Pages

Friday 29 June 2018

Page 7of KAZAMA CE MATATA

💖💖💖💖
*KAZAMA CE,MATA TA*
           💖💖💖💖
Written by Ganarious✌🏻
     7

√...One love keep us 2geda, masu bin wannan labarin.

√... @ mss-ganarious (instagram)

√...ganarious98@gmail.com
√...ganarious book series (facebook group)
√...ganarious.blogspot.com/
        Duk zaku iya droping comments dinku, a daya daga cikins👆🏼,thanks

     **       **       **       **
Bayan kwana uku da kawo wa suwaiba kayan shayi,kwance take a doguwar , sai sharban bacci take abinta, kai da ka gan ta kasan bata da damuwa, lau lau take.

Daga bakin kofa yake kwada sallama,ganin ba'a amsa ya sanya shi kunno kai,sabida kofar a bude take.

Duban falon yakeyi sama da kasa,sai da ya gama kallon falon tsaf, sa'anan ya nemi guri ya zauna, tare da tsira mata ido.
Ya jima zaune,cike da takaicin yanda ya tarar da gidansa.
A hankali ta bude idanunta, dai kan nasa...ta saki murmushi tare da mikewa zaune...."laaahhhhh, zuwa ka kenan muniru?

Fuska tamke ya ke kallonta ba tare da ya amsa ba.
"sannu da isowa ta dake fadi"
Nan ma bai amsa ba.
Ganin haka yasa ta mike...."bara  na kawo maka ruwan sanyi ko?
No... No....koma ki xauna muyi wata magana.

Xama tayi tana dubansa.
"ko kina iya tina maganar da na fada maki, a lokacin da kika zo nan gidan?

Eh kwarai......
Toh fadi naji, me na fada maki.

Cewa na kayyi na dunga sallah akan lokaci.
Da me kuma?
 Kacce kuma baka kaunar kazanta.

Toh meye sa kike kazanta?
Ni yaaaa......ta fadi hakan dafe da kirjin ta.

Kallon ta kawai, yake ba tare da ya ce wani abu ba.
"kazantar mi nayi halan, daga dawowarka sai ka lakarmin cewan ina kazanta?  ...dubi falon nan fa fes fes na share ta.
Duk ko wane sako na share sa'anan ka dube ni kace ina kazanta? Amman dai kam baka da godiya.

Keh....ya fada a tsawace a yayinda yake dakatar da ita,...."idan bikiyi hankali ba, zan maida ki gidanku...shashasahhah,duba fa ki gan yanda kika maida min gida,? Inai maki  magana kuma kiyi min fitsara?
Mikewa yayi a fusace ya nufi sashensa.

Bata sake sanya shi a ido ba, sai washegari da safe ya dawo daga massallaci sallar asubahi.
Tana ganinsa ta gaida shi.

Shi kuwa gogan da kyar yake   amsa mata gaisuwat.
Kai tsaye dakinsa ya wuce.....kamar kullum, yayi azhar da karatun al'qur'ani me girma sa'anan ya sanya kananan kaya ya fito zuwa kitchen.

A nan ya tarar da abin mamaki....a hanzarce ya nufi sashen ta cikin bacin rai.
Kwance ta ke, da ka gan ta kasan bata da damuwar komai.
Da tsawa yayibkiran sunanta
A firgice ta mike tana me murzan idonta.

...."me ke damun kwakwalwarki? Ke wacce irin mace ce?....watau ke baki jin magana ko?  a jere yake wadanan maganar,ba fusstop ba comma.

"mi na na kuma nayyi?
Ya sa hannunsa, ya riko hannunta ya me janta da karfinsa,saura kiris, ta fadi
Kitchen ya nufa da ita... "what's this? , what's all this, for God sake.

Ni fa ban gane mi kaka nufi ba,ka fada min laifin da nayyi...wanan tsawon yana bani tsoro.

Lumshe idanu yayi, tare da yin ajiyar zuciya.
A hankali ya bude su, sukai ido hudu, domin kuwa itama shi din take kallo.

Dubi nan.....ya nuna kasan kitchen,inda ta hasa murhu.
Duban gurin tayi, sa'anan ta da'ga ta dube shi suka sake hada ido.
Sun da'de suna duban juna, sa'anan ta nisa yace inda nake girki kenan.

Wannan kitchen din yayi maki kama da inda ake girkin itace?

'"yo shin ina na zaniyi girki,shin ba kai na kaccemin  dakin girki ba ne kenan?...ita din cikin bacin rai take maida masa,don ganin itace mai gaskiya

Ya kai kimamin minti uku, ya na dubanta sa'anan ya saki hannunta.
Murya kasa kasa yace "suwaiba"

Na'am...
Kina kallon fim ko ta hausa, ko kuma ta yan yare kamar ta indiyawa?

Sosai ma kuwa ina kallon su.
Kina ganin dakin yin girki a fim din da ki ke kallo?
Kwarai ina gani.

Kin taba ganin kitchen makamacin wannan?
Eh...amman a fim din turawa nake ganin irinta.

Yawwa......toh a fim din da kike ganin wannan irin kitchen suna girki fa itace?

Shiru tayi, tana dubansa...
Ke nake sauraro!

Toh ni wallahi, nayi nayi abin can ya kunnu, ya kiya.kuma yanda ka nuna min hakan nayi, ganin bai yi ba, shi yasa na hasa murhu.

Ajiyan zuciya yayi....ya tina shi din ne bai nuna mata yanda ake kunna switch din gas din daga cylinda ba.

Toh naji wannan.....mi ye sa baki tsaftace gurin ba, bayan da kika gama girkin? Duba fa  ki gani gurin nan bashi ba banbanci da bola,ya na maganar ne a yayinda yake nunin gurin da yatsa..ledan maggi,bawon albasar da ya'yan tattasai, har da kamu-kamun tawaska da ta diddiga a gurin Da sauransu.

Niyah ta yau na kwashe su.
Cikin girgiza kai yace..."kar ki sake.!! Daga yau kafin ki fita a kitchen, duk wani abu da kika yi amfani da, da gurin da kika yi girkin,toh ki tabbata kin tsabtace su....kina ji na?
Awo..... Ta fada.

Hannu yasa ya rike kunnensa,..."duk ranar da na sake ganin kitchen din nan a haka, a ranar bazaki kwanan a wannan gidan ba.kinji ko?

