Pages

Monday 27 August 2018

Sauki a gidan ki

*~SAUKI A GIDAN KI~*
Burin mu mata,bai wuci mu gan cewan mun haskaka ✨💥ba. Musamman idan aka zo kan fata, shikenan anzo guri.
  Akwai mafi yawan matan da basu ki su kashe (kudi) masu yawa ba don ganin fatan su na haskakawa.
Wasu mata, hasken fata suke so, a yayinda wasu suke so da kuma burin ganin  fatan su sumul-sumul da laushi.
      Ko kin san da cewan akwai ababe da kike amfani da su a gida ko kitchen, ko kike sha ko ci da za su cika maki burin ki?....a maimako kashe kudi, saye sayen mayuka wanda idan mukayi la'a ko nace idan ba'a yi sa'a ba sai su bata maki fata.
Wadannan ababen da zani lissafa maki basu da side effects, ba kamar mayukan zamani ba da wasun su kam kawo cutan skin cancer sabida karfin chemical da ke tattare da su.
Idan har zaki yi hakuri,da juriyar yin amfani da su,fatarki zata haskaka💥.

Shin ko kin lura,ko kin taba cin karo da =lemon juice=, =citric acid=, a cikin ingredients din mayuka ko sabulan da kike saye?
Toh ki sani lemu🍊🍋 , yana  da matukan anfani ga fata.
Yana kashe cututtukan fata,tare da kuma haskaka fata sabida wata sinadirin da ke cikin ta da ake kira da *citric acid*🍊.
don haka kina iya yankan lemu ko lemun tsami ki matse ruwan sa kina shafawa a fatar ki.

🍅 ga tumatur.!
Jure ki dunga shafawa fatarki ruwan tumatur, ko ki nike shi ki shafa, har na tsawon lokaci.

Ina kika baro dankali🥔.!,
Ko kina da labarin cucumber🥒 yana tare da sinadari me haskaka fata?
..zakiyi mamaki idan nace maki caras🥕 da ayaba🍌, ababe ne masu karfi gun haskaka fata?

Shi ko kin san yanda zakiyi da sukari(sugar) don samun laushi da kuma hasken fata?
Akwai ababe da dama da nayi bincike akan su suke kuma gyaran da kuma taimakawa gun gyaran fata.
Ina kuma rubutu a kansu, idan kina son sani ko kowo game da su, toh ki biyo ni blog di na👉🏼 ganarious.blogspot.com/
Idan ma kina da tamabaya game da abubuwan da na lissafa, toh kiyi tambayar ki.
Ma'assalam🤝🏻

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.