Pages

Friday 3 August 2018

Taimakon kai

DA TAIMAKON KAI NA





  Da karfi ta budo kofar,sai bayan da ta shiga cikin dakin,sa'anan tayi sallama.
   Asiya,wace ke a kwance, ta da'go tana yatsine-yatsinen fuska "me ye haka kuma?"  ta fada.
"a gaskiya ya'Asiya dabi'unki suna damuna,ma'ana dabi'an ki ta sanya hotunan tsiraici a shafinki ta sada zumunta ta instagram...
Ke! Dakata!
Shiru zahra tayi tana dubanta.
''kin sa min ido,kin takurawa rayuwa ta,kin hana ni sakat. haba! Ko iyayena da nake karkashin su, sun shafa min lafiya.....ballantana ke.
Eh!...idan dai gaskiyar da nake fada maki ne sa ido, na ji na dauka don bazan fasa ba. Gaskiya- gaskiya ce ya'Asiya.ki duba fa ki ga,kin zama abin kwatance da magana a gari,kin zubar mana da mutuncinmu. Ke ce   sanya hotunan banza a instagram, ke ce me cinkoson samari har mazan aure,ke ce yawon bin kawayen banza gogaggu ko nace yan duniya...haba! Ya'Asiya kina ganin Na'imah yanzun ta soma kwaikwayon halayen ki,koma dai nace kin soma sanya ta a hanya
Toh! Sai me? Na sha fada maki da ki daina fadamin yanda zan tafiyar da rayuwata....
Nan fa zahra da yar'uwarta su ka soma mussanyar magana.suna tsaka da haka mahaifiyar su ta shigo.
''me ke faruwa" halan dai zahra ce?
Wa ne tou,idan ba ita ba! Fadin Asiya.
  Ba tare da mahaifiyarsu ta nemi sanin abinda ya hada su ba, ta rufe zahra da masifa, har ta kai ga fadin "anya kuwa ba'a sauya min ke a asibiti ba kuwa ? "domin  kuwa ni bani da sa ido da hassada,haka shima mahaifinku..Amman kin gan ki !  Ta fadi hakan a yayinda take nunin zahra da yatsa "banda bakin ciki da hassada da kike yiwa yar'uwar ki,ba abinda ke cikin kirjin nan"
Idan da sabo,zahra kam ta saba da irin haka.sai dai takan yi bakin ciki a duk lokacin da mahaifiyarta ta furta haka.
"haba inna !... Ki sani fa mu amana ne gare ki. ki daina biyewa son zuciya da rudun kyal-kyalin duniya,ki'mar mu da mutuncin mu sun fi....
   "rufe min baki"....marar kunya,ni za kiyi wa wa'azi,watau duk abinda muke yi ba dai dai bane ko ?
....toh, wabillahillazhi'!  Idan kika sake yi min magana makamacin haka, duk abinda ya biyo baya,ke kika saya.
 Allah ya huci zuciyarki inna,don Allah ki gafarta min.
  A daren ranar zahra bata runtsa ba.tunanin rayuwar da yar uwarta ta daukan wa kanta takeyi,ga kuma mahaifiyarsu da ta mara mata baya.
Ganin sai juyi takeyi a shimfida,ya sa ta mike. Ta fito tsakan gida tayi alwala sa'anan ta koma cikin dakinsu.sallah ta gabatar tare da rokon Allah da ya shiryi yan uwanta, ya kuma ganar da mahaifiyarsu.
  Bayan da tagama addu'o'in ta, wayar ta ta jawo ta shiga yanar gizo tana binciken damammaki da gwamnati ke  badawa. Cikin sa'a kuwa tayi karo da wata dama,inda gwamnati ke neman mata wadanda suke da baiwa, suka kuma iya aikin hannu.
Ganin gwamnati zata dauki nauyin su zuwa kasar waje, domin karo ilimi da fasaha akan abinda duk kayi, domin al'umma su amfana.
Ba ta bata lokaci ba, ta cike fom din akan sharada da dokokin su.
   Washe gari da sanyi safiya ta nufi dakin mahaifinta bayan da ta idar da sallan asubahi. "inakwana abba !
Lafiya lau,da fatan kin wayi gari lafiya ? Fuskar sa dauke da murmushi yake amsa mata gaisuwar.
"abba inason zani je abuja yau"
"yo me kuma zaki je yi a abujan ?
Kitso zani je yi wa wata amarya da kawayenta.
Tau Allah shi tsare.
Amin ta fada,tare da mikewa ta nufi dakin mahaifiyarta.
Bayan sun gama gaisuwa ta ce "inna ina son zan je abuja yau"
Tau ! A dawo lafiya.
Zahra tayi shiru na dan lokaci tana duban innarta...sa'anan tace "baki tambaye ni abinda zai kai ni ba"
Eh ! Sabida ni banida sa ido.
Ganin yanda innarta ta maida mata da maganar,ya sa bata ja maganar da tsawo ba. ta mike ta fice zuwa dakinsu, inda ta tarar da sauran yan uwan na ta sharban bacci abinsu.ko sallah basuyi ba. tayi siririn tsuki tare da cire hijabin jikinta..sa'anan ta fita cikin gida ta soma aikace-aikace.
Sai da ta tabbatar ko ina yayi tsaf-tsaf sa'anan ta shiga wanka bayan tayi masu abin kari.
Bayan ta kammala shirinta,ta shiga sukayi sallama da mahaifinta.