Mi na na yayyi zafi haka, bazan ma sake ba, balle kace na tafi gidan mu.

Nan ya shiga kwasan itacen, da dutsinan.
Sai da ya tabbatar da kitchen din yayi fes, sannan ya fita.takaicin sa daya, tiles din  indabta hasa murhun ya kone,sai yayi daban da sauran.

Kashe gari bayan ya gama Azkhar  dinsa,yayi wankan sa, sai da ya shirya tsaf,sannan ya fito rike da brief case dinsa.
Zama yayi gurin dininng. Shiru shiru, bai ji motsin ta ba,don haka ya mike zuwa kitchen.
Daga alama, ba a shiga kitchen din ba ma.
Ya karasa  ciki,ya zuba tuwa a kittle ya kunna.
Tsaye yayi yana me jiran ruwan yayi xafi.
Kofi ya dauko, ya dan dauraye tare da zuba ruwan zafinsa,ba yan da ya yi zafi.
Ya dauko kofin zuwa gun dininng table, inda kayan tea suke.
Ya dauko madara da bonvita ya bude marfinsu, nan mamaki ya rufe shi.
Ya karkada kai, tare da fadin Allah yayi mana sauki.
Ya xuba madara da bonvita a kofin ruwan zafin ya karkada,ba tare da ya hada da burodi ba ya kafa kofin a baki, sai da ya shanye, sanan ya sauke kofin.

"Ahhhh....Alhamdulillah, ya fada a yayinda ya mike zuwa kitchen din,ya wanke kofin ya maidashi inda ya dauko sannan ya fito zuwa office.

Da isan sa office abokan aikinsa suka soma zolayansa.
Wasu na fadin ango ka sha kamshi...wasu na fadin ka sha mai da dai sauran su..
Zuciyarsa ta kusan tsagewa, a lokacin da wasu ke fadin "yaushe za mu zo ganin amarya,mu kuma ci girkin amarya?
 Dariyar ya'ke kawai yakai, a zuciyar sa kuwa fadin yake "tabbas ajina zai zube, idan suka zo suka gan irin matar da na ke aure.

Gidansa ya nufa, bayan da ya tashi daga gun aikinsa.
Kwance ya tarar da ita, wannan karon idon ta biu, ma'ana ba bacci takeyi ba.
Tana ganinsa ta mike zaune...."barka da dawowa ta  fada.
Yawwa, ya maida mata a yayinda ya nufi sashen sa.
Mikewa tayi zuwa kitchen, jim kadan ta fito rike da kulan abinci ta ajiya saman tebur.
Ta koma cikin falon ta zauna.ta kai kimamin minti goma zaune, bai fito ba, don haka ta nufi hanyar sashen sa.
Karo na farko kenan da zata shiga dakinsa.
Da sallamarta ta bude kofar,ba tare da ta jira amsa ba, ta kunsa kai.
Ganin bashi cikin dakin yasa ta karasa gun gadon sa,ta shiga ta'bawa tana shafansa,daga nan kuma ta daga kai tana me duban ilahirin dakin.
Waigowar da zatayi gefen hagunta, yayi dai dai da fitowarsa daga bayi.
  Daure yake da tawul,iya gwiwansa.suna hada ido, ta kau da kai tare da sanya hannunta ta rufe ido...don Allah kayi hakuri, walle bansan cewan kana bayi ba, daman na zo ne na  fada maka cewan abincinka na bisa tebur na ajiye.

Tsaye yayi yana kallonta ba tareda ya ce wani abu ba.
Ya ratsa ta gefen ta zuwa gun wardrob nasa, yar karamar tawul ya ciro.ya shiga goge kansa da jikin sa.

SUWAIBA hooo.....wai fa idan ta a rufe ta ke tafiya zata bar dakin.
Bata ankara ba tayi karo da wata kyakyawan tebur, me tsawo.gefen teburin wata yar doguwar gunki ce ta ado..wannan gunki duk da gilashi aka kerata, don ya zama wa engr. Munir madubin dubawa..
Bayan da tayi karo da teburin, ita kuma teburin ta shike akwai taya a kasarta don haka tayi tafiya zuwa  gunkin,ta buge ta..
Nan gunkin tayi batun fadoea suwaiba, tsaye tayi bayan da taji cewan ta kauri abu...ba ta kuma bude idonta.

Ganin abinda ke shirin afkuwa ya sanya shi barin gun wardrob dinsa a guje har tawul din jikinsa ya sulbe.
Kafin duk gunki ta fadowa suwaiba,ya rikota da karfinsa ya janyo ta jikinsa suka fadi.
Tas...tararassss kawai kake ji,gunki ta tarwatse.
Sai a lokacin suwaiba ta bude idon ta,ta gan kanta a jikinsa.
Kokari take ta zame jikinta daga nasa, tana mikewa ta gan ba bu ma tawul din a jikinsa, ...."subhanalillahi ta fada da karfi a yayinda ta rintse ido tana sauri zata bar dakin.
Fisgo ta yayi..."keh...ya fada a tsawance,ke wace irin marar hankalice,ba ki ganin gilashin da suka tarwatse a kasa.
Idon rufe kika yi sanadi,yanzu kuma idon ki a rufe kike son fita daga dakin don ki yiwa kanki illa ko?
Read More »

Monday 25 June 2018

Page48 of SOYAYYAR MU

*SOYAYYAR MU👫*
         By Ganarious
Page4⃣8⃣

  Sannu a hankali, shakuwa me karfi ta fara shiga tsakanin ilham da nura.

Ilham yarinya ce me fasaha da basira,da zaran ta fara abu, ko da ranar ce farkon farawar ta, sai ka gan ta gwanance.
Duk wani activities na makarantan, tana participating...hakan yasa tayi suna cikin kankanin lokaci, ba a makaranta kadai ba har sauran universities da suke kasar ladon,domin kuwa dayawa mutanen kasan da dalibai mamaki sukeyi wai bakar fata, daga africa itace *miss king's college*...wanda a tarihin wannan makaranta,basu ma baiwa bakin fata daman yin contesting ballantana a zabe shi
Sai kan ilham,kuma mafi abin mamaki wai yar'year one.

