Pages

Friday 21 July 2017

SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫.
          By Ganarious.
6⃣
Mamee tacigaba dabasu labari,Alhaji Aliyu yayi sana'a ne akan fatan dabbobi,yana kaiwa ketare daganan har ya bude kamfanin sarrafa fstar.gunshi mahaifina ya gada.ita kuwa mahaifiyata hajiya hadiza tayi aiki a asusun duniyar(world bank)daga baya tayi resign.
Ni ce ta uku gun mahaifiyata,gun babab na kuwa ni ce ta tara.A lokacin da aka haife ni mahaifiyata tana aiki a asusun duniyar don haka a kasar tursi nafara tashi daga baya mahaifina ya amsoni ya kawo wa hajiya babba watau yar uwar zaman mamata(kishiya)..daga j.s.s.1 class na chigaba da makaranta,kamar yanda na fadamaku Allah yayimin farin jini duk inda na shiga sona a keyi,ya'yyi na, makwabta,mallaman makaranta(islamiyya da boko) duk inda na taka anaso na wasu kuma yanayi na ke burge su kawai.
Ina aji uku mamata tayi resign ta dawo gida da cikin wata biyar,munyi murna sosai,a lokacin bani da wata zance sai na cikin da kuma addu'an Allah yasa mace ce zata haifa na samu yar uwa..Mamata tayi kwana uku tana cikin nakuda,ta sha wahala sosai a lokacin da zata haihu saida akayi ta rokon Allah sa'anan ta haifi kanina Aminu,daga shi bata sake haihuwa ba..
Kamar yanda na fada maku mutane  na sona,hakan ya janyo min kiyayya daga wasu dalibai matan ajinmu.waddannan daliban basu kaunar ganina.sunce na faye salo gani ba kyau ko kuma suce daga zuwa na na amshe mutane kowa yace ni.kiyayyar tasu ma be buya ba a fili suke nuna min.Ana cikin haka akace zamuje fieldtrip excortion a lokacin muna aji hudu hudu,za mu ta biyar kenan watau 3rd term...nayi murna sosai na sanar da iyayena.mahaifiyata ce tayi min shoping domin kuwa sati zamuyi muna tafiye tafiye zuwa garuruka masu tsauni da duwatsu.
Ranar tafiya dakanmu s.s.1 students mun hallara a makaranata sai safiya ce kawai bata zo ba,safiya kawatace sosai tare muke tafiya,komai tare mukeyi.mallamai suna ta tambayata wai lafiya safiya bata zo ba.
Bani da amsar basu,sai cewa nake zata zo.munkai kusan minti arba'in safiya bata zo ba kuma ita ake jira sai p.c yace a tafi kawai idan andawo za a binciko dalilin rashin zuwanta.
   Tare da wani yaro muka zauna ana kiransa Awwal,awwal akwai surutu da barkwanci sai shairi yakemin wsi nazama abin taausayi sabida kawata bata nan toh shi zai cika gurbin ta...a haka dai yake ta zolayyata,matan ajinmu kuwa kamar sun hda baki ba me kulani koyi min magana acikin su.
  Abuja muka fara zuwa don ganin zuma rock daga nan sai ogun state don ganin olumo rock,kwanarmu uku a ogun sa'anan  muka tafi plateau jos kwanar mu biyu a nan,sa'anan sai Adamawa.
Daga adamawa sai gida,ana gobe zamu koma  kaduna aka kwashe mu zuwa wani jeji wanda ke kusa da bodan cameroon.munsha tafiya sosai a wannan jejin kowa ya gaji especially ni da daman tunda muka taho komai a sanyaye nake yi sabida rashin zuwan dafiya,na zama wata kalar tausayi.tare da awwal nake tafiya,wata sa'in kuma ya barni a baya.muna yi nisa can cikin dajin sosai sosai akace to yayi haka nan kowa ya rubuta abinda ya lura sai akoma gun motoccia shiga mukoma masaukinmu.hanyarmu ta koma wa gun motoci sai wasu daga cikinmu suka sami inuwan karkashin icche suka zauna wai a barmu mu huta,icche daman nasamu na zauna can sai ga Awwal yazo ya zauna muna hira,muna cikin hiran ne muka hangi wasu matan ajinmu tahowa inda muke,wadan nan yanmata ko magana basuyi mana,asalima idan muka hadu dasu mukayi masu sallama ba su amsawa sai harara da kallon banza.
Suna isowa sukace ayyah A'isha!ashe safiya bata zo tare da mu ba. Nace eh bata zo ba,sai suka zauna muna ta hira dasu.kamar minti uku da zuwan su abokan awwal sakayi kiranshi yatashi ya tafi.
Tashi suma sukayi wai zasuyi fitsari....har sunyi nisa da inda nake sai daya daga cikinsu ta dawo tace na taso muje mana.a a bana jin fitsari na ce mata tace toh na tashi na rakasu kar su barni ni kadai nan ban musa ba na tashi,mun tashi kenan wani malami yayi kiranmu wai mu dawo za a tafi hutun ya isa hakan,sai tace mashi fitsari zamuyi kuma saura yan uwanta na ciki bara tayi kiran su amman ku tafi kawai gamu nan a bayanku.mun isa inda sauran yan uwanta suke sukace su sunyi fitsarin ko,hafsat zatayi ne wacce ta kirani sai tace eh zatayi ta tsuguna gaba damu kadan sukuma biyun hauwa da rabi'a suka miko min wata bottle water wai ga juice na sha nace masu a a,nagode nima inadashi kuma ma bana shan zaki.sai hauwan ta bata rai,rabi'a kuma tace baza ki sha abinmu ba ko sabida baki daukemu kawayenki ba.nace bs haka bane bana shan zakine.
Toh ai bashi da zaki kisha kiji,maman rabi'a ta hada mata sabida rabi'an ma bata shan zaki.duk da maganarsu ban amshe shi na sha ba sai ga hafsat tazo ta amshi goran a hannunsu tace munason mu zama kawayenki,idan dai kina son haka kina kuma son mu da zuciya daya ki amshi kisha.
  Surutun su da kuma matsuwar barin wannan daji ya sa ni amsar goran nasha ko second ba ayi ba na fara jin idona na nauyi sai kuma na nafar ganin su Blur-blur sai jiri...duk da bana ganinsu da dakyau amma sai ina ganinsu suna dariya harda tafawa,sa'anan suka bar gurin.daga nan ban sake sanin meyafaru ba.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.