Pages

Thursday, 21 December 2017

SOYAYYARM 👫

SOYAYYAR MU👫.
    By A'ishah M.Gana
         (Ganarious)
1⃣9⃣.
Sai da dare yayi Babana ya sake kiranmu falonsa.
Nan yake fadin dalili kiran mu.dalilin kuwa shine batun makaranta ta.nayi farin ciki da haka domin form din makarantan Nigeria civil Aviation training center wanda a yanzu aka fi sani da The Nigeria college of Aviation technology dake zaria ya miko min,ya kuma kara yiwa fillo bayani.
Sai da nacika form din sa'anan muka koma gida.
Mamata taso na fara zuwa jami'a na farayi digiri idan yaso sai na je nan din,baba yace hakan ma yayi ba laifi..idan na gama nan din sai na shiga jami'a daga nan sai naje kasar germany watau makarantar da na baro.
Makarantar tukun jirgi dake zaria,a jihar kaduna tarihinta ba'a taba samun mace musulma daga arewa ba sai ni.
Na sa himma sosai.tukin jirgi kawai na zaba a matsayin course,shi kuma wannan course din shekaru biyu zuwa uku akeyinta.
Zaria na koma da zama,nakan shiga kaduna akai akai domin ganin fillo sabida shi baya samun lokaci...wata sa'in yana zuwa min weekends ko ni naje.
Na dawo gida a yayinda mukayi hutun farko,na iske binta da ciki nayi mata murna da fatan Allah ya sauke ta lafiya...ita kuma addu'ar ta Allah shi sa da namiji zata haifa,sai ni na haifi mace suyi aure.dariya ta bani sosai don har zuwa lokacin abin yara takeyi.
A wannan hutun shakuwar mu da binta ta karu,har idan fillo ya shigo ya ganta sai ya ba'ta rai wai tana takura masa.
         **        **           **
Ina makaranta fillo ya zo dubani,sai yake fa'damin binta ta haihu ta sami da namiji.
Nayi hamdala tare da ji mata dadi burinta ya cika na samun da namiji.
Sai da fillo ya jira na gama darasin ranar,sa'ann muka koma gida tare.bai so na biyoshi ba,nikuma nace mashi bazani iya bacci ba idan ban gan dan binta ba.
   Sashen Binta na nufa kai tsaye domin ganin jaririn.
 
Subhanalillah!!!...godiya da yabo sun tabbata ga Allah sarkin halittu...ba mahalukin da zai kalli wannan jaririn baiyi Allah zikiri ba..
Na da'de tsaye rike da yaron sai kallonsa nakeyi,so da kaunar jaririn ya mamaye min zuciya cikin kankanin lokaci.
Dariyar Binta da yan'uwata ya farkar da ni hankalina ya koma garesu sai a lokacin na tuna ashe fa bamu gaisa ba.
sai da sukayi da gaske sa'anan na bada jaririn,kafin ko na bada shi,sai da ya sha sumbatu ta ko ina.
Ina kai da komowa,zaria da kaduna  sabida wannan jaririn da ya tafi min da hankalina.
Ranar suna yaro yaci sunarsa Abubakar Assadiq. Bayan suna da kwana biyar na dawo ganin jariri,sai naji yan gidan suna kiran sa "jelodi".. cikin bacin rai nace waya sa mashi wannan sunar binta tace babansa ne.
Nace masu idan har baza su kira shi da Assadiq ba,a dinga kiransa "Hisham"....daga nan sunarsa jelodi ya mutu sai dai Hisham.
 Mamee ta dan ja numfashi,tayi shiru na dan lokacin,daga ni har Hisham ita muke kallo.
Tayi murmushi tace Hisham din kenan  a gaba na yau ina bashi labari.
A lokaci guda muka kalli juna nida Hisham,sanan muka Mayarda kallonmu ga mamee...ita ma kallonmu take tana murmusawa.
      **        ***        ****
Kyakyawan jaririn nan ya shiga raina sosai,ina sonsa.
Duk wani abu da zan samu Hisham ne.kudi na a Hisham suke karewa sai dai idan ban gan abin wasan yara ba...mamarshi ta kaiga yafeminshi sai dai kash! Ina makaranta duk da hakan nakan dawo duba shi.

A lokacin da nake rubuta jarabawar barin makaranta,shima fillo a lokacin yake jarabawar gama sekandiri skul.. duk da anyi masa tsallake.
Taro yayi taro.jama'a a makarantan mu kamar ku'da. Makaranta ta gayyaci mutane daga kasashen tsallake har cikin najeriyan ma...yan'uwa da abokan arziki sun zowa daliban don tayasu murna.
Anyi jawabai aka yayemu da za'ayi, ankuma ba da kyautuka zuwa gwarzayen shekaran.
A cikin mata,nice aka baiwa  kyautar wace tafi kowa fasha da basira fanin tuku.,kuma mace ta farko daga arewa wace ta fara zama matukiyar jirgi.
Mama ta tayi farin ciki sosai,burinta ya cika.