Muslim students activities organization(M.S.A.o), wanda mu anan nigeria, mu ka fi sani da (M.S.S),ta makarantan kings college sunyi marhaba da hidima da gudumuwar da ilham take bada wa,a dalilinta yan mata da dama sun soma zuwa gurin taron M.S.A.o, sabida hikima da takan yi anfani dashi idan zatayi tunatarwa.wasu kuwa sabida jin dadin kira'an ta suke hallarar gurin.

Shuwagabannin M.S.A.O, malamai da dalibai sun zauna yin meeting akan cewan wai ko za'a baiwa ilham Amiran makarantat....amman kuma akwai wace take rike da mukamin kuma yar aji biyu ce.
Wasun su sun hangi rashin adalci, idan akayi hakan duk da abinda ilham take gudanarwa a wannan organization din, Amiran bata yin rabinsa.
Ganin ba wata mukami da zasu bata, yasanya sunyi tunanin kirkiran mukamin da babu shi kuma wanda zai zo daya da ta Amiran, don nada ilham da wannan mukamin.

A haka ilham ta cigaba da haskawa a kings college ,duk inda ka shiga ilham,wasu suce kanwar ameer ,ba bu ranar da za'a wayi gari mutane biyu ko fiye da hakan basu yi mata zancen Ameer din ba,don haka ta matsu ta gan wannan Ameer din.

Da haka har aka shiga semestern karshe,daga wannan semestern zata shiga shekara ta biyu.
A yayinda daga wannan hutun za'a tura su nura training.
A wannan semestan ne kuma wadanda suka tafi training din zasu dawo makaranta.
Wata daya ilham tayi a gida nigeria,sa'anan ta koma kings college.

A satin da tayi resuming, ta fito lectures sai ta nufi department dinsu kawayenta watau naziha da Amarah.
Daga nesa ta hange su zaune, a saman kujerun da aka tanada don zaman dalibai.
Tana zama ta soma nishi sama sama....'yunwa'.....wayyoooo cikina,yunwa nake ji
Dariya suka shiga yi mata sabida yanayin da take maganat
"yusrah ta tafi nema mana abinci".....cewan Amarah,tana gama fadin haka,,, wasu gayu kuma dalibai suka iso gurinsu da sallamansu,daga alama musulmai ne.

Dukkaninsu idonsu na kan ilham,a yayinda suka nema guri suka zauna.
....'"Ammmmm.....don Allah tambaya muke,daya da'ga cikinsu ya fada yana duban ilham.
Bata amsa ba, sai ta'be baki tayi, tana dubansa.

Hakan ya bashi daman cigaba da maganarsa..."don Allah ke kanwar Abbakar ce?
Yau kuma da abbakar nayi kama?......oh ni! Wannan fuskan tawa me kama da ta mutane,mutanen ma maza wai....
Abbakar deen fa nake nufi.
Daga Ameer,yanzun kuma Abbakar.....ta fada tana me tafa yatsunta.
Nan su naziha suka fashe da dariya.
Dubansu tayi tace "ni ba kanwar Abbakar bace,asalima nice ta farko a gidanmu.
Cikin rashin yarda da maganarta waninsu ya fiddo wayarsa yayi kira....jim kadan akayi picking daga dayan bangaren.
Dukkanin mutan gurin suna jin abinda ake fadi a wayat,sabida loud mode ya sa.
....."guys how far"daga dayan bangaren ake fadin hakan.
""amman ka cika dan iska, ashe kanwarka ta sami addmission a nan kings din shine baka sanar da mu ba.

Wa ce ce kenan?

Ji ka da wata tambaya kuma? Wace kanwarka ke nan kings?

Kai.....wannan maganar banza kake fadi, ni fa na gaji da tambayoyin mutane,tun da muka yi resuming wasu ke kira na a waya suna tambayata......wai yaya yatinyar nan take?

Shiru sukayi gaba dayan su....."kana nufin kace ba kanwarka ko cousin dinka da aka kawo kings college?

Babu....ya fada a takaice,da haka suka shiga yin hira suna tambayarsa yaushe zai dawo.

Bayan. Sun gama waya da abokinsu,wanda suke ikirarin ya na kamah da ilham,suka mike tare dayiwa su ilham salllam da kuma ban hakuri.
Bayan sunyi nisa naziha ta dubi ilham tace...'ai kuwa yayan naki akwai cool voice"
Dariya su sake yi a karo na biyu.

A ka'idan kings college ko nace department din da ya shafi masu yin karatun fatan dan adam. A ko wani karshen semesta suna gayyatan manyan likitocin fata,da kuma malaman university daga kasashe daban daban,domin su zo su baiwa dalibai shawarwari.

  Ranar jumma'a, ita ce ranar da dukkanin dalibai, ma'ana daga ajin farko zuwa karshe za su hadu a babban dakin taro ta makarantan kings college domin sauraron shawarwarin wadannan mutanen da hukumar makaranta ta gayyato.
   A ranar ilham ta wayi gari da matsanancin ciwon mara, don haka ta yanke cewan baza ta halarci wannan taron ba.
Hidayat wacce suke daki daya,kuma department daya, ta kammala shirin ta tsaf. Duban ilham tayi tare da fadin "tashi mana ko a dad-dafene mu tafi"....

"ki tafi kawai ,bazan iya zuwa   ba"
Toh shikenan,Allah ya baki lafiya,ni na tafi...
Bayan da Hidayat ta fita daki, kai tsaye dakin su naziha ta nufa domin sanar masu halin da ilham take ciki.

Lafiyayyan abinci suka shirya mata, sa'anan suka nufi dakin ta rike da magunguna.
Kwance take tana bacci, Amarah ta sa hannu ta tayarda ita...."tashi ki yi breakfast ki sha magani,ki yi wankanki sai ki koma ki kwanta,
Da taimakonsu ta mike zaune,suka shiga bata abinci a baki....uhmmmm ilham yar'gata son kowa.

Bayan da ta gama ci,ta sha magani sai ta dan jingi ne da bango, jim kadan ta mike kamar wace aka tsakala.
Ta fada bayi tayo wanka sharp sharp,tana fitowa ta bi jikin ta da madarar turare ba tare da ta shafa mai ba.
Doguwar riga me kyaun gaske ta fiddo ta sanya a jikin ta,sa'anan ta bi lebbanta  da tsadaddiyar lip-balm dinta da take ji dashi.
Bin ta kawai da ido su naziha suke, sai da suka gan ta dauki jakka, sa'anan amara tace ba'a shafa mai ba, balle powder.

