Pages

Thursday, 21 December 2017

SOYAYYARMU

SOYAYYAR MU👫.
      Written by Ganarious.

Visit Ganarious.blogspot.com/ for latest update.
1⃣8⃣.
  Kai na da'ga alamar eh.
Aisha kinsan ni mahaifinkin ne ko
Nace mashi eh!.
Kin kuma san duk cikin ya'yana na fisonki.
Eh Baba na sani.
"Ina kwana na kuma tashi da damuwa akan yanayin da nagan kin shiga,idan dai ba kinason ciwon zuciya ta kamani bane,toh ki fadamin asalin abinda ke damunki domin na nemi mafita kafin yayi nisa.

A hankali da kamar ra'da nace "Baba ina son fillo"...soyayyar da nakewa fillo ce ta jefani a wannan halin.
   Ba alamar mamaki a fuskarsa,asalima murmushi yayi sa'anan yace daman ne na kara daga bakinki.....
Ya kara fadin"shi fillon yana sonki?
Da sauri na da'ga mashi kai tare da fadin shima yana sona sosai baba.
Shikenan!ina son daga yau ki cire damuwa a ranki,zan zaunar da mahaifiyarki mu tattauna   akan matsalarki.
Gabana naji yayi ras...jin ya ambaci mamata.
Nace dashi baba ya'ya zan yi da zance makaranta na?mama zatayi fushi dani sosai,baba ko na maimaita ba tare da ta sani ba.
Murmushi yayi yace"ko kin maimaita baza ki ci ba....
...na gwalo idanuwana alaman mamakin maganar.
A hankali yake shafan kai na,tare da fadin "tare zamu koma gida gobe,idan Allah ya kaimu.
 Tare muka koma gida da babana sai dai a tsorarce nake,ga faduwan gaba!
   A kofar falonta muakayi karo da ita,tana ganinmu ta gyara tsayuwa tare da rungumar hannayenta.
Babana ya riko min hannuna domin kuwa mutuwar tsaye nayi.
Gefenta muka ra'ba zuwa  cikin falon.ta juwo tana binmu da kallo,sai da ta dauki mintuna sa'anan itama din ta karaso.
Bayan ta zauna ta samin ido kamar tana son gano wani abu,jikina kuwa sai makarkata yake.
Babana ya lura da hakan sai yace dani na tashi na shiga ciki zasuyi magana.
Bani da masaniyar maganar da sukayi a tsakaninsu.
A tunane na hukunci mai tsauri mamata yankemin,sai dai labari ya sha bambanci.
  Ban Saki jiki ba sai da na cika sati mahaifiyata ba ta canza min ba..a sati dayan ban hada ido da fillo ba,haka yasa ni kasa samun natsuwa a zuciyata.
Zaune nake a falon Babana ina karatun littafin turanci.Babana ne ya shigo,mamata na biye da shi,na sauko daga kan kujeran na rusuna ina masu sannunsu da dawowa.bayan na gaida su,na tashi zan fita a falon,babana yace na zauna za suyi magana dani.
    Yace dani "nasan kina son karatu sosai Aisha!..matsalarki daya shine son dan fillanin nan..
Aisha ina son kinsan cewa duk wani abu da kike so,idan dai mai faranta maki raine toh shi nake so kuma shi zanyi maki.
Na karanci irin soyayyar da kike yiwa dan fillanin nan kuma nayi kokarin fahimtar da mamarki.Rashin amincewar mu da soyayyarku wata illace babba,don haka ni da mahaifiyarki mun amince wa soyayyarku....idan har shima yana sonki yanda kike sonsa.,batare da cutarwa ba.
a shirye nake da na aura mashi ke...bayan auren sai ki koma makaranta,kiyi karatun ki hankali kwance.
  Na fashe da wata irin kuka me kunshe da farin ciki da kuma bakin ciki.
cikin kukan na mike a sanyaye zuwa gun babana  Na rungumeshi.
Mamata dai kallonmu takeyi ba tare da ta ce wani abu ba,amma jikina ya bani bataji dadin zancen ba.
             **          **        **
Bayan kwana hudu da Yin maganar,babana ya umurci fillo da ya shirya domin za suje ruggansu tare.
Tare da Baba Lamido suka dawo.Bayan sun huta gajiyan tafiya ne Babana ya tara mu a falonsa.ciki har da kannen sa,yannena,mamata da hajiya,fillo da Baba lamido.
Bayan addu'a da godiyar Allah! Babana yace kafin ya fara bayani,zai so yayi fillo wata tanbaya.tambayar kuwa itace 'kana son Aisha kamar yanda take sonka?
Da sauri da sauri yace "eh'eh,ina sonata...inason ta sosai"
Toh maa shaa Allah. shi nakeson ji nake kuma son yan uwanka da nawa yan uwan suji domin su duka su zama shaidu.
ya juyo gareni yace Aisha ke fa?
Kaina na jinjina batare da na fadi wani abu ba.
Shikenan..ya fada sa'anan ya cigaba da fadin ya tara su domin su gani su kuma shaida zai baiwa fillo diyarshi.
Diyata kwaya daya tak! Wacce nafiso,ban hada da komai ba.farincikin shine nawa farincikin.
idan bayan auren dan fillo yayi mata ba dai-dai ba,shi ma fa ba zani raga masa ba.shiyasa na tara ku anan ku zama mani shaida'
Sa'anan kuma bayan auren inason ta cigaba da karatun ta.
Ya kalli fillo yana fadin ina fatan zaka iya da kuma amincewa da bukatuna.
Eh na amince baba,na kuma gode maka,Allah ubangiji yasaka maka da gidan aljanna.
ya kuma kai kallonsa gun Baba lamido yace masa idan fa hakan baiyi maka ba,kai da yan'uwa toh muna marhaba da duk wata shawaran da zaku kawo.
Sun zurfafa zancen,daga bisani kanin mahaifina yace wa Baba Lamido su turo magabatansu,idan sunyi shawara.