         TUSHEN LABARI
Malam Hassan mutumin suleja ne da ke jihar neja. Bagware ne kuma manomi. Ya auri Hindu wace yar asalin kasar nijar ce.
Hindu da iyayenta sunyo hijira ne da'ga kasar su,a inda mahaifinta ya samu aikin gadi (watau tsaro)wata kamfani me zaman kanta.
 Malam Hassan mutun ne me zafin nema,ga hakuri da taimako. Gashi da tausayi,domin kuwa tasauyi ce ta kai shi ga auran Hindu wace suke fama da matsanancin yunwa.
Allah ya albarkace su da ya'ya hudu. Uku mata,da da' namiji daya.
Watarana !  Malam Hassan yana shirya gonar sa, a dalilin damina da ta gabato,sai maciji ta sare shi.tun daga wannan lokacin ba shi da isashen lafiya,ga kuma rashin karfin jiki. A lokacin sai inna(Hindu) ta  dauki nauyin gida. Ta soma toya wainar masa a kofan gidansu tana saidawa,cinikin wainar masan suke chefanen gida ta kuma baiwa yara kudin makaranta.
  Asiya ce yar ta, ta fari. yarinya ce me kyan gaske,ba dan Adam da zai dube ta,bai kara dubanta a karo na biyu ba. A lokacin da Asiya ta shiga aji uku a sakandiri maza suka fara cinkoso akanta,gashi kuma makarantar su hade suke maza da mata. Dalibai har malamai,duk sonta sukeyi suna yabon kyan halittarta,haka ko ba  karamar fadada mata kai yakai ba.
A lokacin da Asiya ta shiga aji hudu,wani dalibi dan aji shida ya saya mata waya me tsadan gaske,yana kuma saya mata duk abinda take bukata.
Tunda Asiya tayi waya, ta soma yin facebook,da instagram da dai sauransu...nan da nan idon ta ya da'da bude wa, tana ganin hotunan mata wayayyu sai ta soma kwai-kwayonsu tana sanya hotunanta maza har matan suna yabon ta. Daga nan sanu a hankali ta soma sanya hotunan tsiraici wai duk sabida neman suna...cikin kankanin lokaci, ta zama tauraruwa a yanar gizo.
Da haka Asiya ta soma musanyan Addireshin ta da samari,tana basu damar zuwa ganin ta,su kuma kawo mata tsaraba. wasun har kyautan kudi suke bata.
  Ko da Asiya ta shiga aji shida,ido ya da'da budewa sosai,ta hadu da maza masu aji da kudin gaske. Ta zama sananniya,idan ka hadu da ita ka rantse yar wani minista ce.
 Hindu(mahaifiyar su) abin nema ya samu,bata kwaba mata,asalima yar ta Asiya na matukar birge ta sabida ta dauki nauyin gidan,a yayinda inna ta daina yin masan ma.