Kar ku damu....see u guys later ta fada a yayinda take hanzarin fita daga dakin.


Toh jira mu mana,muyi maki rakiya....cewan naziha.

Nop.....na hutassheku.

Sauri saur, gudu gudu takeyi, tana me nishi sama sama.
Daga wajen dakin taron take jin jawabi, daga alama, ba'a jima da farawa ba.

Tsaye tayi tana huci tukun,tana me busar da iska daga bakinta.
Sai da ta sami, natsuwa sa'anan ta kunna kai dakin taron.
Ta ko'ina jama'a, duk sunyi occupying kujerun, sai waige waige takeyi tana neman inda babu wani ko wata amman kuma a gaba,sabida ta ki jinin zaman baya,kuma kujerun bayan ne kawai. Empty.
Tana waigowa gefenta, ta hangi wasu empty kujeru a layi na uku, don haka ta nufi gurin.
Kafin ta shiga can inda empty seats din suke,dolenta ta bi gaban wasu dalibai domin kuwa kujerun a tsakiya suke.

A hankali ta dunga furta excuse me, su kuma suna janye kafarsu don bata damar wucewa. Da shike dayawan su sun waye ta,wadannda kawai basu san da ita ba sune wadanda suka dawo daga training.

Mutane hudu zuwa biyar da suke zaune daga farkon layin sun janye kafarsu don ta sami damar wucewa,da haka ta gifta ta gabansu tana fadin excuse me,idan kuma ta gifta sai tace thank you.
Da haka ta isa ga kujera ya shida,inda ba kowa zaune nan,ta so zama anan din, amman kujerar ta biyar da ta bakwai duk maza ne ke zaune akansu, don haka ta yanke shawaran karasawa can karshe inda ta hangi mace zaune.
Tana zuwa ta kujeran ta bakwai tace "excuse me"...ta dai gan sa'anda ya daga kafarsa,ta zo dai dai gaban sa zata gifta sai ta jita a kasa tifff....
"ta da'go tace masa oh sorry"....sa'anan ta mike ta karasa ta zauna.
Tana zama abinda ya faru ya soma dawo mata.....amman dai kamar kafa ya samin fa,da saninsa kenan,,don har ina ce masa sorry maimakon ya amsa sai kawai, ya da'ga min gira har da murmushinsa....nan zuciyar ta shiga rayamata cewan da saninsa ta fadi
Ya ja tsaki tare da mike wa a hasale ta dauki jakarta.
Ta nufi gunsa, tana isa ta daga jakar sama ta kwada masa a. Kai
Nan hankulan kowa ya dawo kansu,duk kowa ya da'go yana dubansu.
  "dan iska kawai"....ta fada rai bace,shi ko banda kallonta, ba abinda yake yi.

Doctorn da ke jawabi,yai shiru yana duban su, nan daya daga cikin malaman kings college ya mike..."the both of you should walk out of the hall"
Read More »

Sunday 24 June 2018

Real 47 OF SOYAYYARMU

*SOYAYYAR MU👫*
        By Ganarious.

<><>Assalamu'alaikum yan uwa maza da mata. Inayi mana barka da shan ruwa,barkan mu da Sallah, ubangiji Allah shi karbi ibadun mu, shi amsa mana addu'o'in shi biya mana bukatocin mu shi kuma sakama mana da gidan aljanna...Allah ya nuna mana watannin ramadan masu zuwa(cikin raai da lafiya)
Allah ubangiji shi maimaita mana.
*Allahumma ameen*

*BARKAN MU DA SALLAH*🤝🏻

<><>special greetings to ganarious.blogspot.com/ followers and visitors💞

<><>makarantan soyayyarmu i heart u all.

<><> *Faty bayero*
          *Nazee yareema*
           *Hidayat yusuf*
           *Zuwairah shehu*
            *Rukky dogon daji*
             *Sis Salfat*
             *baby hajara*
              *haj. sa'adat mubi*
              *Aisha gana(namesake)*
*ganarious book series members*
*Hausa novels groups members*
Da sauran wa'anda Allah be bani ikon rubuta sunayensu ba,special greetings to u all.

*Mutan kenya ban mance ku ba,one love keep us 2geda*💞🤝🏻

        Page 4⃣7⃣(real)

          TUNA BAYA..
Aishah mustapha Buba, wace muka fi sani da ilham haifafan garin kaduna ce.

Ilham yarinya ce me kyan gaske,ga ilimin addini da ta zamani.
Ga kyan tarbiya da hali.
Babu mahalukin da zai kalli ilham,bai sake kallonta karo na biyu ko fiye da hakan ba.

Surar da ki'ran jikin ta kawai abin kallo ne ballantana  a kai ga fuskarta.

Fadin malam bahaushe '"mutum dan tara ne,bai cike goma ba"...toh tabbas akan ilham zani mu'sa wannan maganar domin kuwa ta cike goman,har ta goce.

Duk abinda ake so ga macen kirki da nuni ilham ta hada.

  Bayan mutuwan auren iyayenta suka rabu.
Mahaifinta bai kara wai-waiyansu ba, haka ma yan uwansa.
A lokacin cin da kakarta watau mahaifiyar mamee ta dauke ta zuwa kasar ladon, sai ta baro ta a can din domin halin ko in kula da mamee take nuna masu. Nan ta cigaba da karatun ta har sai da kakarta ta koma ga Allah sa'anan mamee ta dawo da ita gunta, sabida tsana da dan uwanta ke nuna mata  yana fadin itace sanadin mutuwar mahaifiyarsu.

