Pages

Sunday 14 January 2018

Page25 of SIYAYYARMU.👫

SOYAYYARMU 👫
   By A'isha M.Gana
         (Ganarious)
2⃣5⃣
Assalam...da fatan muna  lafiya ya yan'uwa...ina me bada hankuri akan rashin typing kwana biyu.

👉🏼Ganarious.blogspot.com/ and drop ur comments and opinions,

Safiya bata koma a ranar ba,dolenta ta kwana sabida yanayin da tagan na shiga.
Yanda nagan sa'fiyah,haka na gan dare...ban rintsa ba sai tunane tunane.
    Washegari da sassafe Babana ya nufi"my precious Estate"...ya tarat fillo ba ya garin don haka ya nufi gida ko nace sashen  Baba Lamido shima baya sun tafi rugga da sauran yan uwansa,hakan ya sashi barin sako,cewan idan sun dawo yana son ganinsu,domin kuwa ance a ranar zasu dawo.

Mamata tayi lallashi,tayi fa'da,tayi fushi..daga karshe kuma ta koma lallashi akan naci abinci,ko da shayi ne....a lokacin ko ruwa bana marmari balle waishi naci abinci,ganin naki sauraron kowa ya sanya safiya kiran mamanta.
Tana isowa,safiya ta sanar da ita abinda ke faruwa.
Itama fa'da ta shiga yi,tayi fadan kamar baza ta bari ba,da'ga karshen ta koma lallashi da nasihohi tana bani magana,....hajiya ce ta shigo rike da tire a hannunta ta dire a gamanmu tareda fadin Bissimillah.
Ganin bani da niyar tashi,yasanta rikoni na zauna sa'anan ta debi abincin tana bani a baki.

Bayan sallah magrib Baba lamido tare da mahaifin fillon,mallam yakubu suka iso gidan mu.
...baba lamido ne ya fara magana bayan sun gaisa,yake ce wa babana "lafiya dai ko??anceka zo neman mu.
Babana ya numfasa yace "a gaskiya ba lafiya"
Gaba dayn suka hada baki da fadin "tauww"
...Buba ne ko?
Kai kawai mahaifina ya da'ga sa'anan ya kwashe komai ya sanar dasu.
Salati baba lamido yayi yana ta'fa hannuwansa.."ai ni ban san yar'nan bata san da zancen auransa ba"fadin baba lamido.
Mahaifin fillo yasa baki da fadin"...wannan lamarin da ban mamaki yake"..mu dai ya same mu kwanakin baya yace  alhaji dauda ya bashi aiki  da kuma babban matsayi..
Daganan kuma ya bashi yarsa,yana sanar da mu, mukace ya tafi ya sanar da kai,duk abinda kace shi za'ayi..
..kwana biyu a tsakani yace sun umurce shi da ya turo magabatar,..mu kuma hankalinmu be bamu mu tambayeshi shawaran da ka bashi ba..
a haka dai suka tattauna,daga karshe suka shigo cikin gida muka gaisa,..sun kuma tausayamin ganin halin da nake ciki.

  A ranar da fillo ya dawo suka taso shi gaba,gidanmu suka zo.
Anyi kirana zuwa falon Babana inda suke zaune.
Mu hada ido,naji faduwar gaba,shi kuwa sai bi na yake da ido.
Na sami guri na zauna tare da gaida su.

Babana ne ya fara magana,yana me tambayar fillo ko da laifin da tayi maka??
Yace a'a.
Tauw meye yi zafi da zaka kara aure baka sanar da ita ba,balle ka nemi shawaranta?..na san aure nufin Allah ne, kamata yayi ka sanar da ita ba wai taji labari a waje ba.
Shiru fillo yayi,bai ce komai ba.
Nan babana ya shiga yi masa fada,ya nuna masa bacin ransa sosai...yayi masa kashedi da'ga karshe yayi masa nasihah..
bayan sati daya, a lokacin auren fillo da hajiya zubaida saura sati biyu,don haka babana ya sa anyimin gyaran gida an kuma canza komai na gidan sannan na koma gida..
Tunda kuwa na koma nake ganin sauyin hali da  ga mutan gidan,da mata har mazan...ba kamar yusuf da salisu(Lamido karami),ba su kaunar ganina.na rasa dalili kiyayya har yara na.