 Zahra wace da'ga Asiyan sai   ita, yarinya ce  me kwazo, ga zafin nema da tausayi Kamar mahaifinta.
A lokacin damahaifin ta bashi da karfi,innarsu kuma tana toya wainar masa, sai ta soma yin kitson kudi, watau idan tayiwa mutun kitso, sai ana biyaa,dan abinda ta samu sai ta baiwa innarta a hada a yi cefanne. itace kuma mai taimakon mahaifiyarta saida wainar,ba kamar Asiya ba, wace aikin ta bai wuci tayi wanka, ta ca'ba ado, ta fita zuwa gun kawaye suna zuwa yawon shakatawa.
  Wannan abinda Asiya takeyi, yana matukar batawa zahra rai. Tayi ban shawara,da nasiha akan Asiya ta daina yawon bin kawaye, a duk lokacin da ta soma bata shawara, toh fa !  Sai anji kansu. ita kuma mahaifiyarsu ta goyi bayan Asiya,tana me gargadin zahra da ta fita hanyar Asiya.
Mahaifin su kuwa bashi da ikon magana,sabida tas !  Inna take zaginsa tana tunasar shi bashi da bakin magana sabida bashi iya daukan nauyinsu ko ciyar da su. don haka,shiru yake yi duk lokacin da yaji hayaniyar zahra da Asiya.
  Na'ima wace daga zahra sai ita,yarinyace da bata wuci shekaru goma sha biyar ba. Itama din fara ce kamar Asiya.kusan komai nasu iri daya da Asiya. Zahra ce baka a cikin su, sai dai ba'a bar ta a baya ba a kyau. ta kuma fita daban cikin su sabida halin Asiya iri daya ce da ta na'ima koma nace Asiyar ce ta sa na'ima a hanya.
 Zahra ta kasance tana sha'awan da son yin aikin hannu.duk wani abu da ya shafi kirkire-kirkire ko ka'ge da hannu tana zumudin koyansa. Haka yasa ta soma koyan din.
Kudin kitso da ta tara,ta sayi waya madai'daici,ba ta komai da wayar,iya bincike-binciken ababe da zata karu dasu...da wayarta ta koyin yin sabulun wanka,wanki da mayukan gashi da ta jiki da sauransu.da kudin kitson ta ta ja jari ta soma yin sabulan wanka masu gyaran fata tana saidawa. A wannan lokacin zahra ta bude shafi a facebook,da instagram tana me tallace-tallacen sabulan da takeyi. Ta karfafa bincike akan gyaran fata,cikin kakanin lokacin ba tare da ta tafi makarantan gyaran fata ba ta kware a dalilin wayarta.
Mahaifiyarsu zahra(inna) tana matukar bakin cikin zahra har tana kiran ta da yar' wahala,sabida taki bin hanya mafi sauki domin samun kudi.