Bayan da mamee ta farfado, ta dau na annabawa.sai tayi kokari ta yakinci zuciyarta ta dawo normal.
Makaranta masu kyau ta sanya ya'yanta.
Turkish international college ilham take zuwa,a yayinda sauran kannenta ta sanya su a *Imperial schools*.
Ita kuma mameen ta soma aikin lecturing a university dake cikin garin kaduna watau K.A.S.U.
Ilham da sauran kannenta sun samu kulawa da tarbiya fiye da zaton me karatu, mamee bata yi sakaci ko wai don aikinta ta dannewa yaranta hakkinsu.
Takan wa're lokaci tace masu "today is for u guys"....tana yi masu tambayoyi ko kuma a je yawon shakatawa,hakan yasa masu kusanci da shakuwa mussamma dan Autan ta wanda ta sangarta domin tausaya masa takai.
Da shike ilham tana da wayau a lokacin da iyayenta suka rabu,kuma ta wayi mahaifinta sabida tsananin so da shakuwa da ke tsakaninsu, don haka da ta kwana biyu ba ta ganshi ba,sai tana tambayar mamee  'ina baba na'?
"tun mamee na fadin babanki baya nan har ta kai ga cewa babanki ya mutu"
Bayan da ta girma ta fara mallakan hankalinta sai tacewa mamee "toh ta kai ta gun yan uwan babanta mana"
Zaunar da ita mamee tayi tareda da yi mata kashedi..."daga yau, idan ba kina son nayi fushi dake ba , kada ki kara furtawa cewan nakai ki gun yan uwan mahaifinki......kina jina ko?
Kai ta daga...
Yauwwa...don haka kiyi shiru da bakin ki.
Ilham ta ji alaman rashin gaskiya tattare da maganar mamee don haka tayi alkawarin fidda kanta daga wannan duhun da mamee ta sanyata.

         **         ***         ****
Bayan ilham ta kammala karatun ta, ta sakandiri mamee ta ba ta daman da ta zabi ko wace kasa take sha'awa da kuma son zuwa domin cigabawa da karatun ta.
Ilham ta ce wa mamee ba ta da zabi, don haka duk inda mameen take ra'ayi ya kuma kwanta mata a rai nan za ta je.
     *UNIVERSITY OF LONDON*(kings college), shine makarantar da mamee ta zaba da ilham ta je.

Cosmetic dermatology shine   course din da ilham ta ke ra'ayi, don daman tun tana yar karamarta take sha'awar  duk wani abu game da fatan jikin dan adam....a lokacin da    take sakandiri,ba ta aiki sai bincike da neman sanin duk wani abu da ya shafi fatan dan adam,kamar lafiyar fata,ciworwukan fata, da kuma yanda za'a magance da  dai sauransu..a bisa ga wannan dalilin yasan ta zabi fanin fata, don taimakawa matan nigeriA wanda yau burin su bai wuci su gan cewan fatan su na walkiyaa kyalli ba.

Daloli masu yawan gaske mahaifin mamee ya baiwa ilham ba tare da mamee ta sani ba.
  Ya kuma gargade ta da kar ta sa ke ta nunawa mamee kudin.
Yan'uwa da abokan arziki duk sun kawo na kudin sallaman ilham.
Ganin irin kudi da abin arziki da ilham ta samu ya sanya mamee ta sallame ta ba tare da ta bata wani abu ba.
"wadannan kudaden da kika samu,sun isheki har zuwa wani shekaran ma"..fadin mamee.
Dariya ilham tayi....a ranta kuwa fadin take ,kadan kika gani ai.
A tare suka tafi da mameen, sai da ta gan cewan ta kammala komai game da registration din makarantat, sa'anan ta yo gida.

Tunda ilham ta saka kafarta a kings college, dalibai har malamai ke kaunarta.
Ilham ta kasance tauraruwa a sararin samaniya..
Dalibai da malamai da dama sun sha tsai da ta a hanya, suna neman sanin ko ita kanwar  *AMEER* ce?
Tun tana maida masu a'a, har ya kai ga idan suka tambaye ta a maimakon ta amsa ,sai ta tambayesu wai yaya wannan AMEER din yake ne?

Wataran ta fito daga dakin karatu, watau labrary, rike da takardun ta,bata ankara ba sukayi karo wani.
Ta duka ta dauki takardun ta da suka zube,ta da'go da niyar bashi hakuri sai tagan irin kallon renin hankali da yake yi mata.
Siririya tsuki tayi tare da ratsa ta gefen sa.
Har tayi nisa da tafiyat,sai gashi ya biyo ta da dan gudu gudunsa,a gabanta yayi tsaye...
"watau sabida kingan yayank i yana yiwa mutanen renin wayau son ransa ba tare da an taka masa birki ba,shi ya baki daman ke ma kiyi ko?...sabida rashin tarbiya,kin bangaji mutun kuma kinyi tafiyarki ba tareda kin iya furta sorry ba?...toh wallahi ki bincika kiji ko shi yayan naki bai isa yayi da ni ba ballantana ke..

Kallonsa take,.....murya kasa kasa tace "Amman dai lafiyarka kalau?,...daga kun gan kamani sai kuyi concluding cewan wannan dan'uwa nane,har kake cin zarafi akansa??.....
Shiru yayi yana dubanta .
Ta cigaba da fadin da alama, akwai kiyayya a tsakaninku, don haka kai tsaidashi can atsakaninku......excuse me ta fada tayi wucewarta.

Daga wannan lokacin,duk sa'anda zata shiga labrary, toh zata tarar da wannan bawan Allahn.
A hankali ya soma yi mata magana tana basarwa, har ta  kai ga amsa masa.
Ganin kulawa da shakuwa na neman shiga tsaninsu,sai ta nema da san ko shi wanene, sabida yanayinsa da komai nasa da takama yake yinsa.

Hidayat yar'year 2,wace suke daki daya da ilham tana karanta dermatologysurgeon ne,ganin course daya suke karantawa da *NURA* kuma mataki daya suke, ya baiwa ilham daman bin ta kanta domin sanin wanene Nura.

Zaune suke kowanensu na ninke kaya.
"yauwwa sis, don Allah ko kinsan wani da ake kira nura a department din ku?"
Nura Abubakar kike nufi?....

Eh toh, ban san surname dinsa ba gaskiya.
Tabbas shi din kike nufi.
Watakila......

Kwarai kuwa nasan Nura...ai nura sananne ne,ba dalibi ko malamin da bai san da zamansa a wannan makarantan ba.

Matsowa kusa da ita ilham tayi..."yauwa fadamin duk wani abu da kika sani game dashi"

Shi dai Nura yan asalin kasar najeriya ne,amman anan aka haife su,anan suka tashi har girman su.
Mahaifinsa yana daya daga cikin board management na wannan makarantan.
Su biyu iyayensu suka haifa, da shi da kanwarsa.a bisa ga wannan dalilin yasanya sun sangarta su,,ba wani tarbiyan kirki sai ta rashin mutunci.
  Nura baya ganin girman kowa, ganin yake kowa na karkashinsa, ga shegen daukan kai da miskilanci.
   A takaice dai, Nura miskiline,ga rashin Son karatu.
Kamata yayi ace yana can tare da yan uwan da suka tafi traininng a  kasar jamani,amman sabida bai sa   kai ba aka maida shi baya.

