~MUMUNAR KARSHE~😢
(continuation, kuma ta'ken karshe)
Salon rubutu: Aisha M. Gana.
Assalamu alaikum ya yan'uwa!!!
Kamar yanda nayi alkawarin kawo maku ci gaban wannan labari, toh gashi nan.
~a gaskiya na ji dadin ganin comments din ku, (ra'ayin ku) akan wannan takaitacen labarin.
A inda wasu suke ganin bai dace Ruka'iyah tayi mumunar karshe ba.
Wasu kuma sun yarda hakan na faruwa, da dai sauran su.
Kar fa mu manta, Allah yakan jarabce mu ta hanyoyi da da'ma don ganin karfin imanin mu...
Wata sa'in zaku gan wasu, a rayuwarsu gabaki daya suna ma su aikata alkhairi da aikin kyau sai anzo karshe Allah ya jarabce su imaninsu ya karkata. A yayinda wasun kuma sai sun zo karshe Allah ya jarabce su ,imanin su ya mike......akwai ire-iren haka da dama da suka faru a zamanin Annabi(s.a.w), kuma har yanzun suna faruwa.
*Allah ubangiji ka karfafa mana imanin mu,ka bamu kyakyawan karshe*🙏🏼🙏🏼
** ** **
Tun bayan rasuwar Rukai'iyah, Aisha bata dawo dai dai ba, a tsorace ta ke kulli-yaumi, da kuma nadamar sanya Rukai'yah a wannan hanyar.
Ita kuwa sumayyah damuwarta na dan lokaci ne, Rukai'yah ta na cike sati biyu da rasuwar, sumayyah ta warware ta soma shirin komawa makaranta sabida a satin nan za su soma jarabawa.
Ta yi kiran layin Aisha yafi a kirga, amman bata da'ga ba, haka yasa ta shirya ta nufi gidan su.
A kofar gidan su Aisha tayi karo da mahaifiyar Aisha ta dawo daga kasuwa , bayan sun gaisa tace mama wai Aisha tana nan kuwa?
Ajiyar zuci tayi tare da fadin "eh, tana nan ciki....duk kwanakin nan na rasa gane mata."
A tare suka karasa ciki, kwance suka tarar da ita ta kifa kai da ciki.
Duk da sallamar da sukayi bai sa ta da'go ba, sai da sumayyah ta je gab da ita ta dafa ta....."wai me ke damun ki?
A lokacin ta dago, ido jajir..
Subhanalillah...lafiyarki kalau kuwa Aisha.
Kai ta daga ba tare da ta dubi sumayyah ba.
Nan sumyyah ta shiga tambayarta abinda ke damun ta, ba nacin da summayah batayi ba, wai Aisha ta fadi damuwarta, amman ta ki fada, haka yasa ta soma fadin "nayi kiran layin ki baki daga ba, daman zan fada maki time table ya fito,nan da kwana biyar za'a fara jarabawa, don haka ki shirya mu koma makaranta gobe.
....kai ta shiga girgizawa, ba zan koma wannan makarantan ba.
Cike da mamaki sumayyah ta dube ta tare da fadin "ban gane ba"
"ina nufin na bar makarantar nan kenan har abada.
"u can't be serious, ta fada a yayinda take mikewa, dai dai lokacin mahaifiyar Aisha ta shigo rike da plate din pure water, daga alamu, sumayyah ta kawo wa.
....wai me ke damunki ne Aisha, ban gane ba, kince baza ki koma makarantar ba.
Nan sumayyah ta shiga yi mata surutai, ganin bata da niyar bari yasa Aisha mikewa ta shige dakin mahaifin ta.
Washe gari ma sumayyah ta sake dawowa, Amman Aisha na nan akan bakanta, don haka mahaifiyar Aisha ta ce wa sumayyah ta tafi, inn'shaa'Allah Aisha na nan tafe.
Bayan tafiyar sumayyah, mahaifiyar Aisha ta zaunar da ita.
'injin dai lafiyar ki lau ko?
Nan Aisha ta fashe da kuka...."wallahi ba kalau nake ba ummah ....wallahi ummah ba lafiya lau nake ba!
Toh me ke damun ki?
Sai da tayi kuka ma'ishi, sa'anan ta soma yiwa umman ta bayani.
