Pages

Thursday 27 July 2017

SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫
      By Ganarious.
9⃣
Wataran muna gun kiwo ni da shi sai nace ni dai har yau bansan sunarka ba..ya kalle ni cikin murmushi sa'anan yace sunana Mustafa amma bakiji ana cemin buba ba?.
Na girgiza kai tare da fadin a'a ni ban ji ba,asalima ban taba ji ko lura da wani ya kira ka ba.
"toh kishee min buba"
Toh malam Buba,nace mashi ina murmushi...
Can kuma nace amma mamarku da yaranta sunyi daban kamar ita tana da surki da buzaye ko?
Eh...buzuwace.
Cikin mamaki nace....kai,!tabdi jam amman ya'ya akayi hakan ta faru?
  Ho...ni ma din ban sani ba.
Na dade ina mamakin yanda akayi bafulace ya auri buzuwa.amma kuma combination din yayi kyau sabida yaranta suna da kyau kamar larabawa ,ga gashi har gadon baya,mazan kuma gashin su yayi luf-luf yakwanta masu.
     **    **  **
Akwana a tashi har nayi sati biyu a wannar ruggan,ina cikin na uku amman ba wani labarin batun komawata...a lokacin ne yayan Buba fillo ya dawo daga kiwo ana kiransa Dahiru.shima yayi mamakin ganina nan aka bashi labarina,cikin kankanin lokaci muka fara shiri da shi...ina cika sati hudu akayi auren dahiru da diyar maigari(mai gari Laamido shine wannan mutumin da yayimin alkawarin maidani ranar d na zo ruggan da buba fillo).shine ya'yansu baban buba(dan fillo).diyar shi bintu da dahiru cousins ne kenan.
Amarya bintu da bata wuce shekara takwas ba sai mamakin abun nakai,ita ma mun shaku,duk da na girmeta nesa ba kusa ba idan muna hira sai nace mata wataran zan kaita birni,sai tayi ta murna.haka dai nayita zama da wayannan mutanen a sannu a hankali.
    ***   ***   ***
Su hafsat ne sukayita tafawa suna murna yau burinsu ya cika."kai ku zo mu tafi fa kar a tafi a barmu"fadin hafsat bayan sun gan cewan bana cikin hayyacina.da gudu suka bi bayan sauran daliban cikin sa'a kuwa suka iske ana shiga mota ne..
Sun isa masauki(hotel) ana fitowa don shiga cikin dakuna,shine Awwal ke tambayar su ina Aisha?
Sun dan dauki lokaci sanan Rabi'a tace ai ba motar mu take ba.ka dudduba motoccin mana,kana wani tanbayarmu.ta karashe maganar ne kamar Me fada.
Bai musa ba ya koma inda aka ajiye motor A daman kuma motan yake amma kowa ya sauko bai ganni ba.sai kuma yakoma gunsu yace aisha fa bata ciki.
Toh miye na mu a ciki.?inji Hafsat
Ban gane miye naku a ciki ba.tare na barku a dajin kunga ai dole ne na tambayeke kenan.
Tsaki sukayi gaba dayansu suka juya zasu tafi..sai ya sha gabansu..Awwal yaro ne da baya daukan renin hankali ko gun yan'uwansa maza.
"wa kukeyiwa tsaki? Ya tambayesu tare da nuna masu dan yatsan.
 Gefenshi suka sake bi batare da sunce mashi komai ba..

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.