  Kwanan Zahra biyu ta dawo da'ga Abujan. Cike da farin ciki ta shigo gida.kai tsaye dakin mahaifinta ta nufa. bayan sun gaisa yayi mata marhaba da zuwa, ta ce "abba nayi wa amarya da kawayen ta kitso,kuma sunyi min alkhairi,dubu dari fa suka bani."
Cikin farin ciki ya sanya wa kudin albarka.
Ta mike ta na fadin abba yau romon danyen kifi (fefesuf din danyen kifi) zani yi maka.
Ta nufi gun inna ta sanar da ita abin alkhairin da ta samo.
Cikin bata fuska inna tace "kamar wani abin kirki kika samu, wannan a gun yar'uwarki,ai chanji ne"
Jiki a sanyaye Zahra ta bar gun inna. A dare ranar,sai da ta ware dubu goma tayi masu fefesuf(romon) danyen kifi.
Washe gari sauran kudin ta dauka taje ta sayi keken dinki.
Sai dai kash ! A ranar bata sha ta da dadi ba,sabida Asiya ta dau alwashin zahra baza ta ajiye keken dinkin a dakin su ba,sabida karansa zai dameta,uwa'uba zai bata masu tsarin daki.
Inna me taya bera bari,ta ari ta yafa.sai masifa take yi tana kiranta yar'wahala, wai zahra ta wuci matsayin da ta zama tela.
 Ganin sun hade mata kai, yasa ta dauki keken zuwa dakin mahaifinta. nan ya shiga lallashin ta.
A hankali ta soma kwarewa..bayan da ta kware ta soma sayan yadi da cinikin sabulu da ta kitso.
Sai tayi dinke-dinke tana sanyawa a shafinta na instagram da facebook, tana kuma kaiwa garin abuja idan sun gayyace ta zuwa yin kitso.
  Watarana tana zaune tana hade-haden sabulai, kwatsam sako ya shigo wayarta, tana dubawa ta gan cewan wannan fom din da ta cike watannin baya ne,inda ake sanar da ita tana daya daga cikin wadanda aka zaba zuwa kasar ingila. Iyaye da abokan arziki sun tayata farin ciki,da kuma fatan alkhairi.
      BAYAN WATANNI TARA
Bayan watanin tara Zahra ta dawo da'ga kasar ingila. nan ta tarar da abin mamaki, domin kuwa ga baki daya gidansu ya sauya ka rantse gidan wani hamshakin me kudi ne. Da ta tambayi inna wane ne gwanin yi masu wannan hidiman ,sai dai me !  Inna ta rufe ta da fada.
Ta shiga gun mahaifinta ta tambayeshi, nan yake sanar mata wanda zai auri Asiya ne yayi masu wannan jigilan.
  Bayan watanin biyu da dawowar Zahra gwamnati ta ba da guri zahra na koyar da mata duk wani abinda ta koya daga can kasar ingila,sa'anan ana biyar ta.
Sannu a hankali Zahra ta soma zama tauraruwa domin kuwa kasuwancinta ta daukaka,ga masu koyi da ita. Nan maza suka soma kawo kai,sai dai ba wanda take kulawa haka na kara batawa inna rai,tayi masifa tayi masifa zahra bata saurareta ba.
Saurayin da Na'ima take so ya fito yace  shifa ya shirya aure,Zahra ba ta so ba, amman da shike bata da baki a gidan, ba yanda ta iya don haka aka soma shirye shiryen bukin Na'ima.
Alhaji salis mazaunin Abuja,wanda ke matukar kaunan Asiya shi ya dauki nauyin komai na bukin,shi ne kuma wanda ya gyara masu gida.
Bayan sun aurar da Na'ima,ya rage Asiya da zahra,duk da kokarin da Alhaji salis yake yi,bai sa Asiya ta natsu ta tsaya gareshi ba,sauya samari takeyi kamar kaya.
Kwance suke Asiya na waya...bayan da ta gama waya Zahra ta dube ta tace '"Ya Asiya"
Duban zahran tayi ba tareda ta amsa ba.
"don Allah ki natsu mana,ki daina yaudaran kanki da wannan kyan halittan da Allah yayi maki..
 Ba tare da Asiya ta bari ta kai maganarta ba,ta soma yi mata masifa.
Suna tsaka da haka wani yaro yayi sallama.
Zahra ce ta dubo shi..."wa kake neme ?
Ana sallama ne da Anty Asiya.
Jeka,gatanan zuwa.