Ummah wata ce me suna Rukai'yah, muka sanya ta hanyar zina, wacce daga alamu bata ta'ba sa'bawa iyayenta ba ballantana ubangijinta....tayi shiru tare da cigabawa da sheshekan kuka har sai da mahaifiyarta ta bukaci da ta cigaba da magana sa'anan.
Ganin Rukai'yah ta ki amincewa da shawarar mu yasanya ni da sumayyah muka nufi gun wani malami ya bamu magani yace mu sanya mata a ruwan wanka, da farko bamu dace ba sai da muka sauya malami sa'anan mukayi nasara ta amince da bukatanmu.
Nan ta kwashe komai ta sanarwa mahaifiyarta, da kuma yanda Rukai'yah ta koma ga ubangijinta.
Kuka take sosai...ita din ma mahaifiyar, jikin ta yayi sanyi sosai...
Ummah ba ki ganin laifinta zai dawo kan mu, don tunani na Allah ba zai yafe mana ba!
Ajiyar zuciya mahaifiyarta tayi, "ki shirya muje gidansu ki fadawa mahaifiyarta domin su dunga yi mata addu'a, ke kuma ki tuba ki roki Allah gafara, sa'anan ki dawwama kinai mata addu'a..
Cike da fara'a mahaifiyar marigayiyah Rukai'yah ta tarbe su, ta kuma kawo masu ruwan sha.
Sai da suka natsu mahaifiyar Aisha tayi mata gaisuwa sa'anan ta umurci Aisha da tayi mata bayani.
Tunda Aisha ta soma magana mahaifiyar Marigayiya Rukai'yah ta soma girgiza kai, ba tare da ta bari Aisha ta. Kai karshen magana ba, ta fita hayyacin ta.
"sam ....sam ban amince da wannan maganar, Rukai'yah ko karya bata ta'ba yi ba, Rukaiya bata taba maganar wani ko wata ba,.......Rukai'yah yarinyace ta daban, na rantse da ubangijn da ya dauki rayuwarta Rukai'yah baza ta aikata abinda kike fadi ba.!
Kuka sosai Aisha ta kai, "don Allah mama ki amince, wallahi ba da yin ta bane, asiri muka yi mata sa'anan ta amince."
Nan mahaifiyar Rukai'yah ta fusata, ta umurci Aisha da umman ta su fitan mata a gida,ta kuma gargade su da kar su sake fadan magana makamacin haka akan yarta..
Cikin kwanaki kadan Aisha ta fice hayyacin ta, kullum idan ta kwanta barci sai tayi mafarki da Rukai'yah, ta shiga damuwa, ta tsotse.... Nan ta yanke shawaran zuwa gun wani malami ta sanar masa abinda ya faru.
Da haka Aisha ta fitar da kanta daga makaranta.
Duk kokawan da take don mahaifiyar Rukai'yah ta amince, abin ya ci tura, ita kuma bata hakura ba.
*BAYAN WATANIN HUDU*
Kwance ta'ke, tana barci..... Karar wayarta ta firgita ta, ta mike a firgice tare da daukan wayar. A hankali tayi sallama tana sauraron amsa daga dayan bangaren sabida sabon lamba ce akayi kiranta da shi.
Wa'alakissalam malama Aisha kina lafiya?
Lafiya lau....!
Naseer ne!
Naseer?...daga ina?
Naseer sani da'ga paris.
Ras! Taji a kirjin ta, ta dafe kirji ba tare da ta ce wani abu ba.
Jin tayi shiru yasa yace hello are there.
Yes ta fada.
Don Allah lambar kawarki nake son ki turo mun, wanda nake dashi baya zuwa.
Shiru tayi ba ta amsa masa ba.
Hello ya sake fada.
Uhmm...hmmm....kana ina ne?
Ina abuja, jiya na sauka!
Ok, toh idan zaka iya kazo please.
Kamar ya? Lambar kawarki Rukai'yah nace ina bukata, kina fadin wata magana.
Dan Allah kayi hakuri kazo, zamuyi wata magana ne me muhimmaci.
Ok....zan shigo daga nan na ganta.
Da haka sukayi sallama ta ajiye waya, sai sabon kuka yazo mata.
Washegari tana zaune inda tayi sallan la'asar wayarta ta soma kara.
