Pages

Saturday 29 July 2017

SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫
       By Ganarious
1⃣0⃣
Shima din bai cemasu komai ba,gun malamai ya nufa yace masu"An fa sami matsala!
Kamar hada baki suka ce na me fa?
Yace Aisha m.Aliyu bata cikin mu.
Malaman cikin rashin fahimtar me hake nufi da haka suka sake tambayar sa.
Aisha m.Aliyu bata cikin daliban da suka dawo,ina nufin batare da ita muka dawo ba.
 Cikin rudani wani malami yace "ya ya akayi hakan ta faru?
 Ni dai nasan na barta tare da su Hafsat Abbakar a gun da muka huta.inji awwal kenan.
'haka ne fa'...nima na gansu tare,suka cemin zasuje fitsarin.cewan malam musa.
Gaba dayansu sukace a kira masu su hafsat. Bayan sun fito malam musa yace na gan ku tare da Aisha m.Aliyu,yanzun nake ji wai bata dawo tare da mu ba
Ya'ya haka ta faru?ku kun dawo ita bata dawo ba
Rabi'a ce ke fadin toh gaaskiya tare muka baro dajin bayan mun gama fitsarin sai dai mu bus'A' muka shiga,bamusan wani bus ita shiga ba.
Nan malamai sukayi tsit..suna tunani wannan abin mamaki da kuma mafita
Malam Ashiru ne yace a tara students gaba daya.bayan sun fito yake tambayarsu ko akwai wanda ya gan Aisha? Ko kafin a shiga mota ko a daji?
  Kowa yace a'a...sai sukace a watse za suyi meeting tsakaninsu.
Wasun su sun kawo shawaran a koma a lokacin,wasu kuma sunce a bari sai gobe da safe tunda yamma tariga tayi.
         ** ** **
Da safe suka koma dajin,gashi da nisa da garin yola.sai dai sunyi rashin sa'a nabi fillo.haka suka dawo garin yola cikin rudani.
 A hakan kuma suka koma makaranta ba    tare da ni ba...malamai na sake-sake abinyi don kuwa basu san me zasu fadawa iyayena ba.gashi makarantace ta kudi.
     VERSATILE COLLEGE makaranta ce da yake a kayyace,daga harabar makaranta har zuwa cikinta,ajujuwa,bayika,gurin cin abinci,gurin wasa da motsa jiki,asibiti da dai sauransu duk    tsarin turawane.don makarantan ta samo asaline daga Germany,hatta rigar makaranta da ta wasa daga can ake kawo mana.
 Iyayen yara sun hallara,suna jiran isowar ya'yansu don  dama hukuman makaranta ta shaida masu ranar dawowan yara...harda babana ciki wayanda suka zo daukan yaransu shi ya yayana Aliyu.
Bayan kowa ya sauko daga mota suka hada kai guri daya me makaranta yazo yayi masu barka da isowa tare da godiyan Allah da ya dawo mashi dasu lafiya...sannan ya umurce su da su tafi gun iyayensu..har an kusan watsewa koma nace an watse amma babana bai ganni ba bai kuma gan alaman zai ganni ba  haka yasa sauko daga mota shi da Ya'Aliyu suka karasa office din mai makarantan,nan suka iske malamai na yiwa mai makaranta bayanin abinda ya faru.
Bayan baba na ya kara gaisawa da me makaranta yake ce mashi,shi fa be gan diyarshi ba...mai makarantan yayi shiru  na dan lokaci sa'anan yace yanzun nan ake shaida min da abinda ya faru,nan ya kwashe ya fadawa babana
..cikin fusata yace baya son jin wannan maganar diyarshi kawai son a bashi kuma yanzu nan..
Mallamai sun shiga bashi da yi mashi alkawari komawa don nemo ta.babana yace sam...cikin kakanin lokaci ya haukace masu,daga malaman har mai makaranta duk ya hada ya zage tas..
Har karfe taran dare abu daya akeyi,daga baya kuwa polisawa  ya kira masu yace ba zai bar makarantan ba sai ankawo mashi diyarshi idan ko ba haka ba sai ya kone makaranta sanan a rufe malamai har abada...uhmmm Babana kenan.
Ba malamai kadai ba hata polisa sun tsorata da yanayin shi,ya'Aliyu tunda aka haifeshi bai taba ganin baba cikin wannnan yanayin ba sai a ranar,ganin baba bashi da niyar zuwa gida,sai ya sabule ya je gida don shaidawa hajia da mama na abinda ke faruwa...gaba dayansu suka nufa  makaranta.
Irin fushin da mahaifina yayi ya bawa su hajia mamaki don kuwa tunda take dashi bai taba kwatankwacin wannan fushin ba.
Abu kamar wasa har karfe sha daya,kuma ba wata mafita daga baya polisawan suka tafi da malamain da suka je field trip din.da kyar da lallashi su hajiya sukayi da babana sannan ya bisu zuwa gida...ya kuma shaidawa mai makaranta cewa zasu hadu a kotu.
Babana baya tuki me nisa amman da sassafe kama hanyar Adamawa..a makarantan versatile kuwa anata bincike..Awwal ne ya dage cewan a binciki su hafsat don bai yarda dasu ba..haka yasa aka sake kiran su hafsat,abinda suka fadawa malamai abaya shi suka sake fadi.
Acan adamawa kuwa babana ya ba da cigiya na gidan redio talabijan da sauransu,yana dawowa yakai kara babbar kotun kasa.
An rufe makaranta an kuma  bawa mai makaranta sati daya kacal a nemo ni.
Babana ya koma abin tausayi su hajiya ke lallashi da amma duk da haka baisa shi nutsuwa ba har mamana ta kai ga jin haushin sa.masu zuwa mashi jaje kuwa ba'a maganar su don kullum gidan mu kamar gidan biki..mutane daga kasashe kamar su indian,korran da dai sauran su.
Su hafsat sunyi da sun sani.basuyi zato abin zai kai nan ba har akai ga rufe makaranta ba.sun kuma yiwa kansu alkawari komai rintsi koman wuna kar su fadawa kowa abinda ya faru ya dai tsaya tsanin su ukun

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.