Bayan yan kwanaki da kammala makaranta,muna falo fillo na zaune kaina na saman kafafuwansa yana sosamin kai,gefen mu Hisham ne kwance yana baccinsa don tunda na dawo na karbo shi.
"A'isha"...fillo ya anbaci sunana.
Ba tare da na amsa ba na juyo fuska,muna fuskantar juna.
Mi kike ganin zamuyi yanzun tunda mun gama makarantar.?
Hmmmm...haka ne kuma fa.,na da'go daga kwancen na kara gyara zama nace mashi ai nawa da sauki,idan na nemi aiki zan samu.kaine dai abin zancen yanzun.
To..me kike ganin ya dace muyi yanxun?.
Wannan ba wata matsala bace.idan dai sakamakon ka ya fito kuma yayi kyau ina da tabbacin Babana zai kula da sauran..
Haka ne...Allah dai ya saka mashi da aljannar firdausi,iya abinda kawai zan kwatanta biyansa dashi kenan.
Murmushi nayi nace ko zamu kai masu gaisuwa gobe ne?
Shikenan Allah ya kaimu.
   Kashe gari tunda sassafe muka shiga kitchen ,da shike nakanyi girke-girken kalolin abincin da Babana yafiso,sai mu tafi masa dashi.

Kamar yanda na fada maku tare muke shiga kitchen da fillo,a ranar ma haka.bayan mun gama komai mun tsabtace gurin da mukayi  ayyuka mukayi wanka sa'anan na shirya hisham din shima amman kuma ba dashi zamu tafi ba,sabida wata sa'in rigima yakeyi sosai...don haka muka kaishi gun mamarsa don bada ajiyarsa kafin mu dawo.
A duk lokacin da muka je masu ziyara,Baba ji yake tamkar ranar ce farkon haduwan mu ko yayi kamar wanda ya shekare bai ganni ba.
A falonsa muka muke,bai yarda mu shiga cikin gida ba.
Abincin da muka je dashi shi sukaci.