"gani na shigo gari,ina zamu hadu, direba na bai san gari sosai ba"
Toh bara na same ku inda kuke!
A hanzarce ta mike ta shirya jikinta sa'anan ta nufi hotel din da ya sauka! Ta jima tana jiransa sa'anan ya sauko.
Ranar farko kenan da ta sanya shi ido, sai dai labarinsa.
Bayan sun gaisa, yake tambayar ina "Rukai'yah?
Ta share dan guntun hawayen da ke makale a idonta....."Rukai'yah ta rasu"
Mikewa yayi yace "what??
No...no.....it can't be, no this can be true.
Sai da tayi kuka anan ma, sanan ta sanar masa abinda ya faru.
Ta kuma nemi alfarman da yazo su tafi gidansu Rukai'yah, ya yiwa mahaifiyar Rukai'yah bayani. Domin ta dunga yi wa yar'ta Addu'an samun rahama.
Bayan sun gaisa da mahaifiyar Rukai'yah, Aisha ta dube shi ta kuma dubi mahaifiyar Rukai'yah, sannnan tace mama don Allah ki bamu aron kunnenki ki saurari abinda zamu fada maki......"wannan shine Naseer" ,daga gunsa Rukai'ya take dawowa ta sami hatsari wanda yayi sanadiyan komawarta ga ubangiji.
Kukan zuci kawai takeyi, tana me girgizan kafafunta.
Naseer ya share hawayen da ke zubo masa ya soma magana kamar haka..."a ranar da na shigo najeriya na nufi hotel din da abokaina sukayiwa Rukai'yah masauki, domin kuwa ta rigani shigowa gari.
Da shike daya daga cikin yan mata da nake haraka da su ta san da zuwa na, don haka ina isa, ta iso... Dalilin kenan da ban hadu da Rukai'yah da wuri ba, sai dare.
Bayan na sallami budurwa tawa ta tafi, sai na nufi masaukin Rukai'yah don cimma burina sabida washe gari zan bi jirgi zuwa Dubai.
Bayan na shiga dakinta na tarar tayi nisa da bacci domin kuwa karfe goma a lokacin.
Na yi taku zuwa gunta tare da dafa kafadarta, nan ta mike, subhanilillah na ambata cikin zuci.
Duk rayuwata ban taba haduwa da mace kamar Rukai'ya ban kuma ta'ba jin ina son mace ba sai ita.
Ta dube ni tayi murmushi tare da fadin barka da isowa, ni ma na maida mata sa'anan na zauna kusa da ita.
Na soma shafan jikinta, a yayinda ta soke kanta kasa....na da'go mata kai hade da hada bakina da nata, sannu a hankali na raba ta da kayan jikinta, a lokacin ta soma fita hayyacin ta....sai da ina gab da cimma burina ,ta firgita hade da ture ni da dukan karfinta.
Kuka ta shiga yi sosai, me kuma ratsa jiki, ni kuwa banda kallonta ba abinda nakai.
Sai da tayi ma'ishi, s'anan ta dago ta dube ni.....'ka ji tsoron Allah, ka tuna mutuwarka da kuma kwanciyan kabari".....nan Rukai'ya ta shiga yi min wa'azi. Soyayyarta da tsinta a lokaci daya yasa na zauna ina sauraron ta, idan ba hakan ba, babu mahallukin fa ya isa yayi min wa'azi, ko ya hana niyin abinda raina ke so....sai da ta gama sannan na dube ta tare da fadin 'yanzun bazaki bani budurcin ki ba kenan?
Zan baka, amman sai kayi abinda zan fada maka.
Cikin hanzari nace 'me kike son nayi?
So nake ka sami wani limami a nan garin a daura mana aure!
What? .... Na fada cikin mamaki.
Kallo na ta shiga yi da kyawawan idanuwanta....
"toh shikenan zanyi yanda kika fada....nan nayi mata sallama na nufi dakin da abokaina suka kama min.
Tun a daren ranar na umurci abokaina da su nema mana limamin da zai daura mana aure.. A daren ranaar ban rintsa ba sabida tunanin yanda mace ta kamani lokaci guda.
Washegari misalin karfe takwas abokaina suka iso,sun kuma shaidamin cewan sun shirya komai, don haka muka nufi inda aka daura mana aure, da yardan Rukai'yah.