Yan'uwan fillo sunyi shawarwari a tsakaninsu,sunyi murna sosai tare da yiwa babana godiya.
Wasun su sun zo domin yin maganar auren,nan ma Babana ya sake yi masu kashedi akan su jawa dansu kunne.
Kafin su koma ruggansu,babana ya dauke su zuwa "my precious estate"
My precious estate da ke hanyar mando,estate ne da mahaifina ya gina shi da sunana.da farko mahaifiyata ta shawarce shi da ya sanya yan haya sai a dinga saving mani kudin hayan...
Shawarar ta chanza sabida babana ya kyautarwa yan'uwan fillo estate din.
Ya umurci baba Lamido dasu dawo nan din da zama sabida shi dai kam bazai aminta da zamana a rugga ba.....cikin gine-ginen akwai sashen da aka ke'ra min,shi wannan sashen gini ne da yasamo asali daga korea.
Wani lokacin na raka babana wata semina na yan' kasuwa da masu kamfunoni,bayan seminar aka kai mu masauki,watau wata karamar hotel ne amman fa tun daga wa'jen hotel zaka rude sabida tsarinta.
Na wangale baki ina me kara kallon ginin ba abinda nake fadi sai'waw....'waw.
Babana kuwa sai murmushi yakeyi ya jin dadin gani na haka.
tsarin ginin ya tafi da hankalina,har muka dawo bani da zance sai na ginin...hakan yasa babana ya ke'be min  gefe daya a cikin estate din aka keramin ginin.

      **             **          **
Ba'a bata lokaci gun sanya ranar aurenmu ba.sabida makarata da zani koma.
     Labarin aurena da fillo ya bi gari,wasu na yabo da jinjina wa babana,wasu kuma na zaginsa,wasun ma suna mamaki har sun kai ga tsaidani a hanya don jin zancen daga bakina ko dagake ne.

Daga lokacin da aka sanya ranar aurenmu nake cikin farin ciki da anashuwa,shima fillon haka don kuwa sai da yayi sadaka da shanayensa biyu.
Mahaifiyata dai ba yabo ba fallasa.tana zani iyacewa tana son auren zani iyace wa kuma bata so ta dai amince ne sabida dalilan babana cewan idan na sami abinda nake so zan natsu nayi karatu hakan yasa ta kwantar da hankali ta tarbi zancen hannu bibbiyu.
Kawayen mamata da yan'uwan basu barta ba.suna fadin yaya za'ayi na auri wanda yafito daji!...sunaye iri-iri ba wanda basu kira fillo dashi ba.
Haka suka sa mamata gaba suna yarfa mata ruwan bala'i...idan sunyi mata sai kuma su dawo kaina suyi min...
Anty amina mamar ya'nazeer tayi magiya,tayi roko wai a fasa auren da fillo na auri nazeer dinta don shi yafi dace wa dani kuma a shirye yake ko yazun nan,amma babana ya kara jadada mata sai wanda nace ina so....tayi kira na gefe daya tace na kara tunani akan wannan auren.

Yan'uwan fillo karka-kaf dinsu sun dawo 'MY PRECIOUS ESTATE'da zama.
Ana sauran kwana hudu daurin aure ya'nazeer ya iso a birkice.sumbatu yakeyi kamar taba'be..sai fadin yake wabillahillazhi idan baki fasa auren dan dajin nan ba zan sace ki,ko na kashe kaina amma zan fara kashe ki sai kowa ya rasa.
Na tausaya mashi,na kuma tsorarta da furucinsa sai dai na fahimta ba'a cikin hayacinsa yake wadannan maganganun ba.
Baba na ya zaunar da ya'nazeer yayi masa nasiha sai dai kirikiri ya'nazeer shi bazai taba hakura dani ba.