Kamar yaya ,an maidashi baya sai kace sekandiri skul?........ilham ce ke wannan tambayar.

Derma-surgeon cours ne da sai an shekara hudu ana karatunsa...ka'idan wannan cous din shine dalibai zasuyi shekaran farko da ta biyu a makaranta,shekaransu ta ukun sai a tura su wata asibitin sauya fata dake kasar germany don yin training.
Toh kafin a turasu, sai an bincika sakamakon jarabawan daliban tun daga shekararsu ta farko.
Wadan da basu cancanci zuwa ba,sai a maida su baya su sake maimata wannan shekaran,toh abinda ya riski nura kenan.ganin yake sabida matsayin mahaifinsa ba yanda za'ayi dashi a wannan makarantan.
Bashi da lokacin yin karatu sai adawa da Amirullah na wannan makarantan,kamar annabi da kafiri suke.
Yanzun mun dawo sa'o'in juna,a yayinda abokan tafiyarsa duk suna can a yayinda shi kuma yana nan damu sai wata shekara.

Cikin tausayawa ilham tace "Ayyah......har na tausaya masa..
Uhmmmmmm....don dai bakisan halinsa bane.
Read More »

Wednesday 6 June 2018

(47) SOYAYYAR MU

*SOYAYYAR MU👫*
        By Ganarious.
Page4⃣7⃣


*ALLAHUMMA INNAKA AFUWWUN TUHIBBUL AFUWAN*....Ameen🙏🏼

*RABBIGFIRLEE ZANBI*..Ameen🙏🏼

<><>mutan  united states of American,  u guys amazed me...thanks for patronizing my blog 🤝🏼.I so much appriciates it.

<><>mutan Kenya,one love keep us together 💖

<><> NAZEE YAREEMA😄

<><>kada ki/ka bari a baka labarin *UMMULKHAIR*...Written by Aisha zahradeen.    
ki/ka na iya samun labari a face book groups kamar 👉🏼ganarious book series,
👉🏼khalisa haydar hausa novels.... da dai sauran.



          *TUNA BAYA*
Aishah mustapha Buba, wace muka fi sani da ilham...............

Ooopps🤦🏻‍♀,ku daka ce ni.
Inn'shaa'Allah,bayan sallah zamu ci gaba da'ga inda muka tsaya.✌🏼
Ko kuna hangen abinda nake hangowa kuwa 🤷🏻‍♀
Shin  mamee zata koma wa fillon ta,ma'ana za amince su maida auren su🤔

Auren ilham da Hisham zai yiyu?

Ya  zance hajiya zubaida da ke tsare gidan kurkutu?
me kuke tunanin zai faru idan iyayenta sun nasaran fito da ita?..

Nidai ina son jin haduwan Hisham da ilham,da yanda suka tafiyar da soyayyar su.

Duk ku biyoni a pagi na gaba inn'shaa'Allahu.sai nake ganin kamar yanzun ma aka soma labarin.

     Inayi mana fatan alkhairi,ina yi mana addu'an gani karshen wannan watan me tattare da albarku,cikin koshin lafiya..Allah ubagiji shi karbi ubadun mu ya kuma amsa mana kira,ya kuma biya mana bukatun mun.
Ameen ya rabbil alameen.
In advance happy sallah😄😍

Ganarious dinku ce..✌🏼
Read More »

Page 46 of SOYAYYAR MU

*SOYAYYAR MU👫*
          By Ganarious.
Page4⃣6⃣

√°•<> inayi mana fatan alkhairi,ya yan'uwa.

√°•<>inayi mana nasiha da mu yawaita yi *SADAKAH* da taimako.

√°•<> kuna iya tura shawarwarinku....
👉🏼ganarious98@gmail.com

Ko ganarious.blogspot.com/

A facebook, Aisha m gana.
      Thanks🤝🏼

    Bai mu'sa ba, ya shiga ciki.
Ya taras da mamme tana jera abinci a kan dinning table.
"Mamee babanmu ya iso,na ce masa ya shigo,shi kuma yace na sanar da ke tukun.
...."je ka, ka shigo da shi,ni zan shiga wanka ne.

  Bayan da mamee ta fito wankan,ta feshe jikinta turarukan jiki masu classic kamshi,ga kuma arabian humra da ta fara shafe jikin da shi.
Abaya ta fiddo, wanda Aunty Hauwa liman me @Afrikabaya ta aiko mata.
Tabi le'benta da tender kia,ta oriflame sa'anan ta laulaye kanta da mayafin abayan .
Duban kanta tayi a madubi tare da rayawa a zuci....."da fatan ba nayi bane don na burge wannan mutum..."
Tsuki tayi a yayinda ta nufi kofa don fitowa.
A falo mujaheed ne da Abba tare da mahaifinsu.
Da sallamanta ta shigo cikinsu tare da samun kujera ta  zauna.
A hankali ya da'go yana dubata...."inakwana ya fada.
Lafiya....kawai ta maida masa.ba tare da ta dubeshi ba.
Na zo ne muyi sallama da mujaheed ,na kuma tqbbatar komai yayi dai dai, duk da bani da damar yin haka.
Shiru tayi bata amsa shi ba.
ya ciro envelop ya mikawa mujaheed...."ga wannan, 20thousand ne a ciki, ka yi hakuri ba yawa..
Haba baba, da ma ka bar su...
A'a...akwai hakkinku a kaina, kaddara ce ta sa a lokacin baya baku sami abinda ya kamata ba,don haka ba zaka gane komai ba yanzu.
Toh baba na gode,Allah ya saka da alkhairi,ya kuma sanya albarka..
Cikin jin dadin furucinsa alhaji buba yace ameen.
...je ka ka kwaso min jakkuna da zakayi tafiya da su.
Toh baba...
Jakkuna biyu ya kawo gaba alhaji buba..."ga su baba.
Dubansa alhaji buba yayi..."iya kan su kenan,?
Eh....
Ka gama shirya kayan, ba abinda zaka ciro ko ka sa?
eh...baba,everything is set.
Hannun ya sa a aljuhu,ya fiddo padlock,ma su dan girma ya rufe jakkunan....sannan ya mikawa mujaheed makullan.
Cikin darawa....yace baba kwado kuma?
Kallonsa yayi ba tare da yace wani abu ba

....jirgi ne ai,ba abinda zai faru...
Ya dafa shi,Kar ka damu,haka dai nake son ka tafi makarantan.
Toh inn'shaa'Allah.
Bayan nan ya shiga yi masa nasiha,daga baya yayi masa addu'a.