A ranar ta yini tana koke-koke, kukan ta ya taba min zuciya sosai.
A daren ranar na ketawa Rukai'yah budurcin ta, daren da baza ni taba mantawa ba.
Washe gari da taimako na tayi wanka, ta shirya, na kuma bata abinci taci.
Bayan ta gama cin abinci ta dube ni tare da fadin "kana iya saki na yanzun"
Na girgiza mata kai, "kece rabin rayuwata,ke matata ce.....
Ta taryeni da fadin 'yaya zaka sanarwa iyayenka da zancen auren.
Nop kar ki damu, iyayena masu fahimta ne.
Nan ta soma kuka tace "toh ni yaya zanyi wa mahaifiyata da yan uwanta bayani...?
Na matsa gab da ita, kar ki samu damuwa, zan rakaki har gida nayi masu bayani.
Ta girgiza kai, tsoro nakeji....muna cikin haka wayarsa ta soma kara, daga yanayin maganarsa da mahaifinsa yake magana.
Bayan ya gama ya dube ni tare da fadin "sam na mance zani dubai, mahaifina ne yayi kirana yace bai gan na zo ba, don haka gobe zan tafi, idan kina so sai muje tare, idan mun dawo sai na raka ki gida......
Daki daya muka kwana, har wayewar gari, sai da abokaina suka zo rakiyata airport sa'anan na raba jikina da nata da alkawarin zuwa gidansu da zarar na gama abinda zan tafe yi.
Miliyan goma na bata kash a hanu, da alkawrin turaa mata wasu cikin accnt dinta. Dubana tayi tace har yanzun baka amince akwai aure a tsakinin mu ba kenan.? Wannan kudin ka bani sune ladan saduwa ko?
A'a....please karkiyi tunanin haka, its just a gift.
Toh bazan karba ba, har sai ka zo gidan mu.
Har na fito zan wuce, sai kuma na dawo na ce ta shirya mu fita tare,sai da muka kaita tasha sannan na tafi.
Daga ranar da muka rabu na rasa farinciki, gashi nasiharta sai yawo yakai akaina,bani da sukuni, gashi lambarta baya zuwa haka yasa na yake hukuncin zuwa daukanta.
Ya dago ya dubi mahaifiyarta da idanunta sukayi jajir...'mamaki yafewa Rukai'yah...ki yafe mana! Wallahi a sanadiyanta na shiryu, na daina aikata zina!
Kuka suke sosai su duka, sai daga baya yayi masu sallama ya wuce masauki.
Naseer bai bar garin ba sai da ya saya masu gida ya kuma sayawa maman Rukai'yah mota hade da bata jari.
Read More »
Global opportunities| Business/Entrepreneurship| Fashion/Beauty| Health/Wellness| Inspirational Stories| Interviews| Guides.
Thursday, 8 November 2018
MUMUNAR KARSHE.!😥
~MUMUNAR KARSHE!😢~
Rukai'yah ta kasan ce cikakkiya. ga ilimin addini da ta boko. Ga biyayya da tausayawa.
Mahaifinsu ya rasu, a lokacin tana j.s.s3, ta na da kanne hudu, uku mata, sai dan autan su.
Rayuwa tayi masu tsanani, duk da hakan mahaifiyarsu ta kasance mace me wadatar zuci, tana kuma horon ya'yanta da su kasance haka,su kuma dunga godewa Allah a duk yanayin da suka sami kansu.
Mahaifiyarsu ta kasance tana tuyan masa tana saida wa,fatan ta,ta ya'yanta su sami ingantaciyar ilimi don haka ba ta yarda suyita tangaririya ba a gari.
Duk inda zata tafi,ko ziyara da ya'yanta take zuwa hakan yasa shakuwa da sabo a tsakaninsu.
Bata da kawaye sai ya'yanta, haka su din ma. Duk idan sun tafi makaranta ko islamiyah, Allah, Allah suke su dawo gida sun rungume mamar su.
Da haka Rukai'yah ta gama makarantar sekandiri. Ga ta da kwazo da basira, amman ba halin cigabawa sabida rashi.
Shekarar ta daya tana zaman gida bayan da ta kamala sekandari. Amman kuma bata yi zaman banza ba, sabida ta shiga haddah(al-qur'ani).
Ta kuma kasance tana suyan warah a kofar gidansu da yammaci.