           **        **       **
Allah ya kaimu ranar aure,an kuma daura lafiya.
Duk wani mahalukin da ya halarci wannan auren yasan ni yar gata ce ta mussaman.
Sai a ranar mamata tayi kuka domin kuwa yan'uwanta sun sat gaba fiye da zaton ku
.....tana kuka tana ce masu ya'ya suke son tayi da rayuwarta!
Ina kwance a dakina tare da kawayena na jiyo hayaniya,har zan fito sai kuma na fasa don a zatona yan taron bikin ne ke hayaniyar..sai ga wata yar uwar ta shigo,nake tambayarta "hayaniyar me akeyi"
Nan take fadamin wai mamata ce da yan'uwanta suke sa'insa, ba tare da na sauriri abinda zata fada ba na mike a guje zuwa falon mamata na kuwa yi sa'a har zuwa wannan lokacin basu daina fadamata maganganu ba.
  A gabansu na zube  ina fadin ba laifinta bane,ita ma bata son auren! Wallahi itama bata so,nice dai nakijin maganarta...don Allah kuyi hankuri
Anty saudat,itace babbansu,ta taso daga inda take zaune..tana kaiwa inda nake takaimin mari...
...kiyi wa mutane shiru! Ashe baki da mutunchi ehee! Baki da kunya har kike fadin bata so amman kin bijire mata! Ko maza sun kare a duniya ne...ehe!
toh bari kiji..tunda kin ki nazeeru,mu ma din bamu sonki. Je ki ki auri jahili amman fa duk abinda ya biyo baya ki nemi mamarki da babanki...ba mu ba ke!
A haka dai sukayita surutansu,ni kuwa ba abinda nakeyi sai kuka.
suna gamawa anty saudatu tace da sauran kannenta su tashi su tafi,ba tare da sun sallameni ko sanyawa auren albarka balleshi wai shawarwari ko rakiya.
Bayan tafiyansu na tashi nakoma inda mamata take zaune na rungume kam..ina fadin mama ki yafe min.
       **         **         **
A lokacin da za'a kai amarya watau ni kenan..Babana yayi kiran fillo da iyayensa da wasu daga cikin yan'wan babana din,da yannena da su hajiya.bayan godiya ga Allah s..w.t da ya nuna mashi ya kuma bashi ikon aurar da diyarshi.yayi bayanai akan yanda yakeji a ransa sa'anan daga baya ya jawa fillo kunne akan ya rike amana.

Yan uwan babana sai wasu daga cikin kawayen mamata sai kawayena ne sukayimin rakiya.
Yan uwan fillo sunyi murna sosai da aka kaini,sunyi kwaliaya irin ta su dai.
Kawayena sun kwana tare dani sabida walima da za'ayi da safe.
Duk sun watse bayan walima...sai a lokacin fillo ya shigo.
Kallo daya zakayi mashi ka fahimci cewan yana cikin farin ciki,sai godiya ma Allah yakeyi yana fadin Allah nagode maka na gode ma baban Aishetu...aljannace kawai zaka saka mashi dashii..kallonsa kawai nakeyi inajin son sa har a raina.
Aurenmu na neman sati uku,amman wani abu na ma'aurata bai shiga tsakaninmu da fillo ba,dalili kuwa shine karanci ko nace rashin ilimi addinin islama a tattare dashi..da kaina na bashi shawarwari neman ilimi da neman sanin yanda ake ayyuka kamar su wanka da sauransu...ba musawa sai ma farin ciki dayayi da bayanai na.
  Akwai masallaci da kuma makaranta a cikin estate din.Babana ya samo mallamai,ya basu gidajen da ba'a shiga ba.domin koyar da yan'uwan fillo.

Zaman jin dadi da annashuwa mukeyi...ba renin hankali a tsakaninmu,ina girmamashi..a matsayina na matarsa wacce ke kasa dashi.
Ban taba kawo wa rai na gatanci na ko kudin babana zai rufe min ido na kaskantashi ko maidashi kasa dani ba.Asalima sarki na maida shi domin kuwa komai nike mashi,nice ke  shafa mashi mai ajiki,nice ke yanke masa farce da sauransu.
shi din ma haka yake baya kaunar ganin na matsa kusa dashi.idan ina kitchen zai biyo ni tare muke komai,idan na gama aiki muyi gyare gyare tare..baya bari nayi aikin gida ni kadai,haka duk inda zani je,tare muke zuwa.
  Binta abin so Ya samu ta dawo birni da zama,kusan kullum tana sashena...godiya kaw sai da nayi da gaske sa'annan ta daina wai nice sanadin zuwan ta birni...tare muke jerawa zuwa islamiya da ita.
  Bayan watanni biyu izuwa uku da yin aurenmu,Banana Ya aiko muzo gida nida fillo.
Ya jidadi sosai da ganinmu sabida farincikinsa a bayayyane yake..
Naje zan rungumeshi,ya tsaida ni yana fadin ai yanzu  kin wuce nan...na ba'ta fuska tare da komawa gefe, shi kuwa fillo tunda muka isa gidan kansa a duke
Bayan gama gaisuwar da  babana ya umurce mu da mushiga cikin  gida don gaisawa dasu hajiya.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.