Ya mike zai tafi abba ya rike masa hannu yana fadin baba ba za ka raka shi abujan ba?
Kai ya girgiza,tare da duban inda mamee take, wace tunda ta zauna a gurin ko uffan batayi ba.
....'ni zan tafi", ya fada
toh an gode ta maida masa ba tareda ta dubeshi ba.

Baba toh ka dakata mana mu ci abinci tare?...murmushi yayi "a'a.....a koshe nake.
Ido waje yace...baba ba kaci komai na sani.

Mikewa mamee tayi tana fadin ku zo kuci abinci mu kama hanya ko?!...

Gam-gam abba ya rike alhaji buba wai ala dole sai ya zo sun ci abinci tare,ba yanda alhaji babu bai yi masa ba da ya tafi shi ya ci abincin amman yaki,da'ga baya ma cewa yayi idan har be zo ya ci abincin ba shima din ba zai ci ba,ya fada hakan ne a shagwabe.
Mamee da mujaheed kam sun dade da isa gun dinning har ta fara zubawa mujaheed abincin sa.
Ganin da gaske abba yake yi yasa alhaji buba amincewa...."ok, toh muje '
kujerar da ke fuskantar ta mamee ya jawo masa,sanna shima ya zauna kusa dashi.
Mamee ta mike ta zuba masu abinci.
Sosai alhaji buba ya ci abincin,yana ci, yana satan kallonta.
Bai ankara ba,sai ganin yayi plate din sa ba komai,ashe ita gimbiyar tana lura da hakan.
Ta mike ta sake zuba masa wani abincin.
"Na gode ya fada,yana kallon fuskarta.

Bayan da sun kammala cin abincin mamee ta yi kira blessing da ta zo ta tsabtace gurin.
Mamee ta dauko jakarta tana me yiwa blessing sallama da fadin zamu kai mujaheed airpot.

Bayan da an fita da kayan mujaheed aka shirya su a mota mamee ta dube su tareda fadin mu ta fi ko?..
Gaba daya suka mike har alhaji buban....suka fito haraban gidan.
Mamee ta kai duban ta ga alhaji buba..."idan kana ra'ayin ganin wucewarsa,kana iya biyo mu"
Toh na gode,ya fada.

Mujaheed ne a gaba,tare da direba.
A yayinda mamee da alhaji buba ke gidan baya,abba ne a tsakaninsu.
tunda suka soma tafiya ba wanda yace wa wani kala,tsakanin mamee da alhaji buba.
Sai abba da yake yiwa mahaifinsa tambayoyi akai-akai....shi kuma mujaheed sai dai ya jiyo ya yi masu hoto.

ZAUne suke a gurin da aka tanada domin zaman jiran jirgi.
Kiran ilham ne ya shigo wayar mujaheed.
Dariya yayi yana fadin anty kenan.....na san zaki kira da zarar kin gan hotunan,...
Wasu hotuna ta gani..? Abba ya nemi sani.
Hotunan da nayi maku a mota, shi na tura mata ta whatsapp.

.....hello anty.!
Kuna tare ne dukan ku?
Eh....ya maida mata.
Ok,zan kira video call yanxu.

KAshe wayan tayi ta sake kira, wannan karon video call ne.
Bayan da mujaheed yayi pickin ta umurce shi da ya baiwa mahaifinta wayan.
Nan suka gaisa, daga nan ya baiwa abba,abba kuma ya baiwa mamee.
01:07pm jirgin ya tashi...don haka sukai harraman tafiya.
Wanna karo a gaban mota abba ya ka'me,mamee da alhaji buba ne  agidan baya.
Ganin lokacin sallah yayi,ya sa mamee ta umurci direba da ya nufi gidan aminiyarta watau hajiya safiya da su....bayan nan ta kira hajiya safiya ta sanar da ita zuwan su.

Mamee da abba ne suka shiga cikin gidan, a yayinda alhaji buba da direba ke cikin mota.
Hajiya safiya na da'ga saman bene ta hange su,don haka ta sakko da gudun,ganin ta a guje ya sanya yaranta biyo ta su ma a guje....ta isa ta rungume mamee...
"Barka barka....marhaba da zuwa
Yawwa kawa ta.... ya ya lafiyar yarana?
Ga sunan..!

Dariya mamee tayi tare da juya wa gun yaran.....yawwa ya'yana masu albarka,kuna lafiya?...
Hajiya safiya ta sa hannu ta rike mamee zuwa falon ta.
Sai da suka natsu sannan mamee ta dube hajiya safiya..."tare da ba'ko muke fa"
Tau....wanene wannan ba'kon kuma?
Uhmmm....dan fillo ne.
Cikin da'fe kirji tace "dan wa....??
Dan fillo,mamee ta maimaita.
Dan fillo fa kikace fa?
Kai mame ta da'ga mata.
Ina kika hadu da shi?
Dafa ta mamee tayi....'akwai labari,amman ki bari inn'shaa'Allah, asabar zani shigo na labarta maki domin kuwa muna kan hanya ne yanzun.
Cikin mamaki hajiya safiya ta mike..'bara na aika masa ya shigo,kar yayi tunanin an wulakantashi.
Dan me suna mus'ab ta kira.
ta umurce shi da ya tafi wajen gida ya shigo da wasu baki maza.
bai jima ba ya shigo...'wai sun tafi masallaci inji me gadi.
Je ka kayi jiransu,idan sun dawo sai ka shigo dasu.
nan mamee ta mike don gabatar da sallan azahar.tare da umurtan abba yaje yayi sallah shi ma.
Bayan ta idar hajiya safiya ta sanar da ita cewan abinci na kan dinning da ta tashi ta je fara ci.
sun fito zasu nufi dinning sukayi karo da mus'ab.....
...mummy na fada masa,shi kuma wai ba zai shigo ba.
Shikenan, shiga daki ka dauko min mayafina.
Mamee da abba kam sunyi nisa da fara cin abinci, sa'anan alhaji buba ya shigo.
Hajiya safiya tayi masa nuni da gun dinning tana fadin "bisimillah"
A'a....alhamdulillah, ya fada tareda yi mata godiya.
Haba don Allah....wallahi sabida ku na girka abincin.