Mukthar makwabcin su ne,mahaifinsu ya rasu ,su dinma talakawa ,sai dai kannensa mata uku da sukayi aure,mazajensu masu kudi ne don haka suka gyara masu gida.
Mukthar ya kan zo siyan wara a gun Rukai'yah. Ya kasance yana sonta sosai, amman bai taba fadawa kowa ba, bai kuma sanar da ita ba, ko da alama..ya barwa zuciyar har sai ya sami abin yi, sannan ya fada mata.
Wataran ya zo gun mahaifiyarsu Rukai'yah sayan wainar masa, sai yake tambayarta ya labarin makarantar Rukai'yah?
Tayi ajiyar zuciya tare da nisawa tace ..."toh ga mu ga Allah, amman ina iya kokari na don ganin ta ci gaba da karatu, sabida Rukai'yah yarinyace me kwazo...na kuma yarda ta ita.
...toh mama Allah ya shige mana...
Bayan sunyi sallama ya tafi gida.
Kwana uku a tsakani, ya sake zuwa ya sanar da mahaifiyar Rukai'yah da su kawo takardun makarantar ta.
Tayi farin ciki sosai sannan ta nemi sanin yanda zai taimaka masu.
"mijin kanwata yana daya daga cikin masu ba da 'schoolarhip, don haka nayi masa magana.'
Ba'a bata lokaci ba aka hada masa komai da suke bukata.
Bayan dan watanni ya sanar masu su kasance cikin shiri, Rukai'yah ta sami karbuwa, sai dai ba cikin garin ba. Ma'ana zata tafi wani gari makaranta.
Mahaifiyarsu Rukai'yah tayi farinci har sai da tayi hawaye. Tayi wa Mukthar godiya, tayiwa Allah godiya.Don haka suka soma shiryawa, duk da ba wani shirin kirki zasuyi ba.
Ana sauran kwana hudu Rukai'yah ta tafi, mukthar ya zo gidansu.
Bayan sun gaisa yayi mata nasiha hade gargadin cewan tasan kawayen zata bi....
Godiya tayi masa...sannan ya dauko jakka....'gashi kayan sayawa kannena suka hada maki, don students suna son saka kaya.
Nan ta sake yi masa godiya cikin farin ciki.
Yasa hannu a aljuhunsa ya ciro envilop, tare da mika mata...."ingo wannan ki kara!
A ranar sai da mahaifiyarta tayi hawaye sabida farin ciki.
Daren ranar da zata tafi ba su rintsa ba, ta kwanta lamo akan cinyar mahaifiyarta , a yayinda mahaifiyar ta ke shafar kanta.
..."mama...!
Na'am Rukai'yah....
Inn'shaa'Allah hutu zai zo maki,nan ba da dadewa ba!
Murmushi mamar tayi..."na sani, na sani Rukai'yah, nasan kalar yar' da na haifa, na yarda dake dari bisa dari, don haka fatan alkhari da addu'a kawai kike bukata....
Washe gari duk idanuwansu sunyi jajir sabida kukan rabuwa, Rukai'yah ta kasance tana tunasar da kannenta da su kyautawawa mahaifiharsu da haka suka rabu ta tafi.
Tunda ta sanya kafarta cikin makarantar, bata shiga sabgar da ba nata ba, daga masallaci sai daki... Bata da kawaye sabida bata sa ba da yin kawaye ba tun a gida, duk da tana birge wasu matan, suna kuma son yin abota da ita sai dai ta ki basu fuska.
Su biyar ne a dakinsu. Rukai'yah da wace ake kira da Fateemah sune yan' year1, 100level kenan. Sumayyah da Aisha sune yan 2, sai grace a cikin su yar' shekarar karshe ce ita.
Rukai'yah ta kasnace bata son kazanta, don haka ita ke sharan daki ta kuma zubar da datti, ganin haka yasa suka bar mata sharan dakin, ba wace keyi sabida girman kai....da alama fateemah itace kawai yar masu kudi a cikinsu, sauran kuwa yan karyane! Sai karyan arziki da samun guri.
Duk wasu ababe da akeyi a hostel ko cikin makaranta, idan dai ba ta addinin ba ce, Rukai'yah bata zuwa.
Shakatawan dare bata zuwa, so dayawa sumayyah takan gayyace ta su je party.amman sam.!