A zatona idan na dawo zamantakewarmu da fillo zai dawo kamar baya,amma ina!! Sai abinda ya karu..ko magana ba ya son yimin.
Watara na lura kafafuna sun kumbura sai nayi tunanin da nayi excersice  ,na kwashi yara muka nufi sashen binta ,bamu tarar da ita ba,daga na  sai sashen Baba Lamido,nan na tarar da Binta da su fadimatu,halima,bingel da dai sauransu,gidan cike yake da yan'uwa daga ruggansu...cikin fara'a na gaishe su ina fadin yau me akeyi ne da ba'a gayyaceni ba.
..yooh kina nufin kice baki san abinda ya kawo mu ba?..fadin Hauwa
Hauwan diyar kanin Mahaifin fillo ne.
A'a wallahi ban sani ba.
Sai wata a cikinsu tace "tau biki muka zo,dan uwan mu zai kara aure"
Gaba naji yayi ras!.ashe fa satin bikin kenan muke..
Zama nayi ina binsu da ido suko sai bushashansu sukeyi,ba tare da sun yimin magana ba,ko sun sanyani a harkansu ba....sai dai idan andauki lokaci Binta ta waigo ko ta zo inda nake tace sannunki mezan baki ki ci?
Ana haka fada ya hargitse tsakanin Hisham da Mahmud (dan Hauwa) ...ganin Hisham a kasa,mahmud na kai masa duka ya sanya ilham zuwa ta kama mahmud ta samasa hankori ta cije shi,dai dai nan salisu watau Lamido karami ya shigo.
..shigowar sa kuwa yayi dai dai da tsaga ihun mahmud sabida azaban cizo.
Lamido ya kama ilham ya zane ta,duk a idona...ya rike mahmud zuwa inda su hauwa ke zaune,tana ganin shaidar hakorin ilham ta taso tana zage-zage tare da bugewa ilham baki  tana fadin "yau sai na cire wannan hakorin..duk dai ban tanka ba sai kallonsu nake alhalin kuwa har araina nake jin abinda suke yi mata.
Lamido ya zo gurin,ita ko ilham sai kuka takeyi sabida bubbuge mata baki da hauwa tayi....mari lamido ya sake kai mata tare da tureta yana fadin "fita ki bawa mutane guri,ya tunkuda ta ta fadi kasa,na kasa jurewa na mike....kai Lamido,wannan wani irin cin zarafi ne? A gaba na kake yi wa yarinya haka? CIkin bacin rai nake maganar,a yayin da nake mikar da ilham daga kasa...." ai  kaine me barin gidan ka bata guri,ba ita...
Kamar jiraye yake danai wannan furucin,sai surutan banza yakeyi ta inda yake shiga,ba tanan yake fita ba....ha yana fadin shi wallahi ba zai kwana a Estate din ba,wai nayi masa gori.
Cikin bacin rai na koma sashena,ina me mamakin wadannan mutanen.
..daga wannan lokacin kannensa mata suka yanke hulda dani.

KWana uku to auren fillo,safiya ta iso...har zuwa wannan lokacin fillo bai ce min komai ba game da auransa balle yayimin bayanai ko ban hankuri,asalima tunda na dawo,hiran kirki bai taba hadani dashi ba...sai dai gaisuwar safe da kuma idan ya dawo nai masa sannu da dawowa.
...bayan mun natsu,safiya ke tanbayata inda za'a ba amarya ta zauna.
Cikin kwantar da murya nace"kin san kuwa har zuwa yanzun nan fillo bai ce min komai ba batun auren nan!..na sanar da ita irin zaman da mukeyi tun bayan dawowata,har yanda yan'uwansa suka juyamin baya.
Safiya kamar zatayi kuka sabida tausayi...ta shiga bani hankuri da magana masu shiga jiki...daga baya tace ki kuma dage da addu'o'i sosai sabida sanin da nayiwa Hajiya zubaida sai da haka....idan akan abinda take sone,ba shakkar yin komai ko da kuwa za'ayi fansan rai ne.
Ido waje nace daman kinsanta haka?
ta da'ga kai..tace na santa,mahaifinta da mahaifin mijina wa' da kani ne,uban su daya,kiwa da uwarsa.
Cikin kaguwa nace me kika sani game da ita?
Hmmm...idan nace zan baki labarin ta yau nan zamu kwana, amman kadan daga cikinsa shine hajiya zubaida wace ta kai kimamin shekaru 29,haifafn garin kaduna ce.ita kadai ce a gun iyayenta.
Babanta hamshakin mai kudine,yana da kanfunoni a nan kasar har ketare,kasancewan hajiya zubaida kadai ce suke da,ya sanya sun nuna mata so da ga'ta..ta taso cikin tarairaya,da ga'ta ga shagwaba.
Ba abinda ta sani sai takama da wulakanta mutane.gashi ta tsani talaka da talauci,haka take wulakanta masu aikace aikacen gidan wai don ta tsani talaka.
Iyayenta sun nuna mata ba abinda zata nema ko bukatu a duniyar nan ta rasa shi ko ya gagareta,ko da kuwa za'ayi fansar rai ne.sabida haka komai isa-isa takeyi,da kuma goyon bayansu.
Tarbiya kuwa ta rasa shi,sabida bata shakkar iyayenta balle dan adam...su suke shakkarta gudun bacin ranta.
a sanadiyar ita da mahaifiyarta yan'uwa da abokan arziki na mahaifin sun wareshi daban...mahaifiyarta kuwa akwai kokari gun shige-shige da bin bokaye da malamai don haka ina me baki shawara da ki rike addu'o'i su zaman maki takobi,ki kuma tashi tsaye da ibada domin kare kanki da'ga shairin hajiya zubaida da mahaifiyarta.Allah shi tsare.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.