 Bai fi minti goma da fitar Asiya ba,Zahra to soma jin hayaniya da'ga kofar gidansu,cike da mamaki ta sanya hijabi ta nufi zaure. Tana fita tayi riski Asiya kwance kasa a yayinda dai dai lokacin wasu mata suka shiga mota ,sukayi tafiyarsu.
Cikin rudani ta duka tana duba yar'uwata wace ke nishi sama sama ta ruga cikin gida tayi kiran innarsu,dagan nan sai asibiti.
 Satin Asiya biyu a asibiti aka sallame ta,amman kash !  Matan nan sunyi mata illa, domin kuwa sun watsa mata wani abu me cin fata ,a fuska,sai dai sa'anta guri kadan ya taba.
 Washe gari bayan an sallamo ta daga asibiti,zaune take tana kukan takaici a yayinda kawayenta da suka zo dubiyarta suna ta aikin ban baki da hakuri.
Zahra na tsakan gida tana hade-haden sabulu sai kwatsam yan sanda suka kunno kai tare da wata mata biye da su. tana ganin su ta nufe su tana tambayar lafiya ? "ke ce Asiya ?
Kai ta girgiza,dai dai nan innarsu ta fito daga dakin ta "Asiya bata nan" ta fada.
Matar da ke bayan yan sanda ta soma masifa..."ku tafi da wannan din,idan sun kawo Asiyan, sai ku sao ta"
 A'a.....mahaifinsu ya fada a yayinda ya iso gurin da rarrafe.
Duk suka juaya suna dubansa..."sai dai ku tafi da mahaifiyar Asiya din, ga ta !  Ko kuma ku bincika gidan,na tabbata tana nan ba inda ta tafi.
Nan yan sanda suka soma bincike,suna shiga dakin su zahra suka riski yan mata zuru zuru,amman ba Asiya,sunyi sunyi da su da su fadi inda Asiya take suka ki fadi,.nan matar ta hasala "ku tafi da su duka,idan ankawo Asiyan sai a sako su. Jin haka yasa wata daga cikin su ta fadi inda Asiya take,don haka yan sanda suka fito da ita suka tafi da ita.
Tashin hankali gun inna har zahran ma. Zahra da inna sun nufi folis station din da aka nufa da Asiya don jin laifin ta.
Nan yan sanda ke sanar dasu wannan matar, matar Alhaji salisu ce,saurayin Asiya. Kuma Alhaji salis yana hannun hukuma an tsare shi sabida satan kudin da yayi,matar sa kuma ta matsa masa da ya fada mata abinda yayi da kudi, ya kuma shaida mata Asiya ya kashewa kudin don haka tana bukatar a biya kudaden sama da miliyan goma
Dafe kirji inna tayi a yayinda Zahra tayi siririyar tsuki...ina ta juyo ta dube ta.
Dai dai nan matar Alhaji salis ta shigo. zahra ta dube ta tace "kina da wata shaida cewan ya baiwa Asiya kudi ?
Ba sai na nemi shaida ba,sabida mijina ba zai yimin karya ba.
Toh shikenan naji,zamu hadu a kotu kenan,har cin zarafi da kika  yi mana sai kinyi bayani. fadin zahra
Ta juya ta rike hannun mahaifiyarta suka fice.
Bayan sun koma gida zahra ta fashe da kuka "Abinda nake hangowa kenan inna, ki dubi yanda mutane ke kallon mu yanzun da muke dawowa ? Sunayi mana zunde.
Toh meye mafita yanzun ?    
Wallahi ban sani ba...fadin Zaha.
Tau meye sa kika cewa matar na za'a hadu a kotu ?
Uhmmm....kar ki damu,na san abinda nakeyi,koda ta amince mu tafi kotun,zamu tafi din sabida ba wata kwakwaran shaida da zata bayar cewan Alhaji salis ya baiwa Asiya kudi fiye da miliyan goma.
Humm...toh shikena.
Mahaifinsu da ke sauraronsu yayi gyaran murya, ya soma gargadin Zahra da ta cire hannunta a sha'anin inna da Asiya.
Cikin ikon Allah Zahra tayi ta fadi tashi don ganin an sako masu yar uwa,cikin sa'a kuwa Asiya ta fito.
 Zahra ta cigaba da gudanar da harkokin ta da sana'aoin ta,ta zama daya tamkar dubu.

Suna
-Aisha M. Gana

Copy/paste

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.