Pages

Sunday 24 September 2017

SOYAYYARMU👫

         By Ganarious
14
Alhamdulillah,maa Shaa Allah...Haj.Fateema A.Bayero(mrs Bash gwandu) ta sauka lafiya.mun sami babby girl me suna umaimah,Allah shirayamana ita kan addinin musulunci.ameen.
Jama'a makarantan soyayyarmu ina muku barka da sallah.Allah shi maimaita mana.
ina me baku hankuri akan rashin typing akan lokaci.kuyi hankuri.
Gaisuwa ta mussamman ga haj.Sa'adat Ahmad(a.k.a sa'adat mubi 4real,basu labari).


Murmushi kawai nayi mashi nace sai kazo.
A mota kuwa salamatu ta kiyimini magana ko nayi mata bata amsawa.haka ya nuna tayi fushi kenan,sai harkan gabanta takeyi.shi ko mallam iro direba sai jinini yakeyi tunda muka bark ruggan wai shi bai San wane halo banana take ciki ba,tunda yasa ran dawowanmu a jiyan.
    Abinda mallam iro kegudu kuwa shi yafaru.
A falo muka iske Babana tare dasu hajia.da mallam iro muka shiga falon Babana,yana hango ni yayi min alama da hannunsa na karaso gun da yake zaune...salamatu ma ta sami guri ta zauna shima  din mallam iro ya sami gu ya xauna..
Mun kara gaida su hajia,bayan gaisuwan ne babana yake neman sanin dalilin dayasa bamu dawo ba.mallam iro ke jawabi domin shi aka tambaya,sai dai daga yanayin maganarsa xaku fahimci yana tare da jin haushi da takaicin abinda nayi jiyan don kuwa a fusace yakeyiwa babana bayani.
Tun bai karasa maganarsa ba mamata ta fusata tana cewa daman tayi tunanin haka.babana dai bai ce komai ba.tana gama fadan ta shige ciki,salamatu ta bi bayanta shi ko mallam iro hankuri ya kara bawa Babana ,nan Baba ke ce mashi kar yasami damuwa.yayi godiya shima ya fice abinsa.
Dagani sai Babana da hajia aka bari a falon,a natse hajia tace hankulanmu duk a tashe yake don haka daga yau kar ki sake makamacin haka...kai na daga mata,sai ta kara maimaitawa tana fadin kinjini kuwa!
eh naji inn shaa Allah baza'a sake ba.nan ta tashi tafita.
Dagani sai babana a falo ya juyo yana kallona cikin yanayin tausayawa yace har kin dan rame!
Murmushi nayi batare da nace wani abu ba.ya kara fadin toh tashi ki shiga ciki kiwatsa ruwa,sai ki ci abinci ni zan shiga cikin gari....har na mike tsaye,sai kuma na kara zaunawa nace yawwa Baba!wannan fillo nan da ya tsince ni a daji yace yana son shigowa birni amman bashi da inda za shi sauka.shine nace mashi zan sanar da kai,idan yazo sai ya sauka anan gidan.
Toh shi kenan ba matsala Allah ya kawo shi lafiya,idan yazo sai ya sauka anan din.amman kuma baki tambayeshi me zai zo yi  a birni ba.
A'a ban tanbayeshi ba.
Toh...Allah ya kaimu.ameen na fada.

          ****      *****     ****
Kwana hudu mamata tayi tana fushi da ni,nayi ban hankuri har na rasa yaya zanyi da rai na taki.sai da hajiya tasa baki sa'annan ta hakura,sai dai bata bani fuska kamar da haka yasa bana cikin walwala.
Akwana a tashi har mun koma makaranta.gashi dan fillo bai zon ba,babu ranar da gari zai waye banyi tunaninsa da sa ran zuwansa ba,haka yasa na fahimci cewan son sa nakeyi kuma so ta hakika.
Tun kafin na koma makaranta watau ana saura kwana hudu muyi resuming mamata ta zaunar dani tana yi min nasihohi da kuma tunatarwa.a ciki... Read more

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.