace mata a ina kuka hadu?
tace duk a semina muke haduwa...na farkon a wata semina ne da muka je a abuja,na biyun kuma shima gun semina ne a nan kadunan shekaranjiya....na so nayi masa bayanin kaina,amma mijina bai yarda ba wai tunda bai ganeni ba a je a hakan.
Na kara taran ta da tambaya.... semina??  Seminan me?
Oohh...kina nufin baki san da seminan ko zuwansa gun ba?
nace mata ina ganin ba buba kika gani ba.me kama dashi ne.
Tabbas Buba dan filaninki na gani...tare na gansu da wata anace mata ZUBAIDA.
tabbas dan fillo ne kuwa.
Oh hooo...yanxun kin yarda na san sa ko.
Cikin share hawaye nace  mata eh.haka muka ci gaba da hiran ba tare da na bari ta fahimci halin da na shigaba.
...daga karshe ta dau alkawarin zuwa dubiyata idan ta sake shigowa kaduna.
Kuka me sauti na shiga yi bayan mun gama waya da safiya..tabbas fillo ta gani.
Ashe har fillo zai shigo gari,batare da ya xo ya dubani ko yaransa ba..tuna nin da na shiga yi kenan,ina me tambayar kaina me ke shirin faruwa ne. Gashi bani da wanda zan fadawa ko neman shawara ila iyayena,su din ma nasan abin zai dame su ya kuma takura masu.kuma bazani so hakan ba.
    Daga karshe hankuri na baiwa kaina ina meyin addu'an Allah shi kare ni da makircin Hajiya Zubaida.
Ranar da fillo gama jarabawa a ranar ya tattara nasa da nasa ya dawo.
Inakwance ,tunaninsa kuwa nakeyi sai gashi ya shigo. Daga kwancen na amsa masa sallamansa  yana shigowa ya ajiye jakarsa ya zo inda nake kwance ya rungumeni yana meyimin sumba.
...maman ilham naji kewarki sosai fa.
Nima cikin murmushi na maida masa tareda fadin na fika jin kewan.
Ya mike yace "Bari na yi wanka"
Har ya shiga cikin daki ya fito yana tambayan ina yara?
Suna sashen binta na ce dashi.
Yayi murmshi yace suna damun ki ko?
Na daga masa kai kawai.
Tunda fillo ya dawo shi yakeyin komai,sabida cikin ya sanya min kasala,abinds nakeyi sai kwanciya..don haka hata abinci shi ke girkawa.
  Hakan yasa baya samun damar fita.kullum yana li'ke da ni.jikin nawa kuwa ya fara dawo wa dai dai ina murmurjewa sabida kwanciyar hankali ma'ana ganin fillo tare dani.
Muna cikin haka,watarana muna zaune yana bani abinci abaki sai wayarsa ta shiga ruri..ya daga ya gan mekiran sai ya ajiye ba tare da ya dauka ba...
Ya cigaba da bani abincin kenan wayar ta sake kara...ya dubi wayan ba tare da ya daga ba....
..na yi saurin hadiye abincin da ke baki na,nace masa ka dauki wayan mana..
Ya kalleni ya girgiza kai tare da turamin abinci a baki..nan wayat ta sake kara,wannan karon ya dauka.
Ban san abinda aka fada masa daga wancan bangaren ba,shi dai naji yana fadin wani lokaci ya ke gida? Bayan gaisuwan kenan.
Bayan nan yace "toh shikenan zan kokarta zuwa innshaa'allah.
Daga nan ya ajiye wayan..idona a kansa,sabida yanda ya sha mur! Kamar kiran na gurin.
yana ajiye wayan ya dibo abinci ya kaimin baki,kafin na hadiye,ya dibo wata yana kokarin turaminshi a bakina sanya hannuna  na ture masa hannunsa.
..ina hadiyewa nace  masa 'waye ke neman ka'
Da kamar bazai amsa ba, sai kuma yace mahaifin Hajiya zubaida ne.
Nan take naji gabana na faduwa,na dafe kirji...
...kallona yake,yace mi ne ne?.
Na dube shi nace "me yake so da kai"
Ya girgiza kai yace sai dai naje na ji.
Abincin ban karasa ci ba kenan..ba yanda baiyi ba don na cinye sauran abincin ,amma ina!

Bayan sallan isha'i fillo ya shirya,nayi masa rakiya zuwa gun kofan falo...a sanyaye na juya zan koma ciki,sai kuma na sake kiransa.
Ya dawo dab dani ya ya sumbaci cikina tare da fadin "ko zaki shirya muje tafi tare?"
Na ce masa a'a,amman dai kayi min alkawarin ba zaka amince da aurenta ba..
Ya fashe da dariya..yace auren wa?
Shiru nayi ina binsa da ido...ni karan kaina ban san dalilin fadin haka ba,sai dai jikina da xuciyata na bani wani abu makamacin haka zai faru.
Ya dade yana dariyan,daga baya ya rikemin hannu muka koma falon.
..zaunar dani yayi sannan shima ya zauna...yana zama ya kara fashewa da dariya,yana me duban fuskata...
Maman ilham kishiii..ina me godiyan Allah da ya bani me sona haka..amma don Allah ki kwantar da hankalinki...inbanda abinki da kira sai a bani mata?.toh albishirinki.alkawarina na nan daram,ke kadai ce har duniya ta nade.
Don haka ki kwantar da hankalinki
Kai na daga masa .
Ya lakata min hanci yana fadin kice wani abu mana.
...hmmm,ni dai gaskiya jikina yana bani wani abu  zai faru,sam sam ban yarda da hajiya zubaidan nan ba.
Ya kalli cikin idona yace "toh shikenan bari na tafi na ji kiran mahaifinta,bayan nan nayi maki alkawari da yardan Allah zan yanke duk wata alaka da ke tsakani na da ita,idan haka zai faranta maki rai.
Nayi masa murmushi nace sai ka dawo..
Ya mike ya tafi.
tunda bayan tafiyansa nake jin faduwan gaba da wata irin yanayi da bazan iya misalta maku ba..tun ina jinsa kadan kadan har soma wuce gona da iri,sai tsoro kuma fara shiga ta...nan na fara addu'a,ina kiran sunayen Allah da cetonsa.
...a nan bacci yayi awon gaba dani,a cikin bacci nayi wata guntun mafarki wai Hajiya zubaida ce rike da hannun fllo tana min dariya tace yanzun dai kam Fillo nawa ne,tana kaiwa nan suka tashi sama suna daga min hannu...ni ko sai ihu nakeyi ina kiran fillo ya dawo gareni don bazani iya rayuwa ba tare da shi ba..nan nayi firgigit na tashi ina me sallati..
NA kai dubata ga agogo karfe goma sha daya da minti bakwai kuma fillo bai dawo ba.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.