Allah sarki,toh ayimin afuwa.! A koshe nake.
Ba yanda hajiya safiya batayi da shi ba, da yaci abinci shi ko ya ki.
Ganin ba shi da niya ya sanya ta zuba masa juice .

Ta dibi abinci a plate ta baiwa mus'ab ya kaiwa direban su mamee.
Bayan mamee ta gama cin abincin tayi kiran hajiya safiya gefa....'akwai fruits a gidan nan"
Eh....akwai
Ok, bara na hada masa fruits salad,nasan zai sha a mota,don tun karin safe ke cikin sa.
Har zuwa gun mota hajiya safiya tareda ya'yanta sukayiwa su mamee rakiya.

Dubu daya alhaji buba ya fito da shi,ya mikawa yara...'gashi ku sayi alawa ko'
Godiya suka yi.

Sai da sukayi ni'a...mamee ta cire tubular bowl me kyan gaske..
ta mikawa alhaji buba..."gashi kasha,please kar ka mu'sa, na san kana tattare da yunwa.
Kallonta yakeyi, ba tareda ya karba ba, be kuma ce wani abu ba.
Ta sake duban sa..."gashi ko?
Ajiyan zuciya yayi,sanan ya sa hannu ya karba.
Na gode kawai ya fada...tareda yin bismillahi, sannan ya soma sha.
Ya gama sha ya maida murfin kwanon ya rufe...."Alhamdulillah" ya fada.
Ya juya ya dubi mamee ....na gode ya sake fadi.
Bata amsa masa ba,ba ta kuma dubeshi ba,sai dannan wayarta takeyi.
Shi kuwa ya tsai da idon sa akanta, ganin ba'ta niyar yi masa ya sanya shi dukowa..."ni fa,ni fa......so nake na maida aurenmu, ko ma nace na maida shi.
Nan ba bata da'go ba.
......'fillonki ne fa ke magana'..
Shiru bata amsa ba.don haka ya fita harkan ta.
Suna shiga cikin garin kaduna, Alhaji buba yacewa direba zai sauka.
Guri ya samu yayi parking mota...
Alhaji buba ya dubi mamee...'na gode sosai... a nan ma bata amsa masa ba, don haka ya budekofan ya fito zuwa inda abba yake zaune.
Dubu daya yamika masa....'gashi, idan ka isa gida lafiya kayi changy ka dau dari biyar kabaiwa direba dari biya...nayi niyar ba ka abinda ya fi hakan sai dai bani da halin sa,don haka kayi hakuri da wannan wataran zan baka wanda ya fi wannan din.
Toh baba....na gode,ya fada cikin fara'a da jin dadin kyautan da mahaifinsa yayi masa.
Alhaji buba ya kai hannu ya shafa kansa..allah shi yi makaalbarka.
"Ameen.

Tunda mamee ta isa gida ta rasa sukuni, furucin fillo sai yawo yakai a kwakwalwanta da kunnenta.....
Kai da komowa takai....wayarta da ta soma kara ce ta ja hankalin ta zuwa kan gado inda ta ajiye shi.
A hankali tayi taku zuwa gurin.
..."kawa"
"Kun isa lafiya?
Lafiya lau alhamdulillah,.....ke ce nake son kira yanxun fa, sai gashi kin riga ni.
Ai dole na riga ki...tunda ku ka bar gida na nake girgan lokaci,don bani son na kira kuna tare da fillo.na kasa hakurin sai kin zo ki bani labari,don haka nayiwa wayata lodi,yanzun ke nake sauraro...
Dariya mamee tayi.....haba kawa, ki bari mana ina kallonki,kina kallona? Ai ya fi dadin labari.
"Na ki, wallahi ban yarda ba, ko so kike na kasa barci?
Toh toh....mamee ta fada, tare da soma bata labarin komai da ya faru da'ga kan soyayyan Hisham da ilham har izuwa yanzun.
..'ikon Allah.".....Allah da ikon yake,sai ya hade su acan bayan sun rabu watau Hisham da ilham kenan.
Ita kuma hajiya zubaida, bata daddara ba....ba ta tunanin mutuwar ta?
Mmmmm....kawai mamee ta fada,.
Gaskiya ku tashi tsaye da addu'a, domin kuwa da zarar tayi nasarar fitowa toh Allah kadai yasan abinda zata aika kuma..
Haka ne, shima din tsoransa kenan...
Nan suka shiga tattaunawa har sai da kudin hajiya safiya ya kare tas.!.

*Ya'Allah kaji kaina,ka kar6i tubana,domin kai ne me kar6an tuba,kuma me jin kai..AMEEN🙏🏼*

*ya'Allah ka yafe min zunubai na...AMEEN🙏🏼*

*ya'Allah ka gafarta min abinda na gabatar da abinda na jinkirta, day abinda nayi a boye, da abinda nayi a bayyane, da abinda kaine ka fini saninsa, domin kai ne me gabatarwa,kuma mai jinkirtawa, babu abin bautawa da gaskiya sai kai...AMEEN🙏🏼*

*ya'ALLAH ina neman tsarinka da'ga tsoro da rowa da mummunar rayuwa da fitinar kirji da azabar kabari..AMEEN🙏🏼*

*ya'Allah kajikansa, kayi masa rahama, kayi masa afuwa,kuma ka girmama masaukinsa,kuma ka yawalta mashigarsa kuma ka wanke shi da ruwan sanyi da ra'6akuma ka tsrkake farin tufafinsa daga dauda kuma ka canja masa gidan da yafi gidansa da iyalin sa suka  fi iyalansa, da matar da tafi matarsa, kuma ka shigar dashi aljanna kuma ka kiyaye shi daga fitinar kabari da azabar wuta...AMEEN🙏🏼*
*Allahumma ameen ya'rabbil alameen*🙏🏼
Read More »
Designed by Jide Ogunsanya.