Mama ta ce ta duba agogo,karfe biyar da minti arba'in da daya ,tace ku tashi ku tafi ko!
Shiru-shiru bamu motsa ba,ta sake magana a lokacin karfe shida dai dai.
Babana ya kalleta ya kalleni muka hada ido,da kamar magana a bakinsa amma ya kiyinsa.
Fillo ne ya mike yace toh mama.
Na sake kallon babana shima ni yake kallo,da alama ba ya son na tafi.
na juya ga mamata nace yauwa mama da abinda ya kawo mu fa .
Cikin mamaki tace lafiya dai?.
Nayi murmushi sabida yanayin kallon da tayimin nace lafiya lau.daman buba ne yace tunda na kammala karatun mizanyi yanzun shine nace sai na nemi shawaranki.
Tayi ajiyan zuciya...ku kwantar da hankalinku,innshaa'Allahu cikin watan nan zan sanar da ku abinda ya dace...shima babana ya sanya baki a maganar.
Mun tashi kenan munayi masu sallama,sai akayi kiran magrib.hajiya babbace tace mu bari a yi sallah sa'anan mu tafi
Hisham ya fara zuwa makaranta da kwana uku  akayi birthday sa na cika shekara biyu..a ranar Babana ya aikowa fillo da takadar shiga jami'a ta Ahmadu Bello university dake zaria.
Fillo yayi farin ciki da haka.farin cikin sa ya sani farin ciki. Gashi daman saura kwana biyar ayi walimarsa ta saukan al'qur'ani maigirma.
  A daren ranar baiyi bacci ba sabida farinciki...daga baya ya mike ya gabatar da sallah nafila sa'anan ya dawo inda nake ya kankame ni.
Cikin kwantar da murya yace A'isha!.
Na'am buba.
Me kike ganin zanyi wa mahaifinki ya fahimci cewan ina me matukar godiya da hasken da ya kawo wa rayuwata?
nayi murmushi tare da kankameshi yanda yayimin nace Addu'ar nan dai da kake yi masa shi zaka cigaba.
Bayan wannan fa?
ka sanya ni farin ciki har karshen rayuwta.
Bayan wannan fa?
Su kadai zakayi masa ya gamsu da godiyarka
Anyi an gama innshaa'Allah.
Yayi waige waige kamar ba dagani sai shi a falon ba.ya matso da bakinsa dai dai kunnena ya rada min wata magana da bata wuce batun haihuwa ba,wai mamarsa ta fara korafi.
Maganar sa ta ta'ba ni,sai dai na daure nayi murmushi nace addua kawai zamuyi.
  Cikin sauki da taimakon Allahu Buba fillo ya samu shi jami'an a.b.u zaria.Babana ne yayi ma sa komai,daga kan gidan da zai zauna har zuwa su abinci.
Bayan kamar wata uku da tafiyarsa makaranta,wataran na tafi gidanmu tunda safe,da shike ranar asabar ce.na tarar Babana da hajiya babba sunyi tafiya tare amman a ranar zasu dawo..mamata ce ke gida,sai yannena da basuyi aure ba sai kanina Al-ameen shima ya dawo hutu ne.
Bayan mun gaisa take fadin kamar kinsan zan aika kiranki.
Banyi mamaki ba,nasan wata abin ta samu kenan..nace sai gani!.
Ta jawo durowa ta ciro wata takarda tace gashi..ki tafi dashi ku duba,sai kuyi shawara.duk abinda kuka yanke sai ku sanar dani.
Takarda ce ta makarantar tukin jirgi dake kasar germany.watau makarantan da na fara zuwa suka maidani baya,ita dince mamata ta kara amsowa.
Cikin murna na tashi na rungumeta ina me sumbatarta tare da fadin wannan karon innshaa'allah zaki sha mamaki mamata.
Daga yanayinta zaku fahimci cewan taji dadin furucina sosai,amma ta daure tace ai sai kinyi shawara da mijinki kar mu shiga hakin sa.
A a mama....Buba  bashida matsala,asalima ya matsamin wai nayi maki magana ,ban daiyi bane don nasan da abinda kike tanadar min.
Dariya tayi tace shikenan Allah shi yi maku albarka.
Ameen na fada tare da kaimata kiss
Babana ya sani kuwa? Na tambaye ta
Yana sane.
Karfe biyu da rabi mamata ta shiga kitchen,na tashi zani taimaka mata da wasu ayyuka,sai na tsinci kaina da jin jiri...na fadama ta,tace na tafi na dan kwanta.
INa kwantawa kuwa bacci yayi awon gaba dani.
SAi da akayi kiran mangariba,Al-ameen yazo ya tada ni wai mama tace na tashi.
SAi a lokacin na tuna banyi sallar azahar ba cikin ambatar salati na mike zuwa bayi donyi alwala.
A falo na tarar da mamata tana cin tuwo
Tana ganin na fito tayi kiran al-ameen wai ya daukomin tuwo na.
na zauna a kasar falonta tare da mimmike kafafuna,don naji dadin cin tuwon
Al-ameen ya shigo rike da tire ya dire a gabana,tuwon masara ce da miyar zogale
Na kalli mamata dake nisa dani nace rabon da nagan anyi wannan tuwon a gidan nan tun ina aji uku a sakandiri.bata amsa ni ta cigaba da cin tuwonta.
Na kai loman farko,zan kai ta biyu sai kawai naji zuciya ta na tashi,da sauri na mike  sabida amai.
Amai na ke kwararawa....cikin tashin hankali da rudani mamata ta biyoni tana fadin ya'ya dai!
Na daga mata.
Kamar zan amayo ya'yan cikina ,har zuwa wannan lokacin tana rike dani,bayan aman ya tsagaita ta wanke min fuska,ta samin ruwa na kuskure baki muka fito falo.shiganmu falo aman ya sake dawowa ta sake biyo ni tana fadin bari na kaiki asibiti dai.
Yayana suleiman ke tukin mota ita kuma tana rike dani a bayan mota.
Asibiti da muka nufa mai zaman kantace wanda abokan juna suka hada kai suka gina ta,ciki harda Babana.
Duk wanda bashi da lafiya a gidanmu nan ake kaishi.
bayan gwaje gwaje da sauransu likita ya fito da sakamako,har zuwa wannan lokacin ina kwance jikinta ....da farko ya mika mata ledan magunguna sa'anan yayi mata albishir,wai ina dauke da ciki.
Tsale tayi tana hamdala.
Muna cikin haka ya shigo cikin rudani,ysna isowa inda muke ya tattaba min jiki yana fadin mamata miye same ki.
Ba komai baba!.
Sai a lokacin ya kai dubansa ga mamata yace me likta yace maku?
Albishir tayi masa tana fadin kasami jika.
Duk sunyi murna daganan muka koma gida.
Mamata bata bari na koma gidana ba wai sai na kara samun karfin jiki amman ta aika a fadawa Baba lamido da sauransu cewan bazan samu dawowa ba sabida bana jin dadi.
    Da sanyin safiya su binta suka diro a gidanmu,sun kuwa yo taron dangi...sun dan jima sa'anan sukayi min Allah shi bada lafiya suka tafi.
Binta suka bari da danta hisham...binta ta matsamin akan na fadamata ciwon da ke damuna nace mata nima ban sani ba.mamatace kawai ta sani.
Kafin binta ta wuce nayi amai ya kai so uku,duk abinda na gani idan har naci ne sai naji zuciya ta na tashi,haka yasa ta gane cikine da ni sai ta shiga zolayata tana fadin Hisham ya sami mata.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.