Akwai ranar da daga ita da fateemah suka kwana a daki, sauran duk an tafi yawon holewa.
Rukai'yah ta dade tana mamaki da tir da halin wasu matan university.
Idan kuwa waya suke, sai ta ji kamar ta nitse ba kamar fateemah wace babu ruwanta da yawoce yawoce, amman soyayyar waya kam,itace ta farko.
Da haka semestan ta kare, ko wacensu ta nufi gida.
A kwana a tashi hutu ya kare sun dawo. Fateemah ce kawai bata dawo cikinsu ba. Hidimomi sumayyah ta yo wa Rukai'yah, ta yo mata sabbin kaya, hade da takalmomi da jakkuna.
A gaskiya Rukai'yah tayi farin ciki sosai, hade da yi mata godiya.
Satin su hudu, fateemah ta dawo. Don haka sun ci gaba da komai as usual, Rukai'yah ce me shara.
Idan sun dawo yawon su, su sayo mata kayan dadi.
Tun bayan da sumayyah ta karanci cewan fa Rukai'yah yar talakawa ce, ta soma kunsa kanta tana bata shawarwari da ta dunga bin maza ta na sami kudi.
Rukai'yah tace sammmmmm....! Allah shi tsare ta, ita ba irin wannan kudin take so ba.
Duk da hakan sumayyah bata hakura ba,ta dunga bin Rukai'yah da wannan maganar da ga karshe Rukai'yah ta daina zaman daki, ta tare a massallaci sabida sumayyah.
Idan ta shigo daki, lallai kaya tazo sauyawa ko kuma zata ci abinci, da haka fa har suka shiga shekara ta biyu.
Duk da haka sumayyah bata hakura ba....
Wataran Rukai'yah ta shigo daki sai ta tarar suna firansu na yan duniya, sauri ta soma yi tana son ficewa, ganin haka yasa Aisha mikewa ta rufe kofa, ta juyo ga Rukai'yah tate da ta'ba mata kirji "ki rantse ke budurwa ce"...ina nufin baki ta'ba sanin namiji ba.
Cike da mamaki Rukai'yah ke binsu da kallo ba tare da ta furta komai ba, sai dai lebenta na alaman motsin neman tsari.
Gira Aisha ta da'ga mata...."sarai kin san abinda nake nufi.
Nan sumayyah ta mike, wannan bakauyar yanzun zata ce ita ustazuwa ce...ustazuwar karya!
Nan Rukaiyah ta ra'ba gefe zata fita, Aisha ta sha gaban ta.
Saurara.....wai ya ya zamuyi da ke na? Muna son mu wayar maki da kai amman gaki dai kamar wata......
Nan Aisha ta kama mata hannu ta zaunar da ita.....ta soma magana murya kasa kasa...."wai kuwa Rukaiyah kin san baiwan da Allah yayi maki kuwa?dube ki fa! Dube ki fa!...wallahi da nice me irin jikin nan naki da yanzun na sayi wannan gari.
Wannan jikin naki ba karamar arziki asset bane..
Ki dube mu daga ni har Aisha ya'yan talakawa ne kamar ki, amman da jikin mu, mun farantawa iyayen mu.
Don haka muna son mu taimaka maki mu wayar maki da kai,kema ki shiga yayi ki sharewa mahaifiyarki hawaye , ki hole rayuwarki...
Sun jima suna bata shawarwari, ita ko banda kallonsu ba abinda takeyi.
Rukai'yah ta kauracewa dakin sam....haka suka soma jin takaicinta.
Wataran ta shigo daki cin abinci, sai ta tarar da fateemah, bayan sun gaisa fateemah ta dubeta,tare da fadin "wai sabida su Aisha kika kaurace wa dakin nan?
Shiru tayi bata amsa ba,
Uhmmm.....Rukai'yah kenan! In banda abinki, matsayinku daya fa,kin zo, sun zo, ba wace tafi wata....yanda suke da iko, kema haka kike da iko don haka ki daina takurawa kanki sabida su....amman kuma kin san wani abu? A gaskiya maganar da suke yi maki gaskiyace.
Batayi mutuwar zaune ba, sai da taji fateemah tana waya da saurayinta ya shigo nijeriya don haka zasu hadu a abuja..nan da nan ta shirya kayanta ta nufi airport.
Sumayyah da Aisha basu kyale Rukai'yah ba, sai da sukayi nasara akanta.
Alokacin zata kammala shkararta ta biyu.
Naseer da' ne ga wani shahararen me kudi,... Abin kunya ne fadin irin tarbiya da kuma halayensa.
Garin yawace yawocensu suka hadu da abokanen abokan sa.
Anan ne sumayyah taji su suna firan Naseer. Daga wannan lokacin hankalin ta ya tashi, tasan dai bata jerin macen da Naseer yake so....nan Rukai'yah ta fado mata a rai,don haka ta shiga hura mata wuta har sai da ta amince da bukatar ta😔.
Sumayyah tare da Aisha suka nufi kasuwa don yi mata sayayya.
Bayan sun dawo suka dauke ta zuwa sallon akayi mata gyaran kai, da farce. Daga nan suka nufi gidan cin abinci don maganar da zasuyi da ita a sirance.
..."cikin murya Aisha ta rungume Rukai'yah.
Sumayyah ta soma magana, gobe idan Allah ya kaimu, zaki tafi Abuja gun Naseer.
Shima gobe jirgin sa zai iso najeriya sabida ke. Naseer da' ne ga wani shahararen me kudi...ya kasance yana holewarsa da mata iri iri, sai dai tun da yake harka da mata bai taba nasarar kecewa mace budurcinta ba, haka yasa yane cigiyar budurwa fil a leda, hade da alkawarin makudan kudi wanda ya iyan sayan gari guda, kingan kenan, talaucin ku yazo karshe muma zamu ci albarkacin ki.
Nan suka tafa suna darawa, a yayinda kirji Rukai'yah ke bugun uku-uku, murmushin karfin hali tayi.
Kashe gari suka yi mata rakiya har tashi, sai da motarsu ta soma tafiya sannan suka koma hostel cikin murna.
Kwanan Rukai''yah hudu kayi kiran tana sanar masu zata dawo.
Ihu suke,suna murna....suna yi mata fatan isowa lfy.
Tun da ta taso suke kira, kin kusan isowa, tace a'ah, har ta soma fadin eh...alokacin da ta iso gari sukayi waya da sumayyah ta tabatat masu ta shigo gari, yanzun zata hau adaidaita sahune ya kawo ta makaranta.
Murna suke, suna wake wake....a haka har an kusan kai awa bata iso ba, don haka suka shiga kiran wayarta....shiru ba'a da'ga bah.
Sun yi kira iya ba adadin, bata da'ga ba, nan Aisha ta fusata.....tabdi jam,renin wayau yarinyar nan take son yi mana fa!
Nan sumayyah tace banason na yarda da abinda zuciyata ke fadamin, don ko ina iya kashe ta idan hakan ya tabbata.
Ba su hakura ba, suka ci gaba da kira har sai da aka da'ga.
Ba tare da sun saurara anyi magana daga dayan bangaren ba, suka soma yarfa masifa.
..."ayyah... A dunga sassauci! Wani ya fada daga bangaren, jin muryan namiji yasa suka sassauta.
Ya cigaba da fadin "ko zan san alakar ku da me wayar,? Nan gabanyayi ras ! Suna tunanin ko yan fashine.
Da sauri sumayyah tace mu kawayenta ne.
....a gaskiya wace kuke son kuyi magana da ita tayi hatsari dazun,tirela ya fado masu suna cikin adaidaita sahu don haka, rai yayi halinsa . Jefar da wayar Aisha tayi,hade da wata iriyar ihu me razanarwa.
Ita kuwa sumayyah jikinta karkar yake,har hakoranta suna karo da juna.....
Mahaifiyar Rukai'yah kuka take sosai, ta matsa kusa da gawar yar'ta ta dafa ta....tana me sumbatu,kanenta ma haka.
A lokacin da za'a tafi da ita, a lokacin su Aisha suka iso, isowarsu ke da wuya aka fito da gawarta, ai nan Aisha ta ruga,da taimakon jama'a a ka kamata don an dauka ta haukace.
Allah sarki Rukai'yah😢😢
Lallai wannan shine mumunar karshe.....
To be continue....👌🏻
Read More »
Subscribe to:
Posts (Atom)
Designed by Jide Ogunsanya.